[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 2⃣1⃣/2⃣2⃣
Yau kwanan Ammi uku asibiti jiki yayi sauk'i Alhmdulillah, don ma suna sa ran yau abasu sallama. Musirrah na zaune gefen Ammi tana lalla6a ta kan tasha tea sai ga Hjy Maijidda ta shigo, bayan Musirrah ta gaida ta take tambayar ta jikin Ammi.
"Ammi jiki yayi sauk'i Hjy yana yuyuwa ma yau mu samu sallama". Nan Hjy ta matso suka gaisa da Ammi, nan ta yita yi mata godiyar d'awainiyar da tayi dasu.
Saboda tun shigowar su asibiti Allah ya had'asu da Hjy Maijidda, inda taci karo da Musirrah zaune tana hawaye ranar da aka zo da Ammi, nan ta tsaya tambayar ta abinda ke da munta. Da k'yar ta shawo kan Musirrah ta gaya mata abinda ke faruwa. Tun daga ranar ta je ta ga jikin Ammi, kuma ita ke basu abinci kullum saboda ganin cewa tun ranar da suka zo ko mutum d'aya bai zo duba jikin Ammi ba. Ita kuma yaron ta aka kwantar asibitin, yanzu haka ko tea d'in da Musirrah ke lalla6a Ammi ta sha ita ta basu shi.
Nan Hjy Maijidda ta lalla6a Ammi ta sha tea sannan ta 6allo maganin ta ta bata ta sha, nan take tambayar ta jikin yaron ta Ibrahim, ta ce' "ya samu sauk'i ina ganin gobe zamu samu sallama don jiya satin mu d'aya kenan".
Suna hakan ne Dr ya shigo ya duba jikin ta, nan ya sallame su tare da k'ara gargad'in Ammi kan cewa ta rage dogon tunani da kuma saka ma ranta damuwa. Nan suka yi godiya suka had'a y'an komatsan su, Musirrah ta lalabo Nokia d'in ta ta yiwa Mubarak flashing.
Hjy Maijidda ta kira direban ta ta ce yazo yakai su Ammi gida saboda yaga guri zata kawo masu ziyara wani lokaci. Nan Mubarak ya shigo suka had'u suna ta yima ta godiya. Hakan suka shiga suna ta yaba halayen Kirki na Hjy har direban ya saka bakin shi, ya ce' "kad'an kenan daga karamcin Hjy Maijidda, mutum ce da abin duniya bai rufe mata ido, ga ta da taimakon mabuk'a ta, abu ko shi kad'ai ne da ita zata iya bawa na k'asa da ita".
Hakan suka yita hirar ta har suka kai gida, direba na sauke su ya ciro kud'i yabawa Mubarak ya ce' "gashi Hjy ta ce abaku". Sai ga mamaki k'arara a fuskar su, Ammi har da guntun hawayen ta. Nan suka kar6a suka k'ara godiya suka shiga gidan, shi ko direba ya juya asibiti.
Bayan sun shiga gidan Musirrah ta yi shara ta kimtsa gidan, nan suka duba kud'in Hjy dubu biyar ne ta basu, murna kamar me a gunsu. Nan aka kasafa kud'i Mubarak ya fita siyo musu y'an kayan abinci dai-dai kud'in su.
<<< >>> <<< >>>
Yau kusan kwana uku kenan tana hana ma idon ta bacci saboda tana so ta zartar da k'udirin ta akan Musirrah. Musamman jiya da Sultan ya rik'a yi mata fad'a kan cewa bata kyauta ba, kwana uku kenan bata ga y'ar aikin ta ba kuma tasan cewa koda ta bar gidannan mahaifiyar ta bata da lafiya, amma ta kasa bincikawa ta ji mike faruwa dasu. Amsar da ta bashi cewa ita ko hanyar gidan su yarinyar bata sani ba barranta na gidan su ita tasa jikin sa ya yi sanyi sosai. Ta d'ora da cewa talaka kamar ta zan nemi sanin gidan su don ta k'ullamin me? Sanin kan kane ko mai kud'i ba kowa ne gabana ba, hakan ya tattara nashi da nashi ya shige bedroom d'in shi.
Yau shine tun tashin ta daga bacci take zaune falo ko Allah zai kawo Musirrah yau, don kwana hud'u kenan tana dakon ta. Tun maganar da suka yi da Khairat hankalin ta ya gaza kwanciya musamman yadda Sultan ke nuna damuwar shi akan yarinyar.
