Saturday 12 November 2016

ADALILIN GATA 6-10

[9:31AM, 11/9/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                 *(6)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Kamar kullum yau ma ta gama kimtsa komai na kula da gidan suka shirya suka fito sai mazaunin su na bara, wanda kullum suka fito wani irin mugun nauyi take ji a ranta.

Saboda a tunanin ta kamar ta ya ci ace ta wuce zama y'ar jagora, sai dai ba yanda za tayi sanadiyyar in har bata kula da mahaifinta ba wa ye ta ajiye da zai kula dashi yanda yadace.

Ga shi dai in har ta ce baza su fito yawon bara ba to batasan wa zai ciyar dasu da sauran lalurorin su ba, tunda mahaifinta ba yada idon da zai fita yane mo musu abinda za suyi lalura.

Don ma Malam Inuwa na k'ok'arin basu abincin dare, duk da shi kan shi ba wata wadata ce dashi ba saboda ba kullum za'a ci abinci sau uku a rana gidan shi ba.

Duk ita kad'ai ke wannan tunanin a ranta, wanda har kullum take tunanin ina za ta ne mo masu mafita akan wad'annan matsalolin.

Sanadiyyar bugawar da motocin biyu suka yi ya janyo hankalin tsirarrun mutanen da ke zaune gefen hanya.

Dattijuwar na fitowa daga motor ta ya tayarda hannu zai sharara mata mari.

Hannun da ya ji ya rik'e na shi hannu ne ya bi da kallo.

"Ka daraja mutum ko da baka san shi ba, wanda ya girme ka haka yake tamkar yaya a gurin ka, haka zalika wanda ya yi sa'ar mahaifin ka tamkar mahaifin kane".

"Bai kama ce kaba kuma hakan bai dace dakai ba, yanda ka daraja manyan ka haka Allah zai sa a daraja na ka iyayen ko bayan idon ka".

Cikin sanyin jiki ya bi dattijuwar matar da kallo, sai wata irin kunya ce ke ratsa ga66an jikin shi, hak'uri yafara bawa matar had'e da neman yafiyar abinda ya tashi aikatawa.

Su duka biyun suka bi gurin da kallo domin ganin ta ina za su ga yarinyar amma ina ta 6acewa ganin su.

*********

Sandar mahaifinta ta rika suka doshi hanyar gida. "Zajla ki daina saka kan ki a cikin rayuwar wa'annan mutanen, ba mutunci ne dasu ba".

"Baba ai Ba  komai na yi ba nasiha ce kawai na yimai saboda abinda naga ya kusa aikatawa bai dace ba".

"To Allah yamaki albarka yaba ki miji nagari inga auren ki da jikoki na".

"Baba ni fa na gaya ma bazan yi aure ba, saboda bansan wa zai kula dakai ba", tana maganar ne had'e da zum6uro baki tamkar yana ganin ta.

"Haba Zajla kidaina fad'ar hakan, Allah zai kula dani saboda shi ya so gani na hakan kuma zai ya yemin lokacin da ya so. Tunda abin ciwo ne bana halitta ba kuma daga baya ya same ni".

"Baba kayi ta addu'a Allah yaba ni hanyar samun kud'i insa a gyara ma idon ka".

****

Fitowa tayi da sunan kai ziyara company maigidan ta, amma sanadiyyar abinda yafaru ne ya sa duk ta ji ba za ta iya k'arasawa ba akalar motar ta taja takoma gida.

Da shigar ta falon Saudat tagani zaune tana waya, ganin shigowar Mum ne ya sa ta yi saurin tsinke wayar had'e da mik'ewa tsaye.

"Mum ba dai har kinje company kin dawo ba?".

"Ban k'arasa ba na dawo". Ta ba ta amsa a tak'aice, ganin 6acin rai kwance saman fuskar Mum ya sa bata k'ara magana ba.

"Me ya hana ki zuwa skul yau?".

"Mum fa har na shirya Hafsat takira ni ce wa lecturer d'in bai zo ba shiyasa nayi zama na saboda dama yau shi kad'ai muke da".

Bayan ta bawa y'an aiki umurnin abinda za'a dafa abincin rana, bedroom d'in ta ta wuce duk ranta jagule.

*02:30*
Talatu mai aiki ce ta gayawa Saudat ta fad'awa Mum an kammala komai.

Bedroom d'in ta wuce ta gaya mata sak'on k'are girkin, nan Mum ta bata umurnin kiran Brother su had'u falon Baban su.

Bayan sun kammalu anyi lunch an k'are ne ta kai duban ta ga Al'amein.

"Za ka iya tuna ranar da kashigowa Dad d'inku cikin 6acin rai har kana gaya mai ka mari wani dattijo?".

"Mum me ya kawo wannan maganar?, ai ina ga ta wuce, ko kuma wani fad'an za'a maimaita min?". Yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi.

"Kaba ni amsa kawai". Ta furta a tak'aice.

"ina ga za'a yi sati biyu ko kwana goma".

"Wannan dai-dai yake da maimaita abinda ka aikata akan fuskar mahaifiyar ka", tana kaiwa k'arshe ta fad'a bedroom d'in Dad.

Cikin razana su duka uku suke kallon junan su kowanne 6acin rai kwance a fuskar shi musamman Al'amein da har jiyojin kanshi sun fara bayyana.

(4 breakfast, luv y'all My fan's)

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[4:08PM, 11/9/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                   *(7)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

"To wai Dad wa ye ya isa har ya d'aga hannu ya kai wa Mum mari kuma ya zauna lafiya a garin nan?".

"Son ni ma wannan shi ne abinda nake tambaya, amma nasan ba wanda zai bamu wannan amsar sai ita kanta, kuma nasan mu shekara muna tambaya ba za ta gaya mana ba".

"Dad mushiga daga ciki muji ko za ta gaya mana d'an gidan uban waye shi". Ce war Saudat.

Hakan suka d'unguma sai bedroom d'in Dad domin sa mun amsar  tambayoyin su.

"Mum Alamein ta shi kigaya min wane isasshe ne zai d'aga hannu duk garin nan yadakar min Mata?".

Wani guntun murmushi ne ta saki a fuskar ta had'e da girgiza kai alamar ina tausayin tsarin ku.

