Monday 17 October 2016

SANADIN KUNCI 71-80

[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 7⃣1⃣/7⃣2⃣��

*BAYAN SATI UKU*

An sallamo Umma daga asibiti kuma ta samu sauk'i alhmdulillah, je kaga zama tsakanin ta da Ammi tamkar su had'iye juna idan ka gansu ba za ka ta6a cewa sunyi zaman rashin fahimta a baya ba abin gwanin ban sha'awa don ko yaran su in har ba ka sani bane ba za ka tantance yaran Umma da Ammi ba.

****

6angaren Haydar kuwa manya sunje gidan su Mela har an saka lokacin aure wata biyu masu zuwa, inda suke gina soyayyar su cikin jin dad'i da walwala tamkar su had'iye junan su.

****

Yau ne Ammi ke ta hada-hadar zuwa Bk domin ta dubo tsohon ta, inda suka yi aje kan ce wa Mubarak zai bi ta domin maganar shi da Mama Baraka.

Hakan suka shirya sai Bk inda ta tarar da Baban ta cikin k'oshin lafiya sai abinda ba za'a rasa ba na tsufa.

Bayan sun huta ne Ammi ta shirya duk ta kaiwa dangin Abban su Mubarak ziyara, sannan ta wuce gidan kakar ta Gwaggo kulu wadda tsufa ya ka ma ta sosai, irin kulawa da taimakon da Ammi ke yi mata su ke saka ta k'ara nadamar abubuwan da ta yi mata a shekarun baya.

"Haba Gwaggo kar ki da mu kan ki ni wallahi komai ya wuce a guri na, da ma a rayuwa ta ba na kwana da ko wa a zuciya ta, ko yanzu na so in mayar da ke guri na da zama don kin nuna min kin fison zama nan ne shiyasa na k'yale ki, amma duk da hakan zan sa mu wadda za ta rik'a kulawa dake ina biyan ta".

Nan ta yita sakawa Ammi albarka da jin dad'in abinda take mata.

Fitar su daga gidan basu za me ko ina ba sai gidan su Mama Baraka, da murnar ta ta tarye su ta ma rasa ina za ta saka su kan dad'i.

"Mubarak ashe da gaske za ka kawomin ziyara wataran".

"Haba Mama ta yaya zan manta dake a rayuwa ta, ko yanzu tahowa nayi in gaya maki ki had'a kayan ki nan da kwana biyu za mu wuce sokoto".

"Anya hakan na yuyuwa Mubarak?, ko hakan na gode da kulawar ku gare ni sosai Allah ya saka da khairan".

Rufe bakin ta kenan k'anen ta na shigowa gidan, bayan sun gaisa da su Ammi ne Mubarak ya sako buk'atar tafiya da Baraka.

"Gaskiya a duniya banda ko wa bayan ita, bazan iya bari kuje da ita ba, zan dai yi maku alfarma d'aya in har Allah ya horemin na mota to zansa aka wo maku ita tayi maku kwana biyu".

Je kaga damuwa k'arara a fuskar Mubarak, saboda gaskiya yana jin Mama Baraka tamkar Ammi a ranshi, bazai ta6a manta yadda ta taimaka masu ba abu d'aya yake so yagan ta a tare dasu.

Tamkar walk'iya haka ta fad'o d'akin cikin kissa da kisisina ta fara magana.

"Haba maigida ai ko Annabi so ya gode wa, kabar ta ta bi su mana mu in mun sa mu lokaci sai mu rik'a kai mata ziyara, kuma a yanda na fahimci maganganun su ai Bk tamkar gida ce a gare su nasan za ta samu lokacin ka wo muna ziyara ko Anty?".

Duk da ta fahimci cikin kissa ne take maganar duk da shi k'anen na ta bai fahimci komai ba a maganar matar shi to ita ta fahimci inda ta sa gaba.

Saboda da ma ba son zama da ita take yi ba kawai don bata sa mu fuska ga maigidan bane shiyasa take danne wasu abubuwan.

Bata San ce wa har ga Allah ta fi son tabi su Ammi ba, ba akan komai ba sai don samun kwanciyar hankalin ta kuma tasan ce wa ba za su ta6a wulak'anta ta ba domin sun san darajar ta.
   Kawai bata so ta nuna tana son binsu ne k'anen na ta yaga bata damu dashi ba, ko yaga ce wa don ta ga masu kud'i ne za ta guje su.

"Shikenan ba matsala sai ta shirya kayan ta in za su wuce suje da ita, amma don Allah yaya kar ki guje mu in da ma ta samu ki rik'a kawo mana ziyara".

