Thursday 6 October 2016

BAHIJJA 50-55

[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* 50-55
Baban Shureim yazo duba jikin maigari Wanda ciwon nashi ya had'a da tsufa, nan Murtala ya tunkari Dad da maganar yana so aje nema mashi auren Bahijja.
Hakan suka kwashi jiki sai gidan Malam salisu, nan akayi gaisuwar yaushe rabo kuma suka tattauna kan maganar nema ma Murtala auren Bahijja.
Malam yace ba komai Alhj Kai kanka Mai bada auren Bahijja ne, amma duk da hakan na bawa Murtala ita halak malak.
Amma Ina neman alfarmar a d'an d'agamin k'afa in har na shirya maganar auren Zan tunkari Alhj saminu inshaAllah.
Alhj yace in har maganar da ka fad'i cewa d'iya tawa ce to Zan so kabar komai a Hannuna, ni Zan d'auki nauyin komai na Amarya da ango.
Kuma inaso a d'aura aure yanzu, saboda gobe Zan wuce England wurin wasu harakoki nawa.
A hakan aka d'unguma sai babban masalacin garin aka d'aura auren ```Murtala``````Saminu```
Da
*Bahijja* *Salisu*
A kan sadaki Mai sauk'i.
Ansamu halartar mutane da dama saboda lokacin sallar azahar ne, kuma in har Alhj ya shigo garin to mutane zasu k'ara taruwa, saboda shi mutum ne Mai yawan kyauta da taimakon mutane.
Hakan suka rabu kowane b'angare suna murnar had'a auren yaran su.
Sai dai sun ajiye maganar kan sai wani sati Mai zuwa za ayi sauran al'adun aure sannan Amarya ta tare gidan ta.
Hakan Malam ya doshi gida cikin murna da farin ciki, saboda ganin yau Allah ya cika Mai burin shi na ganin ya aurar da y'ar Baba.
Yana shigowa Gwaggo ta tarbeshi, tace malam yau na ganka cikin farin ciki meke faruwa?
Nan ya kwashe komai ya gaya Mata, Gwaggo tayi wata irin zabura tace ban gane ba malam, wane irin aure d'iya tamkar d'iya roba za ayi neman aure da d'aurin aure lokaci guda.
Kawai malam kace ka saida y'ar ka saboda kaga kud'i, aini yau an nunamin iya kata kuma an nunamin ban Haifa ba.
Nan taja wani irin kuka had'e da sharce majina tace yau da ace uwar yarinyar nan na raye na tabbata ba za ayi Mata hakan ba.
Haka taci kukan ta da gunzar ta tamkar wadda aka yiwa mutuwa.
Malam yace kiyi hak'uri lami nima ban san da zuwan maganar ba, kuma kinsan Alhj yafi k'arfin komai a guri na.
Mun taso tare tun muna yara, kuma duk sana'ar da nakeyi kinsan da bazar shi nake rawa, kinga ko in har na hana yaron shi y'ata banyi halacci ba.
Da k'yar malam ya shawo kan lami ta sassauto, nan tace to yanzu yaushe ne tarewa?
Yace sai nan da sati, don ina so gobe inje aljannare in gayama dangin mahaifiyar ta saboda a fita hakk'in su.
Lami tace ko baka jeba babu komi, nima na isar musu, malam yace aah kam lami gara agaya masu.
Zanso ma inje musu da ita koda wuni ne ta yi masu.
Hakan Gwaggo ta tashi tamkar zata had'iyi zuciya ta mutu kan tsabar bak'in ciki da hassada.
Bahijja na d'aki tana sauraren maganar Gwaggo da Baban ta, sai murna take yi cikin ran ta jin cewa an d'aura Mata aure, duk da cewa bata San miye auren ba.
Amma tasan ana canja ma mutum gida daga gidan su zuwa wani gidan.
Ita kam in hakane zata yi murna da cewa zata bar gaban Gwaggo ta koma gidan su Murtala da zama, amma fa tasan zata yi kewar Baban ta.
*************
Koma war Dad gida yake gayama Mum an d'aura auren Murtala yau.
Mum tace yaushe Murtala ya nemi Mata har magana tayi tsayi haka?
Dad yace zuwa na ne yake gayamin cewa yana tausayin yarinyar kuma tana shan uk'uba ga matar Baban ta.
Asali ma yace bai ta6a furtama yarinyar yana son ta ba, suna dai mutunci sosai da ita, kuma yarinyar bata ma isa aure ba nan garemu saidai can d'in, y'ar wajen abokina ce Malam salisu.