"Wannan shi zai tabbatar muku ce wa duk abinda kayi na alkhairi ko na sharri za ka had'u da makaman cin shi ko mai dad'ewa".

"Kuma kai da kake ta da jiyojin wuya me za kayi akai ko da na gayama wa ya mare ni? Ko ka manta shi wanda ka mara yana da y'ay'a kuma sun san darajar shi".

"Me kake tunani a wancan lokacin in har ace ko da ka mare shi wani d'an shi na gurin? Ko kana tunanin dukiyar ka za tasa in har suna gurin su k'yale ka?".

"Mum ni fa mutumen laifi ya yimin, har ta ya ya zai zo yana tafiyar ganin dama a saman titi".

"Haka zalika nima laifi nayi yaron ya mare ni".

Cikin damuwa Dad ya bi ta da kallon mamaki, ya rasa ga ne ita wace irin Mace ce da batasan y'ancin kanta ba.
 
Durk'usawa ya yi gabanta ya d'ora hannuwan shi saman k'afafun ta tamkar yayi kuka yake ji ya furta.

"Don Allah Mum ki gayamin ya akayi hakan ta faru? Kuma in kin san waye ki gayamin shi please and please Mum?".

Murmushi ta yi sosai har hak'oran ta suka bayyana, sannan ta kwashe ko mai ta gaya masu had'e da yaba halayyar yarinyar.

Sai lokacin suka saki fuskokin su har Al'amein na furta "wallahi ya kuru da ya aikata wannan d'anyen aikin da ya had'u dani".

"Inna san waye shi ko in ban sani ba? Ko kuma inna gaya maku waye shi za ku d'auki mataki?".

Da hakan dai ta k'ara janyo hankalin su had'e da k'ara lurar dasu kan muhimmancin girmama na gaba dasu, wanda Dad ke zaune yana sauraren su.

******

Duk abinda aka saka ma rana zai zo indai da rai da lafiya. Yau ne ake shirin gabatar da musabak'a ta gari wadda za'a gabatar a makarantar su Zajlah saboda kasancewar makarantar ta su ce babba kuma itace kan gaba a duk sauran makarantin nen garin su.

Daga kan y'an izifi biyu aka fara har zuwa kan izifi sittin wanda aka share sati d'aya ana gudanarwa tsakanin makarantu biyar dake garin.

Inda aka k'are kuma makarantar su Zajlah ta zamo gwarzuwa a musabak'ar wanda har da Zajlah da Salmat acikin gwarzayen, saboda Zajlah ta yi haddar izifi talatin inda Salmat ta yi izifi ashirin.

Bayan kwana ki bakwai ne aka gabatar da ta Jaha a garin Birnin kebbi, daga nan akayi ta k'asa gaba d'aya inda Zajlah ta zo ta d'aya a cikin y'an izifi talatin Salmat kuma ta biyu a cikin y'an izifi ashirin.

Sun sa mu kyaututtuka da dama wanda ya had'a da kud'i da keken d'unki Zajlah harda kujerar Makkah wanda sanadiyyar hakan har da guntun hawayen ta na farin ciki.

Ko Malaman su kaduba lokacin za kaga farin ciki kwance fal a fuskokin su musamman Ustaz Lukman dake kula da 6angaren masu haddar da kuma wani abu da yake ji kwance k'asan zuciyar shi akan Zajlah.

Mahaifin ta farin ciki fal a ran shi harda hawayen shi, ji yake yi ina ma ace yana gani da idon shi yaga wannan rana ta farin ciki da y'ar shi ta zamo gwarzuwar shekara.

Hakan suka tarkata suka dawo gida farin ciki fal ransu, sai mak'ota ke ta shigo masu murna da Allah sanya alkhairi.

Sun samu kud'i sosai musamman Zajlah da tazo ta d'aya, har gida Ustaz Lukman ya biyo su had'e da kyaututtukan da suka sa mu mota ta kawo masu har k'ofar gida.

"Za ku sa mu shigowa makaranta ranar assabar?", ce war Ustaz Lukman.

"Ustaz a bamu sati d'aya mana mud'an huta sannan mu shigo".

"Sati d'aya ya yi yawa gaskiya saboda bazan jure...... Sai kuma ya canja akalar maganar.

"Shikenan Zajlah ku shigo zuwa ranar Larba, tunda kunga yau ta kama Assabar".

"To Ustaz mun gode sosai". Da hakan suka shige gidan su Salmat d'in.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[10:33AM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                  *(8)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Kamin su shiga gidan ne Salmat ta kai duban ta zuwa ga Zajlah had'e da furta.

"Yau kin yarda da abinda nake cewa Ustaz Lukman son ki yake yi?".

"Ke dai ina ga aure kike so shiyasa kullum maganar ki ba ta wuce ta So ba".

"Kina ji fa yau har da furta cewa bazai juri rashin ganin ki ba, sai ya juya maganar saboda kar mu gane inda ya dosa".

Dundu ta sakar mata had'e da janyo gashin kanta sai da ta yi k'ara, da hakan suka shiga gidan.

Mama Inno ce ta tarye su dukan su ta rungume sai albarka take saka masu har da guntun hawayen ta.

"Zajlah yau burin ki zai cika da yardar ubangiji saboda ya yi maki hanyar samun kud'in da za ki kula da matsalar idon mahaifin ki".

"Wallahi Mama ina jin tsabar kud'in da nasamu tun a can matsalar Baba ce nafara kawo wa, sai kuma samun abin Sana'a da zai raba mu da yawon bara".

"Don ko babu kud'in zan soke matsalar bara tunda na samu keken d'unki zan tashi da koyo har in iya".

"Gaskiya kam kinyi tunani mai zurfi, yanzu sai abubuwa sunyi sauk'i ku had'u ke da Salmat kuje koyon d'inki".

Da hakan aka shigo da kayan da suka samu gidan su Salmat, inda kowannen su ke da keken d'inkin sai Salmat dake da kud'i dubu d'ari biyu Zajlah ko na da dubu d'ari biyar da kujerar Makkah da shugaban k'asa ya baiwa duk wanda ya yi na d'aya a matakin haddar su tun daga izifi biyu har zuwa izifi sittin.