Misalin k'arfe tara na safe ta shigo gidan da sallamar ta, ga mamakin ta sai taga Rukayya zaune falo, nan ta durk'usa ta gaida ta. Jin kawai ta yi an watso mata Abu a fuska ta ce' "duk da lokacin biyan ki kud'in aikin ki bai yi ba ni wannan ba matsala ta bace har k'ara maki na yi, to ki kwashe kud'in ki kibar min gida na na sallame ki".
Cikin razana da firgici ta tada kan ta takai duban ta zuwa gare ta, nan take sai ga hawaye sun fara saukowa ga kyakkyawar fuskar ta. Bud'e bakin ta keda wuya zata yi magana, cikin azama Rukayya ta d'aga mata hannu alamar bata son jin komai daga gare ta.
Hakan ta tattara kud'ad'en ta ta mik'e tsaye ta nufi k'ofa, koda ta kawo gate har wani jiri take gani, nan Baba maigadi ya tare ta da tambayar meke faruwa? Nan ta kora mai bayani.
Ya ce' "dai na kuka y'ata nasan maigidan bai San meke faruwa ba, amma daya dawo zan gaya mai".
Cikin razana ta kai duban ta zuwa gare shi ta ce' "don Allah Baba kakka ce mai komai akai, asali ma ko ya tambaye ka wani abu a kai na kace mai baka san komai ba, dama matar gidan ta d'auke ni aikatau kuma ita ta gaji dani ta sallame ni, don haka ba komai Baba Allah ya bani wani guri mafi alkhairi a gare ni".
Da hakan suka rabu da Baba jikin damuwa, har ya yi mata alk'awarin ka wo mata ziyara in ya samu lokaci.
Cikin rud'u da tashin hankali k'arara ta nufi hanyar gida, tana tafiya tana layi tamkar zata fad'i ikon ubangiji ne kawai ya kai ta gida.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_2⃣5⃣/2⃣6⃣
Nok'e take da kanta tana juya wainar da ta soyu, jin sallama yasa ta tayar da kan ta suka had'a ido nan suka gaisa yarinyar ta fitar da d'ari biyar da kula ta ce ta saka mata waina. Musirrah ta ce' "inaga fa wainar baza ta kai ta kud'in ki ba saboda tun d'azu na fito kin ga ta kusa k'arewa". Mukarrama ta ce' " wannan ba matsala ba ce bara in shiga mota kafin ki k'arasa".
Nan ta juya ta koma mota ta zauna ta fitar da wayar ta tana latse-latse, a ranta sai tunanin take yi me yakai wannan kyakkyawar yarinya zama k'ofar gida sayar da waina, gaskiya kyawon ta ace yanzu tana university tana karatu. Ta rasa miye silar da take jin tausayin yarinyar, shin ta gano cewa ita ce k'anwar Rukayya share tane kawai tayi ko kuwa bata gano ba? Koda ba abin mamaki bane ko da bata gano hakan ba, saboda sau d'aya suka had'u da ita gidan ta kawo abinci tana jerawa a dinning table ita ko ta shigo da sallama direct ta wuce d'akin Rukayya, saboda in har bazata manta ba lokacin tana sauri Hjy ta aiko ta kar6ar sak'o, amma ta gan ta cikin gardener sau biyu sai dai tana kyautata zaton ita bata gan ta ba.
Ganin ta yi magana bata ji taba yasa ta d'an buga saman motar, nan ta juyo da murmushi a fuskar ta ta ce' "har an k'are? Amma ko kin yi sauri gaskiya". Ta ce' "eh sai dai ta d'ari uku da hamsin aka samu ga chanjin ki". Ahhh ki bar shi, don in ma wainar ki ta yi man ko gobe zaki ganni". Nan Musirrah ta yi godiya ta juya domin kwashe kayan ta ta shiga gida, Mukarrama kuwa ta tada mota ta wuce.
<<< >>> <<< >>>
Bayan ta shigo gidan ne Hjy ta ce' "har ina kika je sayen waina kika fita da mota hala?". Kinfa san cewa Dad d'in Ku bai son yawon siyen abinci, don in yanzu ya gan ki zai fara fad'a". To ai shiyasa na fita da motar, kuma ma Hjy na ce ki rik'a yi mana waina muna ci kince sai dai y'ar aiki ta rik'a yi niko kinsan ba gwanar cin girkin y'ar aiki bace", tana maganar ne cikin shagwa6a tamkar y'ar shekara hud'u.
