Monday 17 October 2016

SANADIN KUNCI 51-60

[7:25AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣1⃣/5⃣2⃣��

Ohhhh! Duniya ina za ki damu? Kawai akan zamantakewar kishi za ki sa akashe kishiyar ki, miye ribar ki anan? Yanzu da ace an kashe ta da wanne ido za ki kalli ubangijin ki ranar alk'iya ma?", duk Alh Farouk ne ke furta wa'annan maganganun, duk wanda ka kalla a falon za kaga idon shi har sun kumbura kan kuka.

Inda wa'ansu ke tausayin irin wahalhalun da ta sha wanda duk da haka ga su a raye su dukan su, lallai tabbas da gaskiyar bahaushe da yake ce wa' "wahala bata kisa sai kwana sun k'are".

Sai da Baffa ya rarrashi mutanen falon aka samu suka tsagaita kukan, amma fa da ka kalli d'iyan Haj Zainab ka san cewa suna cikin tashin hankali marar misaltuwa.

Baffa ya ce' "Haj Zainab garin ya ya hakan ta kasance har kika ba da kwangilar kisan abokiyar zaman ki?".

Dak'yar ta sassauta kukan da take yi saboda ji take yi tamkar k'asa ta bud'e ta shige, ko kuma yanzu mala'ikan d'aukar rai yazo mata, ta bud'a baki ta ce'

"Wallahi duk abinda ya faru sharrin shaid'an ne da son zuciya, sai kuma zugar wata k'awata Haj Karime, tun lokacin da za ayi auren take ta zuga ni kan cewa kar in kuskura in bari ayi auren, in ba hakan ba zuwa gaba zan zamo abar tausayi, ba akan komai ba sai don ce wa wasu amare in sun shigo neman suke yi su fitar da uwargidan ko kuma su mayarda ita tamkar shara cikin gidan".

Allah shi ne shaida ta lokacin da aka auro Hauwa'u hankali na ya kwanta da ita saboda yadda take ba ni girma, musamman duk abinda za tayi na girki ko makamancin hakan za ta ce min Ummar Jameel ya za'a yi, sai abinda na ce take yi.

Bayan kusan sati biyu ne Haj Karime ta zo gidan, nan ta saka ni gaba tanai min fad'an cewa har kishiya abar yarda ce, barrantana wa'annan amaren masu mugun rawar kan tsiya.

Ta d'ora da ce wa yanzu ga yayar ta can kishiya ta ko rota da yara biyar, jin hakan ya sa na tsora ta sosai musamman ganin cewa Alh na son Hauwa'u sosai.

"Ganin bayyanar ciki gare ta da kuma irin kulawar da Alh ke ba ta shi ya k'ara ta yarmin da hankali, nan na rik'a takura mata amma fa duk abinda nake yi ba na yi a gaban Alh, wannan kuma duk cikin kissar Haj Karime ne, a cewar ta ko da mun ta shi aiwatarda k'udirin mu ba za'a zarge mu ba".

"Sai ga shi haihuwar farko ta fa ra da namiji sai nake ganin tamkar za ta rik'a haifo maza ne sai tashin hankali na ya k'aru a wannan lokacin, da Alh ya biya mata aikin hajji ne na kasa 6oye bak'in ciki da damuwa ta har na fito k'arara na nu nawa Alh wanda yaso zama sa6ani tsakani na da shi, daga baya ne Haj karime ta ba ni shawarar in kwantar da hankali na in ta wuce kawai mu baiwa Mubarak guba ko maganin 6era yasha, in ya so bayan ya mutu za muce fitar da shi ne da akayi daga mamma ya yi ta zawo shine ya zamo ajalin shi".

"Bayan ta wuce ne na so aiwatar da k'udirin mu sai Hassy mai aiki ta zamo Katanga a tsakanin mu, domin ita ke kula dashi ko yaushe, nan da can ba ta d'agawa ta bar shi".

"Ban manta wa akwai lokacin da na jik'a maganin 6era ana saura kwana hud'u Hauwa'u ta dawo da niyyar ce wa zan kai k'arshen shi. Sai da na fito na saka ta aiki da niyyar ta fice in ba shi maganin sai ga shi ta d'auke shi ta sa6a a baya ta fice, ranar ji nayi tamkar in kashe ta".

