[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: _SANADIN_ _K'INCI_ 6⃣1⃣/6⃣2⃣
*WASHE GARI*
*04:30pm*
Harabar gidan Haj Maijidda ta cika da mutane mak'il duk da ce wa mutane basu kammalu ba har yanzu.
Mela, Iman, Mukarrama kaya iri d'aya suka saka wani rantsattsen material ne a jikin su kalar lemon green sai wani gwaggwaro da suka nad'a saman kansu mai ruwan hanta had'e da takalman su kalar gwaggwaron su.
Amarya ce ta fita daban acikin su saboda less ne ta saka mai kalar blue sai gwaggwaro da takalman ta farare, da ka ganta kasan ta had'u iya had'uwa.
Mai kid'an DJ aka kira suka baje sai tik'ar rawa suke yi duk da ce wa Musirrah ba wai rawa ta iya ba amma sai abin ya bada wani style na daban, acan tsakiyar masu rawa na hango Shema'u sai rawa take tik'a kuma daka ganta kasan cewa ita gwana ce a cikin rawar, nan dai na ganta da mutanen ta a tare da ita na hango Mmn Zeenert, Mmn Jameel, Yaha Saddik, Mmn Mamee, Shafa Abasco, Nafisa Alu, Khairat, Salsabila, princess Meenat, sai kuma K'anwa ta Bizzy wanda duk sun cika gurin tamkar dan su ake bikin, (Tabbb Shema ashe kin had'o kan y'an SDY JEGAL NOVELS) ne don ku cin ye kayan biki.
Hakan akayi taron sa lalle inda ya k'ayatar da mutane abin sai son barka.
***
*RANAR JUMA'A*
Yau kuwa ranar walima ce za'a yi y'an nasihohi zuwa ga amarya domin samun zama mai d'orewa na har abada a gidan ta, wanda aka gayyato Malama Khadija Manga ita da Haj Shafa Aleru domin su yi wa Amarya nasiha akan zamantakewar aure.
Nan ta fara da ce wa shi dai aure yana daga cikin sunnar manzo (S.W.A), Saboda yana ce wa yaku al'umma ta kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku a gobe alk'iyama".
"Shi zaman auren kanshi yana k'unshe da abubuwa da dama wad'anda muddin mutum ya tsare biyar daga cikin su to rayuwar auren shi zata yi k'ark'o da ikon Allah.
ABU NA FARKO SHINE LADABI DA BIYAYYA: "Su ne jigon auren gaba d'aya, saboda duk yadda mijin ki ke son ki muddin ba kiyimai ladabi to da sannu zaki siye ticket d'in cire soyayyar ki aran shi, kar kice ni fa ba nason wane aka yimin aure dashi saboda haka bazan girmama shi ba to wannan ba dai-dai bane."
"Kuma ki zamo mai girmama iyayen shi da y'an uwan shi dashi kanshi mijin.
ABU NA BIYU SHINE TSAFTA: Ki kasance mace mai tsafta ta kowane 6angare, kar kiyi tunanin ce wa in har kika tsaftace jikin ko baki tsaftace muhallin ki ba tamkar kinyi dai-dai, saboda gudun mijin ki ya jiki ba dai-dai ba, to wannan ba shi ne abin yi ba, kamata ya yi ki kula da tsaftar jikin ki, muhallin ki da kuma makwancin ki".
ABU NA UKU SHINE GIRKI: Babban kuskuren da iyaye ke tafkawa kenan a yanzu, za ki shiga gida ki tarar da y'an aiki birjik sun cika gida iyayen da yaran gidan ko wa zaune yana hutawa, wasu za su ce ni tunda inada abin hannu na bazan bari in wahala d'ana ya wahala ba, wasu zaki ji suna fad'in ba za su shiga kitchen ba saboda hayak'i kar yasa suyi bak'i, wasu kuwa ko gida aka shigo aka tarar suna aiki idan akace ina y'arki halan? za kaji uwar ta ce wallahi yanzu ta dawo daga skul duk ta gaji kinsan ba ta zama kullum tana hanyar skul".
"To wallahi wannan babban kuskure ne, iyaye mata mu ta shi tsaye cikin lokacin da d'anki yake dashi ko da minti talatin ne ki rik'a koyawa yaran ki girki, domin shi ne ginshik'i na rayuwar aure, duk yadda miji ke son ki in har kika sa mu matsala ta 6angaren girki to kin zamo abin tausayi".
Nan Haj Shafa ta kar6e da sauran bayanan biyu da suka rage, inda take ce wa'
ABU NA HUD'U SHINE SHAGWA6A: Har kullum idan mace tana nu nawa namiji shagwa6a to za ta samu wani bagire ne a zuciyar shi, saboda in har kina narke mai kullum tamkar man gyad'a to ba za ki ta6a fita a zuciyar shi ba".
ABU NA K'ARSHE SHINE KISSA: Kissa ta kasu kashi-kashi, to mu kissar da za mu d'auka ba kissar da za ki koya domin korar kishiya bace, ko kuma had'a miji da y'an uwan shi ko mahaifiyar shi ba, ta mu kissar ita ce wadda za ki koya domin narkadda zuciyar maigida ki shiga zuciyar shi kiyi kane-kane ba boka ba malam".
Hakan suka k'are y'an nasihohin su zuwa ga amarya da sauran mutanen da ke gurin, saboda su ma sun k'aru da wannan gajeruwar nasihar.
