[9:31AM, 11/9/2016] *SDY* *JEGAL*: *ADALILIN GATA*
*(6)*
*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*
®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Kamar kullum yau ma ta gama kimtsa komai na kula da gidan suka shirya suka fito sai mazaunin su na bara, wanda kullum suka fito wani irin mugun nauyi take ji a ranta.
Saboda a tunanin ta kamar ta ya ci ace ta wuce zama y'ar jagora, sai dai ba yanda za tayi sanadiyyar in har bata kula da mahaifinta ba wa ye ta ajiye da zai kula dashi yanda yadace.
Ga shi dai in har ta ce baza su fito yawon bara ba to batasan wa zai ciyar dasu da sauran lalurorin su ba, tunda mahaifinta ba yada idon da zai fita yane mo musu abinda za suyi lalura.
Don ma Malam Inuwa na k'ok'arin basu abincin dare, duk da shi kan shi ba wata wadata ce dashi ba saboda ba kullum za'a ci abinci sau uku a rana gidan shi ba.
Duk ita kad'ai ke wannan tunanin a ranta, wanda har kullum take tunanin ina za ta ne mo masu mafita akan wad'annan matsalolin.
Sanadiyyar bugawar da motocin biyu suka yi ya janyo hankalin tsirarrun mutanen da ke zaune gefen hanya.
Dattijuwar na fitowa daga motor ta ya tayarda hannu zai sharara mata mari.
Hannun da ya ji ya rik'e na shi hannu ne ya bi da kallo.
"Ka daraja mutum ko da baka san shi ba, wanda ya girme ka haka yake tamkar yaya a gurin ka, haka zalika wanda ya yi sa'ar mahaifin ka tamkar mahaifin kane".
"Bai kama ce kaba kuma hakan bai dace dakai ba, yanda ka daraja manyan ka haka Allah zai sa a daraja na ka iyayen ko bayan idon ka".
Cikin sanyin jiki ya bi dattijuwar matar da kallo, sai wata irin kunya ce ke ratsa ga66an jikin shi, hak'uri yafara bawa matar had'e da neman yafiyar abinda ya tashi aikatawa.
Su duka biyun suka bi gurin da kallo domin ganin ta ina za su ga yarinyar amma ina ta 6acewa ganin su.
*********
Sandar mahaifinta ta rika suka doshi hanyar gida. "Zajla ki daina saka kan ki a cikin rayuwar wa'annan mutanen, ba mutunci ne dasu ba".
"Baba ai Ba komai na yi ba nasiha ce kawai na yimai saboda abinda naga ya kusa aikatawa bai dace ba".
"To Allah yamaki albarka yaba ki miji nagari inga auren ki da jikoki na".
"Baba ni fa na gaya ma bazan yi aure ba, saboda bansan wa zai kula dakai ba", tana maganar ne had'e da zum6uro baki tamkar yana ganin ta.
"Haba Zajla kidaina fad'ar hakan, Allah zai kula dani saboda shi ya so gani na hakan kuma zai ya yemin lokacin da ya so. Tunda abin ciwo ne bana halitta ba kuma daga baya ya same ni".
"Baba kayi ta addu'a Allah yaba ni hanyar samun kud'i insa a gyara ma idon ka".
****
Fitowa tayi da sunan kai ziyara company maigidan ta, amma sanadiyyar abinda yafaru ne ya sa duk ta ji ba za ta iya k'arasawa ba akalar motar ta taja takoma gida.
Da shigar ta falon Saudat tagani zaune tana waya, ganin shigowar Mum ne ya sa ta yi saurin tsinke wayar had'e da mik'ewa tsaye.
"Mum ba dai har kinje company kin dawo ba?".
"Ban k'arasa ba na dawo". Ta ba ta amsa a tak'aice, ganin 6acin rai kwance saman fuskar Mum ya sa bata k'ara magana ba.
"Me ya hana ki zuwa skul yau?".