"Hakan dai ta dawo ban samu cika nufi na ba akan Mubarak, nan dai Haj ta ba ni shawarar dole in sa Alh ya ko ri Hassy in ba hakan ba akwai matsala nan gaba, da hakan na ce wa Alh ai Hassy satar shinkafa da kayan abinci take yi muna, Alh ya so in Kira ta yaji in har rashi ne yayi mata yawa a rik'a tallafa mata da abincin nan nayi tsaye sai dai a sallame ta".

Da hakan aka sallami Hassy mu kuma muka cigaba da shawarar hanyar da za mubi mu fitar da ita daga gidan Allah bai k'addarta ba har sai da ta samu cikin wannan Musirrah d'in.

Saboda Alh na tafiya sokoto akai-akai sanadiyyar aikin gidan da yake yi da za mu ko ma, lokacin mu kayi magana da wani d'an daba muka ba shi kwangilar shigowa su d'auke Hauwa'u su fice da ita har yaron ta".

Nan na ba su dubu talatin wanda bayan an yi maganar k'arshe kan ce wa za su kai ta su yar ne, Haj Karime ta kira ni ce wa su ma kashe ta gaba d'ai a huta".

Lokacin na nu na mata cewa bazan iya ba wanda muka so samun sa6a ni ni da ita, sai da ta nu na min cewa in fa ba'a kauda ita ba komai jimawa za ta da wo kuma asirin mu zai tonu, da hakan na amince har na kira d'aya daga cikin su ce wa su kashe ta zan k'a ra masu wasu kud'i akai, bayan sun da wo ne na k'a ra masu wasu kud'in".

"Can gura ren asuba na ta shi na saka fetur a d'akin Hauwa'u, saida na had'a kan yara na da sauran abinda nake buk'a ta guri d'aya sannan na cinna ma d'akin wuta, wanda ni da kaina na firgita na fita neman taimako saboda har d'aki na sai da wutar ta ka wo, ba'a samu kashe wutar ba saida ta lashe komai na gidan part d'in Alh ne kawai bata kaiba sanadiyyar shine na farkon shigowa gidan".

"Bayan an kashe wutar ne na yi kuru-ruwa ina neman shiga gidan ina ambaton Hauwa'u da Mubarak had'e da furta sun mutu, nan hankalin mutane ya kawo aka shiga gidan iya bincike babu alamar su nan aka hakura saboda ganin irin 6arnar da wutar ta yi".

Bayan an yiwa Alh waya ya dawo ne cikin tashin hankali da firgici wanda sanadiyyar hakan sai da ya kwanta asibiti na tsawon sati d'aya, bayan sati uku ne da faruwar wannan lamarin na tunkari Haj karime domin kar6ar gwala-gwalai na da na ba ta ajiya had'e da kud'a d'ena na tarar wayam wai sun ta shi daga garin gaba d'aya, cikin tashin hankali na kira wayar ta bayan ta d'auka mun gaisa ne nake tambayar ta ance wai kun ta shi daga garin? Bu d'ar bakin ta tace min ga ta hanyar kano za ta ko ma garin su, cikin rud'u da tashin hankali nake ce mata kamar yaya, nan take gaya min ta ci banza maganin irin mu kenan kuma ni ce ta biyar da ta yiwa hakan, in ina da kotun da za ta kar6ammin kud'i tana jira, daga hakan ta kashe waya.

Nan na shiga tashin hankali marar misaltuwa, ga zafin kisa da ta saka ni na yi kuma ta gudar min da dukiya, hakan na ja bakina na tsuke saboda ban da abinda Zan yi da hakan muka tattara komai na mu muka da wo nan sokoto da zama".

Tana kaiwa k'arshen labarin ta fashe da wani irin kuka mai k'unar zuciya. Alh Farouk na ta shi tsaye yana nu na ta da yatsa kawai akaga ya zube a some.

       _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣3⃣/5⃣4⃣��

Cikin tashin hankalin da Mus'ab ya manta cewa la6e yake ya yi but ya shigo falon wanda ya kacame da koke-koke sanadiyyar labarin da Haj Zainab ta bada, nan mazan gaba d'aya suka yo kan Alh Farouk da sauri aka watsa mai ruwa amma ko gezau, nan Haj Zainab ta fasa kuka tana mai fad'in ku taimaka akai shi asibiti, Baffa ya sa su Mubarak suka tallafi Abba aka kaishi part d'in shi cikin sauri Mus'ab ya ce' "Baffa bara na kira Dr Shureim ya duba shi", cikin mintunan da basu wuce goma ba sai ga shi ya iso da kayan aikin shi, dak'yar aka samu numfashin Abba ya dawo, nan ya kai duban shi ga Haydar ya ce' "da ma yana da hawan jini ko?", kai kawai ya d'aga mai saboda ko magana bai iya yi, zuciyar shi ji yake yi tamkar zata fashe.

