[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 7⃣5⃣_8⃣0⃣
Bayan tattaunawa tsakanin iyayen Shakur da Munazzafa, sun yanke maganar auren bayan wata d'aya da yin nasu Zarah.
Saboda wasu uzurukka da mahaifin Munazzafa ya bada.
Nan Baban Munazzafa ya shigo gida yana Mai gayama Mamar su yadda suka yanke hukunci magana.
Yace jiya ma munje gidan su yarinyar da musaddik keso, suma munyi magana auren zai zo lokaci guda dana Munazzafa d'in.
Kinga da anyi auren su mun huta sai dai in mun samu jikoki sun zo muna yawo, yana maganar yana murmushi.
Mama tace aini zaka bari da kewa, gida zai yi shiru babu dad'i.
Yace to ko za afasa auren ne a ajiye miki yaran kiyi ta kallo?
Tayi murmushi tace "ai hakan yafi farin ciki gare ni, don duk Wanda Allah ya nuna ma ya wanke d'iya Mace lafiya lau to ya gode ma Allah.
Alhj yace haka ne, kema saiki gode mashi.
Jin cewa ga inda aka tsaya ga maganar auren su, take ta Kira Shakur tana gayamai.
Yace to burin ki ya cika an yimaki yadda kike so kenan, tunda kinci burin cin auren k'awar ki.
Tayi murmushi tace *Reality* inaso koda za ayi auren k'awata ina tare da ita, saboda in rik'a kwantar Mata da hankali har ayi lafiya a k'are lafiya.
Yace waya sani ko wannan plan ne kika iske Baba kika had'a.
Tace wallahi ba haka bane su suka sa lokacin hakan.
Yace nasan kine shiyasa, saboda ranar nazo kamin ki fito Musaddik ke bani labarin plan d'in da kika had'a saboda kauce ma auren dole.
Tace laaah aiko yau had'uwata da yaya Musaddik Allah d'ai zai raba mu.
Saboda jin nauyin yaji abinda tayi tana murmushi ta tsinke wayar.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 8⃣0⃣_8⃣5⃣
*BAYAN* *SATI* *BIYU*
Yau ne yayi dai_dai da sa lallen Zarah.
Wanda tun safe Munazzafa da Aisha Yagani da Asmee suke ta zirga_zirga, basu zaune basu tsaye, tun Munazzafa na jin nauyin Umma har ta rage saboda itace makusan ciyar Zarah di'n, duk da Yagani Nata shisshigewa ala dole gata k'awar Amarya
Zuwa bayan la'asar ne mutane suka Fara hallara, y'an Uwa da abokanen arzik'i kowa yazo, musamman da Zarah ce d'iya ta farko da za ayi auren ta a gidan.
Can d'aki kuma su Munazzafa na can Nata fama da Zarah akan ta tashi ta shirya, mutane sun hallara.
Saida yaha siddik k'anwar Umma tasa bakin ta sannan aka samu ta shiga wanka.
Bayan ta fito ne Munazzafa ta d'auko Mata material d'inta Mai kalar blue, had'e da gwaggoron ta Mai kalar skyblue da takalmin ta suma kalar sky, nan yaha ta karb'i kayan taje wani d'aki ta shirya ta.
Nan Zarah ta haska wuri ta fito tsaf, abinka ga fulanin asali.
Nan su Yagani suka take Mata baya, Wanda Munazzafa da Anty yaha suka sakata a tsakiya.
Bayan Amarya ta fito aka saki kid'a k'awayen Amarya suka fito suka cashe.
Can gefe na hango y'an group d'in greatest women sun hallara da kuma y'an group d'in novels world (3), nan aka fitadda kayan tand'e-tand'e aka ba kowa nashi, greatest women aka ba Saratu saboda itace k'aramar admn, nan na hango su Hindatu da Fati Ana wawason kayan tamkar basu Saba shan lemu ba.
Bayan an sallami kowa ne aka sake sakin kid'a matan Amarya suka k'ara cashewa, nan akaba wata fili tana shawar shoki Ana Mata lik'i, koda naje kusa Ashe Aisha Bizzy ce, ohhh! Ita ko Ina ake biki sai taje rawar shoki.
Bayan anfara watsewa Bizzy ta matsa kusa da Munazzafa tana tambayar ta yaushe ne za ayi walima?
