Tuesday 18 October 2016

BAHIJJA 105-115

[8:24PM, 10/17/2016] Sis  Hauwa: �� *BAHIJJA* *105*- *110*��


Koda aka je da ita asibiti duk bata San in da take ba, nan suka yi aune-aunen su Dr Musa yace gaskiya sai an fita da ita Dubai.
Nan take Dad yasa aka yi biza uku ta tafiya, da malam salisu ya Gan ta sai da yayi kuka sosai, yace lallai tabbas rayuwar duniya ba bakin komai bace.
KO kamin su wuce Dubai sai da yaje gidan su Lateefa tak'i Bari ya Gan ta ta shige d'aki ta rufe, abin har ya Fara bama Umma haushi tace ma Shureim ya je kawai ya k'yale ta.
Hakan suka d'unguma da Gwaggo sai Dubai, har suka shigo k'asar Bahijja kuka take yi saboda tausayin halin da Gwaggo take ciki,  nan Shureim ya Kama musu d'aki biyu su d'aya Baban Bahijja d'aya.
Bayan ya ajiye su masauki ne aka wuce da Gwaggo asibiti, bayan gwaje-gwajen su suka ce dole d'ayar k'afar wadda k'wauron ta ya tartse sai an yanke ta, d'ayar kuma za ayi Mata d'orin kariya na asibiti, hakan Shureim ya yi duk abinda ya Kama ta sannan ya koma masauki saboda baije da Bahijja ba akan kukan da take yi.

**********   ********

Yau kwanan su Bahijja uku da tafiya Mum ta shirya taje gidan su Lateefa.
Tana shiga suka gaisa da Umma tace gani nazo bikon y'ata.
Umma tayi murmushi tace ke kike wahalda kan ki akan wannan sha-sha-shar kawai Ku saka Mata ido har ranar da duniya ta yimata fad'a.
Mum tace ai ba ayi haka ba, suna maganar ne Shema'u ta kawo ma Mum kayan motsa baki, bayan ta ajiye ta durk'usa ta gaida ta.
Mum ta amsa tace shiga ciki ki Kira min Lateefa.
Suna cikin hira ne sai ga Lateefa ta iso nan ta gaida Mum ba yabo ba fallasa.
Mum tayi murmushin su na manya tace Lateefa har yanzu ba agama fushi Dani ba?
Nan ta had'e rai tayi shiru bata ce komai ba.
Mum tace Lateefa kiyi hak'uri shi aure nufi ne na Allah, kuma wannan matar kinsan ba Shureim ya furta cewa zai aure ta ba Dad d'in Ku ne ya yi wannan had'in, kiyi hak'uri ki bar ma Allah kuma kinsan waye Bahijja bata da matsalar zama kiyi hak'uri kinji y'ata.
Tace to shikenan Mum sai na shirya Zan koma.

****  ****  ****  ****

A can Dubai kuma an yi aiki cikin nasara saura jiran shan magani da sauran warkewar Gwaggo.
Kullum da safe zasu je su duba jikin Gwaggo sai marece su koma masaukin su.
Kullum Bahijja kesa towel ruwa ta shafe ma Gwaggo jikin ta, sannan ta zauna ta rik'a ba ta abinci.
Koda Shureim ya dawo daga masallaci ya taradda Bahijja na sallah, bayan ta idar ne suka zauna suka ci abinci suna k'arasawa yakai duban shi zuwa Gare ta yace Sister shine ba ko sanarwa.
Fahimtar inda ya dosa yasa ta soke kan ta.
Yace na kusa fitar da wannan kunya taki saboda tana takura min.
Nan tayi murmushi tace yaya ka Kira Anty Lateefa?
Yace Antyn ki bata sauko ba har yanzu tana fushi kin k'wace Mata sankacecen saurayi.
Nan take ta zare ido dai-dai ya tada kan shi sai suka had'a ido ita ko ta sunne kan ta tana murmushi.
Hakan ya taso ya rik'a hannun ta ya mik'ar da ita ya yi mata rad'a cikin kunne, da sauri ta fizge hannun ta tayi cikin d'aki.
Yana shiga yace taje tayi alwala zasu yi sallah, hakan tayo alwala sai gaban ta ke dukan uku-uku.
Bayan sun gama ya yi Mata tambayoyin da suka shafi addini kuma tana da ilmin ta gwargwado.
Hakan taje tayi wanka ta feshe jikin ta da turare, shima hakan.
Suna kwanta wa ya Jan yota saman k'irgin shi ya yi Mata kyakkyawar runguma ya ja masu bargo.
(Nidai Jegal nace Allah ya bada d'an Dubai, *LOLX*)

~~~~~~~~~~
~~~~~~~~~~

*WASHE* *GARI*

Yana tashi daga bacci yaje yayi wanka sai da yayi sallah sannan ya had'a ruwa masu d'imi yazo ya yaye bargon da ta rufa dashi ya sunkuce ta sai toilet.
Shi ya yi Mata wanka ya gasa ta, tana cewa nidai yaya banaso tana soke Kai.
Sai da ya gama sannan ya d'auko ta ya nad'e cikin towel ya ajiye ta ya d'an fita.
Ko kamin ya dawo ta lalla6a tayi sallah har ta shirya.
Ashe gurin Baban ta ya shiga suka d'an ta6a hira saboda k'a idar asibitin da aka Kai Gwaggo Mai jinya bai kwana can.
Yana shigowa ya iso ya zauna gefen gado yakai dubanshi zuwa Gare ta sai kuma ya Jan yota ya Kai Mata kiss ita ko duk kunya ta ishe ta.
Yace Heeja Ina son in yi maki wata tambaya d'aya.
Tace Ina jin ka yaya, tana Mai Kai duban ta zuwa gare shi.
Yace ya akayi na same ki budurwa bayan kuma kin yi aure sama da shekara biyu sannan Allah ya kar6i ran margyayi?
Nan idon ta suka yi rau-rau tamkar ta yi kuka.
Ya k'ara Jan yota saman jikin shi yana bubbuga bayan ta cikin rarrashi yace kar kiyi kuka.
Tace ka bari in mun yi breakfast mun je dubo jikin Gwaggo mun dawo Zan gayama.
Ba hakan yaso ba saboda ya matsu yaji ya akayi hakan ta kasance, sai dai baison takura ta.

(Nima dai na matsu in ji yadda hakan ta kasance����)


© *SDY* *JEGAL*
[8:24PM, 10/17/2016] Sis  Hauwa: �� *BAHIJJA* *110*- *115*��

Tana d'akin ta Shema'u k'anwar ta ta shigo tace Anty kin yi bak'i.
Tace daga Ina, nifa banson takura wallahi.
Ta ce Mata inaga kamar wannan mak'ociyar ki.
Tace to ki shigo dasu, nan ta fita ta shigo dasu.
Suna shigowa taga cewa maman Zahra ce da Mum zee, nan ta tashi ta taryo su cikin murnar ta da sakin fuskar ta.
Nan Shema'u ta kawo musu kayan motsa baki da abinci.
Bayan sun gaisa Mmn Zahra tace shikenan kin gujemu ko waiwaye babu.
Tayi murmushi tace ba gamu tare ba yanzu, kuma muna waya.
Mum zee tace wallahi baki kyauta ba wa yace maki ana tashi gidan miji saboda kishiya, shifa lamarin duniya sauk'i Gare shi sai Wanda ya wahalda kanshi.
Kuma kishiya abokiyar zama ce don wani lokaci zaka ci amfanin ta itama zata ci naki.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa har fa kullum kina yabon halayen Bahijja kuma kin fad'a da kan ki cewa kullum kina yi Mata addu'a Allah ya bata miji nagari.
In kin manta in tuna maki har cewa kika yi da kina da d'an Uwa namiji da kinsa ya aure ta.
Me yasa ba zaki yarda cewa mijin ki shine mafi alkhairi a gareta ba.
Yanzu mum zee ba zata zama ishara gareki kisan cewa ba duka aka taru aka zamo d'aya ba, gasunan suna zaman su lafiya tamkar ya da k'anwa.
Nan Lateefa ta saukar da wata nauyayyar ajiyar zuciya, tace nifa kar kuga abinda ke tayar min da hankali tamkar Amarya ta shigo cikin gida ta nemi fitar da uwargida.
Wata ma in kina da yara zata nemi hanyar da zata bi ta wulak'antar da su ga ubansu.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa yarda kika San amare da tasu matsalar to ko uwayen gida suna da tasu matsalar, saboda wata uwargida ba zata fitar da Amarya ba amma wallahi zata yi silar wulak'anta ta yarda ko y'ar aiki zata fita daraja, ke dai kawai muyi fatar Allah yadatar damu da kiyoshi na gari masu zuciyar imani.
Mum zee ta kar6a da ameen tana Mai cewa kuma gaskiya kinga wani lokaci uwayen gida Nada tasu matsala.
Abu na farko zaki ga wata da zarar ance za ayi Mata kishiya to zaki ga ta Fara hauka tana sakin maganganu da zasu fita har sukai ga kunnen amarya kinga girma ya fad'i.
Abu na biyu azo ayi aure uwargida ta k'i kama girman ta, shima hakan na kawo raini tsakanin zama saboda kin sake taga makwancin ki.
Amma gaskiya muddin kika rik'e girman ki koda Amarya ta shigo bazata raina kiba kuma in kin dace da tsayayyen miji saboda ko su da tasu matsala.
Mmn Zahra tace yanzu miye ribar ki kinfita kinbar gida, kuma hakan bai hana auren ba don yanzu haka suna Dubai shida Amarya, kinga kuwa kin d'aga musu k'afa susha amarcin su hankali kwance.
Nan tashin hankalin Lateefa ya k'aru saboda batasan sunyi tafiyar ba, Umma ta hana agaya Mata saboda ko y'an gidan ta rage mu'amala dasu ko yaushe tana d'aki.
Nan take ta mik'e ta lalabo layin ta data d'ebe ta saka shi a waya saiga text message d'in shi na shigowa na ban hak'uri, sai ga wasu zafafan hawaye na sauko wa daga idon ta na tausayin kan ta.
Nan dai suka rarrashe ta har ta sauko kuma tayi masu alk'awari zata ba Kimba mamaki don zai dawo ya taradda ita d'akin ta.

*******************

A can Dubai kuma su Shureim sun shirya sai asibiti domin su duba jikin Gwaggo.
Suna shiga Bahijja ta had'a Mata tea Mai kauri tasha sannan ta jik'a towel ta shafe Mata jikin ta.
Nan Gwaggo ta rik'a kuka tana cewa y'ar Baba ki yafemin na cuce ki na zalunce ki yanzu gashi dake da mijin ki ke wahala dani.
Malam yace ki daina wannan kukan bayada fa'ida.
Tace malam dole in yi kuka nan ta rik'a zayyano irin cutar da ta rik'a yima Bahijja har zuwa yanzu data so 6atar da ita Allah ya nuna Mata abinta.
Ta d'ora da cewa ko mahaifiyar ta nice nayi silar zuwan ta barzahu, saboda ciwon ta na tashi malam ya fita kasuwa ni na saka filo na danne ta saida ta daina numfashi.
Nan Bahijja ta fad'i sume, malam ko yayi mutuwar tsaye inda Shureim ya bita da kallon tsana ji yake yi tamkar ya k'arasa gundule k'afar ta d'aya.
Sannan ya durk'usa yana jijjiga Bahijja da k'arfi yace _Heeja_.


© *SDY* *JEGAL*

BAHIJJA 95-110

[8:24PM, 10/17/2016] Sis  Hauwa: �� *BAHIJJA* *95*- *100*��

Lateefa ta shirya ta dawo falo tana jiran shi, yana fitowa suka wuce, saboda zai sauke ta gidan su Muftah shiko zai wuce wurin d'aurin aure.
An d'aura auren *MUFTAH* da matar shi *BILKISU* *BILYAMIN* sai dai fatar zaman lafiya tsakanin su.
Sai zuwa dare da aka Kai Amarya Shureim ya rako ango sannan ya wuce da Lateefa.
Nan yake yiwa Muftah sharri kan cewa sai sun zo barka nan da wata tara, saboda naga zumud'in naka yayi yawa.

********   *********

Yau tun safe Lateefa ke Kai kawo a gidan, tana ba Bizzy umurnin abinda zata dafa.
Can ta shiga d'akin Shureim yace wai yau me ya hana ki zama haka?
Tace ka manta na gaya ma Sis zata zo muna yini yau.
Yace OK shine kike ta rawar Kai haka, ni na zata daga wata k'asa za kiyi bak'i, saboda naga wataran baki tashi daga bacci sai k'arfe goma, amma yau kece da tashi tun takwas.
Tayi murmushi tace Kimba wallahi Ina ji da Sis Bahijja ne tamkar k'anwata Shema'u, naga Kai ko tausaya Mata baka yi.
Nan yayi murmushi yace asha aiki lafiya, koda bak'uwar taki ma sai dai taci girkin y'ar aiki ya bita da gwalo.
Gane cewa tsokana yake ji yasa ta k'yale shi ta shiga wanka.
Koda ta fito ta shirya sai ta dawo falo ta zauna, bata fi minti goma da zama ba sai ga Bahijja ta iso ita da k'awar ta Yagani.
Hakan ta shek'o ta rungume Bahijja sai murna take yi, tace ma Yagani bismillah zauna mana.
Hakan suka zauna tasa Bizzy ta cika masu wuri da kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe.
Suna zaune suna hira ne sai ga Shureim ya fito cikin shiga ta alfarma, ya saka k'ananan kaya ga sajen shi ya kwanta luf, ya had'u iya had'uwa ga kwarjini da ya cika fuskar shi.
Nan Bahijja ta durk'usa har k'asa tace yaya ina wuni.
Ya amsa da k'alau ya d'ora da cewa ya karatun, ya kuka baro Mum?
Tace k'alau Alhmdulillah.
Nan ma Yagani ta gaida shi, ya amsa yace to akula da karatun.
Nan yakai duban shi ga Lateefa yace to ni zan fita, nan ta rakashi sai da ya tada mota sannan ta dawo.
Bayan su Bahijja sun ci iya abin da zasu ci, nan ta jasu har bedroom d'in ta suna ta hira, Lateefa tace yaushe zaku gama karatun?
Tace nan da shekara guda.
Jin kiran azzahar ne yasa suka tashi domin sauke farali.
Bayan sun gama sallah ne Bahijja ta shiga kicin ita da Yagani ta had'a masu abincin dare, sannan suka kimtsa zuwa tafiya gida.
Lateefa tace kiyi hak'uri Kimba ya dawo sai ya sauke Ku nima inaso in bishi in gaida Mum.
Da k'yar ta samu suka zauna, sai da Shureim ya dawo yaci abinci yayi wanka ya canza kaya yayi shigar manyan kaya.
Nan ya kwashe su suka wuce, Yagani ya fara saukewa Lateefa ta bata ledar kayan Shafa tayi godiya sannan suka wuce gida.
Nan suka zauna gurin Mum suna ta hira sai daga baya suka wuce.