"Kakka da mu insha Allah duk k'arshen wata zan rik'a kawo ta, kuma za ku rik'a gaisawa a waya", cewar Mubarak.

Akan murnar an bar shi yaje da Mama Baraka dubu goma ya fitar ya bawa k'anen nata.
    Shi ko je kaga murna gurin shi shi da matar shi sai godiya suke zabgawa, da hakan suka wuce kan ce wa in zasu wuce za su zo suje da ita.

****

Gama breakfast d'in su ke da wuya ta zura da gudu sai toilet, amai ne take lezayawa tamkar za ta had'o da hanjin ta.
    Cikin tashin hankali ya mara mata baya ya tallafo ta sai sannu yake zabga mata, wanda da taimakon shi ta wanke bakin ta had'e da fuskar ta.

Suna dawowa falon ta k'ara wani yunk'uri na amai, tallafo ta d'in da zai yi su koma toilet ta ke ta wanke shi tsaf da wani aman, hakan ya kai ta toilet sai da ya yi mata wanka ya gyara ta sannan ya yi wanka ya shirya suka wuce asibiti.

Awon farko da aka yi mata ya nuna ce wa tana d'auke da ciki na sati uku wanda Mus'ab ya shiga farin ciki sosai, tun asibitin ya rink'a kiran y'an uwa yana gaya masu abin farin cikin da ya sa me su.

Sai dai abu d'aya ke damun shi irin yadda amai ke da munta cikin yini d'aya duk ta zabge tamkar wacce ta yi ciwon sati d'aya.

****

Bayan su Mubarak sun d'auki Mama Baraka ne suka doshi hanyar sokoto, da saukar su ne Haj Maryam ta kar6i mama Baraka da hannun biyu har tana furta ce wa a part d'in ta za ta sauka.

"Duk dai abinki da na yi aure zan d'auke Mama ta".

"Je can tuzuru dakai ka yi kwantai za ka wani ce gidan ka za'a zauna, to bara sai ka k'are ruwan idon na ka".

"Amma ko gaskiya Haj kin gama da yaya, in kika ga matar da zai aura sai kin yi mamaki", ce war Mukarrama.

"Ke gafara can aku, gurin surutu ba'a barki ba ya ba, ke ina na ki mijin yake?".

"Ai ko yau d'innan za ki gan shi, don ca nayi yabari sai yaya Mubarak ya dawo sannan yazo gaida shi", tana maganar da murmushi a fuskar ta.

Da hakan ko wa ya wuce part d'in shi, har Umma ta yi murna da zuwan Mama Baraka.

****

*BAYAN SATI BIYU*

Soyayya ta k'ullu tsakanin Mukarrama da Nibras, sai kuma Mubarak da Imtihal d'iyar Haj Maijidda wanda Ammi ta fi ko wa jin dad'in wannan zumuncin da suka k'ulla tsakanin su, sai kuma Iman da Sudais abokin Haydar, fata d'aya Allah ya nuna mana lokaci musha shagali.

****

"Ni fa wannan cikin ya fara da muna kullum cikin ciwo da k'arin ruwa, duba kaga yanda duk ta zabge tamkar wacce ta shekara kwance tana jinya".
   Mus'ab ne ke ta yiwa Dr Shureim mi ta kan drip d'in da za'a sakawa Musirrah.

"Abin fa sai da hak'uri saboda duk mata hakan suke ta wahala wani lokaci sai cikin ya yi k'wari za kaga sun rage laulayin".

"Gaskiya ina ganin Hayatee ta fi ko wa wahala ji fa yanda komai taci sai ta mayar dashi".

"Kai dai na tane kasani shiyasa".

Hakan dai ya saka mata drip d'in yana mai luradda Mus'ab matsalolin da mata ke fuskanta ya yin d'aukar ciki.

(Na gode sosai da kulawar ku a gare ni, na ji sauk'i sosai Allah yabar zumunci)

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspos.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣3⃣/7⃣4⃣��

*BAYAN WATA TARA*

Yau ne Musirrah ta tashi da nak'uda wanda tun safe take 6oyewa Mus'ab saboda gudun shiga damuwar shi, akan ganin ita ke da cikin amma tamkar ya fi ta shiga damuwa sanadiyyar yadda cikin ke mugun wahalarda ita.
    Tun shigar cikin ta wata takwas Mama Baraka ta ta re gidan su domin ba ta kulawa yadda ya Kama ta.

"Hayatee yau ba za'a yiman rakiya ba ne?".

"K'albee na d'an zazza6i nake ji shiyasa, Allah ya bada sa'a sai ka dawo".