****

Tun lokacin da yarinyar ta hana ma saurayin marin ta take kwana kuma ta tashi da ita aranta, saboda yarinyar ta burge ta sosai, sai tunani take yi ina ma ace y'ar tace ke da halayyar wannan yarinyar.

Hakan take gurin Fadeel wanda duk yanda ya so yafige yarinyar a cikin zuciyar shi abin ya faskara.

Duk inda zuciyoyin mutum biyu suke da tunanin ta suke kwana kuma suke tashi, duk inda suke farautar ta domin su ganta abu ya faskara.

*******

Falon ta shigo ta d'auki remote domin canja tashar, abinda ta ga an nuno ya hana mata canjawa sai gata zaune jagwaf saman kujera.

"Saudat! Saudat!! Saudat!!!".

Gigice ta fito daga d'akin ta ta fad'o falon saboda kiran da Mum ke ta k'wala mata.

Plasma d'in ta bi da kallo saboda itace Mum ke nunawa da yatsan ta, ita dai bata ga komai ba bayan yarinya tana rero karatun Qur'an cikin baiwa kowane harafi hakk'in sa had'e da tajweed.

"Mum me ke faruwa halan? Ban fahimci me kike nuna min ba fa".

Nan Mum ta yi mata bayanin yarinyar. Hakan itama Saudat ta ji yarinyar ta burge ta sosai.

"Ina so kishirya zuwa anjima ki rakani makarantar su yarinyar nan, dama na yita neman ta duk inda nake sa ran ganin ta bangan taba".

"Yanzu Mum me za kije kiyi mata? Sai kita neman yarinya tamkar wacce ta k'ulla maki wani abin arzik'i".

Mugun kallon da Mum ta bita dashi ne ya sa taja bakinta ta tsuke.

*05:00pm*
Dai-dai wannan lokacin Mum ta faka motar ta k'ofar makarantar, da Ustaz Yusuf ta fara cin karo k'ofar makarantar.

Nan ta yimai bayanin abinda ke tafe da ita, mashin d'inshi yahau yayi mata jagora har k'ofar gidan su Salmat, godiya ta yita yimai har da fitarda kud'i taba shi saidai bai kar6a ba yajuya yakoma.

Mota ta hakimce tana wani yatsinar fuska saboda k'ofar gidan da taga sun tsaya wai nan Mum tazo kuma gurin k'aramar yarinya.

"Fito mushiga ciki mana".

"Shiga ki fito Mum zan jira ki a mota".

Fad'a ta dinga yi mata sannan ta fito har da wani handkerchief tana toshe hanci. Gidan suka shiga inda Mama Inno ta yi masu tarbar da ta dace duk da batasan su waye ba.

Bayan sun gaisa Mum ke yi mata bayanin gurin Zajlah tazo. Nan Mama ta kira su daga d'aki suka fito.

Durk'usawa sukayi har k'asa suka gayar da Mum, bayan ta amsa ne take ta yabon musabak'ar su data gani ana ta haskowa a cikin kowace tasha.

Nan ta d'ora da gaya mata itace ta hana wani saurayi ya mara. Har ga Allah ta manta da abinda ya faru sai yanzu data tuna mata.

"Laaah Haj wallahi ba komai, ai yiwa kaine don ni ma zanso a daraja nawa iyayen".

Da hakan Mum ta basu dubu goma-goma suna ta godiya, itako ta fice daga gidan.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[6:14PM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                 *(9)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Da sannu Fadeel ya binciko gidan su Zajlah wanda karo uku kenan yana zuwa k'ofar gidan su amma sai jikin shi yayi sanyi yaka sa tunkarar ta yakoma.

Yau dai da k'arfin gwiywar shi ya tashi na tunkarar ta yaga ya mata gaskiyar lamari ce wa yana son ta.

K'ofar gidan ya zo, amma a tunanin shi na zai iya tunkarar ta yau sai gashi abin ya gagara, ta gaban shi suka zo suka wuce ita da Salmat domin zuwa koyon d'inkin su gidan wata mata dake k'arshen layin su.

"Ni fa Zajlah abin nan ya fara d'aure min kai, in har kin lura kusan kwana uku kenan duk muka wuce zanga wannan motar".

"Kuma fa abin mamaki ba a ganin na cikin motar su waye saboda duhun glass d'in motar".

"Ke kika damu da wannan motar, ni fa zan iya ce maki ban ma ta6a lura da motar ba sai yau dakika yi maganar".

"Ai ke dama ba komai kike lura dashi ba, inaganin wataran sai halaka ta hau kan ki bakisan za ta zo ba".

"Au dama in abu zai same ka zaka san da zuwan shine?".

"Ba hakan nake nufi ba, amma dai ana so ka lura da yanda abubuwa ke tafiya saboda tsaro".

Dariya sosai Zajlah ta yi, da hakan suka isa gidan da suke koyon d'inki.

******

Yau ne aka aje kan za'a yiwa Baban Zajlah aiki a idon shi, Malam Inuwa, Zajlah da Salmat ne suka yi mai rakiya zuwa Birnin kebbi. Asibitin Sir Yahaya ce aka yi mai aiki kuma aka gama cikin nasara wanda sai da suka had'a shi da medical glass saboda rashin ganin abinda ke nesa dashi.

Je kaga murna fal a gurin Mal Abubakar inda yake alfahari da y'ar shi k'waya d'aya tak da Allah ya bashi, wacce ta zame mai y'a d'aya tamkar da dubu.

*****

*Wacece Zajlah?*

Mal Abubukar d'an asalin k'auyen giwa tazo ne shi da matar shi Basira, auren zumunci ne aka yi masu  domin mahaifiyar ta da mahaifin shi ne uwa d'aya uba d'aya.

Sun ta so tare da Mal inuwa ne tun shigowar shi garin Jega sanadiyyar Sana'ar kayan gwari wanda daga baya har ya samu matsakaicin gida ya saye a kusa dashi ya dawo nan da zama.

Allah ya had'a kan matan su wanda inka gansu zaka rantse da Allah y'an uwan juna ne. Basira ta rasu ne tun ranar da ta haifi Zajlah wanda bata ko saka yarinyar a idon ta ba.