**********   **********

```BAYAN``` ```SHEKARA``` ```D'AYA```

Yau ne Bahijja suka gama exam d'in su ta k'are health, daka dube su zaka San cewa suna cikin farin ciki.
Bayan fitowar su da kar6ar address d'in juna kowa ya Kama gaban shi.
Hakan kowa yaje gida cikin farin ciki da murna.

_BAYAN_ _KWANA_ _UKU_

Kamar yadda suka yi alk'awari da Mum kan cewa in ta gama karatu yazo ya wuce da ita.
Hakan yasa yau malam ya zo domin zuwa da Bahijja gida, koda yazo ya taradda Baban margyayi ma yazo hakan suka zauna aka tattauna rayuwar yau da kullum.
Cikin hakan ne Dad yace malam salisu Zan k'ara Neman wata alfarma Karo na biyu zuwa gare ka.
Malam yace haba Alhj wace irin alfarma ce wannan, na gaya ma babu shamaki tsakanin mu.
Ya yi murmushi yace d'an ka Shureim zaka bawa Bahijja aure.
Baban margyayi yace Alhj ya akayi kasan abinda ke cikin zuciya ta, dama wannan maganar ce ta kawo ni.
Nan dai suka yi maganar aka aje d'aurin aure sati guda masu zuwa.
Malam yace to zai je da Bahijja gida sai ranar alhamis zata dawo.
Hakan suka d'ungu ma sai Kimba, saida suka sauka malam yake gayama Bahijja meke faruwa.
Tace Baba don Allah ka taimakeni Ku janye wannan maganar, bazan iya auren Yya Shureim ba, innayi hakan na yaudari Anty Lateefa.
Yace kiyi hak'uri y'ar Baba ba yin kaina bane, kuma kinsan mutanen nan sunfi k'arfin komai a wurin mu.
Gwaggo tace kiyi hak'uri shi aure nufi ne na ubangiji, nan suka rarrashe ta sannan ta tashi ta koma d'aki.
Tana shiga d'aki ta fasa kuka maicin rai, tace mutuwa Mai yankan k'auna, yanzu da wane ido Zan kalli Anty Lateefa naje Mata matsayin kishiya.
Tana cikin tunanin ne taji Gwaggo saman kan ta, tace shegiya mayya kin lashe musu yaro ya mutu yanzu kin koma ga d'an cikin su.
To wallahi Bari in gaya maki ko Zan tafi tsira ra ba zaki aure shi ba, makwad'aiciya Mai idon cin nera ta Kai Mata rank'washi sannan ta fita.

Bayan taje ziyara dangin innar ta, kuma taje gidan su margyari har gidan lantana sai da taje.
Yau Mum ta turo direba ya koma da Bahijja, sannan tasa aka d'auko Mata Lateefa.
Nan ta had'a su tana yi masu nasiha sannan ta furta ma Lateefa abinda ke faruwa.
Dama an gaya ma Shureim ya amsa ba yabo ba fallasa sai dai fargabar had'uwar shi da Lateefa.
Lateefa ta bi Mum da ido tace bangane ba.
Mum tace saura kwana biyu auren Shureim da Bahijja.
Idon sun k'ank'ance ta bud'a baki zata yi magana kome ta tuna, sai ta zabura ta nufi hanya tamkar zararra.
Mum na kiran ta ko waiwayo ta bata yiba da saurin ta tafita daga gidan.
Bahijja ta rik'a kuka maicin rai tace Mum kiyi hak'uri ki janye maganar nan, kin ga Lateefa ba zata ji dad'i ba.
Mum tace mu mukasan dalilin wannan had'in, in kema zaki bijiremin ne kamar yada Lateefa ta yimin to bisimillah, ta tashi ta wuce d'akin ta tabar Bahijja nan.

Yau ne mutane suka shaida auren
_SHUREIM_ _SULEIMAN_
              *DA*
_BAHIJJA_ _SALISU_
A garin Kimba, Allah ya basu zaman lafiya.

(Masoyan Bahijja Ku fito Ku taya ta zaman kishi da Lateefa, _lolx_)


© *SDY* *JEGAL*
[8:24PM, 10/17/2016] Sis  Hauwa: �� *BAHIJJA* *100*- *105*��

Duk mutanen k'auyen Kimba sun shirya an yi mota uku har da dangin innar Bahijja sun nufi jega gurin auren Bahijja.
Amma koda aka yima Gwaggo magana kan a shirya sai tace su tafi zata zo daga baya sai ta kar6oma d'iyar ta wasu abubuwa.
Bayan sun wuce Gwaggo tayi gurin bokan ta, tace boka d'an dugaji na rasa ya Zan yi da wannan shegiyar yarinya nidai yanzu na yarda akashe ta ko a 6atar da ita.
Hhhhhhhh dama tun farko nace ki bari ayi hakan kika k'i, amma yanzu tunda kin amince Zan baki wasu ruwa ki k'ok'ar ta kamin a fita da ita zuwa gidan mijin ki saka Mata su cikin ruwan wanka, hakan zai yi sanadiyyar 6acewar ta har abada.
Da sauri ta tari mota tayi sa'a da saura mutum guda ta fad'a suka kama hanya.
Har sun kusa isowa jega wata babbar mota tabi ta kan motar su, nan aka kwashe su sai asibiti wasu sun rasu, wasu kuma sun ji rauni.

*********   ***********

Lateefa na shiga gida ta fad'a saman jikin mamar ta sai kuka take yi.
Umma tace lafiyar ki kuwa, wa ya rasu?
Da k'yar tayi shiru ta gaya ma Umma meke faruwa.
Nan Umma taja dogon tsaki tace in zai yi aure shine me, dama cewa aka yi dake kad'ai zai zauna sha-sha-shar banza da wofi.
Kuma ni hakan yayi min dai-dai sai shegen kishi amma bakisan ya zaki gyra tumbin mijin ki ba, dama nasan hakan zai faru komi dad'ewa.
Tana cikin yi Mata fad'an ne sai ga Abban ta ya sauko nan yake tambayar meke faruwa.
Umma ta yi Mai bayani nan ya Fara fad'a yace Lateefa ta tashi ta shiga dakin ta, ya d'ora da cewa ba inda zata je yaje ya zauna da amaryar shi.
Umma ta Kai duban ta zuwa gare shi tace ina fatar ba kashe ma y'ar ka aure zaka yi ba, gaskiya kana nuna ma yarinyar nan gatan da bai dace ba.
Yace ko ke da kika haife ta nace Zan yima kishiya sai anga tashin hankali ballan tana ita, ai kishi a jinin Ku yake.
Nan ya sa Kai ya fice yana ta faman fad'a.

**********   ***********

Can gidan su Shureim kuwa an ji Gwaggo shiru kuma ba waya take da ita ba har k'arfe goma bata zoba sai kawai aka yanke hukuncin aje akai amarya d'akin ta k'ila gwagg ta fasa tahowa.
Hakan aka d'unguma Kai amarya, ciki kuwa har da Blkisu matar Muftah su lantana da Hindatu k'anwar margyayi.
Nan dai aka yi Mata hud'uba kowa ya wuce sai Blkisu da Aisha Yagani.
Sai k'arfe goma sha d'aya ango ya shigo shi da Muftah nan ya had'asu ya k'ara yi masu nasiha kan hakk'in miji akan matar shi da kuma hakk'in Mata akan mijin ta.
Bayan yayi addu'ar zaman lafiya ya sa matar shi gaba, Shureim yace su sauke Yagani gida, bayan sun wuce ya rufe gida ya dawo ya taradda Bahijja ta wuce d'aki.
Part d'in shi ya wuce ya watsa ruwa yasa kaya marar nauyi sannan ya fito ya d'auki kayan da ya shigo dasu ya shiga d'akin Bahijja.
Koda ya shiga tayi wanka ta saka kayan bacci, nan ya aji ye kayan yaje kicin ya d'auko plate da cups ya dawo d'akin, ya zuba komai yace ta sauko suci.
Cikin sanyin muryar ta tace yaya na k'oshi.
Yace ki sauko kici ko kad'an ne, ganin cewa bata iya yimai gardama yasa ta sauko, kuma tun fil azal nauyin shi take ji sosai.
Hakan suka ci suka k'oshi, sannan ya umurce ta da ta tashi tayi alwala suyi nafila.
Nan ta rik'a soke Kai ta kasa magana, jin ya maimaita maganar ne yasa ta furta period take.
Hakan yaji ba dad'i duk da bai k'udurta ma ranshi wata doguwar mu'amala tsakanin su.
Hakan suka kwanta saman shimfid'a guda ya janyo ta ya manna saman k'irjin shi.

*********   ************

Lateefa kuwa tana gidan su sai juyi take yi saman gado zuciyar ta tamkar zata k'one saboda suya.
Anyi-anyi ta koma d'akin ta tace Sam ita ta gama da Kimba don bazata iya had'a shimfid'a da shiba yaje ya had'a da wata ba.
Ko su Anty Nafeesa sun zo auren Shureim duk yada ake bada baki sun bata kan ta koma d'akin ta amma Abu ya faskara.
Daga baya ma munafukai ta rik'a ce musu tana cewa har da kwaso jiki suzo aure don za ayi Mata kishiya, kuma kishiyar ma data rik'a tamkar k'anwar ta shema.
Anty Nafeesa tayi murmushi tace koda auren ki ko babu dole muje ma Mum auren Shureim.
Duk yada ake bada baki Shureim ya yi amma tak'i sauraren shi, ko ya Kira waya bata d'auka, yayi text message har ya gaji ba reply.
Kuma ko yazo gidan su data jishi take rufe k'ofar ta.
Shi kuma Abban ta yace ba zai takura taba abar ta sai ranar da ta sauko da kan ta.

Yau da safe aka yi bincike Gwaggo bata Kimba bata Jega nan hankalin mutane ya tashi kan rashin takamemen ina take.
Shureim na breakfast shi da Bahijja yana tsokanar ta sama-sama kan cewa abinci ne bata ci sosai shiyasa tak'i yin k'iba.
Ita ko sai murmushi take yi tana soke Kai, cikin hakan ne wayar Shureim ta hau ruri koda ya duba Dad ne ya Kira shi.
Bayan ya d'auka suka gaisa yake ce Mai yayi sauri yazo yana Neman shi sai ya kashe wayar.
Gaggauce ya gama breakfast ya d'auki key d'in mota har ya Kai k'ofar fita daga falon ya waiwayo idon su suka had'e sai ta soke Kai tana murmushi.
Yace Mata dubo kigani, tana tayar da kan ta ya yima hannun shi kiss ya hura Mata iska ya wuce.
Cikin ran ta tace Ashe haka yaya yake da dad'in zama.
Yana shiga ya gaida iyayen shi, nan aka Kora Mai abinda ke faruwa take ya Kira Muftah yace ya bincika Mai asibiti koda akwai masu hatsari, hakan ya Kira sauran doctors na asibitoci da dama yana basu cigiya.
Ba afi minti goma ba sai ga kiran Muftah yace Mai akwai su nan asibitin su kuma ance akwai y'an Kimba ciki.
Nan suka d'unguma shi da Mum da Dad sai asibitin, cikin bincike ne aka gano cewa tana cikin masu rai sai dai k'afar ta d'aya ta karye d'ayar kuma k'ashin k'wauron ta duk ya tartse fuskar ta duk taji rauni.
Nan Dad ya Kira direba yace yaje Kimba yazo da Baban Bahijja, shiko Shureim ya Kira wani friend d'in shi asibitin F.M.C Birnin kebbi kan cewa yanzu zai turo gwaggon shi aduba ta.

(Fan's na gode sosai da kulawar ku, wasu sun Kira sun yimin ta'aziya, wasu sun yimin ta p/chart, wasu ta groups na gode sosai Allah ya bada lada.)

© *SDY* *JEGAL*

Monday 17 October 2016

SANADIN KUNCI 71-80

[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 7⃣1⃣/7⃣2⃣��

*BAYAN SATI UKU*

An sallamo Umma daga asibiti kuma ta samu sauk'i alhmdulillah, je kaga zama tsakanin ta da Ammi tamkar su had'iye juna idan ka gansu ba za ka ta6a cewa sunyi zaman rashin fahimta a baya ba abin gwanin ban sha'awa don ko yaran su in har ba ka sani bane ba za ka tantance yaran Umma da Ammi ba.

****

6angaren Haydar kuwa manya sunje gidan su Mela har an saka lokacin aure wata biyu masu zuwa, inda suke gina soyayyar su cikin jin dad'i da walwala tamkar su had'iye junan su.

****

Yau ne Ammi ke ta hada-hadar zuwa Bk domin ta dubo tsohon ta, inda suka yi aje kan ce wa Mubarak zai bi ta domin maganar shi da Mama Baraka.

Hakan suka shirya sai Bk inda ta tarar da Baban ta cikin k'oshin lafiya sai abinda ba za'a rasa ba na tsufa.

Bayan sun huta ne Ammi ta shirya duk ta kaiwa dangin Abban su Mubarak ziyara, sannan ta wuce gidan kakar ta Gwaggo kulu wadda tsufa ya ka ma ta sosai, irin kulawa da taimakon da Ammi ke yi mata su ke saka ta k'ara nadamar abubuwan da ta yi mata a shekarun baya.

"Haba Gwaggo kar ki da mu kan ki ni wallahi komai ya wuce a guri na, da ma a rayuwa ta ba na kwana da ko wa a zuciya ta, ko yanzu na so in mayar da ke guri na da zama don kin nuna min kin fison zama nan ne shiyasa na k'yale ki, amma duk da hakan zan sa mu wadda za ta rik'a kulawa dake ina biyan ta".

Nan ta yita sakawa Ammi albarka da jin dad'in abinda take mata.

Fitar su daga gidan basu za me ko ina ba sai gidan su Mama Baraka, da murnar ta ta tarye su ta ma rasa ina za ta saka su kan dad'i.

"Mubarak ashe da gaske za ka kawomin ziyara wataran".

"Haba Mama ta yaya zan manta dake a rayuwa ta, ko yanzu tahowa nayi in gaya maki ki had'a kayan ki nan da kwana biyu za mu wuce sokoto".

"Anya hakan na yuyuwa Mubarak?, ko hakan na gode da kulawar ku gare ni sosai Allah ya saka da khairan".

Rufe bakin ta kenan k'anen ta na shigowa gidan, bayan sun gaisa da su Ammi ne Mubarak ya sako buk'atar tafiya da Baraka.

"Gaskiya a duniya banda ko wa bayan ita, bazan iya bari kuje da ita ba, zan dai yi maku alfarma d'aya in har Allah ya horemin na mota to zansa aka wo maku ita tayi maku kwana biyu".

Je kaga damuwa k'arara a fuskar Mubarak, saboda gaskiya yana jin Mama Baraka tamkar Ammi a ranshi, bazai ta6a manta yadda ta taimaka masu ba abu d'aya yake so yagan ta a tare dasu.

Tamkar walk'iya haka ta fad'o d'akin cikin kissa da kisisina ta fara magana.

"Haba maigida ai ko Annabi so ya gode wa, kabar ta ta bi su mana mu in mun sa mu lokaci sai mu rik'a kai mata ziyara, kuma a yanda na fahimci maganganun su ai Bk tamkar gida ce a gare su nasan za ta samu lokacin ka wo muna ziyara ko Anty?".

Duk da ta fahimci cikin kissa ne take maganar duk da shi k'anen na ta bai fahimci komai ba a maganar matar shi to ita ta fahimci inda ta sa gaba.

Saboda da ma ba son zama da ita take yi ba kawai don bata sa mu fuska ga maigidan bane shiyasa take danne wasu abubuwan.

Bata San ce wa har ga Allah ta fi son tabi su Ammi ba, ba akan komai ba sai don samun kwanciyar hankalin ta kuma tasan ce wa ba za su ta6a wulak'anta ta ba domin sun san darajar ta.
   Kawai bata so ta nuna tana son binsu ne k'anen na ta yaga bata damu dashi ba, ko yaga ce wa don ta ga masu kud'i ne za ta guje su.

"Shikenan ba matsala sai ta shirya kayan ta in za su wuce suje da ita, amma don Allah yaya kar ki guje mu in da ma ta samu ki rik'a kawo mana ziyara".

"Kakka da mu insha Allah duk k'arshen wata zan rik'a kawo ta, kuma za ku rik'a gaisawa a waya", cewar Mubarak.

Akan murnar an bar shi yaje da Mama Baraka dubu goma ya fitar ya bawa k'anen nata.
    Shi ko je kaga murna gurin shi shi da matar shi sai godiya suke zabgawa, da hakan suka wuce kan ce wa in zasu wuce za su zo suje da ita.

****

Gama breakfast d'in su ke da wuya ta zura da gudu sai toilet, amai ne take lezayawa tamkar za ta had'o da hanjin ta.
    Cikin tashin hankali ya mara mata baya ya tallafo ta sai sannu yake zabga mata, wanda da taimakon shi ta wanke bakin ta had'e da fuskar ta.

Suna dawowa falon ta k'ara wani yunk'uri na amai, tallafo ta d'in da zai yi su koma toilet ta ke ta wanke shi tsaf da wani aman, hakan ya kai ta toilet sai da ya yi mata wanka ya gyara ta sannan ya yi wanka ya shirya suka wuce asibiti.

Awon farko da aka yi mata ya nuna ce wa tana d'auke da ciki na sati uku wanda Mus'ab ya shiga farin ciki sosai, tun asibitin ya rink'a kiran y'an uwa yana gaya masu abin farin cikin da ya sa me su.

Sai dai abu d'aya ke damun shi irin yadda amai ke da munta cikin yini d'aya duk ta zabge tamkar wacce ta yi ciwon sati d'aya.