Yanzu da wanne ido za su kalli mutane ace mahaifiyar su ce ta ba da kwangilar kashe rayuwa, wannan abin da me ya yi kama, wani 6angare na zuciyar shi yana jin k'uncin rashin aure tsakanin shi da Musirrah, ashe tsananin son ta da yake ji aranshi so ne na jini wanda har yake tunanin ko mahaifiyar shi tace kar ya aure ta bazai iya ba, wani 6angare kuma yana jin tausayin Ammi yadda ta wahala dasu Mubarak lallai tabbas wani abu sai mahaifiya.

Nan dai Dr Shureim ya yi duk abinda ya da ce har aka samu Abba ya da wo hayyacin shi, sai dai cikin lokaci guda duk ya zabge gwanin ban tausayi, lallai tabbas samun mace ta gari shi ne jigon rayuwa ko a mafalki aka ce mai Haj zata iya wannan abin bazai ta6a yadda ba amma sai gashi yanzu ta furta da bakin ta.

Ana kiran la'asar kowa ya ta shi domin sauke farali, bayan sun gama ne aka kawo abinci hakan suka tsakara ba don ba sujin yunwa ba sai don zuciyoyin su dake cunkushe, nan ko wa ya kammala Ammi ta kai duban ta zuwa ga Mubarak da Musirrah cikin k'arfin hali ta ce' "sai ku ta shi mu wuce gida ko?", har sun mi k'e Baffa ya yi gyran murya ya ce' "Ku zauna".

"Amadadin aboki na Alh Farouk ina mai ba ki hak'urin abubuwan da suka faru wa'anda babu sa hannunshi ko kuma wani babban laifi da ya yi maki, saboda haka ina neman alfarma zuwa ranar larba wato kwana biyar masu zuwa ki had'a kan yaran ki da komai na ki ki koma d'akin mijin ki", cikin razana da jin maganar Baffa ya sa ta d'ago kanta, da sauri ta sadda shi k'asa sanadiyyar idon su da suka had'e guri d'aya ita da Abba.

Cikin sanyin murya da fargaba ta ce' "gaskiya na ya fe zamantakewa dashi, Allah dai ya shige mana gaba", nan dai su Haj Maijidda suka saka baki had'e da ba ta hak'uri sannan ta ce za ta duba.

Baffa ya ce' "kamar yadda aka saka ranar auren Haydar da Musirrah to tana nan ba'a d'age ba za ayita da Mus'ab insha'Allah", wani abu Musirrah ta ji ya tsirga mata tun daga saman kan ta har zuwa yatsan ta, saboda har ta hango Allah ya had'a ta da kurma sun fara soyayya duk da yanzu bata san inda za ta k'ara ganin shi ba, Mus'ab d'in da ko miskilanci ya san da zaman shi, yaushe rabon data saka shi a ido, wai ma yanzu inta ganshi za ta iya ga ne ce wa shi ne?, tabbbb wai kwando ke ce ma rariya na yoyo, har Musirrah za ta hango miskilancin wani, da yake har yanzu hankalin ta bai kai ta ga Mus'ab d'in ba akan tashin hankalin da take ciki, kuma ko ta gan shi ba lallai ne ta ga ne shi ne kurma ba tunda bata san fuskar shiba haka ma maganar shi, don yanzu haka ma ya fita raka Dr Shureim.

Cikin tunanin da take yi ne ta ji an da fa kafad'ar ta nan ta kai duban ta ga Rukayya da hawaye suka wanke fuskar ta sharkaf, dak'yar ta iya furta "ki ya femin Musirrah, ashe ko da na ko re ki lokacin da kike neman taimako ke y'ar uwata ce ta jini", nan kukan ta ya k'aru akan wanda take yi farko sai ga shi kallo ya dawo zuwa gare ta kowanne d'auke da alamar tambaya a fuskar shi, nan dai ta zayyane masu labarin aikatau da Musirrah ta yi a gidan ta.