Ta bata amsa da cewa ranar assabar ne.
Tace to yayi Allah ya kaimu sai mun zo.
Nan na rik'e baki nace gayyar sod'i kenan, *lolx*
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 8⃣5⃣_9⃣0⃣
A yau ne dubban mutane suka shaida auren Hakeem late Alhj Bawa da FATEEMA Zarah Mukhtar Ibrahim, Wanda ya samu halartar d'inbin mutane kama daga y'an kasuwa, manyan y'an siyasa tare da mutane masu fad'a aji.
Bayan an k'are d'aurin aure, Hakeem ya shirya shida abokanen shi akaje gaisuwar iyayen Amarya, saboda wannan al'adar mutanen Jega ce.
Har suka shigo shida tawagar shi Allah bai had'ashi da Zarah ba, nan suka gaida Umma tare da tawagar k'annen ta.
*BAYAN* *LA'ASAR*
Nan aka d'unguma sai gidan Alhj kabeer abokin Abban Zarah, saboda shine ya d'auki nauyin walima, wannan Ma al'adar jegawa ce.
Bayan an natsu kowa ya shirya sai aka Fara shirin walima, nan ma zayyano irin kyawon da Zarah tayi b'ata baki ne.
Nan Anty Ybk ta gabatar da lakca da jero nasihohi sosai akan rayuwar aure, da kuma hakurin zaman aure, da yadda Mace zata rik'e mijin ta da hannu biyu ba boka ba malam.
Bayan Anty Ybk ta gama tata lakca aka sake gabatar da Safiya Ummu Abdoul, itama tayi Nata jawabi sosai tare da janyo hankalin y'an Mata akan yima iyaye biyayya domin dacewa da rayuwa Mai tsafta da amfani, da kuma d'orewa cikin farin ciki.
Daga nan aka Kira Amnya Hjy Shafa domin ta rufe taro da Add'a, bayan tayi addu'o in samun zaman lafiya ga Amarya da ango ta koma ta zauna.
Can na hango y'an group d'in musha karatu Ashe suma sun hallara, y'an mumbari suma sunzo.
Ana rabon kaya ga duk bak'in da suka hallara, naga anba musha karatu nasu kayan da rabon Anty Ybk, nan ta wak'ilta Anty Jidda Musa domin ta karb'a.
Suma y'an mumbari an basu nasu kaya kamin Jamila Muhammad ta karb'a su Bizzy anyi kanzagi an karb'e, nan su Mmn Zarah suka bita da mamakin ko ina sai anyi shisshigi.
Bayan y'an walima sun watse aka koma da Amarya gidansu, saboda gabatowar magrib don za aje Kai Amarya gidanta zuwa 10:00pm.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 9⃣5⃣_1⃣0⃣0⃣
*WASHE* *GARI*
Kiran sallah shine yayi dai-dai da tashin Zarah daga bacci, nan ta fad'a toilet tayo alwala tazo tayi nafila, tana zaune tana lazimi taji an tada sallah, nan ta tashi tayi sallah.
Bayan ta gama ne gari yayi haske nan ta linke sallaya ta koma bakin gado ta kwanta.
Zuwa 10:00am taji motsi cikin falo har zata rega kuma ta fasa ta dawo tayi kwanciyar ta.
Daga baya ta tashi tayo wanka ta shirya, sai taji shigowar text cikin wayar ta.
Tana bud'ewa taga sabuwar number, ga abinda aka turo _ki_ _fito_ _falo_ _ki_ _karya_.
Nan tabi wayar da kallo taja wani mugun tsaki, a haka ake rayuwar auren?
Saidai babu Mai bata amsa.
Hakan ta tashi sanadiyyar yunwar da taji na damun ta, saboda rabon ta da abinci tun jiya bayan la'asar.
Cikin sand'a ta bud'e d'akin ta fito ta nufi falo d'in, nan taga kulolin abinci saman dinning table, ta dudduba taga abinci wurin Kala uku, nan dai ta zuba kunun tsamiya da k'osai tasha.
Bayan ta gama ne ta d'an zazza gaya gidan, ya d'an yimata ba laifi, part guda ne bata shiga ba Wanda tana tunanin na maigidan ne.
Bayan ta gama ta koma d'aki ne taji surutun mutane, ta fito ne suka gaisa nan suke gayamata Nusaiba ce k'anwar mijin ta da sauran y'an uwan angon da bata sani ba.