Hjy ta ce'
"Wannan kuma da kika je kika siyo uwaki ta toya ta, kika sani ma ko y'ar aikin ta fi inda kika siyo wainar tsabta, sarkin iya yi da shegen tsandar tsiya".
Nan tayi murmushi ta d'ora da cewa ina Bross hala bai tashi ba har yanzu?" Je ki duba nima banji motsin shi ba, nan ta ajiye kula ta yi part d'inshi koda ta tura k'ofa yana kwance yana bacci yana sauke numfashi a hankali. Ta ke ta je gurin fridge ta d'auko robar ruwa ta tsiya ya a cup ta je ta bud'e k'ofa sannan ta dawo ta zuba ruwan a hannun ta ta saita fuskar shi ta zuba mai, zaburar shi dai-dai yake da zurawar ta a guje ta 6ace daga d'akin.
Tana zuwa falon ta fad'a kan jikin Hjy tana haki, shiko ya biyota da belt a hannun shi, nan Hjy ta dakatar da shi. Ya ce' "Hjy ni wannan yarinyar zata tarar ina bacci ta zuba min ruwan sanyi a fuska, Allah yau mai raba ni da ita sai ya shirya". Nan Hjy ta juya tana mata fad'a, yo bashi bane na yita tada shi ya k'i tashi ba, har fa filo na dake shi dashi ya k'i tashi", tana maganar cikin shagwa6a da sangarta. Ya ce' "ba zaki ce mutuwa nayi na dawo ba y'ar rainin hankali". Nan dai Hjy ta bashi hak'uri ita ko ta mata fad'a, nan ta sauko ta durk'usa k'asa ta rik'e kunnen ta ta ce' "sorry Bross na yi alk'awari ba zan k'ara ba". To a k'a'idar shi duk laifin da ta yi mai da ta yi hakan zai hak'ura, nan ya yi murmushi ya yi mata nuni da ta tashi. Nan ta ce' "Bross je kayi brush kazo kaga wani abu", sanin cewa nan bata yi mai wasa yasa ya je ya yi brush ya dawo, nan ta d'auko plate ta sakama Hjy waina k'waya biyu su ko suka juya ma Hjy baya suka fara ci.
Hjy ta ce' "yanzu ni za'a bawa waina guda biyu? Tana maganar tana murmushi. Har Mukarrama zata k'ara mata Haidar ya hana, saboda ya fita son waina, haka suka k'arasa cin wainar cikin walwala nishad'i da kuma farin ciki.
(Ni har sun burge ni kamar kar in d'aga, sai dai ina so in rego Musirrah in ga wane hali take ciki, _lolx_)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_2⃣3⃣/2⃣4⃣
Ganin yadda ta shigo gidan yasa da sauri Ammi ta tashi ta taryo ta, mike faruwa Musirrah? Wani abu ya sa meki? Tana tambayar tana duba jikin ta. Mubarak ya tashi ya d'ebo mata ruwa cikin kasko masu sanyi, nan Ammi ta kar6a ta bata sannu-sannu take sauke ajiyar zuciya.
Nan ta fitar da kud'i ta mik'awa Ammi ta ce' "ta sallame ni daga aiki bansan laifin da na yi mata ba". In har wani abu kika san kin yi mata ki gayamin cewar Ammi".
Ina ganin aikin da banje bane kwana uku". Mubarak ya d'ora da cewa ita wacce iri ce da bata san lalura ba?".
Ammi ta ce' "indai akan hakan ne kwantar da hankalin ki Allah shi ke baiwa bawa abinda zai ci, mu da muke hakan ba mu mukaso ganin kan mu hakan ba, Allah yana sane da zaman kowa. Nan ta samu ta rarrashe ta har nutsuwa ta zo mata.
Mubarak ya ce' "Ammi ina ganin mu samu sana'ar da zamu rik'a yi ya fi wannan yawon aikatau, kowane marar mutunci sai anyi sabo zai zo yana wulak'an ta mutane". Maganar ka gaskiya ce nima na gaji da yawon aikatau d'innan".
Nan dai suka tattauna abinda ya dace har suka kawo matsaya kan cewa tunda suna kan titi Musirrah zata rik'a fita k'ofar gida tana toya waina da miya. Nan ma Ammi ta so ta nuna rashin amincewarta saboda cewa tayi bata son talla ga d'iya mace sai dai ita ta rik'a yi da kan ta. Dak'yar Mubarak ya shawo kanta kan cewa abin fa da ban-ban ci saboda ba yawon talla zata je ba a k'ofar gida zata rik'a yi, in yaso daga baya in an samu customers sai ta dawo gida ta rik'a yi. Mubarak ya d'ora da cewa in ma banda abinki Ammi keda lafiya bata isheki ba ta yaya zamu barki ki fita zaman Sana'a k'ofar gida?".