"Mum fa har na shirya Hafsat takira ni ce wa lecturer d'in bai zo ba shiyasa nayi zama na saboda dama yau shi kad'ai muke da".
Bayan ta bawa y'an aiki umurnin abinda za'a dafa abincin rana, bedroom d'in ta ta wuce duk ranta jagule.
*02:30*
Talatu mai aiki ce ta gayawa Saudat ta fad'awa Mum an kammala komai.
Bedroom d'in ta wuce ta gaya mata sak'on k'are girkin, nan Mum ta bata umurnin kiran Brother su had'u falon Baban su.
Bayan sun kammalu anyi lunch an k'are ne ta kai duban ta ga Al'amein.
"Za ka iya tuna ranar da kashigowa Dad d'inku cikin 6acin rai har kana gaya mai ka mari wani dattijo?".
"Mum me ya kawo wannan maganar?, ai ina ga ta wuce, ko kuma wani fad'an za'a maimaita min?". Yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi.
"Kaba ni amsa kawai". Ta furta a tak'aice.
"ina ga za'a yi sati biyu ko kwana goma".
"Wannan dai-dai yake da maimaita abinda ka aikata akan fuskar mahaifiyar ka", tana kaiwa k'arshe ta fad'a bedroom d'in Dad.
Cikin razana su duka uku suke kallon junan su kowanne 6acin rai kwance a fuskar shi musamman Al'amein da har jiyojin kanshi sun fara bayyana.
(4 breakfast, luv y'all My fan's)
® *SDY JEGAL*
Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[4:08PM, 11/9/2016] *SDY* *JEGAL*: *ADALILIN GATA*
*(7)*
*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*
®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
"To wai Dad wa ye ya isa har ya d'aga hannu ya kai wa Mum mari kuma ya zauna lafiya a garin nan?".
"Son ni ma wannan shi ne abinda nake tambaya, amma nasan ba wanda zai bamu wannan amsar sai ita kanta, kuma nasan mu shekara muna tambaya ba za ta gaya mana ba".
"Dad mushiga daga ciki muji ko za ta gaya mana d'an gidan uban waye shi". Ce war Saudat.
Hakan suka d'unguma sai bedroom d'in Dad domin sa mun amsar tambayoyin su.
"Mum Alamein ta shi kigaya min wane isasshe ne zai d'aga hannu duk garin nan yadakar min Mata?".
Wani guntun murmushi ne ta saki a fuskar ta had'e da girgiza kai alamar ina tausayin tsarin ku.
"Wannan shi zai tabbatar muku ce wa duk abinda kayi na alkhairi ko na sharri za ka had'u da makaman cin shi ko mai dad'ewa".
"Kuma kai da kake ta da jiyojin wuya me za kayi akai ko da na gayama wa ya mare ni? Ko ka manta shi wanda ka mara yana da y'ay'a kuma sun san darajar shi".
"Me kake tunani a wancan lokacin in har ace ko da ka mare shi wani d'an shi na gurin? Ko kana tunanin dukiyar ka za tasa in har suna gurin su k'yale ka?".
"Mum ni fa mutumen laifi ya yimin, har ta ya ya zai zo yana tafiyar ganin dama a saman titi".
"Haka zalika nima laifi nayi yaron ya mare ni".
Cikin damuwa Dad ya bi ta da kallon mamaki, ya rasa ga ne ita wace irin Mace ce da batasan y'ancin kanta ba.
Durk'usawa ya yi gabanta ya d'ora hannuwan shi saman k'afafun ta tamkar yayi kuka yake ji ya furta.
"Don Allah Mum ki gayamin ya akayi hakan ta faru? Kuma in kin san waye ki gayamin shi please and please Mum?".
Murmushi ta yi sosai har hak'oran ta suka bayyana, sannan ta kwashe ko mai ta gaya masu had'e da yaba halayyar yarinyar.