Lokacin ita kuma Mama Inno ta haifi Salmat da sati biyu, nan ta kar6i Zajlah ta had'a da Salmat tana shayar dasu.
      (Asalin sunan Zajlatu ne k'awaye ne suka tak'aita shi da Zajlah, abinda sunan ke nufi rayuwa kyakkyawa kuma mai sunan tana daga cikin tabi'ai, me neman k'arin bayani akan asalin sunan da tarihin mai sunan zai iya searching da *KISASUT TABI'AT*, amma da larabci).

Sun shiga tashin hankali sosai musamman Mama Inno da Mal Abubakar, dole suka dangana saboda wanda yafi su son ta ya kar6i abarsa.

Zajlah na da shekara takwas a duniya  Baban ta ya makance sanadiyyar ya jima yana gani bishi-bishi sai bai d'aukin abin wata matsala ba har abin ya ta6a idon duka ya daina gani, tun yana iya lalurar kan shi har abin ya gagare shi.

Lokacin ne sauran tsirarrin dangin shi suka guje shi sanadiyyar ganin ya zama wata lalura a gare su, wanda shi ba hakan yazauna dasu ba don mutum ne mai taimakon dangin shi duk da shi ma ba wani hali ne dashi ba.

Sanadiyyar makarantar shi ne Zajlah ta dawo gurin shi da zama domin taimaka mai da wasu abubuwan da ba za'a rasa ba.

Zajlah yarinya ce mai kimanin shekara goma sha shida zuwa sha bakwai, chocolate colour ce ba wata kyakkyawa ce ta azo a gani ba sai dai manyan idon ta da gashin girar ta shike fitar da kyawon ta, yarinya ce mai shape  sai dai batada k'iba irin sosai d'in nan.

Kamin abubuwa suyi tsanani ansaka su makarantar boko iya primary daga nan basu cigaba ba sai makarantar Arabic dasuka mayar da hankali akan ta.

Saboda kowaccen su ta yi sauka uku sai kuma hadda da suke yi har Ustaz Lukman ya saka su acikin musabak'a, wanda sanadiyyar ne har duniya tasan da zaman su inda iyayen su ke alfahari dasu.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[9:08PM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                  *(10)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

www.sadijegal.blogspot.com

®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Mamaki fal a ran Saudat na miye silar zuwan Mum gidan su wannan kucakar yarinyar, ga shi tana so ta tambaye ta sai dai kuma bata ga fuskar tambayar ba.

Bayan sun dawo ne direct bedroom d'in Dad ta wuce, zaune yake k'asa saman carpet ya jingina jikin shi da kujera yana karatun jarida.

"Daddyn Alamein hutawa kawai ake yi"?.

"Ba dole ba tunda yanzu kin rage So na da tattali na, ina ga aure zan zo in yi ko zan samu mai bani kulawa", yana maganar ne d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar sa.

Murmushi Mum ta yi sosai had'e da tattara hankalin ta guri d'aya ta k'ara matsawa gab dashi.

"Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama, ka ga inka nemo mata sai a had'a da naka auren dana son ad'aura rana guda".

"Yaushe Son ya nemi mata banda labari? Yaron da ko mata bai cika kulawa ba ina yaga macen da yake so?".

"Sanin hakan ne ya sa na nemo mai mata da kaina, yarinya y'ar asali y'ar gidan mutunci mai ilmi".

Wata irin zabura ya yi ya kai duban shi zuwa gare ta.
    "Kina nufin Son ne za ki yiwa auren dole? Ko ni da nake uban shi ba'a yimin auren dole ba barrantana shi da yake cikin k'urciyar shi", yana maganar ne cikin fad'a-fad'a.

"Dad'i na dakai duk yanda ake magana cikin kwanciyar hankali indai aka ta6o yaran ka cikin second d'aya za ka birkice".

"Duk duniya ba ni da farin cikin da ya wuce na yara na, babu takura ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta".

Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna.

Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira.

"Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?".

"Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil".

"Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba".

Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin.

"Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai".
   "Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin.

Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai.

"Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana".

Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai.

"Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum".

Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya.

"Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?".

"Alamein".

Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina.

"Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku".

"Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe.

"Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure".

"Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani".

Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri.

Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi".

"Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

ADALILIN GATA 1-5

[8:24PM, 11/4/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

         *(1)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

*GODIYA*
Ina godiya ga Allah mai kowa da komai, mahaliccin sammai da k'assai, mai kashewa mai rayawa, mai badawa a duk lokacin da yaso, maji6incin bawan shi.

Godiya ta tabbata a gare shi daya bani ikon rubuta wannan littafin, kuskuren da ke ciki Allah ya yafemin.

*JIN JINA CE A GARE KU*
Anty Ybk
Benaxir Omar
Umma ta Lubiee Mai tafseer
Bebeelo
Hauwa Jabo
Ummu Abdul
Feenat Ja'afar
Mmn Shakur
Mum Faty
Zarah B~B
Mamu
Autar Haj.

*KUNA RAINA*
Anty Innah
Anty Fatima
Anty Rukayya
Sis Atiks
Sis Maryam Mela.

*BAN MANTA KUBA*
Jegal families
3stars
Hindatu Jegal
Nafeesa Jegal
Aisha Jegal

5stars
Assy Jegal
Sumee Jegal
Balkisu Jegal
Hauwa Jega
Asmee Jegal

*K'ANNE NA NA KAINA*
Yaha Saddik
Bizzy
Yagani
Ummy
Salma
Yasmeeny
Salmatun Innah
Habiba Yayaji
Maryam Idris katsina
Zainab Abdullahi
Naanah
Umamat
Mmn Sajjad
Khairat
Ummeen Alamein.

*K'AWAYEN ARZIKI*
Hindatu shehu
Shema'u Bello Bari
Shafaatu zakariyya
Y'ar gidan Ango
Khadija Manga
Fati Salihu
Balkisu Bilyamin
Jidda A.K.A
Mum Zee
Mmn Jamila
Mmn Hanan
Princess Meenat
Hauwa'u Ag
Mmn Haneef
Mrs Jawaheer
Deeja Abdul
Mrs Zannah
Maryama
Namcy Sadururah
Stylish
Fatima.
Ban manta da sauran ba ku saurare ni a last page.

*YARA MANYAN GOBE*
Halima
Maryam
Khadija
Abduljalal.
Allah yaraya min ku akan sunnah.
Sai yayyen ku
Lawiza & Zainab.