Mum tace ayyaah, yanzu to ina zasu zauna?
Dad yace shine nake tunanin inda za agyra Mai kamin nan da sati d'aya.
Mum tace me zai hana cikin gidannan abasu part guda, kaga gidan yana da girma kuma akwai part kusan biyar da ba kowa a ciki.
Dad yace kin kawo shawara, nan ya Kira wayar Shureim yace Son kazo falo Ina Neman ka.
Yana zuwa Dad ya gaya Mai maganar auren Murtala, ya d'ora da cewa inaso ka duba part d'aya cikin gidannan duk abin da ake buk'ata asaka nan zuwa sati d'aya.
Shureim yace lallai Murtala ya yimin wayo, Allah ya sanya alkhairi.
Dad ya kar6a da Ameen, yace saura Kai, kuma ka bincika Jega international furnitures show room, ka za6a ma yarinyar kayan d'aki, komai ka tabbatar ansa saboda ni gobe Zan wuce England.
© *SDY* *JEGAL*
[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* 55-60
Duk abin da ya Kama ta ayi tsakanin dangin Amarya da Ango duk anyi.
Inda Inna habiba ta zage damtse da sauran kud'in da Bahijja tace ta aji yema ta ta gyra ta gwargwadon iyawar ta.
Bahijja taje dangin mahaifiyar ta daga wuni, suka rarrashi malam dole hakan ya bar musu ita sai da ta kwana d'aya ta dawo.
Su Gwaggo anyi bak'in ciki tamkar za'a had'i zuciya a mutu, duk hanyar da zata bi domin lalata auren abin yaci tura.
Har wurin bokan ta taje amma abin ya gagara, har abin ya zamo Mata tamkar sabuwar kamun hauka.
Duk abinda take yi bai k'ara yawa ba sai jin cewa bama k'auyen nasu za'a ajiye y'ar Baba ba.
Haba malam ya zaka d'auki marainiyar Allah ka kaita wata Uwa duniya da bata da dangin iya bare na Baba.
Ni gaskiya in zaka bi shawara ta me zai Hana abar ta nan gidan su Murtala?
Malam yace kinsan Murtala bai cika zama nan ba, can Alhj Suleiman ya bashi Sana'a, ciwon maigari ne ma yasa ya dawo garin nan kwana biyu.
Kuma kin ga yanzu ba ni nake da iko da ita ba sai abin da mijin ta ya tsara, kawai muyi Mata addu'ar zaman lafiya ita da mijin ta.
Haka aka d'unguma Kai Amarya, duk y'an Uwa da abokanen arzik'i sun je saboda an baza motocin d'aukar Amarya.
Hakan wasu suka dawo wasu kuma suka kwana can, cikin wa'anda suka kwana har da lantana da kuma Hindatu k'anwar Murtala.
Yau kwanan Amarya uku a gidan ta, duk abinda ya kamata ta sani cikin gidan ta sani.
Hajiya Safiya bata bari tayi komai da kanta, musamman tana ganin ta y'ar k'an k'anuwa itama bata wuce akula da ita ba.
Da Safiya ta waye an kawo musu breakfast sunci Murtala zai wuce shago.
Yau ma bayan sun yi Karin kumallo Murtala yayi shirin fita, yace Bahijja ba zaki raka ni waje ba?
Hakan yasa ta d'auko gyalen ta tace muje, nan ta jawo k'ofar ta rufe suka fito tare.
Nan suka shiga part d'in Mum, bayan Murtala ya gaida ta yace Mum ni Zan fita.
Tace to Murtala sai ka dawo.
Bayan ya fita ne Bahijja tace Mum wane aiki Zan taya ki?
Tace Bahijja ki bar shi kawai akwai y'an aiki zasu yi komai, girki ne kawai nake yi da kaina, shi ma sai anjima kad'an Zan d'ora na Rana.
Tana zaune suna fira da Mum, Mum tace Bahijja kin yi makarantar islamiya kuwa?
Tace eh Mum har nayi izifi ashirin daga baya ayukkan gida suka hanani zuwa, kuma Baba na yaso yasaka ni boko Gwaggo tace lalata yara suke yi shiyasa Baba bai saka niba.
Mum tace to Zan yi maganar da Murtala, Zan saka ki islamiya, kuma Zan sa asamo malamin da zai rik'a yi maki lesson daga baya a saka ki boko.