****

Bayan su Mubarak sun d'auki Mama Baraka ne suka doshi hanyar sokoto, da saukar su ne Haj Maryam ta kar6i mama Baraka da hannun biyu har tana furta ce wa a part d'in ta za ta sauka.

"Duk dai abinki da na yi aure zan d'auke Mama ta".

"Je can tuzuru dakai ka yi kwantai za ka wani ce gidan ka za'a zauna, to bara sai ka k'are ruwan idon na ka".

"Amma ko gaskiya Haj kin gama da yaya, in kika ga matar da zai aura sai kin yi mamaki", ce war Mukarrama.

"Ke gafara can aku, gurin surutu ba'a barki ba ya ba, ke ina na ki mijin yake?".

"Ai ko yau d'innan za ki gan shi, don ca nayi yabari sai yaya Mubarak ya dawo sannan yazo gaida shi", tana maganar da murmushi a fuskar ta.

Da hakan ko wa ya wuce part d'in shi, har Umma ta yi murna da zuwan Mama Baraka.

****

*BAYAN SATI BIYU*

Soyayya ta k'ullu tsakanin Mukarrama da Nibras, sai kuma Mubarak da Imtihal d'iyar Haj Maijidda wanda Ammi ta fi ko wa jin dad'in wannan zumuncin da suka k'ulla tsakanin su, sai kuma Iman da Sudais abokin Haydar, fata d'aya Allah ya nuna mana lokaci musha shagali.

****

"Ni fa wannan cikin ya fara da muna kullum cikin ciwo da k'arin ruwa, duba kaga yanda duk ta zabge tamkar wacce ta shekara kwance tana jinya".
   Mus'ab ne ke ta yiwa Dr Shureim mi ta kan drip d'in da za'a sakawa Musirrah.

"Abin fa sai da hak'uri saboda duk mata hakan suke ta wahala wani lokaci sai cikin ya yi k'wari za kaga sun rage laulayin".

"Gaskiya ina ganin Hayatee ta fi ko wa wahala ji fa yanda komai taci sai ta mayar dashi".

"Kai dai na tane kasani shiyasa".

Hakan dai ya saka mata drip d'in yana mai luradda Mus'ab matsalolin da mata ke fuskanta ya yin d'aukar ciki.

(Na gode sosai da kulawar ku a gare ni, na ji sauk'i sosai Allah yabar zumunci)

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspos.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣3⃣/7⃣4⃣��

*BAYAN WATA TARA*

Yau ne Musirrah ta tashi da nak'uda wanda tun safe take 6oyewa Mus'ab saboda gudun shiga damuwar shi, akan ganin ita ke da cikin amma tamkar ya fi ta shiga damuwa sanadiyyar yadda cikin ke mugun wahalarda ita.
    Tun shigar cikin ta wata takwas Mama Baraka ta ta re gidan su domin ba ta kulawa yadda ya Kama ta.

"Hayatee yau ba za'a yiman rakiya ba ne?".

"K'albee na d'an zazza6i nake ji shiyasa, Allah ya bada sa'a sai ka dawo".

Briefcase d'in hannun shi ya ajiye da saurin shi ya hawo saman bed d'in, hannun shi ya Kai yana ta6a jikin ta ya ji alamar za fi kad'an.

"Ka ta shi ka wuce kasan na gaya ma duk abinda naji ko da kana office ne Zan kira ka, kuma ka ga Mama na kusa ai".

"Yanayin kine bai min ba yau, saboda ba haka na sa ba ganin ki ba".

Cikin k'arfin hali ta sauko daga saman bed d'in ta d'auki briefcase d'in shi, ta sa d'ayan hannun ta ta sagala a kafad'ar shi suka wuce har gurin motar shi.
   Cikin walwala yaja motar shi ya fice, ita ko ta juya zuwa gida inda take addu'ar in ma haihuwa ce Allah ya kawo mata da sauk'i kar tasha wahala tamkar na d'aukar cikin.

Tana kaiwa falo k'afar ta ta rik'e kuma marar ta ta k'ulle, a tsakiyar falon ta zube cikin yarfe hannu da cizon yatsa.

"Mama! Mama!! Mama!!!",  Sai ana ukun ne ta ji yo ta.
   Da saurin ta ta iso falon had'e da tambayar ta me ke faruwa, nan take gaya mata.

"Y'ar nan kinsan kina jin nak'uda har kika bari maigidan ya fita, da safen nan ya shiga gaida ni har yake jaddada min in kula dake ya ga tamkar yanayin ki ya canza, ashe ko da gaskiyar shi".

Nan ta taimaka mata suka wuce d'aki wanda shigar su da minti biyar haihuwa ta zo gadan-gadan.

Cikin zafin ciwo take rok'on Mama Baraka kan ta kira Mus'ab in ma mutuwa za tayi ta mutu hannun shi.
     "Kar ki damu Musirrah da ikon Allah d'akin ki zaki haihu cikin k'oshin lafiya".

Da taimakon Mama Baraka ta yimata addu'ar nak'uda a ruwa ta ba ta sha.
Cikin yaddar ubangiji ta sunkuto y'ar ta, wanda Mama Baraka na jiran uwar tafiya sai ga wata y'ar ta fito da uwar tafiya.

"Alhmdulillah! Alhmdulillah!! Alhmdulillah", sai da Musirrah ta furta hakan har sau uku.

Mama Baraka sai murmushi take yi. Nan ta fara shirya yaran sannan ta taimakawa Musirrah ta kimtsa.

"To bara in Kira su Ammi domin su zo suga kyautar Allah".

"Mama bara in fara kiran shi sannan a kira su Umma".

"Lallai yaran nan ba kuda kunya, ba ma ni zan yi mai albishir ba ke za kiyi da kan ki".

Nan ta yi murmushi ta sunne kai, Mama Baraka ta fita domin kimtsa guri.

"Wayyo baya na", abinda ta furta kenan daga kiran shi ta kashe wayar tana murmushi.

Cikin saurin da tamkar zai ta shi sama da motar ya iso gidan, wanda ko mota bai rufe ba ya fad'a gidan.

Direct d'akin ta ya fad'a, abinda ya ci karo dashi ne ya sa ya yi turus, sai wani tsadadden murmushi take sako mai mai narkar da zuciya.

Da murmushi d'auke a fuskar shi ya ta ka har bakin gadon da take zaune, da d'ai d'aya ya d'auki yaran ya masu addu'a.

"Wai kina nufin wannan kyautar duk ni kad'ai Allah yabawa?". Nan ya d'aga hannu sama ya yi hamdala ga ubangiji.

Waya ya fitar yadinga kiran y'an uwa da abokanen arzik'i yana gaya masu haihuwar.

Mama Baraka ya sa ta kula da yaran ya sunkuci Musirrah sai mota, asibiti ya nufa da ita domin su duba Mai in bata samu wata matsala ba, saboda yana mamakin yanda ta haifi yara biyu da kanta kuma a gida.

Nan suka duba ta aka gaya mai lafiya lau take, sai wasu allurai da suka mata had'e da maganukkan da suka ba ta.

D'auke da ita ya shigo gidan, Ummy, Umma, Haj Maijidda su ya ci karo dasu zaune a falon sun saka yaran a gaba sai murmushi suke yi.

"Yau na ji d'ibar albarka, mai jegon ce ake tallafowa haka tamkar jinjira?" Cewar Haj Maijidda.

"Haj duba yaran da ta haifa ki gani, in tace tayi tafiya za ta ji ci wo ne".

"Sauke ta nace, ke ko kin lafe ajikin shi tamkar wata jinjira", inji Umma.

Cikin jin nauyi Musirrah ke mutsu-mutsu yasauke ta sai k'ara matse ta yake yi.
   Da saurin shi ya wuce bedroom d'in ta da ita, inda su Haj Maijidda suka bishi da ido alamar mamaki, Ummy ko baki ya mutu sai kunya take ji.

Mela da Iman ya tarar a d'akin sun gyara komai tsaf sun kunna turare sai k'amshi d'akin ke yi.

Sum-sum Iman ta ajiye kaskon turaren da take yawo dashi kusurwa-kusurwa ta fice.

"Ohhh ni Mela na ga ta kaina, ina fatar har nak'udar kai ka mata?". Da murmushi d'auke a fuskar ta.

Cikin murmushi ya sauke ta ya wuce zuwa part d'in shi.

"Angaida laila majnun, a hakan kuka wuto su Umma zuwa nan?".

"Bari ke dai Mela, wallahi duk kunya yake saka ni, ko a gaban wa ba ruwan shi, ko yanzu a falo Haj ta ce ya sauke ni tamkar ta k'ara zuga shi ne ya maza ya shige".

"To ai kinji dad'i saboda kina samun kulawa yadda ya kama ta".

Suna maganar ne Haj Maijidda ta shigo ta tasa k'eyar ta sai toilet ta gasa ta sosai had'e da jan kunnen ta kan yadda za ta kula da kan ta.

Ko da suka fito Mukarrama na rik'e da jinjira d'aya tana juyi da ita a tsakiyar falon, wanda Imtihal ke rik'e da d'ayar jinjirar, sai Anty Rukayya dake zaune gefen gado tana murmushi.

"Tunda kun nu na muna ku y'an dangi ne to za mu tattara na mu mubar maku gidan".

"Hakan ya fi kam Haj, daga ce wa an haihu duk ku kwaso jiki ku cika gidan", cewar Umma.

"A'ah Umma kuyi zaman ku falo mu za mu tsaya a nan ba sai an gan mu ba", inji Mukarrama.

"To shikenan muje falon mu da muka iya taryon bak'i, nan suka had'u suka ko ma falon su Imtihal sai murmushi suke yi.

****

*BAYAN SATI D'AYA*

Gida ya cika mak'il da y'an suna tamkar gidan aure, inda yara suka ci suna Fa'ida da Fadila.

Mela, Mukarrama, Iman, Imtihal matar Mubarak, Anty Rukayya da Musirrah ankon wata shadda suka yi mai ruwan purple ta ci aiki sosai har zuwa wuyan hannun su.

Bahijja matar Dr Shureim da Fateema matar uncle Hakeem, sai kuma Mmn Walida, Sophy, Mmn Ansar, Khairat da Mmn Khalil, inda akaci suna cikin walwala da farin ciki.

Sai k'arfe biyar Mus'ab ya had'a masu wata gajeruwar liyafa iya su yara ba da iyaye ba.

Inda suka had'a da Haydar da Mela, Mukarrama da Nibras, Mubarak da Imtihal, Iman da Sudais, Dr Shureim da Bahijja, uncle Hakeem da Fateema sai kuma Anty Rukayya da Sultan, anyi pics da videos saboda tarihi, Jameel ne da Yusrah basu da wo ba har yanzu.

Anyi taro cikin walwala da nishad'i anci ansha sai dai fatar Allah ya raya Fa'ida da Fadila akan tafarkin islama.

*SDY JEGAL*��

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣5⃣/7⃣6⃣��

*BAYAN KWANA ARBA'IN*

Yau ne Musirrah suka yi kwana arba'in da haihuwar twins d'in ta wato F², wanda dama tun jiya Mus'ab ya shaida mata ce wa ta shirya za su fita gaida iyaye da yan'uwa har da abokanen arzik'i.

Yara sunyi 6ul-6ul dasu wanda inka dube su zaka rantse da Allah kowannen su shi kad'ai aka haifeshi.

Bayan sun shirya ne suka fito har Mama Baraka domin ta ce za ta ko ma gidan Ammi tunda sun yi arba'in, in ya so daga baya a sa mo masu y'ar reno.
    Sun had'awa Mama Baraka goma ta arzik'i wanda kan murna har da kukan ta, ita kam tasan lallai wanda Allah bai bawa haihuwa ba yana cikin damuwa, amma ita kam yaran Ammi biyu da Allah ya ba ta sun cire mata duk wata damuwa ta rashin haihuwa.

Da hakan suka fito basu zarce ko ina ba sai gidan su Musirrah. Nan aka yita murnar ganin y'an biyu, ba kamar Umma dake tarairaya da yaran tamkar ta had'iye su saboda kawaicin Ammi ga yaran.

Haj Maryam ma ta yaba da girman yaran har tana tsokanar Musirrah ce wa yaran sun fita girma da kuzari lokacin da tana k'arama.

"Ka jini da mata kamar kinsan k'urciya ta kina wani zuzuta yaran ki sun fini girma".

Karaf Mama Baraka ta kar6e "Ai ko Haj banga abinda yaran ki za su gwada wa y'ata ba, don itama da tana k'arama tubarakallah.

Nan dai su Ammi suka rik'a murmushi. Mama Baraka ta fitar da kayan da su Musirrah suka ba ta ta nunawa su Umma nan suka taya ta godiya had'e da saka masu albarka.

Hakan Umma ta kwashi yaran ta kaiwa Abba su sai washe baki yake yi yana kallon yaran had'e da yi masu wasa.

Suna fita daga gidan suka wuce gidan Anty Rukayya, nan dai suka zazzaga dangi sai marece suka wuce gidan su Mus'ab wanda Ummy ta ma rasa Ina za ta saka yaran kan murna, Baffa ma ya sakama rayuwar yaran albarka sai k'arfe 09:00pm suka wuce gidan su.

A gajiye suka koma gidan inda suka yi wanka suka kwanta, saboda dama sunci abinci gidan su Mus'ab d'in.

****

*WASHE GARI*

Breakfast kawai suka yi suka fice, yau gidan Iman aka fara zuwa nan ya barta ya fice.

Da murnar ta ta tarye su in da take turo d'an cikin ta da bazai wuce wata bakwai ba.

Daga nan sai gidan Mukarrama wanda ta lak'e suka fita tare.

A cewar ta za ta raka ta yawon gaida dangi, daga gidan ta suka wuce gidan yaya Mubarak.

Bayan sun gaisa aka ta6a hira har suna tsokanar Imtihal kan ce wa ita da Iman ba'asan wa zai riga wani haihuwa ba.

Gidan Haj Maijidda suka wuce daga nan wanda ta yi murna sosai da ganin su, har ta had'awa Musirrah maganin Mata na gyaran jiki dangin na sha dana turare saboda ita bata wasa ko kad'an shiyasa ko yaushe take manne a zuciyar maigidan, nan Musirrah tayi ta godiya.

Gidan babbar k'awa Mela ne na k'arshe, inda suka tarar da ita zube a falo da uban cikin ta.
   Dariya suka rink'a tutsurawa wanda ya yi sanadiyyar fitowar yayan su Haydar.

"Yaya barka da yau, ya gidan?".

"Ku bari ku k'arasa iskancin da ya ka wo ku gidan sannan mu gaisa".

Musirrah ta ja bakin ta ta tsuke, Mukarrama kuwa tamkar k'ara zuga ta yake yi.

Da saurin shi ya zabura ya yo kanta, bayan Musirrah ta yi saurin 6oyewa.

"Da ki tsaya ki gani in kin wuce duka a guri na".

"Bross fa igiya uku ke saman kaina, wai ko ka manta ne?".

"Ai na za ta ke talatin aka d'aura maki".

Nan dai su Musirrah suka yi ta dariya ita da Mela, saboda zamantakewar Haydar da Mukarrama na burge su ko yaushe suka had'u sai sun sayar da hali.

Hakan dai suka yi ta hirar su cikin walwala da nishad'i tamkar kar su rabu.

Da marece Mus'ab ya zo d'aukar su har sun hau hanya ya tuna.

"Kinga ya kamata gobe muje gidan Dr Shureim da gidan uncle Hakeem daga can sai mu wuce Bk, ko ya kike gani?".

"Allah na gaji Abban twin's mu bari nan da kwana biyu".

"Ba matsala Allah yakai muna rai".

"Ameen".

Sai da suka biya suka Fara sauke Mukarrama sannan suka wuce gida.

Suna shiga ana magrib, sallah suka fara gabatarwa sannan ta shiga kitchen abinci mafi sauk'i ta girka masu.

Bayan sun ci sun k'oshi ne suka gabatar da sallar isha sannan suka yi wanka suka kwanta.

(Ga wannan kuyi hak'uri dashi 4 breakfast, lolx)

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣7⃣/7⃣8⃣��

*BAYAN KWANA BIYU*

Tun safe suke shirye-shiryen tafiyar su Bk d'in saboda za su biya ta Jega gidan su Dr Shureim da Hakeem.

K'arfe tara dai-dai suka hau hanya. Gidan Hakeem suka fara sauka wanda sunyi murna da zuwan su sosai, kuma sun yi musu tarba wacce ta dace yaran su sai murna suke yi da y'an biyu ji suke yi tamkar a bar masu yaran.

"Kwanan nan fa muke batun kai maku ziyara sai ga shi kun riga mu kun kwashe ladar", cewar Hakeem.

"Wallahi za muje Bk ne ziyara shiyasa na ce ya kamata mu zo mu gaisa".

Hannun Musirrah Fateema ta rik'a suka wuce bedroom d'in ta, nan suka rik'a hira tana k'ara gaya mata dabarun zama da miji.

Kiran da suka ji mazan nai masu ne yasa suka fito.
      "Wai yaushe ne gulma za ta k'arewa Mata ne?, duk hira ba'a yin ta sai an shige uwar d'aka", cewar Hakeem.

"To yanzu ba ga shi kuma mun ba ku guri kun sa mu sake wa ba".

Hakan suka had'a masu goma ta arzik'i suna godiya suka wuce.

Gidan Dr Shureim suka je don ma basu dad'e sosai ba Bahijja da Lateefa sun tarye su yadda ya kama ta. Daga nan suka d'auki hanyar Bk.

Duk inda dangi suke an za ga su har gurin Gwaggon Umma sun je wanda tsufa ya kamata sosai.

