Thursday 6 October 2016

SANADIN KUNCI 6-10

[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 6⃣��

```BAYAN``` ```SHEKARA``` ```TAKWAS```

Zaman k'unci ya yiwa Alh Farouk yawa ya had'a kan iyalan shi gaba d'aya ya koma sokoto da zama.

Dama can yana zuwa saboda wasu harakoki nashi da yake yi a can, ga arzik'in shi yanzu ya k'aru akan na baya.

Yaran shi hud'u Jameel ne babba ya k'are secondary school, sai y'an biyun shi Rukayya da Aliyu suna J.S3 yanzu haka, sai kuma Auta Mukarrama tana primary4, daga Gare tane Allah ya d'auke wa Haj Zainab haihuwa.

Yara ne wa'anda suka taso cikin gata da jin dad'in rayuwa, saboda basu San wani Abu wai shi talauci ba tun tashin su.

Ga wata d'abi'a da suka tashi da ita ta gudun talaka akan muguwar ak'idar da Haj Zainab ta cusa ma yaran, basu ganin k'ima da darajar kowa.

Aliyu ne da Mukarrama Allah ya fitar daban, saboda su halayen mahaifin su suka d'auko na tausayi da kuma jin k'an na k'asa dasu.

Sa6anin Rukayya da Jameel tamkar Haj Zainab ta cire halayen ta ta saka masu a zuciya.

<<<  >>>  <<<  >>>

Abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da cigaban karatun Mubarak don yanzu haka yana gab da zana jarabawar shi ta J.S3.

Wanda ita kuma Musirrah tana primary4 ne.

Da taimakon Baraka dana Hauwa'u ne cikin aikatau d'in ta ta gina yaran ta akan turba ta k'warai, duk da cewa ba makarantar kud'i suke yi ba.

Yau Hauwa'u ta shirya zata je gidan aikin ta.

Musirrah tace'
"Ammi Zan biki tunda yau bamu zuwa makaranta"

Ammi tace'
"Kiyi zaman ki kitaya Mama Baraka aikin gida"

Nan ta tur6une fuska ta koma gefe ta raku6e sai ga hawaye sharrr a fuskar ta.

Nan Baraka ta saka baki tace'
"Tace kije da ita mana tunda basu zuwa makaranta"

Hakan ta sakata gaba suka wuce gidan aikin ta.

Bayan ta k'arasa wanke-wanke ta dawo falo ne tana goge-goge saiga Iman ta sauko daga stairs ta rik'a hannun Musirrah.

Tace'
"Muje d'aki na kiga kayan wasa na da Yaya Mus'ab ya dawo ya zomin dasu"

Hakan ta jata suka wuce d'akin ta suna wasa, saboda Iman akwai son yara.

Bayan ta k'arasa duka ayukkan tane ta gaya ma Haj zasu wuce, amma ayo Mata magana da Musirrah.

Nan Haj ta kiro Mata Musirrah sai ga Iman ta biyo ta da kukan ta tana cewa saita bita gidan su.

Dak'yar Haj ta rarrashe ta, nan takai duban ta ga Ammi tace'
"Zuwa assabar Mai zuwa zamu koma sokoto da zama kuma munyi magana da Alh kan zamu je dake in har zaki bi mu"

(Don had'uwar jinin da ke tsakanin Iman da Musirrah shi yasa Haj ta Fara sassauta Mata kyara da hantarar da take yi Mata)

Tace'
"To Haj Zan duba yuyuwar hakan kafin lokacin tafiyar"

Nan ta rik'a hannun Musirrah suka wuce gida.

Koda ta dawo Mubarak na zaune da Baraka suna hira, nan ta samu wuri ta zauna ta rafka uban tagumi.

Bayan Mubarak ya gaida ita yace'
"Ammi yau meke damun ki hala, na ganki cikin damuwa?

Baraka tace'
"Ka rigani magana ne, saboda tun shigowar ta na hango damuwa k'arara a fuskar ta"

Nan ta ko romusu bayanin abinda ke faruwa.

Sai gasu kowa yayi jugum ya kasa bakin magana.

Nan Baraka tayi k'arfin hali tace'
Ki kimtsa ki bisu kawai tunda kin ga can su zasu baki gurin zama"

"Kuma nan in kin zauna sun wuce kafin ki samu wani aiki karatun yaran ki zai ta6ar6are"

"Tabbas nasan akwai sabo da shak'uwa Mai k'arfi tsakanina dake da yaran ki, amma ki nemi na kanki yafi daki za6i zama dani"

"Ina yi maki fatan alkhairi da kuma fatar wannan tafiyar ta zamo silar ya yewar _k'unci_ a gare ki"

           _SDY_ _JEGAL��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 8⃣��

Da isowar su garin sokoto basu zarce ko ina ba sai unguwar Natu road.