Da hakan Mubarak ya kar6i kud'in Musirrah akayi lisafin abubuwan da za'a siyo na kayan buk'ata afara a gani, nan Ammi ta saka ma abin albarka.
Bayan Mubarak ya fita Musirrah ta tashi ta kimtsa gidan ta d'an d'ora masu abinda zasu ci.
<<< >>> <<< >>>
*BAYAN* *SATI* *D'AYA*
Tun shigowar ta gidan take ta lek'e-lek'e ina zata ga y'ar aikin Anty, kawai tana zaune suna hira taga wata dattijuwa ta zo ta jera abinci a dinning table. Nan takai duban ta ga Antyn ta ce' "ina kika samo wannan Anty". Kedai bayan na kori waccan y'ar iskar wata k'awa ta ta samomin iya, amma fa gaskiya hak'uri ne nake yi da'ita Sam bata iya girki sosai ba, amma ta fiyemin mai batun yimin k'wacen miji".
Nan dai Mukarrama ta yi murmushi cikin ranta sai mamakin hali irin na Anty take yi, ga mugun son jiki dai-dai da ruwan Lipton bata iya shiga kitchen ta dafa, amma fa sai shegen kishin miji batasan uban wa ya gaya mata ta hakan ake tafiyar da miji ba, koni da nake k'anwar ta bazan yi rayuwar aure a hakan ba.
Jin Rukayya ta ta6o ta yasa ta zabura, ta ce' "ina magana ki tashi muci abinci bansan uwarda kike tunani ba". Ni kinsan ko a gidan bana cin abincin y'ar aiki sai wacce ta kwanta min".
Nan ta tashi ta sa6a Jakarta ta ce' "ni zan wuce sai na dawo wani lokaci". Sanin halin yasa ta ce' "kigaida Hjy".
Bayan ya bud'e mata gate ta fita da motar ta nan ta fitar da dubu d'aya ta bashi yana ta godiya. Ta ce' "Baba ina neman alfarma in har kasan gidan su y'ar aikin Anty ka gaya min". Da murnar shi ya ce' "za'a yi biko ne?".
Akwai dai dalilin da yasa nakeson ganin ta, sanin mutunci da karamci irin na Mukarrama yasa ya mata kwatan cen gidan su Musirrah, ya d'ora da cewa in ma da safe kika je zaki gan ta k'ofar gida tana sayar da waina. Nima jiya ne kafin in zo nan na biya duba ta har ta bani waina.
Nan ta yita yimai godiya taja motar ta sai gida. Shi ko sai tunani yake yi ko me zata yi mata, saboda ko maigidan da ya tambaye shi ita cewa ya yi baisan gidan su ba sanadiyyar alfarmar da ta rok'a kan kar ya gaya mai. To Allah dai yasa lafiya take neman ta, da hakan ya rufe gate ya koma ya zauna.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_2⃣7⃣/2⃣8⃣
Lallai tabbas duk yanda Sana'a take komai k'an-k'an tar ta ta fi zaman banza, saboda gaskiya su Musirrah abubuwa sun fara yi masu sauk'i.
Da shigar ta gidan ta had'a duka kayan da take Sana'ar waina dasu da sauran na buk'atar gida ta wanke bayan ta k'arasa ta d'ora masu girki tana saukewa ta shiga wanka.
Mubarak ya shigo da sallamar shi ya samu guri ya zauna, nan Musirrah ta sa masu abinci suka ci, bayan sun k'are ne ta shirya ta fito. Mubarak ya kalle ta ya ce' "sai ina kuma?" Ta ce' "yaya yau Mela zan kaiwa ziyara kasan mun kwana biyu bamu had'u ba". Ai fa yanzu an samu sake dama can nasan don kina wuni wurin aikatau ne shiyasa ba kida lokacin yawo". Kai yaya dama ai banda inda nake zuwa duk duniya in ba gidan su Mela ba". Nan ta d'auki kular da ta saka waina a ciki ta ce' "Ammi na tafi sai na dawo" to kigaida Hajiyar Mela da kyau.