Basma ce k'anwar Yasmeen ta mak'alewa Musirrah ce wa sai ta bisu ta rik'a rainon twin's.

Nan ta yi magana da Mus'ab kan cewa y'ar k'anen Abba za ta bi su me yace akai?

"Ba matsala tunda dama dole za mu ne mi mai renon su, saboda haka ta had'a kayan ta sai mu wuce da ita".

Da hakan suka wuce ta re da Basma y'ar kimanin shekara goma sha d'aya, sai murna take yi aranta saboda tana son yara sosai.

****

*BAYAN SHEKARA GOMA*

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda rasuwar dattijo mai kamala wato Baban Ammi, wanda ta shiga tashin hankali da jimamin rasa shi saboda shi kad'ai yayi mata saura, don kamin rasuwar shi da shekara ukku Gwaggo kulu ta rasu. Sai dai fatar Allah yajik'ansu da rahama.

6angaren su Jameel kuwa ya dawo da nasarori da dama acikin aikin da yaje, yanzu haka yaran shi uku.

****

Fa'ida ce tazo da saurin ta tana fad'in "Mum wallahi ga Fadila can tana dukan Baffa".

Mus'ab ne ya fita ya shiga tsakanin su.

"Haba Baby waya gaya maki ana dukan Baffa na?".

"Abbu shi ne fa yake tsokana ta akan jiya munje islamiya anyi karatu ban iya ba Malam ya dake ni".

"Haba Baffa na ita fa Antyn kace me yasa kake tsokanar ta?".

"Abbu fa kaduba duk girman ta wai bata iya suratul mulk ba, bayan ko gida Mum na koya mana".

"To kasan kowa da K'wak'walwa shi, kuma in kana mata dariya k'ok'arin ka zai koma na ta, kana son hakan?".

"Aah Abbu", da saurin shi ya amsa.

"To karik'a mata addu'a Allah yak'ara mata basira".

Juyawa yayi gurin little Mukarrama dake ta wasan ta da motar yara, cak ya d'auke ta yana duban ta.

"Kina ga su Anty na fad'a baki je kin gaya min ba ko?"

Cikin maganar ta da bata k'ware sosai ba take gaya mai in su Anty na fad'a kan ta ke ciwo.

Da mamaki yake kallon yarinyar saboda miskila ce ta K'arshe sam bata biyo halin mai sunan ta ba.

Haka ya tasa k'eyar yaran duka suka ko ma falo domin yin breakfast.

Shigar su ke da wuya suka tarar Musirrah ta gama jera komai, nan suka hau dinning table domin karyawa.

"Sai Ku shirya za'ayi birthday party na cika 10yrs d'in ku nan da sati d'aya, ana k'arewa sai auren Anty Basma".

Nan suka cukwiy-kuye shi suna murna had'e da furta "Alla ya bar mana kai Abbun mu".

"To ku matsa ku karya shi ku huta", cewar Musirrah.

Cikin sauri suka sake shi sai murmushi suke yi, wanda cikin sauri Baffa ya haura sama domin gaya wa Anty Basma.

****

*BAYAN KWANA BIYU*

Gwaggon Umma ce Allah ya yiwa rasuwa don ma ta yi yawancin rai.

A hanya ne Ammi da Umma zasu je gaisuwa had'e da Mama Baraka ko ince Haj Baraka don Mubarak ya kai ta Makkah, kuma ta yi auren ta da wani abokin Abba shekaru biyar da suka wuce.

Direba ne ya kusa kad'e wata tsohuwa dake jan jiki saman titi ba tada k'afa d'aya.

Umma ce ta fita domin bata hak'uri, had'a idon da suka yi ta zabura da k'arfi saboda ganin Haj karime, duk ta kod'e ta jeme sai warin datti da take yi.

Da sauri ta koma mota had'e da ba direba umurnin yaja suje, hannun da ta rik'a yi masu ne ya sa Ammi ta fita dai-dai matar na kawowa gurin motar.

"Don Allah da son ma'aiki ki gafar ta min Haj Zainab, na ga rayuwa iri-iri nasan hakk'in kune ke bibiya ta".

"Kwatan-kwacin yadda na yi maki nayiwa wata, ashe na ta sharrin ya fi nawa shi ne ta turamin y'an iskan gari suka kwashe komai dana mallaka kuma suka gundulemin k'afa d'aya".

Da ido Ammi ta bi Umma da kallo alamar tambaya.

"Haj Karime ce". Amsar da ta bata a tak'aice kenan.

Wani imani ne ya k'ara ratsa zuciyar Ammi, nan ta k'ara tabbatar da duniya ba bakin komai bace.

"Ki yafe mata Mmn Jameel, ko hakan ta ga jarabawa".

Dak'yar ta furta "Na yafe maki".

Ammi ce da Mama Baraka suka bata kud'i tana ta godiya har da guntun hawayen ta.

Hakan suka ja mota suka wuce, har suka kai suna tad'in rayuwar duniya.

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[9:14AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_7⃣9⃣/8⃣0⃣��

*BAYAN SATI D'AYA*

Yau ne ake ta shirye-shiryen birthday party na Fa'ida da Fadila murnar cikar su shekara goma.

Babban hall ne suka ka ma domin gudanar da party d'in inda abin ya had'a har da kakannin su.

6angare uku akayi nasu Umma daban, sannan su Mus'ab, sai na yaran.

Anko ne suka yi gwanin sha'awa, su Ammi wani Jan less suka saka Ummy, Umma, Ammi, Haj Maijidda da kuma Mama Baraka.
   Sai kuma Abba, Baffa, Alh Sani da kuma Alh Mu'azzam mijin Mama Baraka da suka saka wata bugaggar farar shadda.

Sai 6angaren su Musirrah da suka saka material kalar lemon green, Anty Rukayya, Musirrah, Iman, Mela, Mukarrama, Imtihal, Yusrah, Bahijja, Fateema, Lateefa sai Basma.
    Su ma Jameel, Mus'ab, Haydar, Nibras, Shureim, Sudais, Sultan da Hakeem suko voil kalar lemon green suka saka.

Sai 6angaren yaran suko kayan kanti ne suka saka, yaran mukarrama uku, na Iman biyu, Mela hud'u, Imtihal hud'u, Yusrah uku, Anty Rukayya biyar, sai su little Lateefa ita da k'annen ta da yaran Fateema.

Hakan suka cika hall d'in mak'il abin gwanin sha'awa, nan aka ci snacks da lemukka sannan su Fadila suka yanka kek.
   Haka suka bi iyayen suna saka masu kek d'in ana tafi raf-raf.

Saida suka k'are da iyayen suka ko ma kan kakannin su, cikin nishad'i suke abin su.

Baffa ne da Abba na k'arshen suna ka wowa gurin su suka yi rad'a nan suka d'ibi kek d'in za su kai bakin su sai suka kauce suka manna masu a hanci.
   Nan yaran suka d'auki shewa da tafi da dariya.

"Yau naji ja'iran yara, me ya hana ku yiwa iyayen ku sai mu da kuka rena?".
Haj Maijidda ce ke bambamin fad'a dasu.

"Granny kishi kike yi an yiwa su Baffa ba'a maki ba". Cewar Adal diyar Mukarrama, tana maganar ne ta nufo su gadan-gadan da cake a hannun ta.

Dak'uwar da Iman ta yi mata ne yasa ta ja birki tana dariya.

Da hakan akayi taro cikin farin ciki, walwala, nishad'i inda families d'in suka zamo abin alfahari.

"Abban twin's wai fa wannan taron duk yaran mu aka yiwa shi". Tana maganar ne had'e da guntuwar k'walla a idon ta.

"Ina tuna irin k'uncin da muka shiga a shekarun baya ni da Ammi da yaya Mubarak".

"Sanadin k'unci ai ya koma sanadin farin ciki, ko ba hakan ba?".

"Tabbas ka zamo linzamin farin ciki a rayuwa ta". Sai da ya faki idon mutane sannan ya saka halshe yana lashe hawayen da ke zubo mata.

*TAMMAT BI HAMDILLAH, INA GODIYA GA ALLAH DA YA NUNA MIN NA KAMMALA WANNAN LABARIN*

*KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE MIN*

*DA FATAR ZAKU YI AMFANI DA ABINDA KE CIKI MAI FA'IDA, KU YI WATSI DA AKASIN HAKAN*

Sadaukarwar ta kice Sister Sanah S. Matazu.
Allah yabar k'auna tsakanin mu.

Anty Maijidda Musa ba kina ba zai iya furta godiya zuwa gare ki ba sai dai in kwatanta saboda tsakanina dake sai Allah.

Ku ma ga taku gaisuwar

Anty Ybk
Ummu Abdul
Mmn Haneef
Umma ta Lubiee Mai Tafseer
Zainab (Autar Hjy)
M. Jabonation
Benaxir Omar

Yayye na ga gaisuwar ku.

Anty Innah
Mmn Waleeda
Anty Rukayya
Mmn Meerat
Mmn Abdulmalik
Mmn Ameer.

Three stars
Hindatu Jegal
Nafee Jegal
Aisha Jegal

Five stars
Assy Jegal
Sumee Jegal
Hauwa Jegal
Balkisu Jegal
Asmee Jegal

Yara manyan gobe
Halima
Maryam
Nana Khadija
Abduljalal
Allah ya sakawa rayuwar Ku albarka.

Y'an Uwa na jini
Sis Maryam (Mela)
Sis Atika (Atiks)
Ummu (Mmn Ja'afar)
K'awa ta gari, matsayin ki ba zai ta6a canjawa ba domin kin cancanci hakan.
Shema'u Bello Bari

Ban manta daku ba
Zainab Musa
Lawiza Musa.

K'anne na kaina
Yaha Saddik
Aisha Bizzy
Aisha Yagani
Yasmeeny.

Abokanen karatu na
Aminiya ta Haj Shafa
Saratu (Mrs Abdussalam)
Y'ar gidan Ango.

Naku matsayi na daban ne

Zarah B~B
Hindatu Shehu
Bungud'u
Bebeelo
Zeitunerh Mrs Dr Moh
Mmn Amatullah
Umamat
Mrs Jawaheer
Mumcy na Rabeaht A Danbappah
Mumcy Rabeaht Husain
Mum Faty
Princess Meenat
Blkisu Blymnu
Fati Salihu
Aunty Sis
Aneesa Abubakar Rimi (Anee)
Nana Diso
Deeja Abdul

Kuna raina har kullum

Mmn Shakur
Khairat
Miss Hafcy
Mmn Xeenert
Jamila Moh Ali
Ummietta Wabi
Fatyn Idiriss
Madelty
Ag
Phareederh yahaya
Maryam Yusuf
Ummu Affan
Mrs M. Bawa
Mas'uda (Mmn Walida)
Habiba Yayaji
Ummen Al'amein
Farzana
Maryama
Jidda jangade
Sophy MD
Shatoo Mammaga
Laurat (Mrs Zubair)
Shamseea
Hafsa D
Jidda A.K.A
Innah Habiba
Ameera Maisikeli
Khadija Manga
Mmn Ansar
Mmn Aslam
Nafisa Alu
Maryam G
Mmn Mamee
Ummulkhulthum
Fatima
Mmn Ja'afar
Yaseera

*SDY JEGAL NOVELS*
*M. JABO MUMBARIN NOVELS*
*MUSHA KARATU*
*ZAUREN KARATU*
*ZUMUNCI GROUP*
*GREATEST WOMEN*
*MUM FATY FAN'S*
*ZARAH B~B FAN'S*
*NWA* *KU NA DABAN NE*��

*SDY JEGAL KE GAIDA DUK MASOYAN TA WA'ANDA TA SANI DAMA WA'ANDA BATA SANI BA*

*NA YI K'OK'ARIN SAKA SUNAYEN KU DUKA SAI DAI HAKAN BAI SAMU BA SABODA YAWAN KU, DA FATAR DUK WANDA BAIJI SUNAN SHI BA ZAI YI HAK'URI KUMA YA YIWA Y'AR MUTAN JEGA UXURI*

*NA GAIDA KOWA DA KOWA KYAUTA*��

*SAI KUN JINI A WANI SABON NOVEL NAWA MAI SUNA.........*

*SDY JEGAL*��

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.

SANADIN KUNCI 61-70

[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'INCI_ 6⃣1⃣/6⃣2⃣��


*WASHE GARI*

*04:30pm*
Harabar gidan Haj Maijidda ta cika da mutane mak'il duk da ce wa mutane basu kammalu ba har yanzu.

Mela, Iman, Mukarrama kaya iri d'aya suka saka wani rantsattsen material ne a jikin su kalar lemon green sai wani gwaggwaro da suka nad'a saman kansu mai ruwan hanta had'e da takalman su kalar gwaggwaron su.
   Amarya ce ta fita daban acikin su saboda less ne ta saka mai kalar blue sai gwaggwaro da takalman ta farare, da ka ganta kasan ta had'u iya had'uwa.

  Mai kid'an DJ aka kira suka baje sai tik'ar rawa suke yi duk da ce wa Musirrah ba wai rawa ta iya ba amma sai abin ya bada wani style na daban, acan tsakiyar masu rawa na hango Shema'u sai rawa take tik'a kuma daka ganta kasan cewa ita gwana ce a cikin rawar, nan dai na ganta da mutanen ta a tare da ita na hango Mmn Zeenert, Mmn Jameel, Yaha Saddik, Mmn Mamee, Shafa Abasco, Nafisa Alu, Khairat, Salsabila, princess Meenat, sai kuma K'anwa ta Bizzy wanda duk sun cika gurin tamkar dan su ake bikin, (Tabbb Shema ashe kin had'o kan y'an SDY JEGAL NOVELS) ne don ku cin ye kayan biki.

Hakan akayi taron sa lalle inda ya k'ayatar da mutane abin sai son barka.

***

*RANAR JUMA'A*

Yau kuwa ranar walima ce za'a yi y'an nasihohi zuwa ga amarya domin samun zama mai d'orewa na har abada a gidan ta, wanda aka gayyato Malama Khadija Manga ita da Haj Shafa Aleru domin su yi wa Amarya nasiha akan zamantakewar aure.
Nan ta fara da ce wa shi dai aure yana daga cikin sunnar manzo (S.W.A), Saboda yana ce wa yaku al'umma ta kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku a gobe alk'iyama".
  "Shi zaman auren kanshi yana k'unshe da abubuwa da dama wad'anda muddin mutum ya tsare biyar daga cikin su to rayuwar auren shi zata yi k'ark'o da ikon Allah.

ABU NA FARKO SHINE LADABI DA BIYAYYA: "Su ne jigon auren gaba d'aya, saboda duk yadda mijin ki ke son ki muddin ba kiyimai ladabi to da sannu zaki siye ticket d'in cire soyayyar ki aran shi, kar kice ni fa ba nason wane aka yimin aure dashi saboda haka bazan girmama shi ba to wannan ba dai-dai bane."
  "Kuma ki zamo mai girmama iyayen shi da y'an uwan shi dashi kanshi mijin.

ABU NA BIYU SHINE TSAFTA: Ki kasance mace mai tsafta ta kowane 6angare, kar kiyi tunanin ce wa in har kika tsaftace jikin ko baki tsaftace muhallin ki ba tamkar kinyi dai-dai, saboda gudun mijin ki ya jiki ba dai-dai ba, to wannan ba shi ne abin yi ba, kamata ya yi ki kula da tsaftar jikin ki, muhallin ki da kuma makwancin ki".

ABU NA UKU SHINE GIRKI: Babban kuskuren da iyaye ke tafkawa kenan a yanzu, za ki shiga gida ki tarar da y'an aiki birjik sun cika gida iyayen da yaran gidan ko wa zaune yana hutawa, wasu za su ce ni tunda inada abin hannu na bazan bari in wahala d'ana ya wahala ba, wasu zaki ji suna fad'in ba za su shiga kitchen ba saboda hayak'i kar yasa suyi bak'i, wasu kuwa ko gida aka shigo aka tarar suna aiki idan akace ina y'arki halan? za kaji uwar ta ce wallahi yanzu ta dawo daga skul duk ta gaji kinsan ba ta zama kullum tana hanyar skul".
"To wallahi wannan babban kuskure ne, iyaye mata mu ta shi tsaye cikin lokacin da d'anki yake dashi ko da minti talatin ne ki rik'a koyawa yaran ki girki, domin shi ne ginshik'i na rayuwar aure, duk yadda miji ke son ki in har kika sa mu matsala ta 6angaren girki to kin zamo abin tausayi".

Nan Haj Shafa ta kar6e da sauran bayanan biyu da suka rage, inda take ce wa'
ABU NA HUD'U SHINE SHAGWA6A: Har kullum idan mace tana nu nawa namiji shagwa6a to za ta samu wani bagire ne a zuciyar shi, saboda in har kina narke mai kullum tamkar man gyad'a to ba za ki ta6a fita a zuciyar shi ba".

ABU NA K'ARSHE SHINE KISSA: Kissa ta kasu kashi-kashi, to mu kissar da za mu d'auka ba kissar da za ki koya domin korar kishiya bace, ko kuma had'a miji da y'an uwan shi ko mahaifiyar shi ba, ta mu kissar ita ce wadda za ki koya domin narkadda zuciyar maigida ki shiga zuciyar shi kiyi kane-kane ba boka ba malam".
  Hakan suka k'are y'an nasihohin su zuwa ga amarya da sauran mutanen da ke gurin, saboda su ma sun k'aru da wannan gajeruwar nasihar.

  Yau kam y'an MUSHA KARATU ne suka cika gidan don su ma sun yiwa amarya kara, can na hango Mmn Ansar, Mmn Aslam, Munirat Ayuba, Maryama, Aunty Sis, Baraka, Fatima, Mmn Marhama, Ameera maisikeli, Ummietta wabi, wanda nan Musirrah ta tabbatar lallai MUSHA KARATU na son ta da gaskiya, hakan ta ba wa Mela umurnin taje ta sallame su, haka suka fita cikin farin ciki da karramawar da Musirrah ta yi masu had'e da addu'ar zaman lafiya.

****

*RANAR ASSABAR*
*11:00am*

   Dubban mutane suka shaida auren

*MUSIRRAH FAROUK*
               
            ```WEDS```

*MUS'AB ABUBAKAR*

Wanda ya samu halartar manyan mutane daga wurare daban-daban saboda Baffa da Abba ba baya ba gurin mutunci da mutane, kowa na sune saboda basu da girman kai irin na masu kud'i.