Su Haj Asma'u ne suka Fara isowa saboda Mus'ab na gudu da mota sosai.

Gida ne Wanda ya amsa sunan gida saboda tsaruwar shi da kuma girman shi.

Sai da suka huta da minti goma sha biyar sannan direba D/jumma ya iso shi da su Ammi.

Nan kowa ya tashi aka zagaya gidan kowa Nata yabawa.

Bayan sun zauna ne Haj ta umurci direba ya fito da warmers na abinci, saboda tun daga gida sai da ta had'o abincin ta suka zo dashi.

Don a k'a idar ta tak'i jinin sayen abinci, duk tsiya ita ke shiga kicin ta dafa abinta.

Bayan sunci sun k'oshi ne nan Alh ya sallame su ya ba kowa part d'in shi, inda aka bawa Ammi part d'in ta cikin B/Q ita da yaran ta.

Nan aka yita tak'adda ma da Iman kan cewa ita fa sai dai Musirrah ta dawo part d'in su inba hakan ba to ta koma gurin su.

Nan Alh yace'
"Ba damuwa Iman sai Ku had'a kayan ku keda ita ku koma naki d'akin"

"Hakan ya yi maki ko Iman?

Tayi murmushi tace'
"Eh Baffa kaga nima na samu y'ar Uwa, saboda Ummy tak'i samo min k'anwa"

"Amma kaga yaya Mus'ab su biyu ne shi da yaya Nibras"

"To shikenan kema ga y'ar Uwa nan Ummy ta samo miki"

Tace'
"Baffa tunda yanzu gidan mu d'aya zaka saka mu makaranta d'aya ko?

Tsawar da Haj ta yi Mata ne yasa ta natsu wuri guda saiga hawaye sharrr a idon ta.

Nan ta d'ale k'afar Baffan tace'
"Ka gani ko Baffa nace ma Ummy bata so na, sai ta yita yimin fad'a amma bata yiwa su yaya Nibras fad'a"

Yace'
"Yi shiru daina kuka, kece Iman kin cika surutu ba ki ko gajiya, kinga k'awar ki bata da surutu"

Tace'
"Allah Baffa bata da lafiya, k'ila ma sai an kaita asibiti, Malamin mu yace in kaga mutum shiru-shiru lafiya bata ishe shi ba"

Nan Nibras ya yi murmushi yace'
"Ke kam wannan mugun bakin sai dai akashe ki ba zaki dai na surutu ba"

Nan ta Kai duban ta ga Mus'ab tace'
Kaiko Babban yaya kayi shiru kak'i magana hala Kai ma sai an Kai ka asbiti an k'arama ruwan magana"

Nan Baffa ya yi dariya sosai yace'
"Tashi ja k'awar ki kiyi d'akin Ku, wannan surutun Allah ya yi maki maganin shi"

Tace'
"Kasan me Baffa?

Ya girgiza kan shi yace'
"Ina jin ki parrot, da murmushi a fuskar shi"

Ta had'e fuska tace'
"Yanzu Baffa nice parrot, nifa da hankali na suko dabbobi Mal yace basu da hankali"

Yace'
"To yi hak'uri fad'i maganar ki Ina jinki y'ar Baffa"

Tace'
"Dama Zan ce ne da zan iya hak'ura da rashin Musirrah dasai a mayar da ita d'akin Babban yaya"

"Kaga ita bata magana shima ba ya magana, babu Mai takura wani"

Da gudu ta koma bayan Ummy ta lafe, ganin Mus'ab ya taso zai Kai Mata duka.

Nan Ummy ta janyo ta ta Kai Mata duka tace'
"Me ake yi da shegen surutu irin naki, yarinya k'an k'anuwa dake kin addabi mutane"

Nan ta rik'e bakin ta dai-dai inda Ummy ta kai Mata duka ta Fara kuka.

Baffa ya janyo ta ya rarashe ta yace ta wuce d'akin ta gobe zai fita da ita shan ice cream.
(Nidai Jegal nace wannan ko k'anwar Bizzy ce, ~lolx~)

Nan kowa ya tashi ya kama gaban shi, gurin da aka bama Ammi ba laifi, d'aki biyu ne ita d'aya Mubarak d'aya.