Yau kam y'an MUSHA KARATU ne suka cika gidan don su ma sun yiwa amarya kara, can na hango Mmn Ansar, Mmn Aslam, Munirat Ayuba, Maryama, Aunty Sis, Baraka, Fatima, Mmn Marhama, Ameera maisikeli, Ummietta wabi, wanda nan Musirrah ta tabbatar lallai MUSHA KARATU na son ta da gaskiya, hakan ta ba wa Mela umurnin taje ta sallame su, haka suka fita cikin farin ciki da karramawar da Musirrah ta yi masu had'e da addu'ar zaman lafiya.
****
*RANAR ASSABAR*
*11:00am*
Dubban mutane suka shaida auren
*MUSIRRAH FAROUK*
```WEDS```
*MUS'AB ABUBAKAR*
Wanda ya samu halartar manyan mutane daga wurare daban-daban saboda Baffa da Abba ba baya ba gurin mutunci da mutane, kowa na sune saboda basu da girman kai irin na masu kud'i.
Ranar gidan ya k'ara cika da mutane saboda halartar y'an MUMBARI domin nuna soyayyar su zuwa ga Musirrah wanda Yasmeeny ce ta jagoran ci wannan tafiyar inda Aisha Yagani, Hafsat Mai Sharifai, Jamila Moh Ali, Inna Habiba, Mmn Zahra, Mum Faty su ma ba'a barsu abaya ba.
Fateema Mrs uncle Hakeem da Bahijja Mrs Dr Shureim su ma sun zo da yaran su, saboda mazajen su abokanen Mus'ab ne. 6angare d'aya kuwa amarya ta sha gyara ga Murja ladan wato Madelty da maganin mata na sokoto, sai dai fatan Kai Amarya gidan Ango lafiya.
*SDY JEGAL*
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣3⃣/6⃣4⃣
*10:30pm*
Zuwa lokacin duk an shirya Amarya domin kai ta d'akin mijin ta sai kuka take yi na rabuwa da Ammin ta, saboda dai-dai da rana d'aya bata ta6a rabuwa da Ammi ba.
Duk duniya bata da wanda ta yi sabo dashi kuma take iya gayawa matsalar ta kamar Ammi, dak'yar aka samu aka 6an6are ta daga jikin Ammi, part d'in Abba Haj Maijidda ta wuce da ita nan ya yi mata nasihohi dai-dai gwargwado wanda ya saka jikin ta ya k'ara sanyi, yana saka mata albarka k'anwar shi da Haj Maijidda suka rik'a ta aka saka ta a mota suka wuce.
Mota kusan takwas aka cika domin raka Amarya d'akin ta, ciki kuwa har da Mmn Hanan, Aunty Sis, Feenah Umar, Mum Faty, Ummu Mmn Ja'afar, Fati Salihu, da sauran y'an uwa da abokanen arzik'i.
K'arfe goma sha d'aya kowa ya tattara na shi da na shi suka fice, saboda Iman ce wa tayi ba za ta zauna yaya Mus'ab ya risk'e ta a gidan ba, jin hakan ya sa gaba d'aya suka fice suka bar Musirrah ita kad'ai wanda sai ajiyar zuciya take yi akan kukan da taci.
Bayan ya shigo gidan ne ya wuce part d'in shi sai da ya yi wanka ya saka farar jalabiya sannan ya wuce d'akin ta.
Can ya hango ta duk'un-k'une gefen gado duk ta ta kura kanta da babban gyalen da aka rufa mata.
Hakan ya ajiye kayan da ya shigo dasu sannan ya ta ka har 6angaren da take, gurfane ya yi gaban ta ya sa yannu ya yaye gyalen da ya rufe mata fuska.
"Ki bud'e fuskar kisha iska mana tunda ko wa ya watse, ko kuma sai na siye bakin tukun?".
Cikin jin nauyi ta k'ara jan gyalen domin ta rufe fuskar ta, jin ya rik'e gyalen ya sa ta kauda fuskar ta cikin jin kunyar shi, ga shi ya zo gaban ta ya yi gurfane duk zatin shi ya mamaye gurin.
Gyalen ya cire duka had'e da ba ta umurnin ta shiga toilet tayo alwala domin su gabatar da nafila.
Bayan sun gabatar da nafila ne kuma sunci sun sha ya yi mata tambayoyi da suka shafi addini kuma gwargwado ta amsa iya abinda ta sani sannan ta tashi ta koma saman gado.
Tana so ta rage nauyin kayan da ke jikin ta tayi wanka amma kuma tana jin nauyin shi, ganin ce wa tana jin nauyin shi ne ya sa ya fita zuwa part d'inshi.
Nan ta sa mu sakewa sannan ta fad'a toilet ta yo wanka ta fito sannan ta saka kayan bacci ta hau gado ta kwanta.
Kwanciyar ta da minti uku ya da wo d'akin ga alama wani wanka ya yi.
"Wa ya ce maki mata na kwanciya ba ta re da mijin ta ya shigo ba?", yana maganar had'e da murmushi a fuskar shi.
Filo ta janyo ta rufe fuskar ta, jin take yi wani irin son shi na k'ara shiga zuciyar ta, amma fa tana da tambayoyin da take son yi mashi sai dai tana tunanin ba yanzu ba.