Bayan ta samu napep ne ta wuce sai unguwar gobirawa gidan su Mela, da shigar ta gidan Mela ta tarye ta cikin murna da kewar juna, bayan ta gaisa da Hjy ne ta bata kular wainar, Hjy ta yita saka mata albarka ta d'ora da cewa Allah ya sanya hannu a wannan Sana'ar ya tallafa maku, ai yanzu yanayi ne abubuwan sai addu'a". Nan ta amsa da Ameen suka wuce d'akin Mela suka bud'e shafin hirar yaushe rabo.
<<< >>> <<< >>>
*BAYAN SATI D'AYA*
Mukarrama ta fito zata je siyen waina ta yi tayar da motar ta ta k'i tashi, gashi bata son Dad ya tashi daga bacci ya ganta tasan fad'a zai ta yi mata, saboda bai son yawon siyen abinci, ita ko gata mayyar waina ko sun ce Hjy ta yi masu cewa take yi sai dai a saka y'ar aiki. Da saurin ta ta je part d'in Haidar ta ce' "Bross ban aron key d'in motar ka zan je yanzu in dawo". Gaskiya bazan bada ba kije ki d'auki ta ki", wallahi Bross ta k'i tashi ne kuma ina so in je in siyo waina tun Dad bai tashi daga bacci ba".
Jin hakan yasa ya tashi ya ce' "muje tunda waina za'a siyo" yana maganar da murmushi d'auke a fuskar shi. Nan suka fito da saurin su ya tada mota suka wuce sai unguwar su Musirrah, bayan ya tsaida mota ne gefen ta Mukarrama ta fito ta nufo ta da kula a hannun ta, bayan ta yi sallama Musirrah ta amsa da fara'a d'auke a fuskar ta, ta bata kud'i da kula ta saka mata.
Kalar ta chocolate colour ce, tanada manyan ido masu yalwar gashin gira had'e da sajen da ya kwanta mata luf-luf a gefen fuska, idon ta masu d'aukar hankali ne nan take, tana da 6oyayyen kyau Wanda mutum ba zai ga neshi kai tsaye ba, ita ba ma'abuciyar son k'yale-k'yale bace da ganin ta, kyawon ta irin mai fizgar nan ne, amma fa in ka k'ura mata ido zaka ga cewa ba kyakkyawa ce sosai ba, sai dai kuma ba laifi.
Rufe k'ofar da ta yi ne ya dawo dashi hayyacin shi, cikin mintocin da basu haura uku zuwa hud'u ba ya d'auke hoton surar ta tsaf a cikin k'wak'wal warshi.
Yi sauri Bross ka tayar da mota muje gida ba nason Dad ya tashi bai gan muba, hakan ya tada mota duk jikin shi a sanyaye tabbas ya had'u da kyawawa iri-iri amma bai had'u da wadda taje da imanin shi kai tsaye ba tamkar wannan mai sayar da waina, har suka kawo gida sak'e-sak'e da tunani Kawai yake yi. Bayan sun zauna cin wainar ne yake tambayar ta cewa dama tasan yarinyar ko kuwa siyen waina kawai ya had'a su?. Eh to Bross na San ta sai dai ba wani sani sosai ba", nan ta bashi labarin abinda Anty Rukayya ta yi mata, ta d'ora da cewa gaskiya nidai yarinyar ta kwanta min a rai kuma ina tausaya mata duk da cewa bansan miye silar zaman ta hakan ba". To yanzu miye mafita a kai kuma ta yaya za'a tallafa mata?"
Ta ce'
"So nake yi sai munyi sabo da ita sannan, saboda ba naso ta gano cewa ma inada alak'a da Anty Rukayya", eh to hakan za'a yi, amma in har zaki je ki gaya min sai muje tare". Da hakan suka kai k'arshen maganar tasu.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 2⃣9⃣-3⃣0⃣
Yau tun safe Mubarak ya tashi bayan yaci abinci ya yi wanka ya zo gurin Ammi ya ce' "Ammi zan fita neman aiki a yi mana addu'a".
Ta ce' "to Mubarak Allah ya bada sa'a kuma da rabo, sai ka dawo". Nan ya amsa da Ameen, har ya kusa fita Musirrah ta ce' "shine yaya ni ko aneme ni, ba'a son addu'a ta kenan", nan ya juyo haba k'anwata ba haka bane naga kina ta hada-hadar kayan sana'ar kine shiyasa, amma yanzu zo kiyi min addu'a yana maganar da murmushi d'auke a fuskar shi. Nan ta tako har gurin shi ta ce' " yaya Allah Allah ya taimaka yabada sa'a, nan ya yi murmushi ya ce' "Ameen", yasa kai ya fita.