Cikin ran Haj Maijidda ta ce to su wa'annan mugun ta ko ajinin su take, wannan bala'in dame ya yi kama, nan dai aka k'ara ja janta abin.

Ammi ta Kai duban ta ga Haj Maijidda ta ce' "sai ga shi na ga kin nuna da ma kun sa ba da Ummy, ko da ma y'an uwa kuke?", nan ta yi murmushi ta gaya mata mijin ta ne Alh Sani abokin Baffa, nan ta ga no ce wa shi ne suka je neman auren Musirrah dashi. (Tabbb ashe an kuru su Ammi an yi farin jini, Alh Sani da Baffa duk sun k'yasa, _lolx_)

Bayan an k'are ji ma min abubuwan ne Abba ya ce su ta shi su wuce, nan Umma ta mi k'e ya kai duban shi zuwa gare ta ya ce' "ke ina za ki je?", nan ta ce' "za mu wuce gida ne".

Uhmmmm! "Zama da irin ku ai bala'i ne a doron k'asa saboda haka ki sani inda dare yayi maki na sake ki saki biyu", cikin tashin hankali ko wa ya kai duban shi zuwa ga Abba, ya d'ora da ce wa kuma wallahi ban yadda ki rab'i duk wani d'an uwa na ko aboki na ba, da hakan ya cika rigar shi da iska ya wuce, ko wa sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un yake furtawa.

       _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣5⃣/5⃣6⃣��

Cikin tashin hankali kowa ke salallami a bakin shi, Haj kukan ta ya tsanan ta saboda bata ta6a tunanin ce wa Alh zai iya sakin ta har saki biyu ba, ga shi iyayen ta duk sun rasu dama hannun gwaggon ta ta tashi ganin daula ta yima ta yawa yasa ta yi watsi da lamarin ta, don ma Alh Farouk na iya k'ok'arin shi duk sallah Babba yana had'a kan yaran shi gaba d'aya suje can Birnin kebbi suyi sallah, saboda mahaifiyar shi na raye da k'annen shi mata biyu ya so ya dawo da ita zama sokoto akan izza da tak'amar Haj Zainab ya sa ta ce bata zuwa ko ina.

Gyaran muryar Baffa ya da wo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, ya ce' "gaskiya Haj baki kyauta ma rayuwar kiba duka-duka duniyar nawa ce da har za ki biye mata ki afka kan ki cikin matsalar rayuwa, halan kishi hauka ne?, yanzu miye ribar ki anan? Gaskiya banji dad'in faruwar hakan ba kwata-kwata".

"Amma duk da hakan ba yadda za'a yi saboda an zama d'aya tunda an hayayyafa, yanzu kiyi hak'uri ki je ki had'a kayan ki ki koma gidan Jameel da zama kafin Alh ya sauko zan bashi hak'uri, don ma ya yi na musulunci bai yanke igiyoyin duka ba saboda ko Allah bai son saki uku".

Nan dai kowa ya ta shi ya ka ma gaban shi saboda mai afkuwa ta afku don kuka ba shida magani, hakan Jameel ya saka su a mota suka wuce sai gidan Abba, ko da suka shiga gidan Abba na falo zaune ya jingina kanshi da kujera sai hawaye ke yimai zuba a dattijuwar fuskar shi. Cikin sauri Mukarrama ta isa zuwa gare shi ta kai hannu tana share mai hawaye had'e da bashi hak'urin abinda ya faru, wanda itama da ka dube ta zata baka tausayi sosai saboda har idon ta sun kumbura kan kuka, sa6anin Haydar dake sauke ajiyar zuciya saboda shi kukan ma ya k'i zuwar mai shi da Jameel sai dai wani k'unci dake tattare cikin zuk'a tan su, Rukayya kuwa ta ci kukan har ta gode Allah ta dangana.

Da yatsa Abba ya rik'a nuna Haj ta re da furta mata ce wa wallahi kar ta kuskura ta k'araso cikin falon, nan yaran suka had'u suna masu ba shi hak'uri amma ina ya yi nisa a 6acin rai bai ko jin su.

Hakan Jameel ya ja hannun Umma suka fita ya kai duban shi ga Rukayya ya ce su had'a wa Umma kayan ta su kai gidan shi, da hakan ya fice rai 6ace saboda yana ganin tamkar Abba ya tsaurara hukuncin zuwa ga umma. (Tabbb haba Jameel kai baka hango tarin laifin Umma ba sai na Abba?).