*GORO NE*
Ga dukkan masoya na way'anda na sani da way'anda bansani ba da sannu za ku shigo list d'ina luv y'all.

*SOYAYYAR KU TA DABAN CE*
Nagarta writers association luv y'all, Allah yakara had'a kawunan mu.

*GAISUWA*
Ga kowace Mumcy na.

*SADAUKARWAR TAKI CE*
Anty na, Mai bani shawara had'e da kulawa *Jidda Musa Mmn twin's*.

*TSAKANINA DAKE SAI ALLAH*
Sanah Isma'il Suleiman Matazu.

*LITTATAFAN MARUBUCIYAR*
*FATEEMA*
*BAHIJJA*
*SANADIN K'UNCI*
*ADALILIN GATA*

Cikin shirin shi na alfarma ya fito falon ya durk'usa har k'asa yana gaida mahaifiyar shi. Kafad'ar shi ta rik'o ta mik'ar dashi ya zauna gab da ita.

"Sai ina yanzu son?".

"Mum zanje company ne saboda muna da meeting da za muyi da wasu bak'i ne".

"Sai ka shiga ku gaisa da Dad d'in ka duk da ina tunanin kamar barci yake yi".

"In hakan ne bara kawai in wuce don nasan Dad sai mu wuce 15mnt muna gaisawa, ga shi sauri nake yi".

"Kenan kasan halin abinka nan 6angaren, amma d'ayan 6angaren duk yanda nake lurar da kai ba ka gane wa".

Da saurin shi ya mik'e cikin murmushi ya doshi hanyar fita "inna dawo ma yi maganar".

"Kullum hakan kake ce wa, fatana d'aya Allah yaganar daku baki d'aya".

Yana gab da fita ya ji muryar ta tana furta "Brother ni ma ba za'a tsaya mu gaisa ba kenan"?.

Cikin saurin ta ta k'araso gab dashi, hugging d'in shi ta yi "Mrng Brother".
"Mrng Little Sister, inna dawo za muyi magana".

Da sauri ya fice saboda agogon hannun shi daya duba ya ga saura minti biyar, a k'a idar shi bai son African time yayi ko ayi mai.

Sai da ya hau kan titin ya k'ara gudu sosai saboda saurin da yake yi.

K'eeeeeee kake ji sanadiyyar mugun birkin da yaja wanda saura k'iris ya kad'e mutumen.

Cikin isa da k'asaita da kuma 6acin rai kwance a saman fuskar shi ya fito daga motar.

Mari biyu k'warara ya yiwa dattijuwar fuskar mutumen wanda baki sake ya bishi da kallo.

Hannun shi na dama ya saka ya cire glass d'in shi no respect, yasa d'ayan hannun ya fitar da handkerchief a gaban rigar shi ya goge fuskar shi.

Cikin azama ya koma cikin motar ya tada ta, ganin ce wa zai iya bi saman kan shi yawuce yasa cikin sauri yaja jikin shi gefen titi da mamaki fal a ran shi.

"Ohhh! duniya ho yanzu wannan yaron zai fito ya faffallamin mari hankalin shi kwance kuma yana k'ok'arin takani ya wuce, duniya ce ta ishi kowa riga da wando".

****

Yau kam tana ganin sun makara ga yanda suke fitowa mazaunin su na masu bara gefen wata ma'aikata.
   Bayan sun iso gurin ne ta gayar da wa'anda ta tarar sannan suka ne mi guri suka zauna.

"Har ga Allah ba na son wannan zaman barar da muke yi, kawai abin ne ya riga yafi k'arfi na, don in mun daina bansan miye mafita a garemu ba".

Matar kusa da ita ne ta ta6o ta sanadiyyar wani da ya zo yana raba masu d'ari-d'ari wanda har ya zo kanta bata sani ba nan ta kar6a ta yi godiya.

*12:00pm* suka fara watsewa da kad'an-kad'an inda ita ma Zajla ta rik'a sandar mahaifin ta suka doshi hanyar gida. Asaman hanyar ne suka had'u da yaran da ke tallar zogale da 6ula had'e da k'uli mai magi da yaji.

"Baba ko mu siyi zogale da 6ula?".

"Nawa ne muka sa mu yau hala?". Kud'in ta fitar ta irga taga 350 ne, nan take gaya mai ko nawa ne.

"Siya mana 6ula na 100, zogale da k'uli na 50".

Hakan ta tsayar da yaran ta siya suka wuce gida. Da shigar su gidan ne ta yi masu kwad'o suka ci.

Bayan sun gama ne ta ebi ruwa ta je ta yi wanka ta yi shirin islamiya.

Wasu kod'add'un uniform kalar blue ta saka sannan ta yiwa Baban ta jagora ta fito dashi k'ofar gida cikin inwar icen mangoro gurin su Malam Inuwa.

"Y'ar Baba za'a je makarantar kenan?".

Ta bashi amsa ta re da durk'usa wa ta gaida su. "Sai ki biya ki kira Salmat in ta shirya ku wuce".

Gidan Malam inuwa ta dosa a k'ofar gida suka ci karo da Salmat, hakan suka sa kai sai makarantar su.

(Na so wannan littafin bazan yi posting ba sai 18/11/2016, amma hakan bai samu ba sanadiyyar maganganun wasu da suke furta cewa Jan rai ne. To kuyi hak'uri ba hakan bane daga yau za ku rik'a jina kullum insha Allah, nagode sosai luv y'all)

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[7:07AM, 11/5/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                *(2)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Suna shiga islamiyar suka tarar da mutane na alwala sanadiyyar kiraye-kirayen sallar azahar da ake yi ko ina, nan su ma suka yo alwala suka bi jam'i akayi sallah.

Bayan sun k'are ne suka wuce ajin su na d'aukar hadda, hakan suka biya da d'ai d'aya inda Ustaz Lukman ke sauraren su had'e da gyara ga duk wanda ya yi kuskure.

Da hakan suka k'are har la'asar ta yi suka fito akayi sallah.
    A k'a idar makarantar duk ranar larba za'a za 6i d'alibai uku cikin Maza uku cikin Mata domin gabatarda abubuwan da ake koya masu a cikin class.

Hakan ta kasance yau ga d'aliban da aka za6a sun fito sun gabatar da abubuwan gwanin sha'awa ga ma su saurare.