  Ranar gidan ya k'ara cika da mutane saboda halartar y'an MUMBARI domin nuna soyayyar su zuwa ga Musirrah wanda Yasmeeny ce ta jagoran ci wannan tafiyar inda Aisha Yagani, Hafsat Mai Sharifai, Jamila Moh Ali, Inna Habiba, Mmn Zahra, Mum Faty su ma ba'a barsu abaya ba.

Fateema Mrs uncle Hakeem da Bahijja Mrs Dr Shureim su ma sun zo da yaran su, saboda mazajen su abokanen Mus'ab ne. 6angare d'aya kuwa amarya ta sha gyara ga Murja ladan wato Madelty da maganin mata na sokoto, sai dai fatan Kai Amarya gidan Ango lafiya.

*SDY JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣3⃣/6⃣4⃣��

*10:30pm*

Zuwa lokacin duk an shirya Amarya domin kai ta d'akin mijin ta sai kuka take yi na rabuwa da Ammin ta, saboda dai-dai da rana d'aya bata ta6a rabuwa da Ammi ba.
   Duk duniya bata da wanda ta yi sabo dashi kuma take iya gayawa matsalar ta kamar Ammi, dak'yar aka samu aka 6an6are ta daga jikin Ammi, part d'in Abba Haj Maijidda ta wuce da ita nan ya yi mata nasihohi dai-dai gwargwado wanda ya saka jikin ta ya k'ara sanyi, yana saka mata albarka k'anwar shi da Haj Maijidda suka rik'a ta aka saka ta a mota suka wuce.

Mota kusan takwas aka cika domin raka Amarya d'akin ta, ciki kuwa har da Mmn Hanan, Aunty Sis, Feenah Umar, Mum Faty, Ummu Mmn Ja'afar, Fati Salihu, da sauran y'an uwa da abokanen arzik'i.

K'arfe goma sha d'aya kowa ya tattara na shi da na shi suka fice, saboda Iman ce wa tayi ba za ta zauna yaya Mus'ab ya risk'e ta a gidan ba, jin hakan ya sa gaba d'aya suka fice suka bar Musirrah ita kad'ai wanda sai ajiyar zuciya take yi akan kukan da taci.
   Bayan ya shigo gidan ne ya wuce part d'in shi sai da ya yi wanka ya saka farar jalabiya sannan ya wuce d'akin ta.

Can ya hango ta duk'un-k'une gefen gado duk ta ta kura kanta da babban gyalen da aka rufa mata.
  Hakan ya ajiye kayan da ya shigo dasu sannan ya ta ka har 6angaren da take, gurfane ya yi gaban ta ya sa yannu ya yaye gyalen da ya rufe mata fuska.

"Ki bud'e fuskar kisha iska mana tunda ko wa ya watse, ko kuma sai na siye bakin tukun?".
  Cikin jin nauyi ta k'ara jan gyalen domin ta rufe fuskar ta, jin ya rik'e gyalen ya sa ta kauda fuskar ta cikin jin kunyar shi, ga shi ya zo gaban ta ya yi gurfane duk zatin shi ya mamaye gurin.

Gyalen ya cire duka had'e da ba ta umurnin ta shiga toilet tayo alwala domin su gabatar da nafila.

Bayan sun gabatar da nafila ne kuma sunci sun sha ya yi mata tambayoyi da suka shafi addini kuma gwargwado ta amsa iya abinda ta sani sannan ta tashi ta koma saman gado.

Tana so ta rage nauyin kayan da ke jikin ta tayi wanka amma kuma tana jin nauyin shi, ganin ce wa tana jin nauyin shi ne ya sa ya fita zuwa part d'inshi.

Nan ta sa mu sakewa sannan ta fad'a toilet ta yo wanka ta fito sannan ta saka kayan bacci ta hau gado ta kwanta.
      Kwanciyar ta da minti uku ya da wo d'akin ga alama wani wanka ya yi.

"Wa ya ce maki mata na kwanciya ba ta re da mijin ta ya shigo ba?", yana maganar had'e da murmushi a fuskar shi.

Filo ta janyo ta rufe fuskar ta, jin take yi wani irin son shi na k'ara shiga zuciyar ta, amma fa tana da tambayoyin da take son yi mashi sai dai tana tunanin ba yanzu ba.
    Sai da ya kashe fitilar d'akin sannan ya kwanta saman gadon, hannu ya kai gefen gadon ya kunna dim light, sannan ya matsa gab da ita har suna jiyo numfashin juna.

Hannu ya kai ya janye filon ya maida shi gurin kanta sannan ya janyo ta ya matse cikin jikin shi.

(Ni dai Jegal da sauri na na koma falo na takure saman three seater, saboda ko na tsaya ni kad'ai zan gani bazan iya gaya maku ba, *lolx*)

****

Umma anga rayuwa a gidan Jameel, lallai tabbas rayuwa juyi-juyi ce kwad'o ya fad'a ruwan zafi, cikin kwanakin nan ciwo ya saka ta gaba ga rashin wadataccen abinci ga kuma bak'in ciki da damuwa da suka mata yawa.
   Musamman inta tuna irin zamantakewar da suka yi ita da Alh, bata ta6a tsammanin za su rabu ba saboda ganin ce wa ta kawar da Hauwa'u sai hankalin ta yakwanta.
Ashe akwai lokacin da za ta shiga tashin hankalin da zai fi na Hauwa'u don yanzu ita tana can da mijin ta cikin kwanciyar hankali itako ga ta nan raku6e suruka na wulak'an ta ta son ranta.

Duk yadda ake yi Baffa ya yi domin shawo kan Abba yamayar da Umma amma abin ya gagara, saboda har ta kai Abba ya furta mai in har yana son zaman su ya d'ore na aminci to kar yak'ara yimai maganar mayar da Umma gidan shi.

Har y'ay'an ta sun had'u sun je ba shi hak'uri amma ina zuciyar maza ta hau.

*SDY JEGAL*

dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 6⃣5⃣/6⃣6⃣��

*WASHE GARI*

Cikin farin ciki da walwala suka ta shi, da taimakon Mus'ab ta gyara jikin ta bayan sun yi sallah had'e da azkar suka kuma bacci.
  K'arar wayar shi ce ta falkadda shi ko da ya duba Ummy ce ta kira tana gaya mai ta aiko direba ya ka wo masu breakfast, hakan ya sa ya mik'e ya fita daga waje, bai yi minti biyar ba direban ya iso, kar6a yayi had'e da godiya ya ko ma ciki.

Fitar Mus'ab ke da wuya ta fad'a toilet saboda ta d'an jima da tashi nauyin had'a ido dashi take ji shiyasa ta k'udun-dune tamkar mai bacci.

Ko da ya da wo d'akin ya ji motsin ruwa daga toilet sai ya wuce part d'in shi.
       Material ta saka mai kalar purple riga da siket ne, inda siket ya ka me daga sama sai zuwa k'asa ya bud'e, hakan yasa ya fito da shape d'in ta ga dukiyar fulani tubarakallah.
Jin nauyin fitowa hakan ya sa ta ya fa wani k'aramin gyale, sannan ta d'an kimtsa d'akin.

Da sallamar shi ya shigo d'akin bayan ta amsa ta durk'usa ta gaida shi cikin sunne fuska, kafad'un ta ya rik'o ya mik'ar da ita sannan ya cire gyalen da ta ya fa.

"Me zaki yiman 6oyo ajikin ki, ni fa mijin kine ga shi har da sauri na in kimtsa in zo in taya ki wankan", yana maganar had'e da kashe mata ido d'aya.
  Kanta ta k'ara sunne wa k'asa jin take yi tamkar k'asa ta bud'e ta shige.

Hannun ta ya rik'a suka dawo falo, a dinning suka zube ya bubbud'e kayan abincin, nan ya hango kunun tsamiya da k'osai sai kuma tea da wainar k'wai had'e da kus-kus.

Hannun ta ta cire a nashi ta mik'e, "ina zaki je?".

"Kitchen zan shiga in d'auko cups da plates".

Tana juyawa da ido ya bi ta yadda mazaunan ta ke juyawa, har ta da wo bai san ta iso ba, k'arar plates d'in da ta zo dasu ne ya da wo dashi hayyacin shi.

Hakan ya wayance da sosa kan shi ya mik'o hannu domin kar6ar cups d'in, "me za'a saka ma cikin abincin?".
   Muryar ta mai sanyi ce ta doki kunnen shi, "kunun tsamiya da k'osai zan sha". Ya ba ta amsa.

A ta re suka karya har suka k'oshi, duk da nauyin shi da take ji ya hana mata sakewa ta karya da kyau, hakan ya ja ta duk ya nu na mata gidan k'arshe bedroom d'in shi suka zube ya janyo ta saman shi ya rungume, cikin kasalalliyar murya ya furta mata "bacci za mu ko ma saboda rage gajiyar jiya".
   Hannuwan ta duka biyun ta saka ta rufe fuskar ta, "zanyi maganin wannan kunyar don na ga tana son shiga hakk'ina".

****

Cikin tashin hankali Jameel ya shigo gidan saboda ya rasa ina zai sa kan shi, da yana da iko gaskiya da bazai yi wannan tafiyar ba.

Yadda ya shigo d'akin a hargitse ya tabbatar mata ba lafiya ba, "me ke damun ka haka?, na gayama kar ka bari matsala ta da matar ka ta saka ma wani ciwon".

"Ba wannan ne damuwa ta ba, gurin aiki na ne suka tura ni England wani course na shekara biyu, shi ne nake tunanin ina zaki zauna in har na wuce".

"Uhmm! "Kar ka damu da ma zaman gidan ya ishe ni, zan had'a kayana in koma Birnin kebbi da zama gurin Gwaggo zai fiye min".

"Ba za'a yi hakan ba, yanzu dai bara in fita in dawo ba za mu rasa mafita ba", da hakan ya fita ko Yusrah bata  san ya shigo gidan ba.

Direct gidan su ya wuce, bayan ya gayar da Ammi sannan ya fitar da waya ya kira Haydar kan yazo part d'in Ammi ya same shi, bayan sun kammalu ne har Mubarak da Iman nan yake gaya masu meke faruwa.

Nan suka rik'a kuka had'e da neman alfarmar Ammi kan ta saka ba ki Abba ya mayar da Umma.

"Abban ku kunsan yana da kafiya, amma ku ta shi muje part d'in Haj mu rok'e ta alfarma ko za ta iya tunkarar shi da maganar".

Hakan suka d'unguma sai part d'in Haj, nan Ammi ke gaya mata buk'atar su. Cikin mamaki Haj Maryam ta kai duban ta ga Ammi, wannan wace irin mata ce da har kishiya za ta nemi hallaka ta amma yanzu da kanta take ce wa amayarda ita, cikin zuciyar ta take wannan tunanin.

Nan ta sa Ammi ta kira mata Abba, bayan ya iso ne ta gaya mai buk'atar yaran shi, kai ya rik'a girgizawa alamar bazai iya ba.

"Abba mu aka yiwa wannan abin kuma mun yafe har ga Allah, ka mayar da Umma don Allah", Mubarak kenan da ya je gaban Abba yana rok'on shi.

"Ni dai a zuciya ta komai ya wuce wallahi", cewar Ammi.

Cikin fushi Abba ya ta shi fuu ya wuce, wanda Haydar ya fara ta'allak'a laifin rashin dawowar Umma ga Haj, saboda ita ta haife shi kuma in ta bada umurni dole yabi.

Koda wani 6angare bai ganin laifin ta saboda Umma bata d'auki ko wa da daraja ba, su da ta haifa kawai take son ci gaban su, wani tunani ya fad'o mai arai.

"Gidan da su Ammi suka ta shi can Umma za ta ko ma da zama", nan dai ya yi bayanin yadda akayi gidan ya da wo mallakin shi.
    Ya d'ora da ce wa tun da su Ammi sun sa mu gurin zama sai ta ko ma can".

"Eh hakan ya yi gaskiya, ni kuma na yi maku alk'awari zanci gaba da lalla6a shi har a samu ya sauko da ikon Allah", Ammi ce ke wannan maganar.

Nan suka yita godiya har Ammi ta ji nauyin su, da hakan Jameel ya wuce gidan shi ya gayawa Umma yadda suka yanke.
   Kuka kam ta yishi har ta gode Allah daka dube ta yanzu za ka hango nadama k'arara a fuskar ta.

Da hakan akayi gyaran da ba'a rasa ba a tsohon gidan Ammi, Umma ta had'a kayan ta ta koma can da zama had'e da y'ar aikin da aka sa mo mata wata dattijuwa, shi ko Jameel ya cira da matar shi Yusrah dake jin tamkar ta zuba ruwa k'asa tasha.

****

*BAYAN SATI BIYU*

Yau Rukayya ta shirya domin kaiwa k'anwar ta Musirrah ziyara wadda take ji har cikin ranta har gobe tana jin nauyin abinda tayi mata.

Tana kitchen tana masu girki ta ji sallamar Anty Rukayya da saurin ta za ta fito ta ajiye kular miya saman kantar ajiye kaya ashe bata hau dai-dai ba ta  zubar mata a k'afa.

K'arar da tayi dai-dai take da fitowar Mus'ab daga bedroom d'in shi, da saurin shi har suna rigen-gen shiga kitchen d'in shi da Rukayya.
   Dafe da k'afar take ta saka tissue tana goge gurin sai yarfe hannu take yi alamar tana jin zogi.

Caraf ya sunkuce ta tamkar wata Baby ya dawo falo da ita, sai rufe fuskar ta take yi akan kunyar Anty Rukayya.

Saman three seater ya d'ora ta da saurin shi ya haura sama ya d'auko keyn mota had'e da gyalen ta.

"Plxxx Auntyn mu minti goma, ki kula da gidan yanzu za mu da wo", bai tsaya sauraren amsar ta ba ya kuma sunkutar Musirrah sai mota.

Hakan ya ja motar sai asibitin su Shureim, Musirrah mamaki ya hana ta magana har suka iso asibitin, shi ya d'auke ta sai office d'in Dr Shureim.
    Koda suka shiga yana duba wata mata, hakan Mus'ab ya matsa mai sai da ya duba k'afar Musirrah wanda zogi kawai take mata.

Nan dai ya mata allurar rage zogin had'e da magani daya ba ta, "to laila da majnun a ko ma gida asha magani, saboda gurin bazai d'aye ba", Dr Shureim ke maganar cikin zolayar su.

Cikin kunya Musirrah ta rufe fuskar ta, "yarinya ki gode Allah da kika sa mu miji mai baki kulawa haka, Allah ya baki lafiya", cewar matar da suka tarar a office d'in.

D'aga kan da za tayi karaf suka hada ido cikin mamaki da sakin baki take nuna ta had'e da furta Mama Baraka".
   Duk da k'arancin shekarun ta a wancan lokacin da suka rabu da Mama Baraka bai hana ta ga ne taba, saboda koda suka rabu tana da kusan shekaru takwas da watanni a duniya.

"Y'ar nan wacece ke?, ban ga ne ki ba?".

"Mama ni ce Musirrah k'anwar d'anki Mubarak d'iyan Ammi".

Cikin sauri ta ta shi ta rungume Musirrah duk da ba wani k'arfin jiki ne da ita ba.

"Allah mai iko, mai kowa da komai, ashe da rabon za mu had'u, ina Hauwa'u? Ina yaro na Mubarak?".

"Duk suna nan k'alau Mama", tana maganar farin ciki fal a zuciyar ta.

Nan dai suka gama komai suka wuce da ita gidan su, saboda dama ta gama abinda ta zo yi shawarwari yake bata akan matsalar ciwon da ke damun ta wato ciwon sugar.

Cikin kunya ta shiga gidan ganin yadda Mus'ab yayi mata gaban Anty Rukayya ko kunya baiji ba.
   Hakan dai ta yi mata sannu suka ci abinci had'e da d'an ta6a hira har take yi mata nasiha kan ta rik'e mijin ta da kyau, don irin wa'annan mazan yanzu sunyi wuya.

Nan Musirrah ta yita mata godiya har ta wuce, nan take cewa Mama Baraka ta Bari ta kimtsa sai suje gida gurin Ammi.

*SDY JEGAL*��

      Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣7⃣/6⃣8⃣��

Bayan ta gama kimtsa wa ne suka wuce sai gidan Ammi murna fal a ranta na yau zata ga Ammi duk da ta zo sau d'aya bayan auren ta, 6angare d'aya kuwa ji take yi tamkar ta had'iye Mama Baraka.

Da sallamar ta ta shiga gidan ita da Mus'ab sai Mama Baraka dake biye dasu, kuwar Mukarrama ta fito da ita daga kitchen, manne da juna ta sa me su tamkar wa'anda suka yi wata basu ga juna ba.

"Ku matsa ku hargitsa gida tunda abinku ba na hankali bane".

Nan Musirrah ta saki Mukarrama ta durk'usa ta gaida Ammi, nan ma suka gaisa da Mus'ab ya wuce office.

"Hala ina kika sa mu bak'uwa?", cewar Ammi da yake ko da suka shigo kan mama Baràka soke yake k'asa.

A hankali ta ta ka zuwa gurin Mama Baraka tana rik'e da hannun Ammi, sai da ta isa gurin ta sannan ta had'a hannun su guri d'aya, d'agowar Mama Baraka suka had'a ido.

Da k'arfi Ammi ta furta Baraka!, "da ma kina duniyar nan?, ikon Allah".

Nan dai suka yi ta murnar ganin juna Ammi ta rasa ina za ta saka Baraka akan murna.