****  ****  ****  ****  **

Bayan su Ammi sun isa gida ne sun huta Mubarak ya kai duban shi ga Ammi ya ce' "yaushe za muje gida Birnin kebbi?", "ai tafiyar tana nan gobe, don ka ga bama sai Baffan su Iman ya raka mu ba kawai mu d'auki shatar mota muje mu kwana biyu sai mu dawo saboda shirye-shiryen auren Musirrah", Mubarak ya ce' "ko shirin tarewar ki ba Ammi", yana maganar da murmushi d'auke a fuskar shi.

Ta ce' "to ubana in ka gama shirya komai sai ka d'auke ni ka kaini in san ce wa ka matsu", nan suka rik'a murmushi shi da Musirrah, ya ce' "in ma ba zaki koma ba mu munyi kewar Baban mu saboda haka za mu had'a y'an komatsan mu mu koma gidan mu, ko ba haka ba Sister?", yana maganar yana kashewa Musirrah ido d'aya alamar tsokana.

"Ai tunda na gama wahala daku yanzu kun zama mutane kuna ce wa yanzu ubanku kuka sani, sai ku had'a kayan ku kuje can d'in ni ko zan yita addu'a inna yi aure Allah yaba ni y'an tagwaye na".

Nan ta ke kowannen su ya gimtse fuska tamkar ba su ne ke tsokana suna dariya ba, duk yadda Ammi ta so gimtse dariyar ta sai da ta fito saboda yadda Mubarak ya gimtse fuska tamkar bai ta6a murmushi ba.

"Tabbbb ai wallahi duk wanda ya ce zai zo gidannan da sunan auren Ammi wallahi sai na sheme shi, don abin ma rainin wayo ne".

Nan dai suka dawo hira cikin nishad'i da walwala wanda Ammi ke jin yau tamkar an d'auke mata wani k'aton dutse ne saman kanta saboda warwarewar komai, abu d'aya take ji a ranta matsuwa da ta yi bata ga mahaifin taba, ko ya za ta risk'e shi yanzu?.

Musirrah ta ce' "ni ko Ammi ina ganin tamkar in muka shiga motar kasuwa domin tafiya Baffa bazai ji dad'i ba, tunda kinga da kan ki kika rok'i alfarmar ya rakamu aga gida, to a tunani na tunda komai ya warware to a kira shi ko direba ne ya bamu sai muje".

"Eh lallai kin kawo shawara, ni zumud'in inga Baba yasa duk na manta hakan, Mubarak kira shi sai muji me zai ce akai".

Bayan Mubarak ya kira shi ne suka ajiye kan gobe da sassafe zai turo direba ya kaisu, da hakan suka kai k'arshen magana suka ta shi domin fara shirye-shiryen tafiya.

****  ****  ****  ****

6angaren Mus'ab kuwa yana shigowa gidan Baffa ke gaya mai ce wa yaje ya fara shiri domin auren Musirrah ya da wo saman kanshi, ji yake yi tamkar ya ta so ya rungume Baffa kan murna da jin dad'in wannan albishir, sai dai kawai ya basar tamkar bai ji mi Baffa ya ce ba, sai da Ummy ta mai-maita maganar sannan ya ce' "yanzu don Allah Ummy kama ta za'a yiwa auren dole?, kuma da wannan mitsitsiyar yarinya", Baffa ya yi mai dak'uwa ya ce' "ungo na ka, ita bata ce ka yi mata girma ba ita da zata auri tuzuru sai kai, kyawon abin ba kai kad'ai na haifa ba in har ka d'auko min al'adun wasu (SIS BATUL MAMMAN) sai in saka ma ido in gani in fita k'asar waje karatu hauka ne in mayar da auren kan Nibras saboda shi ma ya isa aure".

Darammm! Gaban shi ya tsinke yau ko zai ga ta kan shi garin jan aji zaren shi zai tsinke, ya ce'  "yi hak'uri Baffa ba haka nake nufi ba ai ban isa kaba ni mata ba ko da daga k'auye ne ko ince ban sonta, Allah ya shige mana gaba", nan ya ta shi ya wuce part d'in shi.