Sai da ya kashe fitilar d'akin sannan ya kwanta saman gadon, hannu ya kai gefen gadon ya kunna dim light, sannan ya matsa gab da ita har suna jiyo numfashin juna.
Hannu ya kai ya janye filon ya maida shi gurin kanta sannan ya janyo ta ya matse cikin jikin shi.
(Ni dai Jegal da sauri na na koma falo na takure saman three seater, saboda ko na tsaya ni kad'ai zan gani bazan iya gaya maku ba, *lolx*)
****
Umma anga rayuwa a gidan Jameel, lallai tabbas rayuwa juyi-juyi ce kwad'o ya fad'a ruwan zafi, cikin kwanakin nan ciwo ya saka ta gaba ga rashin wadataccen abinci ga kuma bak'in ciki da damuwa da suka mata yawa.
Musamman inta tuna irin zamantakewar da suka yi ita da Alh, bata ta6a tsammanin za su rabu ba saboda ganin ce wa ta kawar da Hauwa'u sai hankalin ta yakwanta.
Ashe akwai lokacin da za ta shiga tashin hankalin da zai fi na Hauwa'u don yanzu ita tana can da mijin ta cikin kwanciyar hankali itako ga ta nan raku6e suruka na wulak'an ta ta son ranta.
Duk yadda ake yi Baffa ya yi domin shawo kan Abba yamayar da Umma amma abin ya gagara, saboda har ta kai Abba ya furta mai in har yana son zaman su ya d'ore na aminci to kar yak'ara yimai maganar mayar da Umma gidan shi.
Har y'ay'an ta sun had'u sun je ba shi hak'uri amma ina zuciyar maza ta hau.
*SDY JEGAL*
dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: _SANADIN_ _K'UNCI_ 6⃣5⃣/6⃣6⃣
*WASHE GARI*
Cikin farin ciki da walwala suka ta shi, da taimakon Mus'ab ta gyara jikin ta bayan sun yi sallah had'e da azkar suka kuma bacci.
K'arar wayar shi ce ta falkadda shi ko da ya duba Ummy ce ta kira tana gaya mai ta aiko direba ya ka wo masu breakfast, hakan ya sa ya mik'e ya fita daga waje, bai yi minti biyar ba direban ya iso, kar6a yayi had'e da godiya ya ko ma ciki.
Fitar Mus'ab ke da wuya ta fad'a toilet saboda ta d'an jima da tashi nauyin had'a ido dashi take ji shiyasa ta k'udun-dune tamkar mai bacci.
Ko da ya da wo d'akin ya ji motsin ruwa daga toilet sai ya wuce part d'in shi.
Material ta saka mai kalar purple riga da siket ne, inda siket ya ka me daga sama sai zuwa k'asa ya bud'e, hakan yasa ya fito da shape d'in ta ga dukiyar fulani tubarakallah.
Jin nauyin fitowa hakan ya sa ta ya fa wani k'aramin gyale, sannan ta d'an kimtsa d'akin.
Da sallamar shi ya shigo d'akin bayan ta amsa ta durk'usa ta gaida shi cikin sunne fuska, kafad'un ta ya rik'o ya mik'ar da ita sannan ya cire gyalen da ta ya fa.
"Me zaki yiman 6oyo ajikin ki, ni fa mijin kine ga shi har da sauri na in kimtsa in zo in taya ki wankan", yana maganar had'e da kashe mata ido d'aya.
Kanta ta k'ara sunne wa k'asa jin take yi tamkar k'asa ta bud'e ta shige.
Hannun ta ya rik'a suka dawo falo, a dinning suka zube ya bubbud'e kayan abincin, nan ya hango kunun tsamiya da k'osai sai kuma tea da wainar k'wai had'e da kus-kus.
Hannun ta ta cire a nashi ta mik'e, "ina zaki je?".
"Kitchen zan shiga in d'auko cups da plates".
Tana juyawa da ido ya bi ta yadda mazaunan ta ke juyawa, har ta da wo bai san ta iso ba, k'arar plates d'in da ta zo dasu ne ya da wo dashi hayyacin shi.
Hakan ya wayance da sosa kan shi ya mik'o hannu domin kar6ar cups d'in, "me za'a saka ma cikin abincin?".
Muryar ta mai sanyi ce ta doki kunnen shi, "kunun tsamiya da k'osai zan sha". Ya ba ta amsa.
A ta re suka karya har suka k'oshi, duk da nauyin shi da take ji ya hana mata sakewa ta karya da kyau, hakan ya ja ta duk ya nu na mata gidan k'arshe bedroom d'in shi suka zube ya janyo ta saman shi ya rungume, cikin kasalalliyar murya ya furta mata "bacci za mu ko ma saboda rage gajiyar jiya".
Hannuwan ta duka biyun ta saka ta rufe fuskar ta, "zanyi maganin wannan kunyar don na ga tana son shiga hakk'ina".
****
Cikin tashin hankali Jameel ya shigo gidan saboda ya rasa ina zai sa kan shi, da yana da iko gaskiya da bazai yi wannan tafiyar ba.
Yadda ya shigo d'akin a hargitse ya tabbatar mata ba lafiya ba, "me ke damun ka haka?, na gayama kar ka bari matsala ta da matar ka ta saka ma wani ciwon".
"Ba wannan ne damuwa ta ba, gurin aiki na ne suka tura ni England wani course na shekara biyu, shi ne nake tunanin ina zaki zauna in har na wuce".