K'arfe shida na yamma aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa.

"Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan".

"Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi".

"Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa".

"Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa".

"Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta.

"Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai".

"Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar".

"Ameen", ta amsa a gajarce.

Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida.

****

Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa.

Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are.

Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?.

Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?".
   Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar.

Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit.

Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are.

"Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba".

Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau".

Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba.

Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta

"In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu".

"Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin".

"An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama".

Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi.

Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar.

"Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren.

"Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura.

"To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu".

"Ameen".

® *SDY JEGAL*

Www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[5:16PM, 11/6/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                  *(3)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

www.sadijegal.blogspot.com

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki.

Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta.

"Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi".

Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri.

"Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?".
    Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi.

Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa.

"Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a.

"To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad.

"Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba".

"Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi.

"Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin".

"Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar.

"Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba".

"Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin".

"Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne".

"Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu".

"Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku".

"Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane".
  "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu".

Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru.
D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad.

****

Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta.
   Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku.

Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan.
     Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale.

Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan.

Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci.

Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito.

Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu.

Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat.

Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa.

"Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su".

K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla ta fita ta ja Baban ta suka wuce gida.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[8:36PM, 11/7/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                  *(4)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Zaune suke saman dinning table suna breakfast sai tattaunawa suke yi akan lamarin company.

Sai da aka yiwa wayar shi Kira biyu ana ukun sannan ya d'aga wayar ya nufi hanyar d'akin shi, gaisawa suka fara yi sannan ya fara magana fad'a-fad'a had'e da ya mutse fuska.

"Kana sane da ce wa duk inda ake taro in har akwai Mata ba na nufar gurin, saboda haka kuci gaba kawai idan kun gama ma had'u, ka isar da sak'on taya murna ta zuwa ga Salis, in ya natsu zan kira shi".

Yana kai k'arshen maganar ya dak'ile wayar shi ya bita da wani kallo tamkar ta yimai wani laifi, gado ya fad'a domin ya d'an huta saboda ba mutum ne maison fita ba.

****

Kwanci ta shi asarar mai rai, yau ta ka ma Larba wanda Zajla sai gaban ta ke fad'uwa sanadiyyar tunanin da wuya Ustaz Lukman bai fitar da ita cikin masu karatun k'arshen sati ba.

Kamar kullum yau ma hakan ce ta kasance, bayan gabatar da sallahr azahar suka shiga class domin bitar haddar su saboda k'aratowar lokacin musabak'ar su.

Bayan an gama sallar la'asar ne aka fitar da mimbari da kujeru domin zama tsakiyar makarantar a gabatar da ire-iren abubuwan da ake koya masu.

Mutum uku cikin maza suka gabatar da yadda ake taimama da kuma sallar gawa, sai matan biyu da suka gabatar da koyar da alwala a aikace.

Zajla ce za ta gabatar da bayanin wankan tsalki da kuma addu'o'i.

Bayan ta yi basmala ta gabatar da sunan ta da Zajla Abubakar Zubair sannan ta fara da ce wa'.

"Shi dai wankan tsalki ya kasu zuwa kashi-kashi, akwai wankan janaba, akwai wankan haila, akwai wankan d'aukewar jinin bik'i (jego) da sauran su.

"Kamar yanda kuka sani su dai wad'annan abubuwan wanka iri d'aya ake yi masu sai dai niyyar su ce data ban-ban ta".

"Da farko za'a so mutum ya sa mu ruwan shi tsaftatacce, wa'anda kalar su bata canja ba, d'an-d'anon su bai canja".
  "Anan abinda ake nufi da kala ko d'an-d'ano shine kar mutum ya d'ebi ruwan Lipton ko ruwan wankin shinkafa ko ruwan da ke da gishiri yace wankan tsalki zai yi dasu".

"Da farko mutum zai fara wanke gaban shi, bayan ya wanke zai wanke hannun shi saboda najasar da ya ta6a, zai d'ebo ruwa har sau uku yazuba ma kansa, ya murza kansa har ruwan sukai k'asan kansa, daga nan zai yi alwala shud'i guda-guda sannan ya wanke 6angaren jikin shi na dama daga sama har zuwa k'asa, 6angaren hagu ma haka sannan ya game jikin sa da ruwa ya murza ko ina".

"An samu sa6anin wasu maluma da suka ce idan mutum ya wanke gaban shi zai fara gabatar da alwala, wasu kuma sukace sai bayan ya k'are wankan gaba d'aya sannan yayi alwalar. Allah masani".

"Addu'ar shiga kewaye
*(( Allahumma inni A'uzu bika minah khubithi wal khaba'ithi))*

"Addu'ar fitowa daga kewaye".
*((Gufranak))*

"Addu'ar mugun mafalki".
*((Allahumma inni A'udhu bika min sharri ma ra'aytu fii manaamee an yadurranee fii deeni wa dunyaay))*

"Addu'ar kariya daga azabar k'abari".
*((Allahumma innee As'alukar Jannah, wamaa k'arraba ilaiha min k'aulin wa amal, wa A'udhu bika minan naar wama k'arraba ilaiha min K'aulin wa amal, wa A'udhu bika min fitnatil mahya wal mamat wa min fitnatil k'abr wamin fitnatil masihid dajjal wamin Adhabin naari wasu'il maseer))*

"Addu'ar  neman ya fiyar sa6o.
*((Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika wa ana a'alam wa astagfiruka li maala a'alam))*

Gyaran muryar da akayi da speaker shi ya nu na mata alamar lokacin ta ya yi, speaker ta ajiye ta koma mazaunin ta.
     Kabbara ce ta biyo baya had'e da jin-jina mata akan abubuwan da ta gabatar.

Nan akayi salati ko wa ya ka ma gaban shi sanadiyyar gabatowar magriba, kowa da maganar (ZAZ) ya fita a bakin shi sanadiyyar add'o'in da ta yi tamkar itama Malama ce ba d'aliba ba.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[5:56PM, 11/8/2016] *SDY* *JEGAL*: ���� *ADALILIN GATA*����

                *(5)*

*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

"Gaskiya (ZAZ) kin kawo wuta sosai yau, kinji yanda kike rero addu'o'i tamkar Ustaz Yusuf?".