(Ni dai Jegal na ce anya Mus'ab baka zurma dayawa ba, y'ar k'auye fa kace, koda neman mafita ne kake yi, _lolx_)

        *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣7⃣/5⃣8⃣��



Hakan su Rukayya suka tattara duk wani abin buk'a ta na Umma suka kai mata gidan Jameel, gida ne da ya k'unshi part uku d'aya na Amaryar shi Yusrah, sai na shi, d'ayan da ba kowa ne cikin shi aka bawa Umma duk da ce wa Yusrah bata so hakan ba saboda an yi shine koda sun hayayyafa, hakan Umma ta zauna gidan ba don ta so hakan ba sai don ta riga tasan cewa batada inda zata je akar6e ta da daraja inda ya wuce gidan Jameel d'in.

****  ****  ****  *****

Yau kwanan su Ammi biyu a Birnin kebbi, ta yi murna sosai yadda ta tarar da Baban ta cikin k'oshin lafiya duk da ce wa tsufa ya ka kama shi yanzu, kuma ta ji dad'in yadda ta tarar da ya yi aure da wata Gwaggo Hanne. Hakan dai ta yita za ga y'an uwa da mak'ota har gurin Haj Maryam suka je mahaifiyar Alh Farouk da kuma gidan k'annen shi mata biyu wato Hafsat da Balkisu, sai baban Yasmeen Alh Ibrahim sun yita jima min abinda Haj Zainab ta aikata ta re da kwashe mata albarka saboda abin ya yi muni dayawa, nan dai take ta rok'on Haj Maryam kan ta koma gidan Alh Farouk da zama wanda sun aje kan ce wa sai ta duba ta gani.

Nan dai Baban ta ya yi mata fad'a kan ce wa ta had'a kan yaran ta in sun koma ta tare gidan ta, kuma ta rik'a addu'a sosai domin itace takobin mumini, ta tsare azkar na safe da yamma.

Kwanan su uku Birnin kebbi Baffa ya turo direba ya d'auke su suka koma sokoto cikin kewa da rashin jin dad'in barin mahaifin ta.

*BAYAN KWANA BIYU*

Duk abinda yakamata ayi 6angaren ko mawar Ammi gidan Alh Farouk anyi, sai dai abinda ya d'aure masu kai koda suka binciki maigidan da suke haya don cika mai kud'in shi yace masu bai biyarsu ko dala saboda Haydar ya saye gidan hannun shi. Nan su Ammi suka yita mamakin abin inda har Mubarak ya ce tunda bai ce komai ba akai to su zuba mai ido har suji daga gareshi.

Ranar tarewar Ammi ta ga mutane da dama ciki kuwa har da Mela da Hajiyar ta, sai kuma Haj Maijidda da Ummy da ta rikid'e ta koma k'awar Ammi.

Hakan Ammi ta koma gidan ta ta had'a kan yaran ta da na Umma duka ta rik'e wanda in har ka gansu zaka rantse da Allah ce wa duk ita ta haifesu musamman Mukarrama da suka zamo tamkar tagwaye.

Yau Baffa ya matsawa Mus'ab kan ce wa ya shirya yaje suga juna shi da Musirrah tunda dama basu had'u ba, tun ranar da Baffa ya gaya mai maganar auren yake neman hanyar da zai ga Musirrah sai dai yana jin nauyin hakan, to yanzu da Baffa ya ce ya shirya yaje wani dad'i yake ji a ranshi.

Har ya shirya ya saka manyan kaya kome ya tuna sai kawai ya koma ya canja shiga wanda ni kaina na rik'e ha6a ina mamakin zuwa gidan surukai a haka.

Suna d'aki suna hira sai ga Ammi ta shigo ta ce' "sai ku fito hakanan kuna da bak'o a waje, ko yaushe kuna d'aki tamkar wasu sababbin amare", Ammi kin manta mu ma mun kusa zama amaren", cewar Mukarrama da murmushi d'auke a fuskar ta.

"Ai ko na ga alama shi ne aka fara amarcin tun nan gida, in dai wannan ce ai amarci hali zai tarar don tun fil azal y'ar zaman d'aki ce", Ammi na maganar tana nuna Musirrah sannan ta sa kai ta fice daga d'akin.

Mukarrama ta ce' "sai ki ta shi muje daga nan ma za mu fa ra list na abubuwan da za muyi na auren", hakan dai ta jan yo wani k'aton gyalen ta ta ya fa suka fice.