"Uhmm! "Kar ka damu da ma zaman gidan ya ishe ni, zan had'a kayana in koma Birnin kebbi da zama gurin Gwaggo zai fiye min".
"Ba za'a yi hakan ba, yanzu dai bara in fita in dawo ba za mu rasa mafita ba", da hakan ya fita ko Yusrah bata san ya shigo gidan ba.
Direct gidan su ya wuce, bayan ya gayar da Ammi sannan ya fitar da waya ya kira Haydar kan yazo part d'in Ammi ya same shi, bayan sun kammalu ne har Mubarak da Iman nan yake gaya masu meke faruwa.
Nan suka rik'a kuka had'e da neman alfarmar Ammi kan ta saka ba ki Abba ya mayar da Umma.
"Abban ku kunsan yana da kafiya, amma ku ta shi muje part d'in Haj mu rok'e ta alfarma ko za ta iya tunkarar shi da maganar".
Hakan suka d'unguma sai part d'in Haj, nan Ammi ke gaya mata buk'atar su. Cikin mamaki Haj Maryam ta kai duban ta ga Ammi, wannan wace irin mata ce da har kishiya za ta nemi hallaka ta amma yanzu da kanta take ce wa amayarda ita, cikin zuciyar ta take wannan tunanin.
Nan ta sa Ammi ta kira mata Abba, bayan ya iso ne ta gaya mai buk'atar yaran shi, kai ya rik'a girgizawa alamar bazai iya ba.
"Abba mu aka yiwa wannan abin kuma mun yafe har ga Allah, ka mayar da Umma don Allah", Mubarak kenan da ya je gaban Abba yana rok'on shi.
"Ni dai a zuciya ta komai ya wuce wallahi", cewar Ammi.
Cikin fushi Abba ya ta shi fuu ya wuce, wanda Haydar ya fara ta'allak'a laifin rashin dawowar Umma ga Haj, saboda ita ta haife shi kuma in ta bada umurni dole yabi.
Koda wani 6angare bai ganin laifin ta saboda Umma bata d'auki ko wa da daraja ba, su da ta haifa kawai take son ci gaban su, wani tunani ya fad'o mai arai.
"Gidan da su Ammi suka ta shi can Umma za ta ko ma da zama", nan dai ya yi bayanin yadda akayi gidan ya da wo mallakin shi.
Ya d'ora da ce wa tun da su Ammi sun sa mu gurin zama sai ta ko ma can".
"Eh hakan ya yi gaskiya, ni kuma na yi maku alk'awari zanci gaba da lalla6a shi har a samu ya sauko da ikon Allah", Ammi ce ke wannan maganar.
Nan suka yita godiya har Ammi ta ji nauyin su, da hakan Jameel ya wuce gidan shi ya gayawa Umma yadda suka yanke.
Kuka kam ta yishi har ta gode Allah daka dube ta yanzu za ka hango nadama k'arara a fuskar ta.
Da hakan akayi gyaran da ba'a rasa ba a tsohon gidan Ammi, Umma ta had'a kayan ta ta koma can da zama had'e da y'ar aikin da aka sa mo mata wata dattijuwa, shi ko Jameel ya cira da matar shi Yusrah dake jin tamkar ta zuba ruwa k'asa tasha.
****
*BAYAN SATI BIYU*
Yau Rukayya ta shirya domin kaiwa k'anwar ta Musirrah ziyara wadda take ji har cikin ranta har gobe tana jin nauyin abinda tayi mata.
Tana kitchen tana masu girki ta ji sallamar Anty Rukayya da saurin ta za ta fito ta ajiye kular miya saman kantar ajiye kaya ashe bata hau dai-dai ba ta zubar mata a k'afa.
K'arar da tayi dai-dai take da fitowar Mus'ab daga bedroom d'in shi, da saurin shi har suna rigen-gen shiga kitchen d'in shi da Rukayya.
Dafe da k'afar take ta saka tissue tana goge gurin sai yarfe hannu take yi alamar tana jin zogi.
Caraf ya sunkuce ta tamkar wata Baby ya dawo falo da ita, sai rufe fuskar ta take yi akan kunyar Anty Rukayya.
Saman three seater ya d'ora ta da saurin shi ya haura sama ya d'auko keyn mota had'e da gyalen ta.
"Plxxx Auntyn mu minti goma, ki kula da gidan yanzu za mu da wo", bai tsaya sauraren amsar ta ba ya kuma sunkutar Musirrah sai mota.
Hakan ya ja motar sai asibitin su Shureim, Musirrah mamaki ya hana ta magana har suka iso asibitin, shi ya d'auke ta sai office d'in Dr Shureim.
Koda suka shiga yana duba wata mata, hakan Mus'ab ya matsa mai sai da ya duba k'afar Musirrah wanda zogi kawai take mata.
Nan dai ya mata allurar rage zogin had'e da magani daya ba ta, "to laila da majnun a ko ma gida asha magani, saboda gurin bazai d'aye ba", Dr Shureim ke maganar cikin zolayar su.
Cikin kunya Musirrah ta rufe fuskar ta, "yarinya ki gode Allah da kika sa mu miji mai baki kulawa haka, Allah ya baki lafiya", cewar matar da suka tarar a office d'in.
D'aga kan da za tayi karaf suka hada ido cikin mamaki da sakin baki take nuna ta had'e da furta Mama Baraka".