Briefcase d'in hannun shi ya ajiye da saurin shi ya hawo saman bed d'in, hannun shi ya Kai yana ta6a jikin ta ya ji alamar za fi kad'an.

"Ka ta shi ka wuce kasan na gaya ma duk abinda naji ko da kana office ne Zan kira ka, kuma ka ga Mama na kusa ai".

"Yanayin kine bai min ba yau, saboda ba haka na sa ba ganin ki ba".

Cikin k'arfin hali ta sauko daga saman bed d'in ta d'auki briefcase d'in shi, ta sa d'ayan hannun ta ta sagala a kafad'ar shi suka wuce har gurin motar shi.
   Cikin walwala yaja motar shi ya fice, ita ko ta juya zuwa gida inda take addu'ar in ma haihuwa ce Allah ya kawo mata da sauk'i kar tasha wahala tamkar na d'aukar cikin.

Tana kaiwa falo k'afar ta ta rik'e kuma marar ta ta k'ulle, a tsakiyar falon ta zube cikin yarfe hannu da cizon yatsa.

"Mama! Mama!! Mama!!!",  Sai ana ukun ne ta ji yo ta.
   Da saurin ta ta iso falon had'e da tambayar ta me ke faruwa, nan take gaya mata.

"Y'ar nan kinsan kina jin nak'uda har kika bari maigidan ya fita, da safen nan ya shiga gaida ni har yake jaddada min in kula dake ya ga tamkar yanayin ki ya canza, ashe ko da gaskiyar shi".

Nan ta taimaka mata suka wuce d'aki wanda shigar su da minti biyar haihuwa ta zo gadan-gadan.

Cikin zafin ciwo take rok'on Mama Baraka kan ta kira Mus'ab in ma mutuwa za tayi ta mutu hannun shi.
     "Kar ki damu Musirrah da ikon Allah d'akin ki zaki haihu cikin k'oshin lafiya".

Da taimakon Mama Baraka ta yimata addu'ar nak'uda a ruwa ta ba ta sha.
Cikin yaddar ubangiji ta sunkuto y'ar ta, wanda Mama Baraka na jiran uwar tafiya sai ga wata y'ar ta fito da uwar tafiya.

"Alhmdulillah! Alhmdulillah!! Alhmdulillah", sai da Musirrah ta furta hakan har sau uku.

Mama Baraka sai murmushi take yi. Nan ta fara shirya yaran sannan ta taimakawa Musirrah ta kimtsa.

"To bara in Kira su Ammi domin su zo suga kyautar Allah".

"Mama bara in fara kiran shi sannan a kira su Umma".

"Lallai yaran nan ba kuda kunya, ba ma ni zan yi mai albishir ba ke za kiyi da kan ki".

Nan ta yi murmushi ta sunne kai, Mama Baraka ta fita domin kimtsa guri.

"Wayyo baya na", abinda ta furta kenan daga kiran shi ta kashe wayar tana murmushi.

Cikin saurin da tamkar zai ta shi sama da motar ya iso gidan, wanda ko mota bai rufe ba ya fad'a gidan.

Direct d'akin ta ya fad'a, abinda ya ci karo dashi ne ya sa ya yi turus, sai wani tsadadden murmushi take sako mai mai narkar da zuciya.

Da murmushi d'auke a fuskar shi ya ta ka har bakin gadon da take zaune, da d'ai d'aya ya d'auki yaran ya masu addu'a.

"Wai kina nufin wannan kyautar duk ni kad'ai Allah yabawa?". Nan ya d'aga hannu sama ya yi hamdala ga ubangiji.

Waya ya fitar yadinga kiran y'an uwa da abokanen arzik'i yana gaya masu haihuwar.

Mama Baraka ya sa ta kula da yaran ya sunkuci Musirrah sai mota, asibiti ya nufa da ita domin su duba Mai in bata samu wata matsala ba, saboda yana mamakin yanda ta haifi yara biyu da kanta kuma a gida.

Nan suka duba ta aka gaya mai lafiya lau take, sai wasu allurai da suka mata had'e da maganukkan da suka ba ta.

D'auke da ita ya shigo gidan, Ummy, Umma, Haj Maijidda su ya ci karo dasu zaune a falon sun saka yaran a gaba sai murmushi suke yi.

"Yau na ji d'ibar albarka, mai jegon ce ake tallafowa haka tamkar jinjira?" Cewar Haj Maijidda.

"Haj duba yaran da ta haifa ki gani, in tace tayi tafiya za ta ji ci wo ne".

"Sauke ta nace, ke ko kin lafe ajikin shi tamkar wata jinjira", inji Umma.