Sai lokacin suka saki fuskokin su har Al'amein na furta "wallahi ya kuru da ya aikata wannan d'anyen aikin da ya had'u dani".
"Inna san waye shi ko in ban sani ba? Ko kuma inna gaya maku waye shi za ku d'auki mataki?".
Da hakan dai ta k'ara janyo hankalin su had'e da k'ara lurar dasu kan muhimmancin girmama na gaba dasu, wanda Dad ke zaune yana sauraren su.
******
Duk abinda aka saka ma rana zai zo indai da rai da lafiya. Yau ne ake shirin gabatar da musabak'a ta gari wadda za'a gabatar a makarantar su Zajlah saboda kasancewar makarantar ta su ce babba kuma itace kan gaba a duk sauran makarantin nen garin su.
Daga kan y'an izifi biyu aka fara har zuwa kan izifi sittin wanda aka share sati d'aya ana gudanarwa tsakanin makarantu biyar dake garin.
Inda aka k'are kuma makarantar su Zajlah ta zamo gwarzuwa a musabak'ar wanda har da Zajlah da Salmat acikin gwarzayen, saboda Zajlah ta yi haddar izifi talatin inda Salmat ta yi izifi ashirin.
Bayan kwana ki bakwai ne aka gabatar da ta Jaha a garin Birnin kebbi, daga nan akayi ta k'asa gaba d'aya inda Zajlah ta zo ta d'aya a cikin y'an izifi talatin Salmat kuma ta biyu a cikin y'an izifi ashirin.
Sun sa mu kyaututtuka da dama wanda ya had'a da kud'i da keken d'unki Zajlah harda kujerar Makkah wanda sanadiyyar hakan har da guntun hawayen ta na farin ciki.
Ko Malaman su kaduba lokacin za kaga farin ciki kwance fal a fuskokin su musamman Ustaz Lukman dake kula da 6angaren masu haddar da kuma wani abu da yake ji kwance k'asan zuciyar shi akan Zajlah.
Mahaifin ta farin ciki fal a ran shi harda hawayen shi, ji yake yi ina ma ace yana gani da idon shi yaga wannan rana ta farin ciki da y'ar shi ta zamo gwarzuwar shekara.
Hakan suka tarkata suka dawo gida farin ciki fal ransu, sai mak'ota ke ta shigo masu murna da Allah sanya alkhairi.
Sun samu kud'i sosai musamman Zajlah da tazo ta d'aya, har gida Ustaz Lukman ya biyo su had'e da kyaututtukan da suka sa mu mota ta kawo masu har k'ofar gida.
"Za ku sa mu shigowa makaranta ranar assabar?", ce war Ustaz Lukman.
"Ustaz a bamu sati d'aya mana mud'an huta sannan mu shigo".
"Sati d'aya ya yi yawa gaskiya saboda bazan jure...... Sai kuma ya canja akalar maganar.
"Shikenan Zajlah ku shigo zuwa ranar Larba, tunda kunga yau ta kama Assabar".
"To Ustaz mun gode sosai". Da hakan suka shige gidan su Salmat d'in.
® *SDY JEGAL*
Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[10:33AM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: *ADALILIN GATA*
*(8)*
*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*
®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Kamin su shiga gidan ne Salmat ta kai duban ta zuwa ga Zajlah had'e da furta.
"Yau kin yarda da abinda nake cewa Ustaz Lukman son ki yake yi?".
"Ke dai ina ga aure kike so shiyasa kullum maganar ki ba ta wuce ta So ba".
"Kina ji fa yau har da furta cewa bazai juri rashin ganin ki ba, sai ya juya maganar saboda kar mu gane inda ya dosa".
Dundu ta sakar mata had'e da janyo gashin kanta sai da ta yi k'ara, da hakan suka shiga gidan.
Mama Inno ce ta tarye su dukan su ta rungume sai albarka take saka masu har da guntun hawayen ta.
