[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣7⃣_2⃣0⃣
By *Sdy* *Jegal*
Tun suna kan hanya Shakur ke damun Zarah da cewa "gaskiya yaga Munazzafa ta girma".
Zarah tace "Broda baka ganin girmanka shiyasa", Nan yake tambayeta "yaushe za kuyi exam halan"
Zarah ta bashi amsa da cewa saura kwana goma su gama.
Har suka kawo gida zancen Munazzafa Shakur ke yi Zarah kuwa dariya take tayi don ta Fara halbo jirginshi.
Koda suka k'araso gida y'an rigimar Umma na waje suna jiransu, khadeeja ta had'e fuska tamkar hadari, tace Anty ni nayi fushi dake, tunda kika ga Broda ya dawo shikenan kika manta damu, ai can farko ko shopping zaki je mune y'an rakiya, nan ta Kama hannun Mubarak fu suka shiga gida.
Zarah ta juya da kallonta zuwa ga Shakur tace "ka gani ko Broda, khadeejar nan anyi rigimammiya, yanzu fa har gun Abba saita Kai maganar cewa na fita bada ita ba.
Shakur yace kin Riga kinsaba fita dasu dole suji ba dad'i, to ai laifin Kane Broda da cewa nayi mu tsaya aje dasu zaka ce bazaka iya da rigimar suba shiyasa na wuce.
Shakur yace saiki shiga musu da ice cream d'in ko zaki wanke laifinda kika yimasu.
Zarah tace ba dai khadeeja ba, don shegen rik'o ne da ita wai har tasan fushi, Mubarak ne Mai sauk'in Kai shiko in har ta hau fushin zakaga shima ya tayata, abin nasu har mamaki yake bani.
Nan Shakur yace shi zaije gurin frnd d'inshi Naseer, ya juya akalar motar itako Zarah ta shiga gida.
Mubarak ya mik'e zai karb'o Leda hannun Zarah sai khadeeja ta rik'e Mai hannu, nan take ya tuna cewa ai suna fushi ne da Anty, sai Zarah tayi murmushi taje kusa da Umma ta zauna gami da gaidata.
Umma tace Zarah kun d'an jima baku dawo ba, nan Zarah ke gayamata Saida suka biya duba jikin Mamar Munazzafa.
Umma tace to ya jikin ta?
Zarah ta karb'a da cewa taji sauk'i, dama malaria ce ke damunta, tace ma agaida ke.
Zarah tace Umma wai kinga khadeeja fushi takeyi Dani, Umma tace aishine daidai, tunda yayanku ya dawo kikayi watsi dasu.
Nan Zarah tayi murmushi ta d'auki kayanta ta hau stairs sai d'akinta saboda gabatowar magriba.
Bayan ta gama sallah da addu'o'in tane tana zaune Mubarak yayi sallama Saida ta bashi izni sannan ya shigo, yace kizo Abba na nemanki, amma kiyi hak'uri Anty kibani sweet d'aya kinga bani nake fushi dake ba khadeeja tace mu rama abinda kikaimana shine nima nak'i yimaki magana.
Zarah tayi murmushi ta bashi sweet, nan yafita yana murna, itama ta biyoshi daga baya domin karb'a kiran Abba.
Zarah ta gaida Abba had'e da yimin barka da dawowa, bayan ya karb'a ya jefomata tambayar waya tab'a twins d'in Umma? Nan Zarah ta bisu da murmushi, ta Kora mashi bayanin yadda sukayi, nan Abba yasa baki sannan khadeeja ta sauko.
Tana Mai cewa Abba kagayama Anty ta daina share mu don taga Broda ya dawo, Abba yayi murmushi yace zata daina.
Zarah tace Mubarak yaje d'aki ya d'auko musu ice cream, nan suka je suna murna.
****
Abba ya maida duban shi zuwa ga Umma, "yace ban samu gayamaki anga file d'ina daya b'ata kamin inje Egypt, nan ya koramata bayanin yadda sukayi da Hakeem.
Yace sanadiyyar hakan nagayamai na bashi auren d'iyata *Fateema* ranar da duk ya shirya yaturo magabatanshi da maganar aure.
Nan Umma ta bishi da kallo tana Mai cewa haba Abban twins ya zaka yanke hukunci ga mutumenda bakasan waye shiba, ya halayenshi suke?
Nan Alhj yayi murmushi yace halayen yaro bayyane suke, saboda abinda yayi shi zai baki tabbacin Mai Amana ne.
Umma tace to Allah ya sanya alkhairi, Alhj ya Amsa da Ameen "haka nakeso inji daga gareki.