Tana zaune gefen katifa ta rafka uban tagumi, tana ta tunanin yanzu wane hali Baraka take ciki.

Zaman ta gidannan tana fatar ya zama silar ya yewar k'unci a gare ta, tana ji tana gani an raba ta da garin su  saboda ayi ```Sanadin``` ```K'unci``` a gare ta.

Sai ga hawaye duk sun wanke Mata fuska, nan Mubarak ya taso yana rarrashin ta har nutsuwa ta sauko Mata.

       ```SDY``` ```JEGAL```��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 9⃣��

Abubuwa sun rage ma Ammi sanadiyyar nauyin karatun yaran ta da Baffan su Iman ya d'auke Mata, kuma cin ta da shan ta su ma suna wuyan su.

Duk wannan ya faru ne sanadiyyar naci irin na Iman, saboda Allah ya had'a jinin su sosai da Musirrah.

Yanzu haka ko kaya bata saka wa in har Musirrah bata da irin su.

Ummy ta yi fad'an tayi dukan har ta gaji ta k'yale ta, amma fa abin na ci Mata rai wai d'iyar Mai aiki ta zamo dai-dai da y'ar da ta haifa.

Wannan masifa dame tayi Kama, ta Jan yoma kan ta alak'ak'ai.

<<<  >>>   <<<  >>>>


Abubuwa sun faru da dama Wanda ya had'a da kammala k'aramar makarantar su Iman.

Yanzu haka sun zana jarabawar junior living sakamako suke jira.

Inda shima Mubarak da Nibras suna D/Fodio university 100Level, shak'uwa da aminci Mai k'arfi ke tsakanin yaran.

Wanda ko yaushe Ummy take da k'udirin wace hanya zata bi domin sallamar Ammi daga gidan.

Saboda ta gaji da ganin irin hidimar da Alh ke yiwa su Ammi saboda ko kishiyar tace hakan zai tsaya.

Ko 6angaren yara abin na yi Mata k'una sosai saboda duk abinda aka yiwa Iman da Nibras shi za'a yiwa Musirrah da Mubarak.

Yau ta gama yanke ma kanta hanyar da zata bi domin raba kan ta da alak'ak'ai a cewar ta.

Bayan Nibras ya dawo daga Kai Baffa airport zai je England akan wasu harakoki nashi.

Tace'
"Iman ki shirya Nibras ya sauke ki gidan k'awata Maimuna"

"Saboda ta Kira ni cewa sark'ok'in ta sun iso, kije ki za6o muku keda Musirrah"

Tace'
"Ummy ki bari idan Musirrah ta samu sauk'in ciwon kan da ke damun ta sai muje"

Ummy tace'
"Idan aka za6e sark'ok'in fa, kin ga ki daure kije Nibras zai tsaya sai kin fito Ku dawo tare"

Da k'yar da dabara ta samu ta amince zata je nan ta wuce babu dad'i a ranta.

Sai da Ummy ta tabbatar sun tada mota sun wuce ta shigo d'akin tamkar wadda aka jefo.

Nan ta kaiwa Musirrah wani wawan Mari sai da ganin ta ya d'auke na y'an seconds.

Nan ta rik'a fitar da kayan ta tana saka Mata a wata trolley.

Tace'
"Asamu k'arawa gaba kun zo kun ta remin cikin gida kun zame min jaraba keda uwar ki, don haka wallahi yau sai kun bar gidannan"

Musirrah sai kuka take yi tana Mai bata hak'uri ko sauraren ta ba tayi ba.

Haka ta gama loda Mata kayan ta ta saka ta gaba sai B/Q gurin Ammi.

Tace'
"Wallahi minti biyar na baki ki had'a komai na buk'atar ki kibar gidannan, na gaji da jaraba kun zo kun mak'ale ma mutum, zuwa gaba sai dai in ji kin zamo kishiya ta"

Ammi ta dube ta cikin razana tace'
"In har kika yi muna hakan baki yi adalci ba"

"Bai dace ki raba mu da farin cikin muba, kizo daga baya ki saka mu cikin k'unci"

"In zaki yi duba a gare mu garinnan bamu San kowa ba ke kika zo damu, ya kamata kiyi muna halacci"

Nan ta kar6e tace'
"Da shiga k'unci na gara shiga naku, saboda ku cikin shi kuka taso"

"Kuma da kike maganar Baku San kowa a gari ba, can da kika zauna waye naki a ciki?