"Zajlah yau burin ki zai cika da yardar ubangiji saboda ya yi maki hanyar samun kud'in da za ki kula da matsalar idon mahaifin ki".
"Wallahi Mama ina jin tsabar kud'in da nasamu tun a can matsalar Baba ce nafara kawo wa, sai kuma samun abin Sana'a da zai raba mu da yawon bara".
"Don ko babu kud'in zan soke matsalar bara tunda na samu keken d'unki zan tashi da koyo har in iya".
"Gaskiya kam kinyi tunani mai zurfi, yanzu sai abubuwa sunyi sauk'i ku had'u ke da Salmat kuje koyon d'inki".
Da hakan aka shigo da kayan da suka samu gidan su Salmat, inda kowannen su ke da keken d'inkin sai Salmat dake da kud'i dubu d'ari biyu Zajlah ko na da dubu d'ari biyar da kujerar Makkah da shugaban k'asa ya baiwa duk wanda ya yi na d'aya a matakin haddar su tun daga izifi biyu har zuwa izifi sittin.
****
Tun lokacin da yarinyar ta hana ma saurayin marin ta take kwana kuma ta tashi da ita aranta, saboda yarinyar ta burge ta sosai, sai tunani take yi ina ma ace y'ar tace ke da halayyar wannan yarinyar.
Hakan take gurin Fadeel wanda duk yanda ya so yafige yarinyar a cikin zuciyar shi abin ya faskara.
Duk inda zuciyoyin mutum biyu suke da tunanin ta suke kwana kuma suke tashi, duk inda suke farautar ta domin su ganta abu ya faskara.
*******
Falon ta shigo ta d'auki remote domin canja tashar, abinda ta ga an nuno ya hana mata canjawa sai gata zaune jagwaf saman kujera.
"Saudat! Saudat!! Saudat!!!".
Gigice ta fito daga d'akin ta ta fad'o falon saboda kiran da Mum ke ta k'wala mata.
Plasma d'in ta bi da kallo saboda itace Mum ke nunawa da yatsan ta, ita dai bata ga komai ba bayan yarinya tana rero karatun Qur'an cikin baiwa kowane harafi hakk'in sa had'e da tajweed.
"Mum me ke faruwa halan? Ban fahimci me kike nuna min ba fa".
Nan Mum ta yi mata bayanin yarinyar. Hakan itama Saudat ta ji yarinyar ta burge ta sosai.
"Ina so kishirya zuwa anjima ki rakani makarantar su yarinyar nan, dama na yita neman ta duk inda nake sa ran ganin ta bangan taba".
"Yanzu Mum me za kije kiyi mata? Sai kita neman yarinya tamkar wacce ta k'ulla maki wani abin arzik'i".
Mugun kallon da Mum ta bita dashi ne ya sa taja bakinta ta tsuke.
*05:00pm*
Dai-dai wannan lokacin Mum ta faka motar ta k'ofar makarantar, da Ustaz Yusuf ta fara cin karo k'ofar makarantar.
Nan ta yimai bayanin abinda ke tafe da ita, mashin d'inshi yahau yayi mata jagora har k'ofar gidan su Salmat, godiya ta yita yimai har da fitarda kud'i taba shi saidai bai kar6a ba yajuya yakoma.
Mota ta hakimce tana wani yatsinar fuska saboda k'ofar gidan da taga sun tsaya wai nan Mum tazo kuma gurin k'aramar yarinya.
"Fito mushiga ciki mana".
"Shiga ki fito Mum zan jira ki a mota".
Fad'a ta dinga yi mata sannan ta fito har da wani handkerchief tana toshe hanci. Gidan suka shiga inda Mama Inno ta yi masu tarbar da ta dace duk da batasan su waye ba.
Bayan sun gaisa Mum ke yi mata bayanin gurin Zajlah tazo. Nan Mama ta kira su daga d'aki suka fito.