"Musirrah ina kuka had'u da Baraka halan?".

"Wallahi kin ga Ammi miya ce ta zubar min a k'afa, shi ne ko da muka je office d'in abokin shi muka gan ta, kin ga ma Ammi ni na fara ga ne ta, ai nasan da yaya Mubarak ne ba za tak'i ga ne shiba", tana maganar ne cikin shagwa6a.

"Yo banda abinki ta ya za'a yi in k'i ga ne Mubarak?, ai ko da ban yiwa kaina adalci ba".

"Ah ba ma yaya Mubarak d'in ne baki wa adalci ba kan ki ne baki wa ba?".

Nan dai suka had'u suna hira da farin ciki fal a ransu, Musirrah ta fitar da wayar ta sabuwa da Mus'ab ya siya mata ta kira yaya Mubarak tana shaida mai duk inda yake yayi sauri ya taho gida yaga wani abu.

Da saurin shi ya shigo falon hankalin shi ta she saboda ya zata wani abu ke faruwa.

"Zo nan kusa Mubarak in ganka". Muryar da ya ji ta do ki kunnen shi kenan, juya warda zai yi kenan ya ga Mama Baraka, murna da farin ciki su suka hana mai magana.

Hakan ya ja jiki har ya isa inda take zaune ya durk'usa gaban ta had'e da ce wa "Mama ina kika shiga hala? Kwanakin baya na je neman ki gidan da muka yi zama amma aka ce min kin dad'e da ta shi, wanda ko Ammi ban gaya wa na je ba".

"Saboda so nayi sai na ne mo ki kawai ta gan mu tare, ashe Sister ce ke da rabon fara ganin ki".

"Da ma kina cikin garin sokoto ne da zama ko yaya?".

"Ai dai kana bari ta sa mu abinda tacci sannan ka je ro mata tambayoyi?", cewar Ammi.

"Ai na ci abinci gidan Musirrah k'oshe nake, ahh su Musirrah har an yi aure, to ni ina suruka ta?".

"D'an na ki bai gama ruwan ido ba har yanzu", cewar Ammi.

Nan dai suka ne mi sanin tarihin ta bayan rabuwar su, hakan ya sa ta gaya masu ce wa bayan ta koma garin su Birnin kebbi ne ta auri wanda suka so auren juna har ta gudu sanadiyyar an hana su auren juna.

Nan ta d'ora da gaya masu bayan auren ta shiga matsaloli da dama wanda bata jin sanyin mijin daga baya, ka ma daga kanshi har y'ay'an shi dama mahaifiyar su.

Bayan aure na da shekara biyu ne Allah ya yiwa mahaifina rasuwa, wanda naji mutuwar sosai har cikin raina, nan na fara fuskantar cewa abinda maigidan ke yimin ba yin kanshi bane asiri ne, saboda fuskantar ce wa yana so na sosai".

"Saboda ranar da kaina na ga abokiyar zama na na binne layu a tsakar gidan mu, wanda bayan ta d'aga ne na tone abin na k'o nasu sai ga shi zaman mu dashi ya dawo lafiya lau har yana ba ni kulawa fiye da farko, wannan ya k'ara haddasa yaran ta suka d'oramin k'iyayya, duk da ina iya bakin k'ok'ari na don nusar dashi wasu abubuwan".

"Shekara biyu da suka wuce Allah ya yiwa maigida na rasuwa sanadiyyar had'arin mota da yayi".

"Na shiga tashin hankali sosai wanda lokacin daka kalli abokiyar zama na za kace mutuwar tamkar abin murna ce a gare ta".

"Sanadiyyar yaran ta shida, hud'u maza mata biyu wanda ni ko ko 6atan wata banta6a yi ba".

"Bayan gama takaba d'ita ne da wata biyu yaran ta suka saka ni gaba Dole sai na bar masu gidan su, duk da ba wata dukiya ne da mahaifin su ba, hakan na had'a y'an kaya na na koma gaban mahaifiya ta domin kulawa da ita ga tsufa ya zo mata".

"Lokacin da maigida na yacika wata goma da rasuwa Allah ya kar6i ran mahaifiya ta wacce ita kad'ai ta rage min a duniya sai kuma wani k'ane na, fad'ar tashin hankalin da nashi ga ma 6arnar baki ne".

"Hakan nake zaune gidan tare da matar k'ane na da imani bai gama game zuciyar ta ba, don ko abinci tsiyar ta ta tashi banda rabo a cikin shi".

"Daga baya ne ciwon sugar ya bayyana a gare ni wanda daga Birnin kebbi aka turo ni nan domin ganin likita, nan ne muka had'u da Musirrah".

Sun tausaya mata sosai musamman Mubarak dake jin ta tamkar k'anwar Ammi.

"Daga yau kukan rashin haihuwa ya k'are maki Mama, ke da kike da kamar ni a duniya dama na dad'e da k'udurta ma rayuwa ta neman ki duk inda kike".

Ammi ba k'aramin dad'i taji ba akan furucin Mubarak, don tabbas Mama Baraka ta taimake su lokacin da suke cikin tsananin neman taimako.

"Yanzu ke da wa kuka zo Mama?" Cewar Mubarak.

Nan ta d'an razana alamar tunawa da wani abu.

"Ai ko ka ga murnar had'uwa daku na manta da ina tare da wani Sule da k'ane na Ibrahim ya had'ani dashi".

"Yana ina yanzu Mama?".

"Dama mun ajiye ne sai ya gama jigilar shi in zai koma yatai asibiti ya d'auke ni".

"To kiyi zaman ki Mama in yaso nan da kwana biyu yaya Mubarak yakai ki gida", cewar Musirrah.

"Aah ba ayi hakan ba, yanzu dai Mubarak yaje yakai ta asibiti d'in su wuce da mutumen, ai zamu shigo Bk d'in nan da kwana uku za muje har gidan asan tayi".

Da hakan aka had'a wa Mama Baraka goma ta arzik'i, har Abba ya fito suka gaisa yana ta yi mata godiya, har gurin Haj Maryam mahaifiyar Abba aka kaita suna ta mata godiya.

****

Yau satin Umma biyu a gidan da su Ammi suka ta shi, ita kad'ai ranta gidan sai dattijuwar da ke taya ta zama a gidan.

Duk da cewa lokaci zuwa lokaci Haydar da Mubarak har ma da Mukarrama suna kawo mata ziyara, musamman Haydar da Mubarak kusan kullum nan suke cin abincin dare, saboda da wuya kagan su ba tare ba, don Haydar na son y'an uwan shi sosai.

Wani lokaci Umma in ta ga yadda Mubarak ke bata kulawa har hawaye take yi, saboda abinda yake yi mata ko Ammi mahaifiyar shi nan zai tsaya, saboda sau da dama yake siyo mata kayan abinci ya kawo mata yace shi da Haydar suka siya mata, wanda wataran Haydar ke gaya mata bai ma san ya yiba, saboda yanzu Mubarak ya samu aiki a Eco bank, wanda Haydar suke business da Abba saboda dama shi ya karanta.

*03:00am*

Tana kwance kawai ta ji dirar mutane a gidan kafin tayi wani yunk'uri sai gasu a d'akin ta.

Iya rud'ewa da tashin hankali ta shige su, ba abinda bakin ta ke furtawa sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

D'ayan ya nuna ta da bindiga yana ce wa "kud'i ko rai".

"Don Allah kuyi hak'uri wallahi banda kud'i".

"Oga in ba kud'i ta ba mu gwala-gwalai", Cewar d'ayan saboda su uku suke.

"Don Allah Ku yimin rai wallahi su ma ban da", cikin tashin hankali take rok'on su, saboda maganar gaskiya yanzu bata da komai sai rai da hak'uri, don ko sati bata yi ba da siyar da gwal d'in ta d'aya da tayi mata saura.

Ganin ce wa za ta ka wo masu cikas d'ayan ya halbe ta da bingida saitin damtsen ta, nan suka haura katanga suka tsere.

Note: kuyi hak'uri da rashin jina jiya, wannan ya faru ne sanadiyyar fafutukar canja blog da nayi saboda ance mywapblog zai daina aiki.
    Yanzu ga sabon blog d'ina domin gyaran kuskure na in kun ganshi. Www.sadijegal.blogspot.com

*SDY JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣9⃣/7⃣0⃣��


K'arar bindigar ne ya tayar da dattijuwar da ke taya ta zama daga bacci, da saurin ta ta fad'a d'akin ganin Umma ta yi zube a k'asa ga jini na biyar kafad'ar ta.

Nan ta d'auki wayar Umma ta kamo lambar Haydar ta kira take gaya mai meke faruwa, kiran asubar farin ya yi dai-dai da ta da mota da ya yi, cikin sauri Mubarak ya cimma shi da tambayar ina zaije haka?.

"Iya lantana ta kira ni wai 6arayi sun shiga gidan Umma har sun harbe ta".

Cikin azama ya fad'a motar suka wuce sai gidan ta, haka suka kwashe ta sai asibiti mafi kusa, dak'yar aka samu fitar da albarushin da aka harbe ta dashi.

Sai kusan k'arfe bakwai suka bar iya tare da ita kan ce wa za su je gida su dawo.

Da sallama suka fad'a falon suka ci karo da Ammi tana batun shiga kitchen.

"Ina kuka shiga Abban ku ya fito ta daku kuje masallaci ya tarar wayam ba ku nan?".

"Wallahi Ammi 6arayi suka shiga gidan Umma har sun harbe ta a kafad'a, daga asibiti muke", Mubarak ne ke gaya mata.

"Subhanalillah, injin abin da sauk'i?".

"Eh to anyi nasarar ciro albarushin yanzu ko da muka fito ta sa mu bacci", cewar Haydar.

"To bara in d'ora breakfast in gama sai muje akai mata daga nan in dubo jikin na ta".

Shesshek'ar kukan Mukarrama suka jiyo a falon, nan dai Ammi ta yita rarrashin ta su kuma suka wuce part d'in su.

Bayan ta gama aikace-aikacen ta ne ta had'a abinci a warmer, sai ruwan tea a flask tana fitowa da kayan ne falo sai ga Abba ya fito.

"Ammin yara me ake had'awa hakan duk gida ya game da k'amshi haka?".

Nan ta yimai bayanin abinda ke faruwa har ta d'ora da ce wa' "yanzu nake batun shiga in gaya ma zan bi su in dibo jikin na ta in ya so Mubarak sai ya dawo dani".

Nan ya yi kicin-kicin da fuska tamkar bai ta6a dariya ba.

"In dai har ni ke iko dake ban yarda kije ko ina ba, su suje kawai Allah yabata lafiya".

Da hakan ya juya ya ko ma bedroom d'in shi, wanda ya yi dai-dai da fasa kukan Mukarrama.

Nan dai Ammi ta taushi zuciyar su ta had'a kayan abincin ta ba su suka wuce, wanda duka rayukan su basuyi dad'i ba da abinda Abba ya yi.

****

Yau ta ka ma weekend Mus'ab na gida sai kai kawo yake yi, duk inda Musirrah ta saka k'afar ta yana biye da ita don har girki tare suke shiga kitchen.

"Haba K'albee na ya kama ta kaje falo ka zauna har in k'ara sa aikin mana, kai ba kuku ba sai zaman kitchen", tana magana da murmushi a fuskar ta.

"Ke kan ki Hayatee kin san bazan zauna kina fama da aiki ba, in kuma kora ta zaki yi sai in fice daga gidan gaba d'aya".

'Ni na isa, kawai ina so kaje ka huta ne karka wahala".

Nan dai ta kammala aiki ta had'a komai suka zube k'asan kafet a falon, saboda al'adar shi a k'asa yake cin abinci.

Zaune ya yi dirshan ya janyo ta saman cinyar shi ya d'ora cikin dariya ta furta.

"Zan ga yadda za'a ci abinci yau, ka kawo ni saman cinya ka d'ora haka tamkar wata jinjira".

"Ai yadda nake jin ki jinjiri bazai kai ki ba, yadda kikasan d'an cikin k'wai haka nake jinki araina".

Da hakan ya rik'a ciyar dasu tana saman cinyar shi har suka k'are, a tare suka kwashe kayan abincin kuma suka kimtsa gurin.

"Yanzu abu d'aya ya rage mana shine wanka sai mu kimtsa in kai ki gidan Dr Shureim da uncle Hakeem, saboda na gaji da mitar su kan cewa 6oyon ki nake yi".

Da hakan suka shiga wanka a tare, saboda tun tana jin nauyin shi kan wasu abubuwan har ta saba yanzu.
   Suna gurin wankan ne wayar ta ta d'auki ruri, sai bayan sun k'are ne ya nad'ota a towel tamkar wata jinjira, bai sauke ta a ko ina ba sai gaban mirror.

Falo ya wuce inda ta ajiye wayarta ya d'auko ya mik'a mata, ko da ta duba taga ce wa Mukarrama ce ta Kira ta har sau uku, nan ta shiga kiran lambar.
  Bayan ta d'aga ne take gaya mata abinda yafaru da Umma, sannan ta gaya mata asibitin da suke daga nan suka yi sallama.

Mai ta d'auko tana sha fa mar nan take gayamai abinda ke faruwa da Umma, shi ma ya jajanta abin.
  Ya d'ora da ce wa "to mu d'age tafiyar sai zuwa next week, yanzu sai mu wuce asibiti d'in".

Da hakan suka kimtsa sai asibitin, ko da suka je d'akin ya cika mak'il da mutane don har surukan ta Ummy da Baffa, Iman da Nibras duk sun zo.

Nan dai suka zauna had'e da jajanta ma juna abinda yasamu Umma.

Mukarrama ce ta ta shi ta je har gaban Baffa ta durk'usa had'e da rok'on shi alfarma kan yaje ya rarrashi Abban su yamayar da Umma.

"Ban can-can ci hakan ba, matsayi na na mace mai son kanta dayawa, bana zargi ko ganin laifin Abban ku ko kad'an saboda ni mai laifi ce wanda nasan ce wa banga sakamako ba har yanzu".
   Tana maganar ne idon ta taff da hawaye wanda har kullum tana cikin nadama marar misaltuwa, musamman yau da Mukarrama ke gaya mata har da Ammi suka so tahowa Abba ne yahana ta zuwa.

Gefe d'aya kuma yadda Mubarak ke wahala da ita ganin tun faruwar abin har yanzu bai sa mu zama ba.

Rukayya ce da Musirrah suka zo gaban gadon suna rarrashin ta, wanda Musirrah har da guntun hawayen ta.

Nan Baffa ya saka baki yana mai she da masu yanzu zai wuce gidan na shi ayita ta k'are, wannan zuciya tashi ta yi yawa ace mutum bai tank'waruwa, yana mitar ne yace Ummy ta ta shi su wuce gidan.

Da hakan ya ja mota suka wuce. Bayan shigar su gidan ne aka gaggaisa Ammi ta shiga ta kira Abba, yana fitowa ya had'e fuska don yasan kwanan zancen.

"Allah ba fuska ba komai kake had'ewa yau dole ayita ta k'are, wannan zuciyar ina za kaje da ita ne?".

Nan dai suka gaisa ya nemi guri ya zauna, nan yake k'ara tunkarar shi da maganar yana mai ba shi hak'uri. Haka ma Ummy ta saka baki ita ma ta d'ora da ce wa kadubi girman Allah da kuma darajar yaranta ka tausaya mata".

"Ni inaji duk wanda akayiwa laifi bayana yake, kuma wallahi ni har ga Allah na yafe ka mayar da uwar y'ay'an ka".

Hara rar da ya bita da ita ne ya sa ta sunne kai k'asa tana murmushi, saboda tasan kwanan zancen duk randa tayi mai maganar ya mayarda Umma ce wa yake yi batasan ciwon kanta ba.

"So kuke yi in maida ta wataran mugun halin ta yasa dani har yara na ta banka mana wuta a gida mu k'one k'urmus".

Nan dai suka yi murmushi su duka Baffa ya d'ora da ce wa.
    "Kawai ka fito kace mana baka shiryawa mutuwa ba shiyasa kake wannan kame-kamen".

"Yo ai kai shi ne naga ka shiryawa mutuwar har ka rungumi transformer".

Nan dai suka yi ta dariya cike da walwala da nishad'i har suka ciyo kan Abba ya furta ce wa ya mayar da Umma, amma da sharad'in muddin ta dawo ta nemi ta yar mai da hankali to wallahi zai tsinke sauran igiya d'ayar da ta yi saura tsakanin su.

"Ai gaskiya daka ganta Abban Haydar za kasan ce wa ta yi nadama sosai", cewar Ummy.

"Yo ai ke ma saura k'iris ki yiwa rayuwar ki gi6i Allah ne kawai ya ku6utar da ke", inji Baffa.

"Me nayi ni kuwa Baffan Iman?", tana maganar ne cikin fargaba da sauraren me ke faruwa.

Nan dai ya kwashe abubuwan da tayi na korar Ammi da mak'alawa Mubarak sata yagaya mata.

K'asa ina ma za ki bud'e in shige, ashe ni ina dubin yara na kawai suka san da maganar ashe har Baffa ya sani, kai amma dai ya kwafsamin gaban surukan mu yake wannan maganar, ko dai ya manta iyayen matar Mus'ab ne? Yasan dai akwai surukanci tsakani, ohh shi har ya manta kenan ya fi ba wa abota muhimmanci.