Cikin mamaki Musirrah ke kallon shi, wannan shigar da ita kurma ke zuwa siyen waina kuma tana tunanin to me zai kawo kurma gidan su? Dama yasan sun ta shi daga wancan gidan ko kuma tambaya ya yi? To in ma hakan ne mi ye had'in shi da ita bayan siyen waina da zai nemi gidan su? Duk wa'annan tambayoyin kanta take yiwa su duk da tasan ba za ta ta6a samun amsar su ba sai ga kurma.

Jin sanyayyiyar muryar shi suna gaisawa da Mukarrama ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka, ohhhh! Dama ba kurma bane? To me hakan ke nufi?

Sai da ta saita nutsuwar ta sannan suka gaisa dashi, jin Mukarrama ta ce' "Yaya Mus'ab mun yi fushi sai yanzu zaka zo?", shi yasa ta k'ara tayarda kanta karaf suka had'a ido ta yi saurin sadda kanta k'asa.

"Kuyi hak'uri k'anwa ta abubuwa ne suka yi yawa shiyasa kuma kinga Antyn ta ki tafiya tayi amma ko tsaraba bata ba muba", "to shikenan ayi hak'uri yaya". Ita dai hakan ta zamo tamkar mutum mutumi saboda tabbas yanzu ta yarda ce wa shi ne Mus'ab, saidai abinda ke d'aure mata kai me yasa ya je mata a zuwan kurma?, nan wata zuciyar ta ce mata shi da kan shi yaga ya maki kurma ne?, ehhh to me yasa yake rubuta magana madadin yafurta ta?, kika sani ko baida ra'ayin maganar ne, hakan dai ta yita tafka muhawara da zuciyar ta har ta gaji, wai ashe har sun k'are tattaunawar su shi da Mukarrama akan bikin da za'a yi.

Tsinka yo muryar shi kawai ta yi suna sallama da Mukarrama, sannan ya kai duban shi zuwa gare ta ya ce' "sai mun yi waya amarya", da hakan ya ja mashin d'in shi su ko suka wuce gida wanda duk hankalin Mukarrama bai ba ta yanayin da Musirrah take ciki ba, kawai tana tunanin nauyin angon take ji shiyasa ba ta magana.

(Plxxxxx ina neman addu'ar ku zuwa ga Anty na Maijidda Musa)

      *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[7:28AM, 10/17/2016] *SDY* *JEGAL*: �� _SANADIN_ _K'UNCI_5⃣9⃣/6⃣0⃣��

*BAYAN SATI D'AYA*

Zama ya fara tsanani tsakanin Yusrah da Umma, saboda kwata-kwata ba ta girmama  Umma kuma ga ta da wata al'ada ta ba'a karyawa a gidan su sai 11:00am ita ko Umma ga ta da ulcer, wanda Jameel ya lura ce wa can farko ulcer d'in Umma bata cika ta shi ba, amma yanzu mawuyacin abune Umma tayi kwana biyu lafiya lau wanda ta kai yanzu shi ke tasa Yusrah da kan shi har kitchen yace sai ta yiwa Umma girki, cikin an matsa mata ne za ta daure ta dafa mata indomie.

Yau ma kamar kullum ko da ya shiga bedroom d'in Yusrah k'arfe goma amma tana kwance sai bacci take yi, cikin 6acin rai ya tada ita ya ce' "yanzu don Allah ki duba lokaci kigani ace har yanzu baki ta shi kika girkawa Umma abinda za ta ciba", nan ta kai duban ta ga agogo ta ce 11:00 fa bata yi ba, kuma bayan ka siya mata kayan tea da komai na buk'ata za'a zo a tayar dani ina bacci na", tana maganar tana zum6ure baki.

Nan ya fita fuu ya koma part d'in Umma ya zauna rai 6ace ya ce' "Umma ki bincika cikin mutanen ki in za'a samu y'ar aiki sai a samo ta rik'a kula da abincin ki", nan ta yi wani murmushi mai had'e da nadama tattare a fuskar ta, ka basshi kawai ba sai an samo ba ko hakan nagode sosai ta shi ka wuce gurin aikin ka".