"Banson sharri wallahi, kina ji yanda murya ta ke wani rawa-rawa alamar tsorace nake. Ni fa shiyasa kika ga ko wannan musabak'ar da za muyi gabana ke ta fad'uwa saboda na k'i jinin karatu a cikin bainar jama'a".

"Tabbb ai wannan shafin mai ne wallahi, kina ganin yanda ake taro sosai idan lokacin musabak'a yayi. Kuma hakan da ake yi duk Larba anaso abin yabi jikin mune har mu saba mu daina jin tsoro", cewar Salmat.

"Ranar da duk Ustaz Lukman ya ji kina furta wannan (ZAZ) d'in a bakin ki kya yi bayani, saboda kinsan ya ce adaina kira na da hakan".

"Yo ai ba sai kin gaya min kina da mai tare maki ba, duk kauce-kaucen ku za ku fito kuyi bayani ne".

"Shin tsaya me kike nufi ne, ban fahimce kiba?".

"Kinsan dai ko kin 6oyewa ko wa soyayyar ku da Ustaz Lukman bai dace ni ki 6oyemin ba".

Cikin gwalo ido da wani cin birki tamkar mai tuk'in mota ta ja ta tsaya, mamaki kwance fal a fuskar ta.

"In har kin yarda kalmar "So" bata ta6a ratsawa tsakanina dashi ba, sai dai mutunci".

"Ke ce baki fahimci hakan ba, amma duk wanda ya yi mai duba na natsuwa idan kina gaban shi to zai hango son ki kwance a k'wayar idon shi".

"Allah yashirye ki, ke kika san wani abu "So" ni kam da saura na".
   "Ke ma za ki sani idan lokacin kisani yazo, wa yaga ana soyewa tsakanin Malami da D'alibar shi".

"Allah ni ko guntun namiji bai cikin tsari na ko Aure zan yi, na fison dogon namiji wanda zai yi guda da rabi d'ina".

Dundu Salmat ta kai mata had'e da furta, "makira kika ce baki san So ba kuma amma ga shi kina wassafa mijin da kike son Aure".
    "Shi ne sai aka ce maki wassafa ra'ayin ka shi ne So d'in?".. Yanzu bara in tambaye ki akawo maki gabjejen namiji wanda yayi hud'u d'in ki ya kika ga abin?", tana maganar ne had'e da dariyar k'eta.

"Bakin ki yasari d'anyen kashi muguwa kawai, Allah ya kiyaye ni".
   Dariya Zajlah tayi sosai akan yanda Salmat ke maganar had'e da ya mutse fuska tamkar ga mijin nan gaban ta.

Da hakan suka k'araso gida sannan suka gabatar da duk wani abu daya dace kafin Zajla taja sandar Baban ta su wuce gida.

****

Har gida yau suka kawo mai ziyara shi da Salis, bayan sun gayar da Mum suka fita gardener, saboda a al'adar shi in har yana gida indai ba bacci yake yi ba to nan ne gurin hutawar shi.

"Gaskiya (A.K.A) baka kyauta min ba, yanzu ace ayi birthday d'ina ko wa ya hallara kai baka je ba, kuma kana sane da ce wa duk duniya banda friends d'in da suka wuce ku kai da Imran".

"To ku ne da jaye-jaye kuce duk abinda za kuyi sai kun saka Mata a ciki shi ne birgewa a gare ku, ni ko in har hakan za ta cigaba da kasancewa to ina mai tabbatar maku za kuyi lamurran ku ba dani ba".

"Ni wannan abin na ka na d'aure min kai, zanga ranar auren ka da kuma matar da za ka aura, saboda wannan abin na ka ya yi yawa", ce war Imran.

Murmushi ya rik'a yi sama-sama wanda har fararen hak'oran shi na bayyana had'e da dimple d'in shi.

"indai ku kuka ta shi auren Allah sanya alkhairi don kunsan ba dani ba a y'an dinner da sauran su, zan dai je d'aurin aure shi ne na mu".

Kallon da suka bi shi dashi ne ya sa ya yi saurin kauda kan shi yana dariya k'asa-k'asa.

"Ka ma mayar damu wasu sha ka wuce za ka gani ne. Na ma manta in gaya ma Lubnah ta ce in ba ta number d'in ka".

Mugun kallon da ya yimai ne ya sa ya fahimci amsar da yake nufi zuwa gare shi.

"Baiwa wata Mace number ta na nufin rabuwar mu ta har abada dakai, ka sanni kasan waye ni. Duk cikin contacts d'ina number Mace biyu nake da, Mum da Lil Sis".

Cikin 6acin rai ya mik'e ya tattara wayoyin shi ya nufi hanyar shiga gida, duk yanda ya so tsayar dashi don ya nuna mai wasa yake yi abin yaci tura.
   Bayan ya shige ne gidan Imran ya kai duban shi ga Salis had'e da hararar shi sannan ya furta.

"Sai ka ta shi mu fice tunda ka takaro zuciyar manya". Dariya sosai Salis ya yi had'e da furta.

"Ni fa suk'uwar shi dariya take ba ni, da abin 6acin rai da wanda bana 6acin rai ba za kaga ya had'e fuska ala dole shi fushi yake yi".

"Allah wataran da gayya nake tsokanar sa saboda inyi dariya".

"Don kasan duk rintsi yana tare damu ne, ko ya yi fushi dole yasauko shiyasa kake mai hakan", ce war Imran.

Hakan suka had'a nasu da nasu suka fice saboda sanin in kwana za suyi gurin bazai kuma kula su ba sai ranar da ya sauko daga zuciyar.

® *SDY JEGAL*

Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

Tuesday 1 November 2016

KOMAI AKA SAKA MA RANA

������ *DUK ABINDA AKA SAKA MA RANA*������

      *ONE TO END*

*DAGA ALK'ALAMIN Y'AR MUTAN JEGA*✍��.

Wayar tace ta d'aga cikin sauri had'e da furta "don Allah kuyi hak'uri ga munan fitowa, dama Issuhu muke jira yazo kuma gashi nan ya iso".

"Assy! Assy!! Assy!!!".

Sai ana ukun ne ta kar6a had'e da fitowa daga d'akin rik'e da riga a hannu.

"Kina nufin ma ko shiryawa baki yi ba?, to wallahi yanzu Ramu ta kira kan cewa an kammalu mu kad'ai ake jira".