Durk'usawa sukayi har k'asa suka gayar da Mum, bayan ta amsa ne take ta yabon musabak'ar su data gani ana ta haskowa a cikin kowace tasha.
Nan ta d'ora da gaya mata itace ta hana wani saurayi ya mara. Har ga Allah ta manta da abinda ya faru sai yanzu data tuna mata.
"Laaah Haj wallahi ba komai, ai yiwa kaine don ni ma zanso a daraja nawa iyayen".
Da hakan Mum ta basu dubu goma-goma suna ta godiya, itako ta fice daga gidan.
® *SDY JEGAL*
Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[6:14PM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: *ADALILIN GATA*
*(9)*
*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*
®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Da sannu Fadeel ya binciko gidan su Zajlah wanda karo uku kenan yana zuwa k'ofar gidan su amma sai jikin shi yayi sanyi yaka sa tunkarar ta yakoma.
Yau dai da k'arfin gwiywar shi ya tashi na tunkarar ta yaga ya mata gaskiyar lamari ce wa yana son ta.
K'ofar gidan ya zo, amma a tunanin shi na zai iya tunkarar ta yau sai gashi abin ya gagara, ta gaban shi suka zo suka wuce ita da Salmat domin zuwa koyon d'inkin su gidan wata mata dake k'arshen layin su.
"Ni fa Zajlah abin nan ya fara d'aure min kai, in har kin lura kusan kwana uku kenan duk muka wuce zanga wannan motar".
"Kuma fa abin mamaki ba a ganin na cikin motar su waye saboda duhun glass d'in motar".
"Ke kika damu da wannan motar, ni fa zan iya ce maki ban ma ta6a lura da motar ba sai yau dakika yi maganar".
"Ai ke dama ba komai kike lura dashi ba, inaganin wataran sai halaka ta hau kan ki bakisan za ta zo ba".
"Au dama in abu zai same ka zaka san da zuwan shine?".
"Ba hakan nake nufi ba, amma dai ana so ka lura da yanda abubuwa ke tafiya saboda tsaro".
Dariya sosai Zajlah ta yi, da hakan suka isa gidan da suke koyon d'inki.
******
Yau ne aka aje kan za'a yiwa Baban Zajlah aiki a idon shi, Malam Inuwa, Zajlah da Salmat ne suka yi mai rakiya zuwa Birnin kebbi. Asibitin Sir Yahaya ce aka yi mai aiki kuma aka gama cikin nasara wanda sai da suka had'a shi da medical glass saboda rashin ganin abinda ke nesa dashi.
Je kaga murna fal a gurin Mal Abubakar inda yake alfahari da y'ar shi k'waya d'aya tak da Allah ya bashi, wacce ta zame mai y'a d'aya tamkar da dubu.
*****
*Wacece Zajlah?*
Mal Abubukar d'an asalin k'auyen giwa tazo ne shi da matar shi Basira, auren zumunci ne aka yi masu domin mahaifiyar ta da mahaifin shi ne uwa d'aya uba d'aya.
Sun ta so tare da Mal inuwa ne tun shigowar shi garin Jega sanadiyyar Sana'ar kayan gwari wanda daga baya har ya samu matsakaicin gida ya saye a kusa dashi ya dawo nan da zama.
Allah ya had'a kan matan su wanda inka gansu zaka rantse da Allah y'an uwan juna ne. Basira ta rasu ne tun ranar da ta haifi Zajlah wanda bata ko saka yarinyar a idon ta ba.
Lokacin ita kuma Mama Inno ta haifi Salmat da sati biyu, nan ta kar6i Zajlah ta had'a da Salmat tana shayar dasu.
(Asalin sunan Zajlatu ne k'awaye ne suka tak'aita shi da Zajlah, abinda sunan ke nufi rayuwa kyakkyawa kuma mai sunan tana daga cikin tabi'ai, me neman k'arin bayani akan asalin sunan da tarihin mai sunan zai iya searching da *KISASUT TABI'AT*, amma da larabci).