Cikin jin nauyi Musirrah ke mutsu-mutsu yasauke ta sai k'ara matse ta yake yi.
   Da saurin shi ya wuce bedroom d'in ta da ita, inda su Haj Maijidda suka bishi da ido alamar mamaki, Ummy ko baki ya mutu sai kunya take ji.

Mela da Iman ya tarar a d'akin sun gyara komai tsaf sun kunna turare sai k'amshi d'akin ke yi.

Sum-sum Iman ta ajiye kaskon turaren da take yawo dashi kusurwa-kusurwa ta fice.

"Ohhh ni Mela na ga ta kaina, ina fatar har nak'udar kai ka mata?". Da murmushi d'auke a fuskar ta.

Cikin murmushi ya sauke ta ya wuce zuwa part d'in shi.

"Angaida laila majnun, a hakan kuka wuto su Umma zuwa nan?".

"Bari ke dai Mela, wallahi duk kunya yake saka ni, ko a gaban wa ba ruwan shi, ko yanzu a falo Haj ta ce ya sauke ni tamkar ta k'ara zuga shi ne ya maza ya shige".

"To ai kinji dad'i saboda kina samun kulawa yadda ya kama ta".

Suna maganar ne Haj Maijidda ta shigo ta tasa k'eyar ta sai toilet ta gasa ta sosai had'e da jan kunnen ta kan yadda za ta kula da kan ta.

Ko da suka fito Mukarrama na rik'e da jinjira d'aya tana juyi da ita a tsakiyar falon, wanda Imtihal ke rik'e da d'ayar jinjirar, sai Anty Rukayya dake zaune gefen gado tana murmushi.

"Tunda kun nu na muna ku y'an dangi ne to za mu tattara na mu mubar maku gidan".

"Hakan ya fi kam Haj, daga ce wa an haihu duk ku kwaso jiki ku cika gidan", cewar Umma.

"A'ah Umma kuyi zaman ku falo mu za mu tsaya a nan ba sai an gan mu ba", inji Mukarrama.

"To shikenan muje falon mu da muka iya taryon bak'i, nan suka had'u suka ko ma falon su Imtihal sai murmushi suke yi.

****

*BAYAN SATI D'AYA*

Gida ya cika mak'il da y'an suna tamkar gidan aure, inda yara suka ci suna Fa'ida da Fadila.

Mela, Mukarrama, Iman, Imtihal matar Mubarak, Anty Rukayya da Musirrah ankon wata shadda suka yi mai ruwan purple ta ci aiki sosai har zuwa wuyan hannun su.

Bahijja matar Dr Shureim da Fateema matar uncle Hakeem, sai kuma Mmn Walida, Sophy, Mmn Ansar, Khairat da Mmn Khalil, inda akaci suna cikin walwala da farin ciki.

Sai k'arfe biyar Mus'ab ya had'a masu wata gajeruwar liyafa iya su yara ba da iyaye ba.

Inda suka had'a da Haydar da Mela, Mukarrama da Nibras, Mubarak da Imtihal, Iman da Sudais, Dr Shureim da Bahijja, uncle Hakeem da Fateema sai kuma Anty Rukayya da Sultan, anyi pics da videos saboda tarihi, Jameel ne da Yusrah basu da wo ba har yanzu.

Anyi taro cikin walwala da nishad'i anci ansha sai dai fatar Allah ya raya Fa'ida da Fadila akan tafarkin islama.

*SDY JEGAL*��

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣5⃣/7⃣6⃣��

*BAYAN KWANA ARBA'IN*

Yau ne Musirrah suka yi kwana arba'in da haihuwar twins d'in ta wato F², wanda dama tun jiya Mus'ab ya shaida mata ce wa ta shirya za su fita gaida iyaye da yan'uwa har da abokanen arzik'i.

Yara sunyi 6ul-6ul dasu wanda inka dube su zaka rantse da Allah kowannen su shi kad'ai aka haifeshi.

Bayan sun shirya ne suka fito har Mama Baraka domin ta ce za ta ko ma gidan Ammi tunda sun yi arba'in, in ya so daga baya a sa mo masu y'ar reno.
    Sun had'awa Mama Baraka goma ta arzik'i wanda kan murna har da kukan ta, ita kam tasan lallai wanda Allah bai bawa haihuwa ba yana cikin damuwa, amma ita kam yaran Ammi biyu da Allah ya ba ta sun cire mata duk wata damuwa ta rashin haihuwa.

Da hakan suka fito basu zarce ko ina ba sai gidan su Musirrah. Nan aka yita murnar ganin y'an biyu, ba kamar Umma dake tarairaya da yaran tamkar ta had'iye su saboda kawaicin Ammi ga yaran.