Yau ma kamar kullum ta had'a komai na sana'ar ta ta fita, tamkar ita yake jira sai gashi ya iso gurin ya bata dubu d'aya had'e da guntuwar takarda an rubuta *A rabawa almajirai waina* wannan d'abi'ar shi ce tun fara tuyar wainar ta da kwana uku kullum sai yazo ya bada dubu d'aya had'e da short note yanzu har ya zamo kullum k'ofar gidan su baka rabata da almajirai.
Sai dai Abu d'aya ne ke d'aure mata kai tun ranar da mutumen ke tahowa gurin ta sayen waina bata ta6a ganin fuskar shi ba, saboda kullum zai zo mata da riga mai had'e da hulan nan wadda take rufe fuska gaba d'ai, kuma da ya bata kud'in zai juya saman mashin d'in shi ya wuce. Sai dai abu d'aya ke tsaya mata arai rashin maganar shi ta fi tunanin k'ila kurma ne, saboda kullum sai dai kawai taga mutum ya tsayar da mashin gaban ta ya mik'o kud'i da takarda.
In har ba zata manta ba ranar da ya fara zuwa can nesa da ita ya tsaya ya kira yaro ya bashi kudi da takarda ya kawo mata ya nuna mata mutumen. To tun daga ranar shike zuwa da kan shi.
Nan dai ta ji hayaniyar yara tayi yawa saman kanta suna jira ta sallame su, dole ta dawo hayyacin ta saboda suna jira ta rabamasu wainar.
Bayan ta sayar da wainar tane ta kwashe kayan ta ta shiga gida nan tayi wanke-wanke had'e da d'ora masu girkin rana, ana hakan ne suka ji sallamar mutum koda suka duba ashe Hjy Maijidda ce da murnar Musirrah ta taryo ta ta kar6i yaron ta Ibrahim daga hannun ta. Bayan ta zauna ne suka gaisa Ammi ta ce' "ashe Ibrahim jiki ya yi sauk'i", kin ganshi nan wallahi sicklier ke damun shi, munyi yawon asibiti har mun gode Allah", Ammi ta CE' "Allah ya ya yemai da sauran musulmai duka, Ameen ta ce' ta d'ora da cewa kema jiki ya yi sauk'i, gaskiya kam Alhmdulillah na samu sauk'i. Nan Musirrah ta kawo mata ruwa had'e da abinci Hjy ta bud'e abinci taci ta ce' "kamar kinsan inason wake da shinkafa sosai a tsarin abinci na, nan taci Saida ta k'oshi babu k'yama ko nuna su talakawa ne.
Tsarin gidan su ya burge ta sosai saboda ko ina ka duba tsaf a share ko Karen tsin-tsinya ba zaka gani a filin gidan ba. Nan ta mayar da hankalin ta ga Ammi ta ce' "gaskiya Ammin Musirrah na dad'e ina nazari kan ki keda yaran ki lokacin da kika yi kwanciya asibiti, ba wai sa ido ba amma naga har kuka yi zama asibitin aka sallame ki banga kowa yazo duba kiba, sai kuma ranar zan wuce naji yaranki na tattaunawa akan rashin sanin ina asalin su yake suna cikin damuwa sosai, naso lokacin in yi masu magana sai naga cewa dake ya dace muyi maganar bada yara ba, shi yasa na yi tunanin had'a ki da direba na yaga gidan ku saboda maganar nason nutsuwa". Kuma nayi hakan ne saboda yabawa da d'abi'ar ki data yaran ki, ya kamata ki natsu kiyi nazari duk abinda ke rayuwar ki na damuwa ki cire shi ki dangana yaran ki ga mahaifin su", duk duniya babu gata kamar yaro ya tashi gaban mahaifin shi, in auren d'iya mace ya tashi karon farko mahaifin ta ake nema ba mahaifiya ba, ko nan ya kamata kiyiwa yaran ki gata".
Nan take hawaye suka wanke dattijuwar fuskar Ammi ta ce' "nagode sosai Hjy Allah ya saka da khairan, kuma zan samu lokaci in zo har gida in baki tarihin rayuwa ta". Nan ta goge hawayen ta ta kira Musirrah ta ce ta d'auko waya ta saka lambar Hjy sai ta bata tasu lamba.
Nan Hjy ta tashi zata wuce Musirrah tana d'auke da Ibrahim ta rakata har gurin mota, bayan ta kar6i Ibrahim ne ta d'auko wata leda cike da kaya ta mik'a ma Musirrah, nan ta yita godiya ta juya zuwa gida.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
No comments:
Post a Comment