"Wallahi minti goma na baku Ku had'a kayan Ku kubar gidannan, muddin Iman ta dawo ta taradda Ku to Karon mu na gaba bazai muku dad'i ba.

Mubarak ya tashi tsaye ya had'a iya abinda zai d'auka yace'
"Ammi had'a kayan ki Ku fito dasu zanje in samo keke napep"

"Ke kuma Ina Mai tabbatar miki ki bi duniya a sannu domin duniya tafi bagaruwa iya jima"

"Kuma ke da kike ganin ki Mai arzik'i ba ke kikayi kan ki hakan ba"

"Kuma Mai wadata shine Mai arzik'i ba Mai dukiya da tak'ama ba"

Nan yasa Kai ya wuce, bayan ya samo napep ne ya dawo ya tarar da Ammi da Musirrah har lokacin kuka suke yi.

Ya kwashi kayan su yasa napep yace'
"Ammi Ku tashi muje"

Bayan ya tasa su gaba ne ya Kai duban shi zuwa ga Ummy.

Yace'
"Ga gida nan an bar maki sai ki jik'a kisha"

Tace'
"Na dai ji sai a k'ara gaba gayyar tsiya gayyar arna a idi"

Nan suka shiga keke napep ba tare da sanin ina zasu dosa ba.

D'aga war su ko minti goma ba'a yi ba sai ga su Iman sun dawo, da murnar ta ta shigo gidan.

Tana shigowa falo tace'
"Ummy sark'a d'aya aka samu ni Zan barwa Musirrah in yaso daga baya in an kawo wasu ni na d'auka"

Da saurin ta ta nufi d'akin su tana cewa Sis am back.

Ummy tace'
"Ke zo nan kiji"

Tana zauna wa kusa ga Ummy tace gani.

Ummy tace'
"Ki natsu ki saurare ni da kyau, yau na gaji da ganin wa'annan mutane a gidana, saboda haka na ko resu gudun su zamo jaraba a gare ni nan gaba"

Ba Iman ba Nibras kanshi sai da yaji zuciyar shi ta buga.

Iman ta murza idon ta, ta girgiza kan ta duk don ta tabbatar ba mafalki take yiba.

Tace'
"Ummy akan me kika aikata wannan mummunan abin, ba zaki yi gudun hakk'insu ya hau kan kinki ba? kece fa silar zuwan su garin nan?

Tace'
"Saboda na gaji da ganin gatan da Baffan Ku ke nuna musu, nan gaba uwar su ai sai ta aure uban Ku"

Iman na mik'e wa tsaye zata wuce d'akin su sai kawai ta tafi luuuu ta zube k'asa a sume.

       ```SDY``` ```JEGAL```��

Just for visit
Sadiyajegal.mywapblog.com

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 7⃣��

Lallai tabbas sabo wani abune a zaman takewa ta d'an Adam.

Tun safe Ammi ke shirin kayan su tana hawaye, ji take yi tamkar ta fasa wannan tafiyar, kuma tana tunanin in ta fasa wace Sana'a zata Kama.

Gashi duk sun shirya amma ta kasa motsawa can da nan, ta yi zaune ta rafka wani uban tagumi.

Baraka ta shigo d'akin tace'
"Ki tashi ki k'arasa had'a kayan ku tunda kinsan cewa k'arfe tara aka ce maki zaku wuce"

Nan ta d'ago kanta idon ta taf da hawayen da ta kasa tsaida su.

Tace'
"Gaskiya Baraka inaga Zan fasa tafiyar nan ne, Ina dubin in har na tafi na barki bansan ranar da Zan k'ara saka ki a idona ba"

Tace'
"Wannan kuma bamu San lokacinda Allah zai had'a mu ba, nidai a kullum Ina Mai yi maki fata na alkhairi akan wannan tafiya taki"

Suna cikin hakan ne sai ga Musirrah da gudun ta.

Tace'
"Ammi wai kiyi sauri ga direba nan yazo d'aukar mu, kuma yace Mum Iman tace muyi sauri mu kad'ai ake jira"

Nan Baraka ta d'auki jakar kayan su ta fita da ita wurin direba, sannan ta dawo takai sauran kayan mota.

Tana shigowa ta rik'a hannun Ammi suka fita, koda suka iso Musirrah har ta kame gidan gaba tayi zugum.

Mubarak ya koma gefen mota ya raku6e har wani zazza6i yake jin na ratsa shi.

Saboda idan har za'a yiwa sabo kuka to shi yana ganin nashi hawayen zasu k'are.