Duk acikin zuciyar ta take wannan maganar, nan dai ta fuske ta furta cikin k'arfin hali da borin kunya.
  "Baffan Iman ai wannan sharrin shaid'an ne, kuma ga wannan lokacin dubin nake yi tamkar za ka iya auren Ammin su Mubarak ne, ina zan iya had'a kishi da ita", tana maganar ne cikin murmushi da jin nauyi.

Har zai furta ai ko ita na so na aura inda mijin ta rasuwa yayi, komai ya tuna kawai ya ja bakin shi ya tsuke.

Nan dai ta rok'i gafarar Ammi.
  "Haba ai komai ya wuce wallahi, Allah dai yak'ara had'a kan mu da yaran mu baki d'aya", nan suka amsa da Ameen suka rabu cikin farin ciki da walwala.

*SDY JEGAL*

www.sadijegal.blogspot.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.

SANADIN KUNCI 51-60

[7:25AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣1⃣/5⃣2⃣��

Ohhhh! Duniya ina za ki damu? Kawai akan zamantakewar kishi za ki sa akashe kishiyar ki, miye ribar ki anan? Yanzu da ace an kashe ta da wanne ido za ki kalli ubangijin ki ranar alk'iya ma?", duk Alh Farouk ne ke furta wa'annan maganganun, duk wanda ka kalla a falon za kaga idon shi har sun kumbura kan kuka.

Inda wa'ansu ke tausayin irin wahalhalun da ta sha wanda duk da haka ga su a raye su dukan su, lallai tabbas da gaskiyar bahaushe da yake ce wa' "wahala bata kisa sai kwana sun k'are".

Sai da Baffa ya rarrashi mutanen falon aka samu suka tsagaita kukan, amma fa da ka kalli d'iyan Haj Zainab ka san cewa suna cikin tashin hankali marar misaltuwa.

Baffa ya ce' "Haj Zainab garin ya ya hakan ta kasance har kika ba da kwangilar kisan abokiyar zaman ki?".

Dak'yar ta sassauta kukan da take yi saboda ji take yi tamkar k'asa ta bud'e ta shige, ko kuma yanzu mala'ikan d'aukar rai yazo mata, ta bud'a baki ta ce'

"Wallahi duk abinda ya faru sharrin shaid'an ne da son zuciya, sai kuma zugar wata k'awata Haj Karime, tun lokacin da za ayi auren take ta zuga ni kan cewa kar in kuskura in bari ayi auren, in ba hakan ba zuwa gaba zan zamo abar tausayi, ba akan komai ba sai don ce wa wasu amare in sun shigo neman suke yi su fitar da uwargidan ko kuma su mayarda ita tamkar shara cikin gidan".

Allah shi ne shaida ta lokacin da aka auro Hauwa'u hankali na ya kwanta da ita saboda yadda take ba ni girma, musamman duk abinda za tayi na girki ko makamancin hakan za ta ce min Ummar Jameel ya za'a yi, sai abinda na ce take yi.

Bayan kusan sati biyu ne Haj Karime ta zo gidan, nan ta saka ni gaba tanai min fad'an cewa har kishiya abar yarda ce, barrantana wa'annan amaren masu mugun rawar kan tsiya.

Ta d'ora da ce wa yanzu ga yayar ta can kishiya ta ko rota da yara biyar, jin hakan ya sa na tsora ta sosai musamman ganin cewa Alh na son Hauwa'u sosai.

"Ganin bayyanar ciki gare ta da kuma irin kulawar da Alh ke ba ta shi ya k'ara ta yarmin da hankali, nan na rik'a takura mata amma fa duk abinda nake yi ba na yi a gaban Alh, wannan kuma duk cikin kissar Haj Karime ne, a cewar ta ko da mun ta shi aiwatarda k'udirin mu ba za'a zarge mu ba".

"Sai ga shi haihuwar farko ta fa ra da namiji sai nake ganin tamkar za ta rik'a haifo maza ne sai tashin hankali na ya k'aru a wannan lokacin, da Alh ya biya mata aikin hajji ne na kasa 6oye bak'in ciki da damuwa ta har na fito k'arara na nu nawa Alh wanda yaso zama sa6ani tsakani na da shi, daga baya ne Haj karime ta ba ni shawarar in kwantar da hankali na in ta wuce kawai mu baiwa Mubarak guba ko maganin 6era yasha, in ya so bayan ya mutu za muce fitar da shi ne da akayi daga mamma ya yi ta zawo shine ya zamo ajalin shi".

"Bayan ta wuce ne na so aiwatar da k'udirin mu sai Hassy mai aiki ta zamo Katanga a tsakanin mu, domin ita ke kula dashi ko yaushe, nan da can ba ta d'agawa ta bar shi".

"Ban manta wa akwai lokacin da na jik'a maganin 6era ana saura kwana hud'u Hauwa'u ta dawo da niyyar ce wa zan kai k'arshen shi. Sai da na fito na saka ta aiki da niyyar ta fice in ba shi maganin sai ga shi ta d'auke shi ta sa6a a baya ta fice, ranar ji nayi tamkar in kashe ta".

"Hakan dai ta dawo ban samu cika nufi na ba akan Mubarak, nan dai Haj ta ba ni shawarar dole in sa Alh ya ko ri Hassy in ba hakan ba akwai matsala nan gaba, da hakan na ce wa Alh ai Hassy satar shinkafa da kayan abinci take yi muna, Alh ya so in Kira ta yaji in har rashi ne yayi mata yawa a rik'a tallafa mata da abincin nan nayi tsaye sai dai a sallame ta".

Da hakan aka sallami Hassy mu kuma muka cigaba da shawarar hanyar da za mubi mu fitar da ita daga gidan Allah bai k'addarta ba har sai da ta samu cikin wannan Musirrah d'in.

Saboda Alh na tafiya sokoto akai-akai sanadiyyar aikin gidan da yake yi da za mu ko ma, lokacin mu kayi magana da wani d'an daba muka ba shi kwangilar shigowa su d'auke Hauwa'u su fice da ita har yaron ta".

Nan na ba su dubu talatin wanda bayan an yi maganar k'arshe kan ce wa za su kai ta su yar ne, Haj Karime ta kira ni ce wa su ma kashe ta gaba d'ai a huta".

Lokacin na nu na mata cewa bazan iya ba wanda muka so samun sa6a ni ni da ita, sai da ta nu na min cewa in fa ba'a kauda ita ba komai jimawa za ta da wo kuma asirin mu zai tonu, da hakan na amince har na kira d'aya daga cikin su ce wa su kashe ta zan k'a ra masu wasu kud'i akai, bayan sun da wo ne na k'a ra masu wasu kud'in".

"Can gura ren asuba na ta shi na saka fetur a d'akin Hauwa'u, saida na had'a kan yara na da sauran abinda nake buk'a ta guri d'aya sannan na cinna ma d'akin wuta, wanda ni da kaina na firgita na fita neman taimako saboda har d'aki na sai da wutar ta ka wo, ba'a samu kashe wutar ba saida ta lashe komai na gidan part d'in Alh ne kawai bata kaiba sanadiyyar shine na farkon shigowa gidan".

"Bayan an kashe wutar ne na yi kuru-ruwa ina neman shiga gidan ina ambaton Hauwa'u da Mubarak had'e da furta sun mutu, nan hankalin mutane ya kawo aka shiga gidan iya bincike babu alamar su nan aka hakura saboda ganin irin 6arnar da wutar ta yi".

Bayan an yiwa Alh waya ya dawo ne cikin tashin hankali da firgici wanda sanadiyyar hakan sai da ya kwanta asibiti na tsawon sati d'aya, bayan sati uku ne da faruwar wannan lamarin na tunkari Haj karime domin kar6ar gwala-gwalai na da na ba ta ajiya had'e da kud'a d'ena na tarar wayam wai sun ta shi daga garin gaba d'aya, cikin tashin hankali na kira wayar ta bayan ta d'auka mun gaisa ne nake tambayar ta ance wai kun ta shi daga garin? Bu d'ar bakin ta tace min ga ta hanyar kano za ta ko ma garin su, cikin rud'u da tashin hankali nake ce mata kamar yaya, nan take gaya min ta ci banza maganin irin mu kenan kuma ni ce ta biyar da ta yiwa hakan, in ina da kotun da za ta kar6ammin kud'i tana jira, daga hakan ta kashe waya.

Nan na shiga tashin hankali marar misaltuwa, ga zafin kisa da ta saka ni na yi kuma ta gudar min da dukiya, hakan na ja bakina na tsuke saboda ban da abinda Zan yi da hakan muka tattara komai na mu muka da wo nan sokoto da zama".

Tana kaiwa k'arshen labarin ta fashe da wani irin kuka mai k'unar zuciya. Alh Farouk na ta shi tsaye yana nu na ta da yatsa kawai akaga ya zube a some.

       _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣3⃣/5⃣4⃣��

Cikin tashin hankalin da Mus'ab ya manta cewa la6e yake ya yi but ya shigo falon wanda ya kacame da koke-koke sanadiyyar labarin da Haj Zainab ta bada, nan mazan gaba d'aya suka yo kan Alh Farouk da sauri aka watsa mai ruwa amma ko gezau, nan Haj Zainab ta fasa kuka tana mai fad'in ku taimaka akai shi asibiti, Baffa ya sa su Mubarak suka tallafi Abba aka kaishi part d'in shi cikin sauri Mus'ab ya ce' "Baffa bara na kira Dr Shureim ya duba shi", cikin mintunan da basu wuce goma ba sai ga shi ya iso da kayan aikin shi, dak'yar aka samu numfashin Abba ya dawo, nan ya kai duban shi ga Haydar ya ce' "da ma yana da hawan jini ko?", kai kawai ya d'aga mai saboda ko magana bai iya yi, zuciyar shi ji yake yi tamkar zata fashe.

Yanzu da wanne ido za su kalli mutane ace mahaifiyar su ce ta ba da kwangilar kashe rayuwa, wannan abin da me ya yi kama, wani 6angare na zuciyar shi yana jin k'uncin rashin aure tsakanin shi da Musirrah, ashe tsananin son ta da yake ji aranshi so ne na jini wanda har yake tunanin ko mahaifiyar shi tace kar ya aure ta bazai iya ba, wani 6angare kuma yana jin tausayin Ammi yadda ta wahala dasu Mubarak lallai tabbas wani abu sai mahaifiya.

Nan dai Dr Shureim ya yi duk abinda ya da ce har aka samu Abba ya da wo hayyacin shi, sai dai cikin lokaci guda duk ya zabge gwanin ban tausayi, lallai tabbas samun mace ta gari shi ne jigon rayuwa ko a mafalki aka ce mai Haj zata iya wannan abin bazai ta6a yadda ba amma sai gashi yanzu ta furta da bakin ta.

Ana kiran la'asar kowa ya ta shi domin sauke farali, bayan sun gama ne aka kawo abinci hakan suka tsakara ba don ba sujin yunwa ba sai don zuciyoyin su dake cunkushe, nan ko wa ya kammala Ammi ta kai duban ta zuwa ga Mubarak da Musirrah cikin k'arfin hali ta ce' "sai ku ta shi mu wuce gida ko?", har sun mi k'e Baffa ya yi gyran murya ya ce' "Ku zauna".

"Amadadin aboki na Alh Farouk ina mai ba ki hak'urin abubuwan da suka faru wa'anda babu sa hannunshi ko kuma wani babban laifi da ya yi maki, saboda haka ina neman alfarma zuwa ranar larba wato kwana biyar masu zuwa ki had'a kan yaran ki da komai na ki ki koma d'akin mijin ki", cikin razana da jin maganar Baffa ya sa ta d'ago kanta, da sauri ta sadda shi k'asa sanadiyyar idon su da suka had'e guri d'aya ita da Abba.

Cikin sanyin murya da fargaba ta ce' "gaskiya na ya fe zamantakewa dashi, Allah dai ya shige mana gaba", nan dai su Haj Maijidda suka saka baki had'e da ba ta hak'uri sannan ta ce za ta duba.

Baffa ya ce' "kamar yadda aka saka ranar auren Haydar da Musirrah to tana nan ba'a d'age ba za ayita da Mus'ab insha'Allah", wani abu Musirrah ta ji ya tsirga mata tun daga saman kan ta har zuwa yatsan ta, saboda har ta hango Allah ya had'a ta da kurma sun fara soyayya duk da yanzu bata san inda za ta k'ara ganin shi ba, Mus'ab d'in da ko miskilanci ya san da zaman shi, yaushe rabon data saka shi a ido, wai ma yanzu inta ganshi za ta iya ga ne ce wa shi ne?, tabbbb wai kwando ke ce ma rariya na yoyo, har Musirrah za ta hango miskilancin wani, da yake har yanzu hankalin ta bai kai ta ga Mus'ab d'in ba akan tashin hankalin da take ciki, kuma ko ta gan shi ba lallai ne ta ga ne shi ne kurma ba tunda bata san fuskar shiba haka ma maganar shi, don yanzu haka ma ya fita raka Dr Shureim.

Cikin tunanin da take yi ne ta ji an da fa kafad'ar ta nan ta kai duban ta ga Rukayya da hawaye suka wanke fuskar ta sharkaf, dak'yar ta iya furta "ki ya femin Musirrah, ashe ko da na ko re ki lokacin da kike neman taimako ke y'ar uwata ce ta jini", nan kukan ta ya k'aru akan wanda take yi farko sai ga shi kallo ya dawo zuwa gare ta kowanne d'auke da alamar tambaya a fuskar shi, nan dai ta zayyane masu labarin aikatau da Musirrah ta yi a gidan ta.

Cikin ran Haj Maijidda ta ce to su wa'annan mugun ta ko ajinin su take, wannan bala'in dame ya yi kama, nan dai aka k'ara ja janta abin.

Ammi ta Kai duban ta ga Haj Maijidda ta ce' "sai ga shi na ga kin nuna da ma kun sa ba da Ummy, ko da ma y'an uwa kuke?", nan ta yi murmushi ta gaya mata mijin ta ne Alh Sani abokin Baffa, nan ta ga no ce wa shi ne suka je neman auren Musirrah dashi. (Tabbb ashe an kuru su Ammi an yi farin jini, Alh Sani da Baffa duk sun k'yasa, _lolx_)

Bayan an k'are ji ma min abubuwan ne Abba ya ce su ta shi su wuce, nan Umma ta mi k'e ya kai duban shi zuwa gare ta ya ce' "ke ina za ki je?", nan ta ce' "za mu wuce gida ne".

Uhmmmm! "Zama da irin ku ai bala'i ne a doron k'asa saboda haka ki sani inda dare yayi maki na sake ki saki biyu", cikin tashin hankali ko wa ya kai duban shi zuwa ga Abba, ya d'ora da ce wa kuma wallahi ban yadda ki rab'i duk wani d'an uwa na ko aboki na ba, da hakan ya cika rigar shi da iska ya wuce, ko wa sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un yake furtawa.

       _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣5⃣/5⃣6⃣��

Cikin tashin hankali kowa ke salallami a bakin shi, Haj kukan ta ya tsanan ta saboda bata ta6a tunanin ce wa Alh zai iya sakin ta har saki biyu ba, ga shi iyayen ta duk sun rasu dama hannun gwaggon ta ta tashi ganin daula ta yima ta yawa yasa ta yi watsi da lamarin ta, don ma Alh Farouk na iya k'ok'arin shi duk sallah Babba yana had'a kan yaran shi gaba d'aya suje can Birnin kebbi suyi sallah, saboda mahaifiyar shi na raye da k'annen shi mata biyu ya so ya dawo da ita zama sokoto akan izza da tak'amar Haj Zainab ya sa ta ce bata zuwa ko ina.

Gyaran muryar Baffa ya da wo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, ya ce' "gaskiya Haj baki kyauta ma rayuwar kiba duka-duka duniyar nawa ce da har za ki biye mata ki afka kan ki cikin matsalar rayuwa, halan kishi hauka ne?, yanzu miye ribar ki anan? Gaskiya banji dad'in faruwar hakan ba kwata-kwata".

"Amma duk da hakan ba yadda za'a yi saboda an zama d'aya tunda an hayayyafa, yanzu kiyi hak'uri ki je ki had'a kayan ki ki koma gidan Jameel da zama kafin Alh ya sauko zan bashi hak'uri, don ma ya yi na musulunci bai yanke igiyoyin duka ba saboda ko Allah bai son saki uku".

Nan dai kowa ya ta shi ya ka ma gaban shi saboda mai afkuwa ta afku don kuka ba shida magani, hakan Jameel ya saka su a mota suka wuce sai gidan Abba, ko da suka shiga gidan Abba na falo zaune ya jingina kanshi da kujera sai hawaye ke yimai zuba a dattijuwar fuskar shi. Cikin sauri Mukarrama ta isa zuwa gare shi ta kai hannu tana share mai hawaye had'e da bashi hak'urin abinda ya faru, wanda itama da ka dube ta zata baka tausayi sosai saboda har idon ta sun kumbura kan kuka, sa6anin Haydar dake sauke ajiyar zuciya saboda shi kukan ma ya k'i zuwar mai shi da Jameel sai dai wani k'unci dake tattare cikin zuk'a tan su, Rukayya kuwa ta ci kukan har ta gode Allah ta dangana.