Nan Bahijja ta yita murna tana yima Mum godiya.
Lateefa na fitowa tabi Bahijja da kallo, tace Mum wannan ce matar Murtala?
Ta bata amsa da eh, tunda kin k'i zuwa duba ta ai ita gata nan tazo.
Tace Mum ba haka bane, kinsan ni bana son hayaniyar mutane shiyasa ban shiga gurin ta ba, amma nayi niyyar yau in rega tun da y'an uwan ta sun wuce.
Yanzu don Allah Mum wannan mitsitsiyar yarinya za akalla ace ma Amarya?
Mum tayi murmushi tace al'adar garin su ce.
Nan Lateefa tazo gurin ta ta zauna, cikin ranta take fad'in wannan ma me ta sani aure, barranta na wani Abu zaman takewar auren, amma inshaAllah nayi alk'awari da sannu Zan wayarda Bahijja, hakan naji tausayin ta ya tsirga min lokaci guda, hakan nake jin ta tamkar k'anwa ta Shema'u.
Nan ta Kama hannun Bahijja ta yi d'akin ta da ita.
Tace Bahijja wannan kwalliyar fa?
Tace ai haka garin mu muke tamu kwalliyar.
Lateefa tayi murmushi ta ja wota sai gaban mirror ta zaunar da ita tace bara in maki kwalliya.
Tace ina fatar kin yi wanka yau?
Tace ai nayi jiya.
Nan Lateefa ta bita da kallo tace wa ya gayamaki in anyi wanka jiya ba ayi yau?
Lateefa tayi murmushi.
Nan ta shiga toilet ta had'a ruwan wanka ta saka turaren wanka, ta fito taja Bahijja suka shiga toilet ta fara wanke Mata kan ta ga gashi har gadon bayan ta, nan ta nuna Mata yada zata yi amfani da kayan wankan sannan ta fito.
Bayan ta gama wankan ta fito nan Lateefa ta gyara Mata kan ta ta yimata kwalliya, dama taje part d'in ta cikin kayan lefenta ta za6o Mata kaya.
Nan dai ta shirya ta sai gashi ta fito tsab bafulatanar usuli.
Ta rik'o hannun ta suka dawo falo, Mum ta Saki baki ta bisu da kallo.
(Nima hakan na Saki baki na bisu da kallo, Ashe dama Bahijja haka kike)
© *SDY* *JEGAL*
[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* 60-65
Yau ne Bahijja ta cika sati biyu da aure, ta murje tayi jikin ta dai-dai gwargwado.
Duk wata iya kwalliya ko dressing tana koyo wurin Lateefa.
Lateefa ta Mai data tamkar k'anwar ta, duk in da ka gansu gidan suna tare.
Mum tasa an saka Bahijja makarantar islamiya kuma an samo wani malami dake yi Mata lesson gida, gwargwado tana fahimta ba laifi, saboda akwai ta da saurin d'aukar Abu cikin kanta.
Tana zaune part d'in Mum ta fito daga kicin kenan taji sallamar Shureim.
Nan ta kar6a ta durk'usa har k'asa tace yaya Shureim sannu da dawowa.
Yace yauwa Bahijja, Ina Mum halan?
Tace yanzu ta shiga wanka.
Yace latee fa?
Ita ma ta kar6a mashi da cewa tana d'aki bacci take yi.
Nan ya girgiza kanshi ya wuce d'akin shi, ita ko ta gama jera kaya a dinning ta yi part d'inta domin tayi wanka.
Saboda wannan na daga cikin al'adar da Lateefa ta koya Mata cewa duk ta shiga kicin ta k'are girki to tayi wanka.
Hakan ta shiga tayi wanka ta fito, ta yi kwalliyar ta dai-dai gwargwado duk da bata iya sosai ba.
Shureim na falo zaune yana kallo sai ga Mum ta fito, bayan ya gaida ta yace Mum wai me yasa kullum Zan shigo Zan taradda Bahijja na taya ki aikin gida, amma Latee na d'aki tana bacci ko charting?
Mum tayi murmushi ta bashi amsa da cewa nima matsalata guda da ita bata k'aunar shiga kicin ko kad'an, inaga ko ruwan coffee bata San ya ake dafa suba.
Shureim yace Mum ki rik'a saka ta girki mana.
Tace son kasan halin Lateefa zata iya aikin komai amma bada girki ba kam, sai dai ayi ta hak'uri zuwa gaba in kun yi aure nasan tunda tana son ka zata yima.