Duk da k'arancin shekarun ta a wancan lokacin da suka rabu da Mama Baraka bai hana ta ga ne taba, saboda koda suka rabu tana da kusan shekaru takwas da watanni a duniya.
"Y'ar nan wacece ke?, ban ga ne ki ba?".
"Mama ni ce Musirrah k'anwar d'anki Mubarak d'iyan Ammi".
Cikin sauri ta ta shi ta rungume Musirrah duk da ba wani k'arfin jiki ne da ita ba.
"Allah mai iko, mai kowa da komai, ashe da rabon za mu had'u, ina Hauwa'u? Ina yaro na Mubarak?".
"Duk suna nan k'alau Mama", tana maganar farin ciki fal a zuciyar ta.
Nan dai suka gama komai suka wuce da ita gidan su, saboda dama ta gama abinda ta zo yi shawarwari yake bata akan matsalar ciwon da ke damun ta wato ciwon sugar.
Cikin kunya ta shiga gidan ganin yadda Mus'ab yayi mata gaban Anty Rukayya ko kunya baiji ba.
Hakan dai ta yi mata sannu suka ci abinci had'e da d'an ta6a hira har take yi mata nasiha kan ta rik'e mijin ta da kyau, don irin wa'annan mazan yanzu sunyi wuya.
Nan Musirrah ta yita mata godiya har ta wuce, nan take cewa Mama Baraka ta Bari ta kimtsa sai suje gida gurin Ammi.
*SDY JEGAL*
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣7⃣/6⃣8⃣
Bayan ta gama kimtsa wa ne suka wuce sai gidan Ammi murna fal a ranta na yau zata ga Ammi duk da ta zo sau d'aya bayan auren ta, 6angare d'aya kuwa ji take yi tamkar ta had'iye Mama Baraka.
Da sallamar ta ta shiga gidan ita da Mus'ab sai Mama Baraka dake biye dasu, kuwar Mukarrama ta fito da ita daga kitchen, manne da juna ta sa me su tamkar wa'anda suka yi wata basu ga juna ba.
"Ku matsa ku hargitsa gida tunda abinku ba na hankali bane".
Nan Musirrah ta saki Mukarrama ta durk'usa ta gaida Ammi, nan ma suka gaisa da Mus'ab ya wuce office.
"Hala ina kika sa mu bak'uwa?", cewar Ammi da yake ko da suka shigo kan mama Baràka soke yake k'asa.
A hankali ta ta ka zuwa gurin Mama Baraka tana rik'e da hannun Ammi, sai da ta isa gurin ta sannan ta had'a hannun su guri d'aya, d'agowar Mama Baraka suka had'a ido.
Da k'arfi Ammi ta furta Baraka!, "da ma kina duniyar nan?, ikon Allah".
Nan dai suka yi ta murnar ganin juna Ammi ta rasa ina za ta saka Baraka akan murna.
"Musirrah ina kuka had'u da Baraka halan?".
"Wallahi kin ga Ammi miya ce ta zubar min a k'afa, shi ne ko da muka je office d'in abokin shi muka gan ta, kin ga ma Ammi ni na fara ga ne ta, ai nasan da yaya Mubarak ne ba za tak'i ga ne shiba", tana maganar ne cikin shagwa6a.
"Yo banda abinki ta ya za'a yi in k'i ga ne Mubarak?, ai ko da ban yiwa kaina adalci ba".
"Ah ba ma yaya Mubarak d'in ne baki wa adalci ba kan ki ne baki wa ba?".
Nan dai suka had'u suna hira da farin ciki fal a ransu, Musirrah ta fitar da wayar ta sabuwa da Mus'ab ya siya mata ta kira yaya Mubarak tana shaida mai duk inda yake yayi sauri ya taho gida yaga wani abu.
Da saurin shi ya shigo falon hankalin shi ta she saboda ya zata wani abu ke faruwa.
"Zo nan kusa Mubarak in ganka". Muryar da ya ji ta do ki kunnen shi kenan, juya warda zai yi kenan ya ga Mama Baraka, murna da farin ciki su suka hana mai magana.
Hakan ya ja jiki har ya isa inda take zaune ya durk'usa gaban ta had'e da ce wa "Mama ina kika shiga hala? Kwanakin baya na je neman ki gidan da muka yi zama amma aka ce min kin dad'e da ta shi, wanda ko Ammi ban gaya wa na je ba".
"Saboda so nayi sai na ne mo ki kawai ta gan mu tare, ashe Sister ce ke da rabon fara ganin ki".
"Da ma kina cikin garin sokoto ne da zama ko yaya?".
"Ai dai kana bari ta sa mu abinda tacci sannan ka je ro mata tambayoyi?", cewar Ammi.
"Ai na ci abinci gidan Musirrah k'oshe nake, ahh su Musirrah har an yi aure, to ni ina suruka ta?".
"D'an na ki bai gama ruwan ido ba har yanzu", cewar Ammi.
Nan dai suka ne mi sanin tarihin ta bayan rabuwar su, hakan ya sa ta gaya masu ce wa bayan ta koma garin su Birnin kebbi ne ta auri wanda suka so auren juna har ta gudu sanadiyyar an hana su auren juna.
Nan ta d'ora da gaya masu bayan auren ta shiga matsaloli da dama wanda bata jin sanyin mijin daga baya, ka ma daga kanshi har y'ay'an shi dama mahaifiyar su.