Haj Maryam ma ta yaba da girman yaran har tana tsokanar Musirrah ce wa yaran sun fita girma da kuzari lokacin da tana k'arama.

"Ka jini da mata kamar kinsan k'urciya ta kina wani zuzuta yaran ki sun fini girma".

Karaf Mama Baraka ta kar6e "Ai ko Haj banga abinda yaran ki za su gwada wa y'ata ba, don itama da tana k'arama tubarakallah.

Nan dai su Ammi suka rik'a murmushi. Mama Baraka ta fitar da kayan da su Musirrah suka ba ta ta nunawa su Umma nan suka taya ta godiya had'e da saka masu albarka.

Hakan Umma ta kwashi yaran ta kaiwa Abba su sai washe baki yake yi yana kallon yaran had'e da yi masu wasa.

Suna fita daga gidan suka wuce gidan Anty Rukayya, nan dai suka zazzaga dangi sai marece suka wuce gidan su Mus'ab wanda Ummy ta ma rasa Ina za ta saka yaran kan murna, Baffa ma ya sakama rayuwar yaran albarka sai k'arfe 09:00pm suka wuce gidan su.

A gajiye suka koma gidan inda suka yi wanka suka kwanta, saboda dama sunci abinci gidan su Mus'ab d'in.

****

*WASHE GARI*

Breakfast kawai suka yi suka fice, yau gidan Iman aka fara zuwa nan ya barta ya fice.

Da murnar ta ta tarye su in da take turo d'an cikin ta da bazai wuce wata bakwai ba.

Daga nan sai gidan Mukarrama wanda ta lak'e suka fita tare.

A cewar ta za ta raka ta yawon gaida dangi, daga gidan ta suka wuce gidan yaya Mubarak.

Bayan sun gaisa aka ta6a hira har suna tsokanar Imtihal kan ce wa ita da Iman ba'asan wa zai riga wani haihuwa ba.

Gidan Haj Maijidda suka wuce daga nan wanda ta yi murna sosai da ganin su, har ta had'awa Musirrah maganin Mata na gyaran jiki dangin na sha dana turare saboda ita bata wasa ko kad'an shiyasa ko yaushe take manne a zuciyar maigidan, nan Musirrah tayi ta godiya.

Gidan babbar k'awa Mela ne na k'arshe, inda suka tarar da ita zube a falo da uban cikin ta.
   Dariya suka rink'a tutsurawa wanda ya yi sanadiyyar fitowar yayan su Haydar.

"Yaya barka da yau, ya gidan?".

"Ku bari ku k'arasa iskancin da ya ka wo ku gidan sannan mu gaisa".

Musirrah ta ja bakin ta ta tsuke, Mukarrama kuwa tamkar k'ara zuga ta yake yi.

Da saurin shi ya zabura ya yo kanta, bayan Musirrah ta yi saurin 6oyewa.

"Da ki tsaya ki gani in kin wuce duka a guri na".

"Bross fa igiya uku ke saman kaina, wai ko ka manta ne?".

"Ai na za ta ke talatin aka d'aura maki".

Nan dai su Musirrah suka yi ta dariya ita da Mela, saboda zamantakewar Haydar da Mukarrama na burge su ko yaushe suka had'u sai sun sayar da hali.

Hakan dai suka yi ta hirar su cikin walwala da nishad'i tamkar kar su rabu.

Da marece Mus'ab ya zo d'aukar su har sun hau hanya ya tuna.

"Kinga ya kamata gobe muje gidan Dr Shureim da gidan uncle Hakeem daga can sai mu wuce Bk, ko ya kike gani?".

"Allah na gaji Abban twin's mu bari nan da kwana biyu".

"Ba matsala Allah yakai muna rai".

"Ameen".

Sai da suka biya suka Fara sauke Mukarrama sannan suka wuce gida.

Suna shiga ana magrib, sallah suka fara gabatarwa sannan ta shiga kitchen abinci mafi sauk'i ta girka masu.

Bayan sun ci sun k'oshi ne suka gabatar da sallar isha sannan suka yi wanka suka kwanta.

(Ga wannan kuyi hak'uri dashi 4 breakfast, lolx)

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣7⃣/7⃣8⃣��

*BAYAN KWANA BIYU*

Tun safe suke shirye-shiryen tafiyar su Bk d'in saboda za su biya ta Jega gidan su Dr Shureim da Hakeem.