Don yafi kowa sabo da ita, domin tafi kowa sanin halayyar shi.

Da hakan suka shiga mota har Baraka d'in don tana son ganin wuce warsu.

Koda direba yaje har su Haj sun shiga mota suda yaran su, su kawai suke jira.

Suna isowa Baraka ta fito tana hawaye tana Mai Shafa kan Mubarak.

Tace'
"Yaro na Allah ya sada mu da alkhairin sa sai watarana ka kula da karatu, Allah ya sakawa rayuwar Ku albarka"

Nan kukan shi ya tsanan ta yace'
"Mama nayi maki alk'awari a rayuwa duk inda na shiga muddin na zama wani Abu sai na nemo ki"

Suna hakan sai ga Haj ta fito daga d'ayar motar tana rik'e da hannun Iman, akan ta rik'a rigima ita dole sai an Mai data gurin Musirrah.

Bayan Haj ta saka tane takai duban ta ga Baraka tace'
"Ki koma gida kuyi hakuri saboda mu zamu wuce"

"Kuma ma in banda abinki miye na damuwa akan zata tafi ta barki tunda babu gamin iya bare na Baba"

Nan ta ta6e baki tace ma direba "ka tada mota mu wuce Rana tayi"

Hakan Ammi ta shige motar tana hawaye, Mubarak ma sai ajiyar zuciya yake yi.

Nan mota ta tashi suna masu d'aga ma juna hannu.

Suna 6ace ma ganin juna Ammi ta Saki wani kuka Mai cin rai, Mubarak sai girgiza ta yake yi alamar rarrashi shima yana ajiyar zuciya.

Nan Musirrah ta juyo ta kai duban ta ga Ammi tace'
"Ammi kiyi hak'uri ki daina kuka kin ga zamu koma sabon gida ne inji Iman"

Nan direba yayi murmushi yace'
"Kiyi hak'uri Maman Mubarak ansan sabo wani Abu ne a zaman takewa, amma tunda rabuwar ta zama dole kiyi hak'uri idan da rai watarana zaku had'u"

Nan ta share hawayen ta tana tunani a ranta ko ya ya rayuwar ta zata kasance Zan gaba.

(Nima kaina Jegal na tausaya masu don  sai da suka saka ni kuka  ```Lolx```)

           *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣0⃣��

Tunani kawai Mubarak keyi kan ina zasu dosa, bai shirya ma ko mawa Jega ba yanzu.

Yasan dai suna da isasshen kud'in da zasu nemi gidan haya, saboda idan Baffa ya bashi kud'i ajiyewa ya keyi.

Kuma Ammi ba zata rasa kud'i a hannun ta ba saboda basu cin komi da kud'in aikatau d'inta, kuma Alh yasa an k'ara Mata sun koma dubu goma.

Sai dai in yace su kama gidan haya gidan su suka d'ai zasu can ye kud'in ne basu k'arasa karatun su ba.

Mai keke napep yace'
"Malam sai tafiya muke yi baka gaya min ina zamu je ba"

Maganar ce ta dawo dashi hayyacin shi, ya Kai duban shi ga Ammi yaga har lokacin hawaye take fitarwa.

Musirrah ma tayi jugum sai ajiyar zuciya take sauke wa.

Yace'
"Muje Gobirawa nan zamu samu gurin zama inshaAllah"

Bayan Mai napep ya tsaya nan yafita yaje gurin wani Mai shago ga alama tambayar shi yake yi, Wanda bana jiyo me suke cewa na dai hango yana yi mashi nuni da hannu.

Daga nan ya nuna Mai napep wata kwana, bayan ya shiga ne suka sauka gaban wani gida.

Nan ya fitar da kud'i ya sallame shi, sannan ya nuna ma su Ammi gurin wata inwa yace su zauna su bashi minti goma.

Bayan yaje ya dawo ne da maigidan nan suka shiga ya duba d'aki biyu cikin d'aki shida dake gidan.

Sauran d'aki uku akwai mutane cikin sa, bayan sun k'arasa cinikin ne ya ciro kud'i ya bashi.

Nan suka fito a Jere mutumen ya wuce shiko yaje ya d'auko kayan su had'e gayawa su Ammi cewa ya gama komai su tashi su k'arasa ciki.

Bayan sun shiga ne sun gaisa da mutanen gidan suka shiga d'akin.

Mubarak yace'
"Ammi ke ga inda rayuwa ta Mai damu da zama, saboda haka kuyi hak'uri komi yayi farko zaiyi k'arshe inshaAllah.