Hakan dai ya fice ko karyawa bai yiba, don dama yawanci a office yake breakfast. Fitar shi ke da wuya Umma ta zuba tagumi sai hawaye ke yi mata zuba a ranta take furta lallai tabbas duk abinda ka shuka shi ne zaka girba, saboda ita gaba d'aya hana amayar da ta ta suruka ta yi saboda ganin za'a takura ta, amma ita ga ta ga ta ta suruka sai horon yunwa take mata, kuma ba tada mafita don babu abinda za ta iya saboda ta san da ace Yasmeen ce Jameel ke aure ba za ta fuskanci wannan wulak'ancin ba.

**** **** **** ****

6angaren su Musirrah kuwa maganar aure ta kanka ma saboda gobe ne saka lalle, duk wani abu na al'adar bahaushe akan aure duk an kawo abinda ya shafi kayan lefe da kayan sa lalle.

Har yanzu Musirrah ta rasa wace hanya ce za ta bi domin tambayar Mus'ab me yasa ya rik'a zuwar mata a zuwan shi kamar kurma ne, ga shi dai sun d'an shak'u da juna sama-sama duk da ta ka sa sakin jikin ta dashi saboda su na waya kusan kullum zai kira ta, sai dai wayar daga gaisuwa bazai iya k'a rawa da wata magana ba sai dai yayi shiru itama hakan, miskilai biyu sun had'u guri d'aya.

Duk inda ka za ga cikin gidan cike yake da mutane, 6angaren y'an uwan Abba da Umma, sai kuma mukarrama da Mela da suka ta re a gidan tun jiya, haka suka had'e su hud'u tamkar y'an hud'u sai dai Mela da suka fiya girman jiki. Haj Maryam ma ta zo ta re da yaran ta k'annen Abba har da su Yasmeen da sauran dangi, Ammi sai murna take yi yadda gidan ya cika da jama'a tun kafin zuwan bikin, wanda take fatar rik'e Haj Maryam nan sokoto inshaAllah.

A d'an zaman da Mela ta yi gidan ne na fahimci y'ar guntuwar soyayya tsakanin ta da Haydar, saboda duk abinda za'a yi za kaji ya ce Mela zo kiyi abu kaza in ma abincin shi za'a kai mai to zai kira Musirrah yace aba wa Mela abincin shi ta ka wo mai.

Had'uwar shi da Mela ne ma yake ganin ce wa tabbas tsakanin shi da Musirrah wancan lokacin so ne na jini matsayin ta na k'anwar shi, don yanzu yasan ma mi ye son kan shi, (To su Haydar ayi a hankali kar a zurma dayawa)

Haj Maijidda Musa ta kira Ammi tana k'ara jadda da mata kan ce wa kar fa ta manta gobe gidan ta za'a saka wa amarya lallen har yinin gaba d'aya, Ammi ta ce' "na isa in manta maganar saka lalle gidan ki ke da y'ar ki, abinda ma za'a yi zan had'a ta ita da k'awayen ta zuwa bayan magrib sai direba ya kawosu nan su kwana".

"Gaskiya ko da na ji dad'i da hakan, ina jira sai sun iso d'in", da hakan suka yi sai anjima suka kashe wayoyin su.

Ammi ta kira Mukarrama ta ce' "ku had'a kayan ku na buk'ata ku da k'awayen ku saboda bayan magrib direba zai kai ku gidan Haj Maijidda", nan Mukarrama ta amsa ta fita.

Tana gayawa Musirrah ta fara zum6ure-zum6uren baki "ni fa kunga irin abubuwan da ke 6atamin rai ace da an tashi auren mutum shikenan ya fara yawo tamkar matar titi aje gidan d'an uwa yau gobe gidan amini, ta d'ora da ce wa randa nake da Ammi ta ban ta6a kwana wani gurin ba".

"Tabbb aiko aiki ya sa me ki, don yanzu kin kai k'arshen kwana ta re da Ammin ki, saboda mai gaba d'aya zai hau kan ki ke da zama da Ammi sai in kin zo wankan jego", nan dai suka had'u suka fara zolayar ta har jikin ta ya yi sanyi tamkar za tayi kuka.

Da hakan suka had'a kayan su sai da suka yi sallar isha sannan direba ya wuce dasu gidan Haj Maijidda.

(Gobe ko wa ya tashi tunda safe muje sa lalle, wanda ya makara mu wuce ba dashi ba, *lolx*)

      *SDY* *JEGAL*��

Dedicated to Sanah S. Matazu.

No comments:

Post a Comment