Tace kaga yanzu haka Bahijja in dai tana part d'innan bai ta6a yuyuwa in shiga kicin ba tare da ita ba koda kuwa zance tayi zaman ta, yanzu haka ta fara gano kan wasu girke-girke.
Nan ya ta6e baki yace Allah ya kyauta, ya tashi ya yi nashi d'akin.
*WA CECE* *LATEEFA*?
Lateefa d'iya ce gun Alhj Isma'il Mai dala da Hjy Saratu.
Alhj Isma'il fitaccen Mai kud'i ne kuma sananne a garin Jega, yana da yaran shi Mata guda hud'u, Wanda Allah bai bashi d'a namiji ba.
Ta farko itace Nafeesa wadda tana sokoto tana aure da yaran ta uku, sai kuma Bilkisu dake aure a Birnin kebbi da yaron ta guda.
Sannan Lateefa, Shema'u itace Autar su, Lateefa ta taso cikin jin dad'i da sangar ta Wanda duk abinda tayi ga mahaifan ta bata laifi, musamman gun Abban ta, don ma Hjy Saratu na k'ok'arin kwa6ar ta in tana wasu abubuwan.
Da Hjy Saratu da Hjy Safiya mahaifan su guda su kad'ai iyayen su suka haifa.
Tun tasowar Lateefa Allah ya had'a jinin ta da son zama gidan su Shureim, Wanda yanzu hakan ake gab da auren su.
*******************
A yau ne iyalan gidan maigari Alhj Abubakar suka tashi da bak'in cikin rasa maigari, Wanda ciwon shi ya tashi jiya akayi dai-dai da ajali.
Dama ya d'an jima baida lafiya Wanda an yita yawo dashi asibitoci da dama har Egypt Alhj Suleiman ya fita dashi, sai dai ciwon ya had'e da tsufa.
Hakan su Hjy Safiya suka Kama hanyar Kimba domin zuwa zaman makoki, Wanda har da Bahijja aka zo.
Gidan su na garin suka sauka, dama suna da gida a garin wanda in Abu ya samu nan suke sauka.
Haka su kayi koke-koken su suka hak'ura, saboda sun yi rashin dattijo Mai nagarta da kamala.
Nan aka yi mashi sutura sai gidan shi na gaskiya.
Bayan sadakar uku ne Mum tace Bahijja ki shirya muje gidan Ku ki gaida mutanen gida.
Nan take gaban Bahijja ya rik'a bugawa, saboda har ga Allah tama manta da wata halitta Gwaggo, tun auren ta da sati d'aya da Gwaggo taje ranar ma taci masifa har da rank'washi aka Kai Mata.
Hakan dai ta wuni gidan ta hana Bahijja sakewa, data tashi tafiya Hjy Safiya ta had'a Mata sha tara na arzik'i, amma duk da hakan Saida ta kwashi sabulayyen wanka dana wanki, ta ebi mayukkan Shafa duk da wasu bata Masan ya ake amfani da suba.
Maganar Hjy ta dawo da ita daga tunanin da ta Lula, tace ki tashi muje kinsan gobe zamu wuce.
Hakan ta tashi jiki babu k'wari suka nufi gidan su Bahijja d'in.
Sun shiga gidan Gwaggo ganin Hjy aka tashi jiki na rawa aka shimfida tabarma hakan suka zauna aka kawo ruwa da fura taji nono, nan suka sha aka gaisa, sai ga malam ya shigo suka gaisa ya yima Mum gaisuwa.
Ya Kai duban shi ga y'ar Baba yace haka kika koma, kin k'ara girma kinyi 6ul-6ul.
Tayi murmushi ta ce Baba kaga Mum ta sakani islamiya kuma yanzu na iya karatun boko.
Nan yayi murmushi ya yima Hjy godiya sosai.
Gwaggo sai binta take yi da harara tamkar ta shak'e ta take ji.
Hakan Hjy ta basu kud'i suka fito, nan Bahijja tace Mum Ina so in lek'a lantana ga gidan su nan mak'waf tan mu.
Nan suka shiga gidan lantana na ganin ta ta shek'o suka rungume juna, saiga Inna Habiba ta fito nan suka gaisa da Mum.
Hakan mak'wab ta ke lek'o wa ana kallon Bahijja sai mamaki ake yi yadda ta koma.
© *SDY* *JEGAL*

No comments:

Post a Comment