Zarah ko ta Lula duniyar tunani, hawaye duk sun wanke Mata fuska, Abbanta yace tashi kije Allah ya yimaki albarka, ta Amsa da Ameen ta wuce.
Daga alk'alamin *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn Shakur.
[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 2⃣0⃣_2⃣5⃣
Shigar Zarah d'aki keda wuya, ta fad'a saman bed d'inta tana rusa kuka sai tunani ke zomata iri iri, tun tana magana a zuci har ta fito waje.
Oh! ni Zarah wane irin miji ne wannan da Abba da yayimn? Ya yanayin shi yake? Ya halayyarshi take? Dogo ne ko gajere? Shin ni banda zab'i kenan, duk da cewa nasan bansan miye *SO* ba saidai inji k'awayena na hirar hakan.
Kinada zab'i Zarah saidai zab'in mahaifinki shine zab'i a gareki.
Jin muryar Umma yasa tabi k'ofa da kallo, sai yanzu tasan cewa Ashe duk maganar da takeyi a fili takeyinta bata saniba.
Tun shigowar Zarah d'aki Umma ta biyota saboda ta rarrashe ta, kuma ta nusar da ita muhimmancin biyayya zuwa ga mahaifa.
Umma tace Zarah kiyi hak'uri, nasan cewa mahaifinki Nada tunaninda zai zab'a maki miji nagari, kinga wannan yaron ya taimaki Abban ki sosai, saboda rashin ganin file d'in zai iya dak'ushe company d'inshi nayin takalma.
Zanso ki fitadda damuwa cikin ranki kisamu k'arfin gwuywar yiwa mahaifinki biyayya, kuma shine yake da hakk'in zab'a maki miji a Karo na farko.
Nan kukan Zarah yak'aru tana Mai cewa Umma Inna tuna da cewa Naseer yayi SO na bai samu fuska gare niba har ya hak'ura sai raina yak'ara b'aci, da ace shine Zan Aura nasan da sauk'i Umma.
Umma tace kiyi hak'uri wani bai auren Matar wani.
*TUNA* *BAYA*
Naseer aboki ne ga Shakur tare sukayi degree d'insu a D'an Fodio university, kuma tsakanin unguwassu data su Naseer ba nisa sosai.
Ziyaradda Naseer ke kawoma Shakur yasa yaga Zarah har ya yaba da hankalinta da nutsuwarta.
Tun yana nunamata yana sonta a fuska har ya kasa hak'ura ya furta Mata, Wanda itako taketa kauce kauce, saboda a tsarinta gaskiya batada ra'ayin gajeren miji, shiko Naseer gajere ne fari yana da kyawon shi ba laifi.
Akwai lokacinda Zarah taje kaima Shakur wasu takaddu d'akinshi, koda ta shiga yana toilet jin motsin ruwa ya bata tabbacin wanka yakeyi. Juyawarta kenan taci Karo da Naseer zai shigo, nan ya tsare ta da tambayar cewa sai yaushe Zata bashi amsa akan maganassu?
Zarah tace yaya kayi hak'uri ka tsaya matsayin yayana, saboda haka nake jinka tamkar Broda Shakur.
Tun daga ranar Naseer bai k'ara tuntub'ar Zarah da wata kalma *SO* ba.
Bayan dawowar Zarah daga dogon tunanin da ta afka, ta k'ara fashewa da kuka tana Mai tausayin kanta na cewa yanzu wai Abbanta ya kyautar da ita da wani.
Kucigaba da kasancewa da alk'alamin *Sdy* *Jegal*✍
Dedicated to Mmn Shakur.
[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 2⃣5⃣_3⃣0⃣
Munazzafa na shiga d'aki daidai wayarta na ringing, tana dubawa taga cewa Zarah ce ta kira ta, tana d'agawa kawai taji kukan Zarah tamkar wadda aka yima mutuwa.
Munazzafa na tambayatta meke faruwa? Amma kukanda takeyi tasa ta kasa magana, sai kuma ta kashe wayar.
Gaba d'aya hankalin munazzafa ya kasa kwanciya akan rashin sanin takamemen abnda ke damun Besty d,inta, nan ta shiga d'akin Mama tana gayamata wayassu da Zarah, kuma tana neman alfarmar zuwa gidansu Zarah d'in.
Mama tace taje amma kar ta jima, nan munazzafa ta shirya gaggauce ta fito tasamu napep sai unguwar su Zarah.
Tana shiga gidan taci Karo da y'ar aiki suka gaisa tsaitsaye, kota kan Umma bata biba saboda hankalinta na wurin Zarah, nan ta haura sama d'akin Zarah ta taradda ita tana ta kukanta.