"Kuma ki karanci zama da mutanen da muka tarar a gidannan ba lallai ne ki sa same su yar da kika samu rayuwar Mama Baraka ba"

"Zaman gidan taro matsala ne dashi kowa da irin halayyar shi"

Yakai duban shi ga Musirrah yace'
"Kiyi hak'uri ki daina kukan ya isa haka"

Ammi tace'
"Jikin ta ma yayi zafi kasan dama tana fama da zazza6i"

Yace'
"Bara in je in nemo Mata magani daga nan in in sawo muna kayan buk'ata"

Tace'
"Inada kud'i hannuna bara in baka ka k'ara"

Yace'
"Ki ajiye na hannun ki in har na natsu Zan ne moma Sister makaranta ne"

Nan ya fita ya siyo magani had'e da abincin da zasu ci da kayan buk'atar su.

Ammi tayi ta saka mashi albarka da jin dad'in yada yasan ciwon kan shi har ya iya ajiye kud'i haka.

Saboda Baffa nada k'ok'arin basu kud'i shida Nibras, akan ya d'auke masu ko wace lalura ce yasa ya bud'e account yake ajiye su can.

<<<  >>>  <<<  >>>

Cikin firgici Ummy tayo kan ta da salati a bakin ta, tana girgizata tana Mai kiran sunan ta amma bata ko motsa ba.

Nan Nibras ya tashi da sauri ya bud'e fridge ya d'auko ruwa a gora aka zuba Mata, duk da hakan bata motsa ba.

Ummy ta d'ora hannu a ka ta kurma wani uban ihu tace'
"Wayyo! Allah na Iman kar ki mutu ki bar ni".

Nibras ya d'auko wayar shi ya Kira Dr Mukhtar ya gaya mashi ana Neman shi da gaugawa.

Cikin mintunan da basu Kai biyar ba ya iso da kayan aikin shi.

Nan yayi aune-aunen da zaiyi da k'yar ya samu ta farfad'o.

Sai dai tana farfad'o wa da Musirrah ta tashi a bakin ta.

Tace'
"Ummy ki ne momin Musirrah, bazan ji dadin rayuwa ni kad'ai ba".

Nan Dr Mukhtar
yace'
"Ya kamata a nemo Mata abinda take so, in ba hakan ba zuciyar ta zata iya samun matsala".

Nan Ummy taja wani gwauron numfashi Uhmmm!
Tace'
"To Dr za'a nemo Mata inshaAllah".

Nan ya bada maganin da zata rik'a sha ya sa Kai ya wuce.

Nibras yakai duban shi ga Ummy
Yace'
"Gaskiya abinda kika aikata bai yi dad'i ba, yanzu gashi matsala na son shigar Iman".

Tace'
"Yanzu kam sai dai tayi hak'uri saboda bansan Ina Zan gansu ba".

"Kuma ko ba hakan ba bazan zauna da abinda zai yi *SANADIN* *K'UNCI* agare ni ba".

Takai duban ta ga Iman
Tace'
"Ki fitar da wannan yarinyar daga zuciyar ki, kin ga duk abinda kike so ina yi maki muddin bai fi k'arfi na ba".

Nan Iman ta fashe da wani irin kuka Mai cin rai.
Tace'
"Ummy duk yar da Zan gaya maki yadda Allah ya had'a jini na Musirrah ba zaki ga ne ba".

"Amma nasan idan Baffa ya dawo duk in da Musirrah take a fad'in garinnan zai sa a ne mo min ita".

Tace,
Ke! "Kina hauka ne zaki gaya ma Baffan Ku cewa ni na Kore ta?".

"To wallahi ahir d'in ki, don na shirya abin da Zan gaya Mai".

"Kuma muddin kika 6a tamin plan to ina mai tabbatar miki gamo na dake ba zai yi dad'i ba".

Ta tashi fuuu ta wuce part d'in ta.

Nan Nibras ya matso kusa yana Mai rarrashin ta.
Yace'
"Na rasa wane irin son Kai ne ya yiwa Ummy yawa, Baffa dake kula da komi na mutanen nan bai ce ya gaji ba sai ita".

"Kiyi hak'uri zuwa dawowar Baffa muga yada abin zai kasance"

Da hakan ya shawo kan ta tayi shiru sai wata ajiyar zuciya take sauke wa.

        ```SDY``` ```JEGAL```��

Dedicated to Sanah S. Matazu.

No comments:

Post a Comment