"To ku kai kaya napep kamin in k'arasa shiryawa".

Issuhu ne ya taimakawa Hauwa suka saka kayan a napep sai ga Assy ta shirya ta fito, daga nan suka yi bankwana da iyayen su suka d'auki  hanya sai school of health.

Da suka isa gurin sun sha surutun mutane kan ce wa sun tsayar dasu musamman Maryam.

"Kawai kice kin matsu baki je tsafe ba shiyasa kika ta damun mu da kira kan cewa mu fito hakanan", cewar Assy.

"Me zai sa in matsu don zanje dajin Allah? Ke fa ni dazan fito daga gida har da hawaye na in bakiji tsoro ba".

Da hakan dai aka cika bus biyu d'aya ta maza d'ayan ta mata suka kama hanya sai tsafe.

Bayan sun sauka ne sai kallon kallon suke yi saboda mamakin dajin Allah da aka kawo su, hakan dai aka raba masu guri kowa ya d'auki kayan shi.

Hauwa, Assy, Maryam, Ramu sama aka basu masauki, sai sun kalli kayan da suka jibgo su kalli yanda zasu hawa su kai su sama ga uban gajiyar da suka kwaso.

Dole hakan suka jure suka rik'a jidar kaya suna kai masaukin su, bayan sun had'a komai ne suka dawo jiganiyar d'ibar ruwa suna kai saboda su samu na lalurar su.

Hauwa har da guntun hawayen ta tana furta "wannan bak'ar wahala ta yi yawa, tun ba'aje ko ina ba har na fara kewar iyaye na, in gida ne ya za'ayi nayi wannan wahalar".

Assy ce ta bita da harara tana furta "Dama ai ko gidan baki da kata6us don ba kowane aiki kike iyawa ba".

Ramu ce taja Hauwa suka wuce da robar ruwan da suka ebo.

Maryam da Assy suka mara masu baya. Bayan sun shiga masukin sune aka koma shawarar me za'aci.

Ga dai spaghetti, indomie, cus-cus da 6ula har da miyar su da dallaki da sauran kayan tarkace.

Nan dai suka yanke shawara suka ci 6ula, sun kwanta kenan Hauwa ta kai duban ta zuwa gare su.

"Me kuke nufi bazaku tashi muje d'akin karatu ba kuka samu guri kuka kwanta?".

"Duk wannan gajiyar da muka jibgo za kice muje karatu, Allah yakai ki lafiya mukam Asuba ta gari".

Ganin sun yi kwanciyar su yasa ta kwashi kayan karatu ta fice daga d'akin.

Ko minti ashirin batayi da fita ba sai gashi ta rik'a jin bacci dak'yar ta samu wani ya raka ta ta koma masauki.

****

*BAYAN KWANA BIYU*

Yau tun safe suka tashi saboda yau ne zasu fara exam d'in da ta kawo su a garin na tsafe. Da hakan suka shiga paper one da safe sai paper two bayan azzahar.

Ranar alhamis suka fara practical da hakan aka rik'a tantance su d'aya bayan d'aya ana masu signing.

Kuka su Assy suka hango Hauwa nayi, koda suka isa gurin ta da tambayar me ke faruwa kuka ta k'ara saki.

"Kayan practical d'ina aka sace, na yi nema bangan su ba".

"Ke dai Allah ya yi maki sauk'in saunan ci", ce war Assy.

Gurin wani malami ta je tana gaya mai ansace mata kayan practical, ko kallon ta bai yi ba.

Wani Malami ta hango zaune ta tunkare shi  tana hawaye tana gaya mai.

"Kin tabbatar an maki signing a takardun ki?".

"Eh wallahi Malam anyimn".

"To je ki ba matsala insha Allah".

Da hakan suka fice zuwa masaukin su suka dafa cus-cus sukaci.

Ranar Friday suka yi viber suka k'are, daga nan ne suka fara shirya kayan su domin haramar dawowa gida. Bayan sun kimtsa ne sai ga bus d'aya ta zo ta Maza amma ta Mata bata zo ba.

Da hakan aka kira wayar shi yake gaya masu motar shi ta samu matsala, shi ko direban bus d'in Maza ya matsa kan cewa sauri yake yi saboda yana da lodi zuwa Abuja.

Dole matan na gani Maza suka wuce suka bar matan daga Malamin da aka had'osu dashi sai Ahmad daya jira su.

Suna nan zaman jiran isowar direba har y'an tsafe da aka turo exam garin Jega suka koma.

Nan akayi waya da H.O.D d'in su sannan suka biyo motar da ta ajiye y'an tsafe d'in suka dawo gida.

Basu iso Jega ba sai wurin k'arfe tara na daren Juma'a, nan suka yi waya gida aka tura Umar ya d'auko su daga health zuwa gida.

Ranar assabar ne ni Sdy, Anty Ruky, Sis Nafee, Sis Blkisu muka kammalu gida domin taya su Assy murnar k'are makaranta da fatar fitowar kyakkyawan result.

Lallai tabbas *DUK ABINDA AKA SAKA MA RANA ZAI ZO IN HAR DA RAYUWA*

(Duk abinda ke cikin wannan gajeren littafin gaske ne ya faru, na yi shine domin nishad'antarwa da kuma taya K'anne na murnar kammala karatun su.)

Fatan alkhairi da fatan samun nasara zuwa ga k'anne na.

Na sadaukar da wannan gajeren littafin gare ku.
Asiya Labaran
Hauwa Labaran
Maryam Abubakar Muhammad
Aisha Bello (Ramu).

Gaisuwar ta ka ce da babbar murya Ahmad Abdulkareem.

*SAKON GAISUWA DAGA HAUWA AND ASSY*

All praise be to Allah the most gracious the most merciful.
Our special thanks to our parents for their personal support and attention towards our studies (May God continues to guide you).
Also special thanks to u our luvly brothers and sisters for ur help����.
Also special thanks to u our friends.
A special thanks to the staff of medical laboratory technician and including the staff of health technology jega,kebbi state.
The long journey ends today, those that we are still going to meet again I pray that we shall meet in peace not in pieces missing you all our *COURSE MATE*������.
And finally to God who made all the things possible to us till the end.
     *Your's Asiya and Hauwa'u Labaran Jega*.

*BY SDY JEGAL*