Munazzafa ta samu ta shawo kanta tayi shiru, har take tambayatta meke faruwa?
Ta bata amsa da cewa Abba ya badani sadaka ga wani, kamar yaya? Banganeba? Duk cikin tashin hankali take jeromata way'annan tambayiyin.
Nan Zarah ta kwashe komi ta gayamata yadda sukayi da Abbanta.
Munazzafa ta nisa ta Fara bata hak'uri tana Mai cewa duk duniya ba Wanda zai fitadda ke daga wannan lamari da kike ciki face Allah, kuma ni a ganina hak'uri zakiyi kiyima Abba biyayya saboda nasan bazai zab'a maki mijinda zakiyi kuka dashi ba.
Kuma kinsan biyayyar iyaye da addu'assu tana bin d'a duk inda ya shiga, kuma hakan zai kawo kwanciyar hankalin aure.
Nidai amatsayina na k'awarki Mai baki shawara kiyi hakuri ki dage da addu'a kuma ki fawwalama Allah lamurranki, inshaAllah zakiga haske acikin rayuwar aurenki.
Nan Zarah ta d'an Saki ranta, har suka Fara hira tana k'ara kwantar Mata da hankali.
Munazzafa tace tashi muje ingaida Umma don bata Masan na shigo gidannan ba, saboda jin yanayinki duk ya rud'addani, nan take gayamata cewa Umma bata nan ta fita unguwa.
Nan suka sauko domin ta raka munazzafa, suka ci Karo da Shakur ya shigo suka gaidashi, sai ya bisu da kallo tare da tambayar ina zasuje hakan? Ta bashi amsa da cewa zata raka Munazzafa ne waje ta samu napep.
Yace ta shiga ciki bara ya sauke munazzafa d'in gida.
Bayan sun shiga mota sun d'auki hanya yake jefo Mata tambayoyi cewa in har ta gama secondary tana da ra'ayin cigaba ko kuma aure zatayi?
Ta amsa mashi da cewa duk Wanda ya samu tana Mai k'ara nok'e kanta, saboda wani irin nauyin shi takeji, ya k'ara jefo Mata wata tambayar cewa ko tana da saurayi?
Murmushi kawai tayi ta kauda kanta, har suka kawo unguwassu ba Wanda ya k'ara magana, saidai kowa da abinda yake sak'awa a ranshi, da kuma sautun kid'a dake tashi ga motar, har ya sauke ta tayi mashi godia zata juya ya tsaida ita yana tambayar ta bashi number wayarta, sai tace ya krb'a gun Zarah, har zai k'ara janta da wata magana saita shige gida saboda gudun Babanta ya fito yaganta da wani akwai matsala.
By *Sdy* *Jegal*✍
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 3⃣0⃣_3⃣5⃣
Yau ce rana ta farin ciki ga su Zarah, bama su kad'ai ba duk Wanda yak'are makarantar, sanadiyyar yau ne suka k'are paper d'issu ta k'arshe.
Duk Wanda ka dubi fuskasshi zaka ganshi cikin walwala da farin ciki, sai musayar number sukeyi da address d'in juna.
Kowa yana cikin walwala, sab'anin Zarah da take jin tamkr yau ne za'a d'auketa zuwa gidan Wanda batasan waye ba, sai hawaye ke zuba ga fuskarta.
Isowar munazzafa kenan ita da Asmee da wata k'awarsu Aisha Yagani suka ganta tana hawaye.
Yagani ke ce Mata kodai kewar uncle Hakeem ne ke damunta, nan ta k'ara had'e fuska tare da Kama hannun Munazzafa tana Mai nuna Mata direba fa nacan na jiran su.
Nan sukayi bankwana da juna tamkar kada su rabu da juna kowa ya Kama gabanshi.
Saida suka sauke Munazzafa gida sannan suka wuce gida.
Shigassu keda wuya taga Abbanta ya rako wasu mutane su hud'u, nan ta durk'usa har k'asa ta gaida su sannan ta wuce ciki.
Shigar Zarah gida ta taradda kowa na falon zaune, itama nan ta zube tare da duban Broda tace kaga yau munyi graduate wlh duk na gaji, kaga gobe zansha bacci har in gaji tana murmushi.
Shakur yace kodai ki d'aga ki barmana gida mu huta, yana maganar yana kallon Umma tare da murmushi.
Nan Umma tace kana so ne kawai ka birkita ta yanzu ka sakata kuka, Umma tace Zarah tashi kije d'akin ki kiyi wanka ki sauko ga abinci kici.