Nan ta tarbesu hannu bibbiyu ta kawo musu dubulan da alkaki, suna ci suna fira cikin walwala da sakin fuska.
Nan Nusaiba ke yaba kyawon Zarah, tana cewa gaskiya kun dace da yaya.
Nan Zarah tayi wani murmushi da bai Kai ciki ba.
Nusaiba tace hala yaya bai nan banji motsin shi ba?
Nan ta rasa wace amsa zata bata, shin zata ce Mata itama bata gan shi ba ko yaya.
Mai maita tambayar ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka.
Ta bata amsa da yana ciki, bara akira maku shi.
Nan tayi part d'inshi ta lab'e wani korido, ta yimai text kmr haka, _ka_ _fito_ _ga_ _y'an_ _uwan ka_ _sun zo_.
Nan ya gani yayi murmushi, kamin ya fito ta koma d'akin ta.
Nan ya fito suka gaisa har tobasan shi na zolayar shi da cewa jiya zuwa yau har ya fara shinning na angon ci.
Tabbb ni sdy haka za ayi rayuwar aure ta text message.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 9⃣0⃣_9⃣5⃣
Bayan an koma gida su Munazzafa sun gabatar da sallah sunci abinci, nan suka had'u ita da Asmee da Yagani suka Fara tsokanar Zarah.
Saida suka ga zata Fara kuka sannan suka daina.
Zarah tace wannan auren haka nake ji tamkar za akaini gidan yari ne, wannan masifar dame tayi Kama.
Ace tun ranar da akace anbada ita bataji d'uriyar mijin ba, fari ne ko bak'i ita bata ma sani ba.
Nan dai suka taru hadda yaha saddik k'anwar Umma suna rarrashinta, har suka samu ta sakin ranta.
*10:00pm*
Abba ya Kira Umma yace a shirya Zarah saboda shi zai kaita d'akinta da kanshi.
Umma tace watau kaima ka Fara d'aukar al'adar mutane.
Yace wannan al'adar bata jegawa bace, wasu malamai sunce Annabi Muhammad (S.A.W) shi yakai Nana Fad'ima gidan ta da kanshi , to dashi ne zanyi koyi nima.
Nan Umma tayi murmushi tace to ya za ayi da masu rakiyar Amarya?
Yace zasu iya shiryawa suje kamin muje ko kuma bayan na kaita.
Nan Umma ta shiga d'aki taga har an gyra Zarah, nan take gaya musu sak'on Abba.
Munazzafa tace Umma mu za muje kamin Abba ya karaso da ita.
Nan suka fita mota ta d'aukesu sai gidan Amarya.
Bayan shima Abba ya kai Zarah ya dawo, nan aka faka motocin y'an rakiya.
Ciki kuwa hadda y'an group d'in Zarah B -B sun zo rakiyar Amarya, bayan tasu mota ta d'aga naga princess Meenat ta had'o kaf y'an group d'inmu suma sun cika mota ukku sai gidan Amarya.
Zarah kam tasha y'an rakiya, ita ko tana d'aki tana ta darzar kuka su Yagani sai faman rarrashin ta akeyi.
Zuwa 11 akace kowa ya fito za amaida mutane gida, nan kowa ya watse sai Munazzafa da Asmee da suka tsaya k'ara rarrashin ta, daga baya suma suka wuce aka barta ita kad'ai abin tausayi.
Yau ni Zarah naga ta kaina, shikenan yanzu nabar rayuwar gidan mu na dawo rayuwar gidan Wanda baya so na, ko yaya rayuwata zata kasance a gidannan.
Tun tana sak'e-sak'e har taji idon ta sun yi nauyi alamar tana jin bacci.
Jin k'arar bud'e falo ne yasa ta tashi da sauri ta sama d'akinta key ta koma ta yi kwanciyar ta.
Koda Hakeem ya shigo gaban shi na fad'uwa yana tunanin da wane ido zai kalli Zarah.
Koda ya shigo gaban shi na fad'uwa ya tunkari d'akinta, murd'awar da yayi yaji gambun rufe Saida yayi ajiyar zuciya.
Wadda ni kaina na rasa wace irin ajiyar zuciya ce, lolx.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*.
No comments:
Post a Comment