K'arfe tara dai-dai suka hau hanya. Gidan Hakeem suka fara sauka wanda sunyi murna da zuwan su sosai, kuma sun yi musu tarba wacce ta dace yaran su sai murna suke yi da y'an biyu ji suke yi tamkar a bar masu yaran.

"Kwanan nan fa muke batun kai maku ziyara sai ga shi kun riga mu kun kwashe ladar", cewar Hakeem.

"Wallahi za muje Bk ne ziyara shiyasa na ce ya kamata mu zo mu gaisa".

Hannun Musirrah Fateema ta rik'a suka wuce bedroom d'in ta, nan suka rik'a hira tana k'ara gaya mata dabarun zama da miji.

Kiran da suka ji mazan nai masu ne yasa suka fito.
      "Wai yaushe ne gulma za ta k'arewa Mata ne?, duk hira ba'a yin ta sai an shige uwar d'aka", cewar Hakeem.

"To yanzu ba ga shi kuma mun ba ku guri kun sa mu sake wa ba".

Hakan suka had'a masu goma ta arzik'i suna godiya suka wuce.

Gidan Dr Shureim suka je don ma basu dad'e sosai ba Bahijja da Lateefa sun tarye su yadda ya kama ta. Daga nan suka d'auki hanyar Bk.

Duk inda dangi suke an za ga su har gurin Gwaggon Umma sun je wanda tsufa ya kamata sosai.

Basma ce k'anwar Yasmeen ta mak'alewa Musirrah ce wa sai ta bisu ta rik'a rainon twin's.

Nan ta yi magana da Mus'ab kan cewa y'ar k'anen Abba za ta bi su me yace akai?

"Ba matsala tunda dama dole za mu ne mi mai renon su, saboda haka ta had'a kayan ta sai mu wuce da ita".

Da hakan suka wuce ta re da Basma y'ar kimanin shekara goma sha d'aya, sai murna take yi aranta saboda tana son yara sosai.

****

*BAYAN SHEKARA GOMA*

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda rasuwar dattijo mai kamala wato Baban Ammi, wanda ta shiga tashin hankali da jimamin rasa shi saboda shi kad'ai yayi mata saura, don kamin rasuwar shi da shekara ukku Gwaggo kulu ta rasu. Sai dai fatar Allah yajik'ansu da rahama.

6angaren su Jameel kuwa ya dawo da nasarori da dama acikin aikin da yaje, yanzu haka yaran shi uku.

****

Fa'ida ce tazo da saurin ta tana fad'in "Mum wallahi ga Fadila can tana dukan Baffa".

Mus'ab ne ya fita ya shiga tsakanin su.

"Haba Baby waya gaya maki ana dukan Baffa na?".

"Abbu shi ne fa yake tsokana ta akan jiya munje islamiya anyi karatu ban iya ba Malam ya dake ni".

"Haba Baffa na ita fa Antyn kace me yasa kake tsokanar ta?".

"Abbu fa kaduba duk girman ta wai bata iya suratul mulk ba, bayan ko gida Mum na koya mana".

"To kasan kowa da K'wak'walwa shi, kuma in kana mata dariya k'ok'arin ka zai koma na ta, kana son hakan?".

"Aah Abbu", da saurin shi ya amsa.

"To karik'a mata addu'a Allah yak'ara mata basira".

Juyawa yayi gurin little Mukarrama dake ta wasan ta da motar yara, cak ya d'auke ta yana duban ta.

"Kina ga su Anty na fad'a baki je kin gaya min ba ko?"

Cikin maganar ta da bata k'ware sosai ba take gaya mai in su Anty na fad'a kan ta ke ciwo.

Da mamaki yake kallon yarinyar saboda miskila ce ta K'arshe sam bata biyo halin mai sunan ta ba.

Haka ya tasa k'eyar yaran duka suka ko ma falo domin yin breakfast.

Shigar su ke da wuya suka tarar Musirrah ta gama jera komai, nan suka hau dinning table domin karyawa.

"Sai Ku shirya za'ayi birthday party na cika 10yrs d'in ku nan da sati d'aya, ana k'arewa sai auren Anty Basma".

Nan suka cukwiy-kuye shi suna murna had'e da furta "Alla ya bar mana kai Abbun mu".

"To ku matsa ku karya shi ku huta", cewar Musirrah.

Cikin sauri suka sake shi sai murmushi suke yi, wanda cikin sauri Baffa ya haura sama domin gaya wa Anty Basma.

****

*BAYAN KWANA BIYU*

Gwaggon Umma ce Allah ya yiwa rasuwa don ma ta yi yawancin rai.