Ta amsa da to Umma, nan ta kwashi kayan ta tahau stairs, tana shiga d'aki ta cire kayan jikinta ta fad'a wanka, bayan ta fito ne ta Shafa Mai tasa less d'inta Buba Mai kalar purple ta yane kanta da gyale kalar purple.
Tana saukowa daga stairs zata zo taci abinci, jin maganar Abbanta ya tsaida ita kuma ya saka ta fad'uwar gaba har tanaji tamkar numfashinta ya yi Mata k'aranci.
Hjy wato mutanen ne akwai karamci, kinga yadda suke ta yabon halayen Zarah, saboda zasu fita ita kuma ta shigo.
Gaisuwar da ta yimasu ce suke ta magana akai da kuma yabawa.
Tak'aice dai yanzu sun kawo sadakin Zarah kuma munkai k'arshen magana nan da 2month za ayi auren kowa ya huta.
Wannan ce maganar da kunnen Zarah ya jiyo Mata, har zata juya ta koma Shakur ya hangota.
Nan Abba yace ta k'araso, tazo ta zauna kusa da Abbanta, nan yake gayamata maganar aurenta, yana Mai k'ara rarrashinta da nusar da ita muhimmancin yiwa iyaye biyayya, har yana had'amata da cewa katta damu duk abinda takeso muddin baifi k'arfin shiba zai Mata.
Nan Umma da Shakur suka sa baki har aka samu ta sauko taci abinci kad'an ta koma d'aki.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*.
[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 3⃣5⃣_4⃣0⃣
A b'angaren Munazzafa da Shakur kuwa, soyayya ta k'ullu Mai tsanani had'e da shak'uwa wadda a kullum suna tare, inbai zo gurinta ba to suna mak'ale da waya, suna hira ko charting.
Haka yake ko yanzu tana d'aki suna waya da Shakur ta jiyo muryar Umma na kiranta, nan take cemai *Reality* ina zuwa Mama na kirana, (nan na rik'e hab'a ni jegal Ina mamakin Munazzafa, lallai an kwankwad'i soyayya).
Tana fitowa taga Babanta suna magana da Mama, nan ya bata umurnin ta duba d'akin Musaddik in yana nan ta kirashi, bayan ta Kira shi ne suka zo tare, har ta juya zata koma d'aki sai Baban yace ta dawo ta zauna zaiyi magana dasu.
Bayan ta zauna sai Baban su yayi gyran murya yana Mai cewa, "Na hadaku nan ne domin k'ara had'a zumunci tsakaninmu.
Nayi sauraren tun gama masters d'inka ko zaka tun ka reni da maganar aure, amma hakan bata samu ba saboda kunya irin taka da kawaici.
Don haka na yanke hukunci Zan had'aka aure da k'anwar ka, Ku tashi kuje Allah ya yimaku albarka, Musaddik ya amsa da Ameen, Wanda Munazzafa ta kasa magana.
Koda ta shiga d'aki har wani duhu take gani ga idonta, kukan ma ya kasa zuwa Mata, Ashe ma kuka Rahama ne.
Kenan mu hakan Allah ya tsara muna auren mu nida k'awata, bamu da zab'i kenan, haka rayuwar mu zata kasance cikin k'unci da damuwa.
Har ta jawo waya zata Kira Zarah sai kuma wata zuciyar tace me zaki ce Mata? Kar fa ki manta kece kika kwantar Mata da hankali har kina Mai bata shawara kan ta yima Abbanta biyayya zata ga riba zuwa gaba.
Toke me zai hana ki yima naki mahaifin biyayya kema kici riba?
Wata zuciyar tace naki da Nata ba d'aya bane, Zarah bata san miye *SO* ba har yanzu, ni kuma Shakur ya ko yamin yadda Zan soshi har mun shak'u da juna, Wanda Ina ganin rabamu zai iya kawo matsala ga zuciyoyunmu.
Duk da zuciyar ta take wannan maganar, k'arar wayar ta ya dawo da ita daga sak'e-sak'en da take yi.
Nan ta furta *Reality* bazan iya d'aga kiran kaba, saboda bazanso ka shiga damuwar da na shiga ba, su love manya, _lolx_.
Shigowar sak'o a wayar ta taji tana bud'ewa taga text d'in mutumenta kamar haka.
*Precious* _ki_ _d'aga_ _Kira_ _na_ _ko_ _zanji_ _sanyi_ _araina_
Cikin tunanin tane ta samo mafita, nan take ta fad'a saman gado tana murmushi tare da kaima text d'in Shakur kiss.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn Shakur.
No comments:
Post a Comment