Bayan aure na da shekara biyu ne Allah ya yiwa mahaifina rasuwa, wanda naji mutuwar sosai har cikin raina, nan na fara fuskantar cewa abinda maigidan ke yimin ba yin kanshi bane asiri ne, saboda fuskantar ce wa yana so na sosai".
"Saboda ranar da kaina na ga abokiyar zama na na binne layu a tsakar gidan mu, wanda bayan ta d'aga ne na tone abin na k'o nasu sai ga shi zaman mu dashi ya dawo lafiya lau har yana ba ni kulawa fiye da farko, wannan ya k'ara haddasa yaran ta suka d'oramin k'iyayya, duk da ina iya bakin k'ok'ari na don nusar dashi wasu abubuwan".
"Shekara biyu da suka wuce Allah ya yiwa maigida na rasuwa sanadiyyar had'arin mota da yayi".
"Na shiga tashin hankali sosai wanda lokacin daka kalli abokiyar zama na za kace mutuwar tamkar abin murna ce a gare ta".
"Sanadiyyar yaran ta shida, hud'u maza mata biyu wanda ni ko ko 6atan wata banta6a yi ba".
"Bayan gama takaba d'ita ne da wata biyu yaran ta suka saka ni gaba Dole sai na bar masu gidan su, duk da ba wata dukiya ne da mahaifin su ba, hakan na had'a y'an kaya na na koma gaban mahaifiya ta domin kulawa da ita ga tsufa ya zo mata".
"Lokacin da maigida na yacika wata goma da rasuwa Allah ya kar6i ran mahaifiya ta wacce ita kad'ai ta rage min a duniya sai kuma wani k'ane na, fad'ar tashin hankalin da nashi ga ma 6arnar baki ne".
"Hakan nake zaune gidan tare da matar k'ane na da imani bai gama game zuciyar ta ba, don ko abinci tsiyar ta ta tashi banda rabo a cikin shi".
"Daga baya ne ciwon sugar ya bayyana a gare ni wanda daga Birnin kebbi aka turo ni nan domin ganin likita, nan ne muka had'u da Musirrah".
Sun tausaya mata sosai musamman Mubarak dake jin ta tamkar k'anwar Ammi.
"Daga yau kukan rashin haihuwa ya k'are maki Mama, ke da kike da kamar ni a duniya dama na dad'e da k'udurta ma rayuwa ta neman ki duk inda kike".
Ammi ba k'aramin dad'i taji ba akan furucin Mubarak, don tabbas Mama Baraka ta taimake su lokacin da suke cikin tsananin neman taimako.
"Yanzu ke da wa kuka zo Mama?" Cewar Mubarak.
Nan ta d'an razana alamar tunawa da wani abu.
"Ai ko ka ga murnar had'uwa daku na manta da ina tare da wani Sule da k'ane na Ibrahim ya had'ani dashi".
"Yana ina yanzu Mama?".
"Dama mun ajiye ne sai ya gama jigilar shi in zai koma yatai asibiti ya d'auke ni".
"To kiyi zaman ki Mama in yaso nan da kwana biyu yaya Mubarak yakai ki gida", cewar Musirrah.
"Aah ba ayi hakan ba, yanzu dai Mubarak yaje yakai ta asibiti d'in su wuce da mutumen, ai zamu shigo Bk d'in nan da kwana uku za muje har gidan asan tayi".
Da hakan aka had'a wa Mama Baraka goma ta arzik'i, har Abba ya fito suka gaisa yana ta yi mata godiya, har gurin Haj Maryam mahaifiyar Abba aka kaita suna ta mata godiya.
****
Yau satin Umma biyu a gidan da su Ammi suka ta shi, ita kad'ai ranta gidan sai dattijuwar da ke taya ta zama a gidan.
Duk da cewa lokaci zuwa lokaci Haydar da Mubarak har ma da Mukarrama suna kawo mata ziyara, musamman Haydar da Mubarak kusan kullum nan suke cin abincin dare, saboda da wuya kagan su ba tare ba, don Haydar na son y'an uwan shi sosai.
Wani lokaci Umma in ta ga yadda Mubarak ke bata kulawa har hawaye take yi, saboda abinda yake yi mata ko Ammi mahaifiyar shi nan zai tsaya, saboda sau da dama yake siyo mata kayan abinci ya kawo mata yace shi da Haydar suka siya mata, wanda wataran Haydar ke gaya mata bai ma san ya yiba, saboda yanzu Mubarak ya samu aiki a Eco bank, wanda Haydar suke business da Abba saboda dama shi ya karanta.
*03:00am*
Tana kwance kawai ta ji dirar mutane a gidan kafin tayi wani yunk'uri sai gasu a d'akin ta.
Iya rud'ewa da tashin hankali ta shige su, ba abinda bakin ta ke furtawa sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
D'ayan ya nuna ta da bindiga yana ce wa "kud'i ko rai".
"Don Allah kuyi hak'uri wallahi banda kud'i".
"Oga in ba kud'i ta ba mu gwala-gwalai", Cewar d'ayan saboda su uku suke.
"Don Allah Ku yimin rai wallahi su ma ban da", cikin tashin hankali take rok'on su, saboda maganar gaskiya yanzu bata da komai sai rai da hak'uri, don ko sati bata yi ba da siyar da gwal d'in ta d'aya da tayi mata saura.
Ganin ce wa za ta ka wo masu cikas d'ayan ya halbe ta da bingida saitin damtsen ta, nan suka haura katanga suka tsere.