Da yatsa Abba ya rik'a nuna Haj ta re da furta mata ce wa wallahi kar ta kuskura ta k'araso cikin falon, nan yaran suka had'u suna masu ba shi hak'uri amma ina ya yi nisa a 6acin rai bai ko jin su.

Hakan Jameel ya ja hannun Umma suka fita ya kai duban shi ga Rukayya ya ce su had'a wa Umma kayan ta su kai gidan shi, da hakan ya fice rai 6ace saboda yana ganin tamkar Abba ya tsaurara hukuncin zuwa ga umma. (Tabbb haba Jameel kai baka hango tarin laifin Umma ba sai na Abba?).

****  ****  ****  ****  **

Bayan su Ammi sun isa gida ne sun huta Mubarak ya kai duban shi ga Ammi ya ce' "yaushe za muje gida Birnin kebbi?", "ai tafiyar tana nan gobe, don ka ga bama sai Baffan su Iman ya raka mu ba kawai mu d'auki shatar mota muje mu kwana biyu sai mu dawo saboda shirye-shiryen auren Musirrah", Mubarak ya ce' "ko shirin tarewar ki ba Ammi", yana maganar da murmushi d'auke a fuskar shi.

Ta ce' "to ubana in ka gama shirya komai sai ka d'auke ni ka kaini in san ce wa ka matsu", nan suka rik'a murmushi shi da Musirrah, ya ce' "in ma ba zaki koma ba mu munyi kewar Baban mu saboda haka za mu had'a y'an komatsan mu mu koma gidan mu, ko ba haka ba Sister?", yana maganar yana kashewa Musirrah ido d'aya alamar tsokana.

"Ai tunda na gama wahala daku yanzu kun zama mutane kuna ce wa yanzu ubanku kuka sani, sai ku had'a kayan ku kuje can d'in ni ko zan yita addu'a inna yi aure Allah yaba ni y'an tagwaye na".

Nan ta ke kowannen su ya gimtse fuska tamkar ba su ne ke tsokana suna dariya ba, duk yadda Ammi ta so gimtse dariyar ta sai da ta fito saboda yadda Mubarak ya gimtse fuska tamkar bai ta6a murmushi ba.

"Tabbbb ai wallahi duk wanda ya ce zai zo gidannan da sunan auren Ammi wallahi sai na sheme shi, don abin ma rainin wayo ne".

Nan dai suka dawo hira cikin nishad'i da walwala wanda Ammi ke jin yau tamkar an d'auke mata wani k'aton dutse ne saman kanta saboda warwarewar komai, abu d'aya take ji a ranta matsuwa da ta yi bata ga mahaifin taba, ko ya za ta risk'e shi yanzu?.

Musirrah ta ce' "ni ko Ammi ina ganin tamkar in muka shiga motar kasuwa domin tafiya Baffa bazai ji dad'i ba, tunda kinga da kan ki kika rok'i alfarmar ya rakamu aga gida, to a tunani na tunda komai ya warware to a kira shi ko direba ne ya bamu sai muje".

"Eh lallai kin kawo shawara, ni zumud'in inga Baba yasa duk na manta hakan, Mubarak kira shi sai muji me zai ce akai".

Bayan Mubarak ya kira shi ne suka ajiye kan gobe da sassafe zai turo direba ya kaisu, da hakan suka kai k'arshen magana suka ta shi domin fara shirye-shiryen tafiya.

****  ****  ****  ****

6angaren Mus'ab kuwa yana shigowa gidan Baffa ke gaya mai ce wa yaje ya fara shiri domin auren Musirrah ya da wo saman kanshi, ji yake yi tamkar ya ta so ya rungume Baffa kan murna da jin dad'in wannan albishir, sai dai kawai ya basar tamkar bai ji mi Baffa ya ce ba, sai da Ummy ta mai-maita maganar sannan ya ce' "yanzu don Allah Ummy kama ta za'a yiwa auren dole?, kuma da wannan mitsitsiyar yarinya", Baffa ya yi mai dak'uwa ya ce' "ungo na ka, ita bata ce ka yi mata girma ba ita da zata auri tuzuru sai kai, kyawon abin ba kai kad'ai na haifa ba in har ka d'auko min al'adun wasu (SIS BATUL MAMMAN) sai in saka ma ido in gani in fita k'asar waje karatu hauka ne in mayar da auren kan Nibras saboda shi ma ya isa aure".

Darammm! Gaban shi ya tsinke yau ko zai ga ta kan shi garin jan aji zaren shi zai tsinke, ya ce'  "yi hak'uri Baffa ba haka nake nufi ba ai ban isa kaba ni mata ba ko da daga k'auye ne ko ince ban sonta, Allah ya shige mana gaba", nan ya ta shi ya wuce part d'in shi.

(Ni dai Jegal na ce anya Mus'ab baka zurma dayawa ba, y'ar k'auye fa kace, koda neman mafita ne kake yi, _lolx_)

        *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣7⃣/5⃣8⃣��



Hakan su Rukayya suka tattara duk wani abin buk'a ta na Umma suka kai mata gidan Jameel, gida ne da ya k'unshi part uku d'aya na Amaryar shi Yusrah, sai na shi, d'ayan da ba kowa ne cikin shi aka bawa Umma duk da ce wa Yusrah bata so hakan ba saboda an yi shine koda sun hayayyafa, hakan Umma ta zauna gidan ba don ta so hakan ba sai don ta riga tasan cewa batada inda zata je akar6e ta da daraja inda ya wuce gidan Jameel d'in.

****  ****  ****  *****

Yau kwanan su Ammi biyu a Birnin kebbi, ta yi murna sosai yadda ta tarar da Baban ta cikin k'oshin lafiya duk da ce wa tsufa ya ka kama shi yanzu, kuma ta ji dad'in yadda ta tarar da ya yi aure da wata Gwaggo Hanne. Hakan dai ta yita za ga y'an uwa da mak'ota har gurin Haj Maryam suka je mahaifiyar Alh Farouk da kuma gidan k'annen shi mata biyu wato Hafsat da Balkisu, sai baban Yasmeen Alh Ibrahim sun yita jima min abinda Haj Zainab ta aikata ta re da kwashe mata albarka saboda abin ya yi muni dayawa, nan dai take ta rok'on Haj Maryam kan ta koma gidan Alh Farouk da zama wanda sun aje kan ce wa sai ta duba ta gani.

Nan dai Baban ta ya yi mata fad'a kan ce wa ta had'a kan yaran ta in sun koma ta tare gidan ta, kuma ta rik'a addu'a sosai domin itace takobin mumini, ta tsare azkar na safe da yamma.

Kwanan su uku Birnin kebbi Baffa ya turo direba ya d'auke su suka koma sokoto cikin kewa da rashin jin dad'in barin mahaifin ta.

*BAYAN KWANA BIYU*

Duk abinda yakamata ayi 6angaren ko mawar Ammi gidan Alh Farouk anyi, sai dai abinda ya d'aure masu kai koda suka binciki maigidan da suke haya don cika mai kud'in shi yace masu bai biyarsu ko dala saboda Haydar ya saye gidan hannun shi. Nan su Ammi suka yita mamakin abin inda har Mubarak ya ce tunda bai ce komai ba akai to su zuba mai ido har suji daga gareshi.

Ranar tarewar Ammi ta ga mutane da dama ciki kuwa har da Mela da Hajiyar ta, sai kuma Haj Maijidda da Ummy da ta rikid'e ta koma k'awar Ammi.

Hakan Ammi ta koma gidan ta ta had'a kan yaran ta da na Umma duka ta rik'e wanda in har ka gansu zaka rantse da Allah ce wa duk ita ta haifesu musamman Mukarrama da suka zamo tamkar tagwaye.

Yau Baffa ya matsawa Mus'ab kan ce wa ya shirya yaje suga juna shi da Musirrah tunda dama basu had'u ba, tun ranar da Baffa ya gaya mai maganar auren yake neman hanyar da zai ga Musirrah sai dai yana jin nauyin hakan, to yanzu da Baffa ya ce ya shirya yaje wani dad'i yake ji a ranshi.

Har ya shirya ya saka manyan kaya kome ya tuna sai kawai ya koma ya canja shiga wanda ni kaina na rik'e ha6a ina mamakin zuwa gidan surukai a haka.

Suna d'aki suna hira sai ga Ammi ta shigo ta ce' "sai ku fito hakanan kuna da bak'o a waje, ko yaushe kuna d'aki tamkar wasu sababbin amare", Ammi kin manta mu ma mun kusa zama amaren", cewar Mukarrama da murmushi d'auke a fuskar ta.

"Ai ko na ga alama shi ne aka fara amarcin tun nan gida, in dai wannan ce ai amarci hali zai tarar don tun fil azal y'ar zaman d'aki ce", Ammi na maganar tana nuna Musirrah sannan ta sa kai ta fice daga d'akin.

Mukarrama ta ce' "sai ki ta shi muje daga nan ma za mu fa ra list na abubuwan da za muyi na auren", hakan dai ta jan yo wani k'aton gyalen ta ta ya fa suka fice.

Cikin mamaki Musirrah ke kallon shi, wannan shigar da ita kurma ke zuwa siyen waina kuma tana tunanin to me zai kawo kurma gidan su? Dama yasan sun ta shi daga wancan gidan ko kuma tambaya ya yi? To in ma hakan ne mi ye had'in shi da ita bayan siyen waina da zai nemi gidan su? Duk wa'annan tambayoyin kanta take yiwa su duk da tasan ba za ta ta6a samun amsar su ba sai ga kurma.

Jin sanyayyiyar muryar shi suna gaisawa da Mukarrama ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka, ohhhh! Dama ba kurma bane? To me hakan ke nufi?

Sai da ta saita nutsuwar ta sannan suka gaisa dashi, jin Mukarrama ta ce' "Yaya Mus'ab mun yi fushi sai yanzu zaka zo?", shi yasa ta k'ara tayarda kanta karaf suka had'a ido ta yi saurin sadda kanta k'asa.

"Kuyi hak'uri k'anwa ta abubuwa ne suka yi yawa shiyasa kuma kinga Antyn ta ki tafiya tayi amma ko tsaraba bata ba muba", "to shikenan ayi hak'uri yaya". Ita dai hakan ta zamo tamkar mutum mutumi saboda tabbas yanzu ta yarda ce wa shi ne Mus'ab, saidai abinda ke d'aure mata kai me yasa ya je mata a zuwan kurma?, nan wata zuciyar ta ce mata shi da kan shi yaga ya maki kurma ne?, ehhh to me yasa yake rubuta magana madadin yafurta ta?, kika sani ko baida ra'ayin maganar ne, hakan dai ta yita tafka muhawara da zuciyar ta har ta gaji, wai ashe har sun k'are tattaunawar su shi da Mukarrama akan bikin da za'a yi.

Tsinka yo muryar shi kawai ta yi suna sallama da Mukarrama, sannan ya kai duban shi zuwa gare ta ya ce' "sai mun yi waya amarya", da hakan ya ja mashin d'in shi su ko suka wuce gida wanda duk hankalin Mukarrama bai ba ta yanayin da Musirrah take ciki ba, kawai tana tunanin nauyin angon take ji shiyasa ba ta magana.

(Plxxxxx ina neman addu'ar ku zuwa ga Anty na Maijidda Musa)

      *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣9⃣/6⃣0⃣��

*BAYAN SATI D'AYA*

Zama ya fara tsanani tsakanin Yusrah da Umma, saboda kwata-kwata ba ta girmama  Umma kuma ga ta da wata al'ada ta ba'a karyawa a gidan su sai 11:00am ita ko Umma ga ta da ulcer, wanda Jameel ya lura ce wa can farko ulcer d'in Umma bata cika ta shi ba, amma yanzu mawuyacin abune Umma tayi kwana biyu lafiya lau wanda ta kai yanzu shi ke tasa Yusrah da kan shi har kitchen yace sai ta yiwa Umma girki, cikin an matsa mata ne za ta daure ta dafa mata indomie.

Yau ma kamar kullum ko da ya shiga bedroom d'in Yusrah k'arfe goma amma tana kwance sai bacci take yi, cikin 6acin rai ya tada ita ya ce' "yanzu don Allah ki duba lokaci kigani ace har yanzu baki ta shi kika girkawa Umma abinda za ta ciba", nan ta kai duban ta ga agogo ta ce 11:00 fa bata yi ba, kuma bayan ka siya mata kayan tea da komai na buk'ata za'a zo a tayar dani ina bacci na", tana maganar tana zum6ure baki.

Nan ya fita fuu ya koma part d'in Umma ya zauna rai 6ace ya ce' "Umma ki bincika cikin mutanen ki in za'a samu y'ar aiki sai a samo ta rik'a kula da abincin ki", nan ta yi wani murmushi mai had'e da nadama tattare a fuskar ta, ka basshi kawai ba sai an samo ba ko hakan nagode sosai ta shi ka wuce gurin aikin ka".

Hakan dai ya fice ko karyawa bai yiba, don dama yawanci a office yake breakfast. Fitar shi ke da wuya Umma ta zuba tagumi sai hawaye ke yi mata zuba a ranta take furta lallai tabbas duk abinda ka shuka shi ne zaka girba, saboda ita gaba d'aya hana amayar da ta ta suruka ta yi saboda ganin za'a takura ta, amma ita ga ta ga ta ta suruka sai horon yunwa take mata, kuma ba tada mafita don babu abinda za ta iya saboda ta san da ace Yasmeen ce Jameel ke aure ba za ta fuskanci wannan wulak'ancin ba.

**** **** **** ****

6angaren su Musirrah kuwa maganar aure ta kanka ma saboda gobe ne saka lalle, duk wani abu na al'adar bahaushe akan aure duk an kawo abinda ya shafi kayan lefe da kayan sa lalle.

Har yanzu Musirrah ta rasa wace hanya ce za ta bi domin tambayar Mus'ab me yasa ya rik'a zuwar mata a zuwan shi kamar kurma ne, ga shi dai sun d'an shak'u da juna sama-sama duk da ta ka sa sakin jikin ta dashi saboda su na waya kusan kullum zai kira ta, sai dai wayar daga gaisuwa bazai iya k'a rawa da wata magana ba sai dai yayi shiru itama hakan, miskilai biyu sun had'u guri d'aya.

Duk inda ka za ga cikin gidan cike yake da mutane, 6angaren y'an uwan Abba da Umma, sai kuma mukarrama da Mela da suka ta re a gidan tun jiya, haka suka had'e su hud'u tamkar y'an hud'u sai dai Mela da suka fiya girman jiki. Haj Maryam ma ta zo ta re da yaran ta k'annen Abba har da su Yasmeen da sauran dangi, Ammi sai murna take yi yadda gidan ya cika da jama'a tun kafin zuwan bikin, wanda take fatar rik'e Haj Maryam nan sokoto inshaAllah.

A d'an zaman da Mela ta yi gidan ne na fahimci y'ar guntuwar soyayya tsakanin ta da Haydar, saboda duk abinda za'a yi za kaji ya ce Mela zo kiyi abu kaza in ma abincin shi za'a kai mai to zai kira Musirrah yace aba wa Mela abincin shi ta ka wo mai.

Had'uwar shi da Mela ne ma yake ganin ce wa tabbas tsakanin shi da Musirrah wancan lokacin so ne na jini matsayin ta na k'anwar shi, don yanzu yasan ma mi ye son kan shi, (To su Haydar ayi a hankali kar a zurma dayawa)

Haj Maijidda Musa ta kira Ammi tana k'ara jadda da mata kan ce wa kar fa ta manta gobe gidan ta za'a saka wa amarya lallen har yinin gaba d'aya, Ammi ta ce' "na isa in manta maganar saka lalle gidan ki ke da y'ar ki, abinda ma za'a yi zan had'a ta ita da k'awayen ta zuwa bayan magrib sai direba ya kawosu nan su kwana".

"Gaskiya ko da na ji dad'i da hakan, ina jira sai sun iso d'in", da hakan suka yi sai anjima suka kashe wayoyin su.

Ammi ta kira Mukarrama ta ce' "ku had'a kayan ku na buk'ata ku da k'awayen ku saboda bayan magrib direba zai kai ku gidan Haj Maijidda", nan Mukarrama ta amsa ta fita.

Tana gayawa Musirrah ta fara zum6ure-zum6uren baki "ni fa kunga irin abubuwan da ke 6atamin rai ace da an tashi auren mutum shikenan ya fara yawo tamkar matar titi aje gidan d'an uwa yau gobe gidan amini, ta d'ora da ce wa randa nake da Ammi ta ban ta6a kwana wani gurin ba".

"Tabbb aiko aiki ya sa me ki, don yanzu kin kai k'arshen kwana ta re da Ammin ki, saboda mai gaba d'aya zai hau kan ki ke da zama da Ammi sai in kin zo wankan jego", nan dai suka had'u suka fara zolayar ta har jikin ta ya yi sanyi tamkar za tayi kuka.

Da hakan suka had'a kayan su sai da suka yi sallar isha sannan direba ya wuce dasu gidan Haj Maijidda.

(Gobe ko wa ya tashi tunda safe muje sa lalle, wanda ya makara mu wuce ba dashi ba, *lolx*)

      *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.