Sun shiga tashin hankali sosai musamman Mama Inno da Mal Abubakar, dole suka dangana saboda wanda yafi su son ta ya kar6i abarsa.
Zajlah na da shekara takwas a duniya Baban ta ya makance sanadiyyar ya jima yana gani bishi-bishi sai bai d'aukin abin wata matsala ba har abin ya ta6a idon duka ya daina gani, tun yana iya lalurar kan shi har abin ya gagare shi.
Lokacin ne sauran tsirarrin dangin shi suka guje shi sanadiyyar ganin ya zama wata lalura a gare su, wanda shi ba hakan yazauna dasu ba don mutum ne mai taimakon dangin shi duk da shi ma ba wani hali ne dashi ba.
Sanadiyyar makarantar shi ne Zajlah ta dawo gurin shi da zama domin taimaka mai da wasu abubuwan da ba za'a rasa ba.
Zajlah yarinya ce mai kimanin shekara goma sha shida zuwa sha bakwai, chocolate colour ce ba wata kyakkyawa ce ta azo a gani ba sai dai manyan idon ta da gashin girar ta shike fitar da kyawon ta, yarinya ce mai shape sai dai batada k'iba irin sosai d'in nan.
Kamin abubuwa suyi tsanani ansaka su makarantar boko iya primary daga nan basu cigaba ba sai makarantar Arabic dasuka mayar da hankali akan ta.
Saboda kowaccen su ta yi sauka uku sai kuma hadda da suke yi har Ustaz Lukman ya saka su acikin musabak'a, wanda sanadiyyar ne har duniya tasan da zaman su inda iyayen su ke alfahari dasu.
® *SDY JEGAL*
Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.
[9:08PM, 11/10/2016] *SDY* *JEGAL*: *ADALILIN GATA*
*(10)*
*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*
www.sadijegal.blogspot.com
®NWA
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Mamaki fal a ran Saudat na miye silar zuwan Mum gidan su wannan kucakar yarinyar, ga shi tana so ta tambaye ta sai dai kuma bata ga fuskar tambayar ba.
Bayan sun dawo ne direct bedroom d'in Dad ta wuce, zaune yake k'asa saman carpet ya jingina jikin shi da kujera yana karatun jarida.
"Daddyn Alamein hutawa kawai ake yi"?.
"Ba dole ba tunda yanzu kin rage So na da tattali na, ina ga aure zan zo in yi ko zan samu mai bani kulawa", yana maganar ne d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar sa.
Murmushi Mum ta yi sosai had'e da tattara hankalin ta guri d'aya ta k'ara matsawa gab dashi.
"Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama, ka ga inka nemo mata sai a had'a da naka auren dana son ad'aura rana guda".
"Yaushe Son ya nemi mata banda labari? Yaron da ko mata bai cika kulawa ba ina yaga macen da yake so?".
"Sanin hakan ne ya sa na nemo mai mata da kaina, yarinya y'ar asali y'ar gidan mutunci mai ilmi".
Wata irin zabura ya yi ya kai duban shi zuwa gare ta.
"Kina nufin Son ne za ki yiwa auren dole? Ko ni da nake uban shi ba'a yimin auren dole ba barrantana shi da yake cikin k'urciyar shi", yana maganar ne cikin fad'a-fad'a.
"Dad'i na dakai duk yanda ake magana cikin kwanciyar hankali indai aka ta6o yaran ka cikin second d'aya za ka birkice".
"Duk duniya ba ni da farin cikin da ya wuce na yara na, babu takura ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta".
Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna.
Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira.
"Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?".
"Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil".
"Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba".
Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin.
"Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai".
"Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin.
Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai.
"Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana".
Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai.
"Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum".
Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya.
"Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?".
"Alamein".
Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina.
"Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku".
"Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe.
"Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure".
"Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani".
Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri.
Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi".
"Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa.
® *SDY JEGAL*
Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.