A hanya ne Ammi da Umma zasu je gaisuwa had'e da Mama Baraka ko ince Haj Baraka don Mubarak ya kai ta Makkah, kuma ta yi auren ta da wani abokin Abba shekaru biyar da suka wuce.

Direba ne ya kusa kad'e wata tsohuwa dake jan jiki saman titi ba tada k'afa d'aya.

Umma ce ta fita domin bata hak'uri, had'a idon da suka yi ta zabura da k'arfi saboda ganin Haj karime, duk ta kod'e ta jeme sai warin datti da take yi.

Da sauri ta koma mota had'e da ba direba umurnin yaja suje, hannun da ta rik'a yi masu ne ya sa Ammi ta fita dai-dai matar na kawowa gurin motar.

"Don Allah da son ma'aiki ki gafar ta min Haj Zainab, na ga rayuwa iri-iri nasan hakk'in kune ke bibiya ta".

"Kwatan-kwacin yadda na yi maki nayiwa wata, ashe na ta sharrin ya fi nawa shi ne ta turamin y'an iskan gari suka kwashe komai dana mallaka kuma suka gundulemin k'afa d'aya".

Da ido Ammi ta bi Umma da kallo alamar tambaya.

"Haj Karime ce". Amsar da ta bata a tak'aice kenan.

Wani imani ne ya k'ara ratsa zuciyar Ammi, nan ta k'ara tabbatar da duniya ba bakin komai bace.

"Ki yafe mata Mmn Jameel, ko hakan ta ga jarabawa".

Dak'yar ta furta "Na yafe maki".

Ammi ce da Mama Baraka suka bata kud'i tana ta godiya har da guntun hawayen ta.

Hakan suka ja mota suka wuce, har suka kai suna tad'in rayuwar duniya.

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[9:14AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣9⃣/8⃣0⃣��

*BAYAN SATI D'AYA*

Yau ne ake ta shirye-shiryen birthday party na Fa'ida da Fadila murnar cikar su shekara goma.

Babban hall ne suka ka ma domin gudanar da party d'in inda abin ya had'a har da kakannin su.

6angare uku akayi nasu Umma daban, sannan su Mus'ab, sai na yaran.

Anko ne suka yi gwanin sha'awa, su Ammi wani Jan less suka saka Ummy, Umma, Ammi, Haj Maijidda da kuma Mama Baraka.
   Sai kuma Abba, Baffa, Alh Sani da kuma Alh Mu'azzam mijin Mama Baraka da suka saka wata bugaggar farar shadda.

Sai 6angaren su Musirrah da suka saka material kalar lemon green, Anty Rukayya, Musirrah, Iman, Mela, Mukarrama, Imtihal, Yusrah, Bahijja, Fateema, Lateefa sai Basma.
    Su ma Jameel, Mus'ab, Haydar, Nibras, Shureim, Sudais, Sultan da Hakeem suko voil kalar lemon green suka saka.

Sai 6angaren yaran suko kayan kanti ne suka saka, yaran mukarrama uku, na Iman biyu, Mela hud'u, Imtihal hud'u, Yusrah uku, Anty Rukayya biyar, sai su little Lateefa ita da k'annen ta da yaran Fateema.

Hakan suka cika hall d'in mak'il abin gwanin sha'awa, nan aka ci snacks da lemukka sannan su Fadila suka yanka kek.
   Haka suka bi iyayen suna saka masu kek d'in ana tafi raf-raf.

Saida suka k'are da iyayen suka ko ma kan kakannin su, cikin nishad'i suke abin su.

Baffa ne da Abba na k'arshen suna ka wowa gurin su suka yi rad'a nan suka d'ibi kek d'in za su kai bakin su sai suka kauce suka manna masu a hanci.
   Nan yaran suka d'auki shewa da tafi da dariya.

"Yau naji ja'iran yara, me ya hana ku yiwa iyayen ku sai mu da kuka rena?".
Haj Maijidda ce ke bambamin fad'a dasu.

"Granny kishi kike yi an yiwa su Baffa ba'a maki ba". Cewar Adal diyar Mukarrama, tana maganar ne ta nufo su gadan-gadan da cake a hannun ta.

Dak'uwar da Iman ta yi mata ne yasa ta ja birki tana dariya.

Da hakan akayi taro cikin farin ciki, walwala, nishad'i inda families d'in suka zamo abin alfahari.

"Abban twin's wai fa wannan taron duk yaran mu aka yiwa shi". Tana maganar ne had'e da guntuwar k'walla a idon ta.

"Ina tuna irin k'uncin da muka shiga a shekarun baya ni da Ammi da yaya Mubarak".

"Sanadin k'unci ai ya koma sanadin farin ciki, ko ba hakan ba?".