Note: kuyi hak'uri da rashin jina jiya, wannan ya faru ne sanadiyyar fafutukar canja blog da nayi saboda ance mywapblog zai daina aiki.
Yanzu ga sabon blog d'ina domin gyaran kuskure na in kun ganshi. Www.sadijegal.blogspot.com
*SDY JEGAL*
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: _SANADIN_ _K'UNCI_6⃣9⃣/7⃣0⃣
K'arar bindigar ne ya tayar da dattijuwar da ke taya ta zama daga bacci, da saurin ta ta fad'a d'akin ganin Umma ta yi zube a k'asa ga jini na biyar kafad'ar ta.
Nan ta d'auki wayar Umma ta kamo lambar Haydar ta kira take gaya mai meke faruwa, kiran asubar farin ya yi dai-dai da ta da mota da ya yi, cikin sauri Mubarak ya cimma shi da tambayar ina zaije haka?.
"Iya lantana ta kira ni wai 6arayi sun shiga gidan Umma har sun harbe ta".
Cikin azama ya fad'a motar suka wuce sai gidan ta, haka suka kwashe ta sai asibiti mafi kusa, dak'yar aka samu fitar da albarushin da aka harbe ta dashi.
Sai kusan k'arfe bakwai suka bar iya tare da ita kan ce wa za su je gida su dawo.
Da sallama suka fad'a falon suka ci karo da Ammi tana batun shiga kitchen.
"Ina kuka shiga Abban ku ya fito ta daku kuje masallaci ya tarar wayam ba ku nan?".
"Wallahi Ammi 6arayi suka shiga gidan Umma har sun harbe ta a kafad'a, daga asibiti muke", Mubarak ne ke gaya mata.
"Subhanalillah, injin abin da sauk'i?".
"Eh to anyi nasarar ciro albarushin yanzu ko da muka fito ta sa mu bacci", cewar Haydar.
"To bara in d'ora breakfast in gama sai muje akai mata daga nan in dubo jikin na ta".
Shesshek'ar kukan Mukarrama suka jiyo a falon, nan dai Ammi ta yita rarrashin ta su kuma suka wuce part d'in su.
Bayan ta gama aikace-aikacen ta ne ta had'a abinci a warmer, sai ruwan tea a flask tana fitowa da kayan ne falo sai ga Abba ya fito.
"Ammin yara me ake had'awa hakan duk gida ya game da k'amshi haka?".
Nan ta yimai bayanin abinda ke faruwa har ta d'ora da ce wa' "yanzu nake batun shiga in gaya ma zan bi su in dibo jikin na ta in ya so Mubarak sai ya dawo dani".
Nan ya yi kicin-kicin da fuska tamkar bai ta6a dariya ba.
"In dai har ni ke iko dake ban yarda kije ko ina ba, su suje kawai Allah yabata lafiya".
Da hakan ya juya ya ko ma bedroom d'in shi, wanda ya yi dai-dai da fasa kukan Mukarrama.
Nan dai Ammi ta taushi zuciyar su ta had'a kayan abincin ta ba su suka wuce, wanda duka rayukan su basuyi dad'i ba da abinda Abba ya yi.
****
Yau ta ka ma weekend Mus'ab na gida sai kai kawo yake yi, duk inda Musirrah ta saka k'afar ta yana biye da ita don har girki tare suke shiga kitchen.
"Haba K'albee na ya kama ta kaje falo ka zauna har in k'ara sa aikin mana, kai ba kuku ba sai zaman kitchen", tana magana da murmushi a fuskar ta.
"Ke kan ki Hayatee kin san bazan zauna kina fama da aiki ba, in kuma kora ta zaki yi sai in fice daga gidan gaba d'aya".
'Ni na isa, kawai ina so kaje ka huta ne karka wahala".
Nan dai ta kammala aiki ta had'a komai suka zube k'asan kafet a falon, saboda al'adar shi a k'asa yake cin abinci.
Zaune ya yi dirshan ya janyo ta saman cinyar shi ya d'ora cikin dariya ta furta.
"Zan ga yadda za'a ci abinci yau, ka kawo ni saman cinya ka d'ora haka tamkar wata jinjira".
"Ai yadda nake jin ki jinjiri bazai kai ki ba, yadda kikasan d'an cikin k'wai haka nake jinki araina".
Da hakan ya rik'a ciyar dasu tana saman cinyar shi har suka k'are, a tare suka kwashe kayan abincin kuma suka kimtsa gurin.
"Yanzu abu d'aya ya rage mana shine wanka sai mu kimtsa in kai ki gidan Dr Shureim da uncle Hakeem, saboda na gaji da mitar su kan cewa 6oyon ki nake yi".
Da hakan suka shiga wanka a tare, saboda tun tana jin nauyin shi kan wasu abubuwan har ta saba yanzu.
Suna gurin wankan ne wayar ta ta d'auki ruri, sai bayan sun k'are ne ya nad'ota a towel tamkar wata jinjira, bai sauke ta a ko ina ba sai gaban mirror.
Falo ya wuce inda ta ajiye wayarta ya d'auko ya mik'a mata, ko da ta duba taga ce wa Mukarrama ce ta Kira ta har sau uku, nan ta shiga kiran lambar.
Bayan ta d'aga ne take gaya mata abinda yafaru da Umma, sannan ta gaya mata asibitin da suke daga nan suka yi sallama.
Mai ta d'auko tana sha fa mar nan take gayamai abinda ke faruwa da Umma, shi ma ya jajanta abin.
Ya d'ora da ce wa "to mu d'age tafiyar sai zuwa next week, yanzu sai mu wuce asibiti d'in".
Da hakan suka kimtsa sai asibitin, ko da suka je d'akin ya cika mak'il da mutane don har surukan ta Ummy da Baffa, Iman da Nibras duk sun zo.
Nan dai suka zauna had'e da jajanta ma juna abinda yasamu Umma.
Mukarrama ce ta ta shi ta je har gaban Baffa ta durk'usa had'e da rok'on shi alfarma kan yaje ya rarrashi Abban su yamayar da Umma.
"Ban can-can ci hakan ba, matsayi na na mace mai son kanta dayawa, bana zargi ko ganin laifin Abban ku ko kad'an saboda ni mai laifi ce wanda nasan ce wa banga sakamako ba har yanzu".
Tana maganar ne idon ta taff da hawaye wanda har kullum tana cikin nadama marar misaltuwa, musamman yau da Mukarrama ke gaya mata har da Ammi suka so tahowa Abba ne yahana ta zuwa.
Gefe d'aya kuma yadda Mubarak ke wahala da ita ganin tun faruwar abin har yanzu bai sa mu zama ba.
Rukayya ce da Musirrah suka zo gaban gadon suna rarrashin ta, wanda Musirrah har da guntun hawayen ta.
Nan Baffa ya saka baki yana mai she da masu yanzu zai wuce gidan na shi ayita ta k'are, wannan zuciya tashi ta yi yawa ace mutum bai tank'waruwa, yana mitar ne yace Ummy ta ta shi su wuce gidan.
Da hakan ya ja mota suka wuce. Bayan shigar su gidan ne aka gaggaisa Ammi ta shiga ta kira Abba, yana fitowa ya had'e fuska don yasan kwanan zancen.
"Allah ba fuska ba komai kake had'ewa yau dole ayita ta k'are, wannan zuciyar ina za kaje da ita ne?".
Nan dai suka gaisa ya nemi guri ya zauna, nan yake k'ara tunkarar shi da maganar yana mai ba shi hak'uri. Haka ma Ummy ta saka baki ita ma ta d'ora da ce wa kadubi girman Allah da kuma darajar yaranta ka tausaya mata".
"Ni inaji duk wanda akayiwa laifi bayana yake, kuma wallahi ni har ga Allah na yafe ka mayar da uwar y'ay'an ka".
Hara rar da ya bita da ita ne ya sa ta sunne kai k'asa tana murmushi, saboda tasan kwanan zancen duk randa tayi mai maganar ya mayarda Umma ce wa yake yi batasan ciwon kanta ba.
"So kuke yi in maida ta wataran mugun halin ta yasa dani har yara na ta banka mana wuta a gida mu k'one k'urmus".
Nan dai suka yi murmushi su duka Baffa ya d'ora da ce wa.
"Kawai ka fito kace mana baka shiryawa mutuwa ba shiyasa kake wannan kame-kamen".
"Yo ai kai shi ne naga ka shiryawa mutuwar har ka rungumi transformer".
Nan dai suka yi ta dariya cike da walwala da nishad'i har suka ciyo kan Abba ya furta ce wa ya mayar da Umma, amma da sharad'in muddin ta dawo ta nemi ta yar mai da hankali to wallahi zai tsinke sauran igiya d'ayar da ta yi saura tsakanin su.
"Ai gaskiya daka ganta Abban Haydar za kasan ce wa ta yi nadama sosai", cewar Ummy.
"Yo ai ke ma saura k'iris ki yiwa rayuwar ki gi6i Allah ne kawai ya ku6utar da ke", inji Baffa.
"Me nayi ni kuwa Baffan Iman?", tana maganar ne cikin fargaba da sauraren me ke faruwa.
Nan dai ya kwashe abubuwan da tayi na korar Ammi da mak'alawa Mubarak sata yagaya mata.
K'asa ina ma za ki bud'e in shige, ashe ni ina dubin yara na kawai suka san da maganar ashe har Baffa ya sani, kai amma dai ya kwafsamin gaban surukan mu yake wannan maganar, ko dai ya manta iyayen matar Mus'ab ne? Yasan dai akwai surukanci tsakani, ohh shi har ya manta kenan ya fi ba wa abota muhimmanci.
Duk acikin zuciyar ta take wannan maganar, nan dai ta fuske ta furta cikin k'arfin hali da borin kunya.
"Baffan Iman ai wannan sharrin shaid'an ne, kuma ga wannan lokacin dubin nake yi tamkar za ka iya auren Ammin su Mubarak ne, ina zan iya had'a kishi da ita", tana maganar ne cikin murmushi da jin nauyi.
Har zai furta ai ko ita na so na aura inda mijin ta rasuwa yayi, komai ya tuna kawai ya ja bakin shi ya tsuke.
Nan dai ta rok'i gafarar Ammi.
"Haba ai komai ya wuce wallahi, Allah dai yak'ara had'a kan mu da yaran mu baki d'aya", nan suka amsa da Ameen suka rabu cikin farin ciki da walwala.
*SDY JEGAL*
www.sadijegal.blogspot.com
Dedicated to Sanah S. Matazu.
No comments:
Post a Comment