"Tabbas ka zamo linzamin farin ciki a rayuwa ta". Sai da ya faki idon mutane sannan ya saka halshe yana lashe hawayen da ke zubo mata.

*TAMMAT BI HAMDILLAH, INA GODIYA GA ALLAH DA YA NUNA MIN NA KAMMALA WANNAN LABARIN*

*KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE MIN*

*DA FATAR ZAKU YI AMFANI DA ABINDA KE CIKI MAI FA'IDA, KU YI WATSI DA AKASIN HAKAN*

Sadaukarwar ta kice Sister Sanah S. Matazu.
Allah yabar k'auna tsakanin mu.

Anty Maijidda Musa ba kina ba zai iya furta godiya zuwa gare ki ba sai dai in kwatanta saboda tsakanina dake sai Allah.

Ku ma ga taku gaisuwar

Anty Ybk
Ummu Abdul
Mmn Haneef
Umma ta Lubiee Mai Tafseer
Zainab (Autar Hjy)
M. Jabonation
Benaxir Omar

Yayye na ga gaisuwar ku.

Anty Innah
Mmn Waleeda
Anty Rukayya
Mmn Meerat
Mmn Abdulmalik
Mmn Ameer.

Three stars
Hindatu Jegal
Nafee Jegal
Aisha Jegal

Five stars
Assy Jegal
Sumee Jegal
Hauwa Jegal
Balkisu Jegal
Asmee Jegal

Yara manyan gobe
Halima
Maryam
Nana Khadija
Abduljalal
Allah ya sakawa rayuwar Ku albarka.

Y'an Uwa na jini
Sis Maryam (Mela)
Sis Atika (Atiks)
Ummu (Mmn Ja'afar)
K'awa ta gari, matsayin ki ba zai ta6a canjawa ba domin kin cancanci hakan.
Shema'u Bello Bari

Ban manta daku ba
Zainab Musa
Lawiza Musa.

K'anne na kaina
Yaha Saddik
Aisha Bizzy
Aisha Yagani
Yasmeeny.

Abokanen karatu na
Aminiya ta Haj Shafa
Saratu (Mrs Abdussalam)
Y'ar gidan Ango.

Naku matsayi na daban ne

Zarah B~B
Hindatu Shehu
Bungud'u
Bebeelo
Zeitunerh Mrs Dr Moh
Mmn Amatullah
Umamat
Mrs Jawaheer
Mumcy na Rabeaht A Danbappah
Mumcy Rabeaht Husain
Mum Faty
Princess Meenat
Blkisu Blymnu
Fati Salihu
Aunty Sis
Aneesa Abubakar Rimi (Anee)
Nana Diso
Deeja Abdul

Kuna raina har kullum

Mmn Shakur
Khairat
Miss Hafcy
Mmn Xeenert
Jamila Moh Ali
Ummietta Wabi
Fatyn Idiriss
Madelty
Ag
Phareederh yahaya
Maryam Yusuf
Ummu Affan
Mrs M. Bawa
Mas'uda (Mmn Walida)
Habiba Yayaji
Ummen Al'amein
Farzana
Maryama
Jidda jangade
Sophy MD
Shatoo Mammaga
Laurat (Mrs Zubair)
Shamseea
Hafsa D
Jidda A.K.A
Innah Habiba
Ameera Maisikeli
Khadija Manga
Mmn Ansar
Mmn Aslam
Nafisa Alu
Maryam G
Mmn Mamee
Ummulkhulthum
Fatima
Mmn Ja'afar
Yaseera

*SDY JEGAL NOVELS*
*M. JABO MUMBARIN NOVELS*
*MUSHA KARATU*
*ZAUREN KARATU*
*ZUMUNCI GROUP*
*GREATEST WOMEN*
*MUM FATY FAN'S*
*ZARAH B~B FAN'S*
*NWA* *KU NA DABAN NE*��

*SDY JEGAL KE GAIDA DUK MASOYAN TA WA'ANDA TA SANI DAMA WA'ANDA BATA SANI BA*

*NA YI K'OK'ARIN SAKA SUNAYEN KU DUKA SAI DAI HAKAN BAI SAMU BA SABODA YAWAN KU, DA FATAR DUK WANDA BAIJI SUNAN SHI BA ZAI YI HAK'URI KUMA YA YIWA Y'AR MUTAN JEGA UXURI*

*NA GAIDA KOWA DA KOWA KYAUTA*��

*SAI KUN JINI A WANI SABON NOVEL NAWA MAI SUNA.........*

*SDY JEGAL*��

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.

No comments:

Post a Comment