[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣6⃣
_WASHE_ _GARI_
Bayan tayi aikace-aikacen ta na gida ne ta k'are sai tayi wanka ta fito.
Nan ta taradda Ammi kwance tana sauraren radio ta durk'usa ta gaida ta.
Ammi ta ce'
"Har kin k'arasa aikin kin fito?".
Ta ce'
"Eh Ammi saboda mun yi da matar kan cewa in shigo kafin k'arfe tara.
Ammi ta ce'
"Gashi ko karyawa bakiyi ba, Mubarak ya fita ya siyo koko ko zaki jira shine?".
Ta ce'
"A'ah Ammi Zan wuce ne kar in Fara da rashin zuwa cikin lokaci asamu matsala".
Ta ce'
"Shikenan sai kin dawo Allah yasa afara a sa'a".
Ta kar6a da Ameen".
Koda taje gidan matar gidan ko tashi bata yiba.
Da maigidan ta fara cin Karo ya fito zai fita office, nan ta durk'usa ta gaida shi ya amsa ya fice.
Falon ta k'arasa da sallamar ta taji shiru.
Wata zuciya ta ce Mata ki fita daga waje ki jira har ta fito.
Wata ta ce Mata in kika yi hakan ta fito tace kinyi ba dai-dai ba fa.
Tana wannan tunanin ne ta sake k'wala sallama da k'arfi.
Sai ga Rukayya ta fito tana yatsinar fuska ta bita da wani kallon raini.
Ta ce'
"Kin ci arzik'in jiya ban gaya maki wannan cikin dokoki na ba, da wallahi na lahira sai ya fiki jin dad'i".
"Daga yau sai yau kar ki kuskura kizo Ina bacci ki tada ni, don wallahi ko maigidan bai isaba baranta na ke y'ar aiki".
Jiki na rawa Musirrah ta ce'
"Anty kiyi hak'uri inshaAllah bazan k'ara ba".
Nan ta bita da kallon raini.
Ta ce'
"Biyo ni muje in nuna maki aikin ki".
Bayan sunje kicin ne ta nuna Mata komai sannan ta juya takai duban ta zuwa gare ta.
Ta ce'
"Kin yi karatun boko?".
Musirrah ta ce'
"Eh Anty na k'are secondary".
Ta nuna Mata bakin k'ofa.
Ta ce'
"Gobe in kika zo zaki ga time table anan, zaki duba duka aikin ki na kullum".
"Saboda in kika zo ki hau aikin ki kar ki kuskura ki k'ara tada ni".
"Kuma in kin zo tun safe sai marece".
Nan ta bata umurnin abin da zata dafa ta juya ta koma bedroom d'in ta.
<<< >>> <<< >>>
Tun shigar shi makaran tar yake zaune k'ofar department d'in su Mubarak.
Yafi awa d'aya zaune, tun yana latsar wayar shi har abin ya ishe shi.
Ji yake yi tamkar ya tashi ya koma gida don yau ko lecture basu da, cika umurnin Baffa kawai ya kawo shi makaran tar.
Yana cikin wannan tunanin ne Salim ya dafa kafad'ar shi.
Ya ce'
"Haba aboki wannan zurfin tunanin fa?".
"Tun d'azu nake saman kanka Ina magana shiru, ko an yi kamun wata ne department d'in nan?".
Nibras ya Kai duban shi zuwa gare shi.
Ya ce'
"Hala cema akayi kowa mayen Mata ne irin ka?".
Ya ce'
"Ai ko Mata abin so ne".
Nan ya bashi hanu suka tafa suna masu zolayar juna.
Nibras ya dube shi ya ce'
"Wallahi Mubarak nake ta jira tun d'azu, gashi har na Fara gajiya da zaman bai zo ba".
Rufe bakin shi ke da wuya sai ga Mubarak ya kunno Kai.
Suna had'a ido ya juya da k'arfi zai koma, da sauri Nibras ya sha gaban shi.
Ya ce'
"Babu yak'i me zai kawo gaba?".
"Babu irin Neman da ban yi maba ban ganka ba, jiya Baffa ya ce ya ganka shiyasa ya takurani in zo in ji miye silar barin Ku gidan mu?".
Nan Salim ya ce'
"Ni Zan wuce sai mun yi waya".
Mubarak ya nisa ya ja hannun Nibras suka samu guri suka zauna.
Ya ce'
"Nibras yawan cin zuwan da kake yi nema na Ina ganin ka, sai dai in la6e sai ka wuce in fito".
"Hak'ik'anin gaskiya bana so mu had'u, saboda nasan tatsuniyar gizo ba zata wuce ta k'ok'i ba".
Nan dai ya zayyane Mai irin korar Karen da Ummy ta yi masu.
Ya d'ora da cewa'
"Kaga ko kauce wa had'uwa da ku shine mafi alkhairi a gare mu".
"Mun gode sosai da irin karamcin da kuka yi muna, da kuma soyayyar da kuka nuna muna, Allah ya saka da khairan".
Nibras ya ce'
"Ba wannan nake son ji daga gare ka ba, yanzu miye mafita? Me Zan cema Baffa in har ya tambaye ni na gan ka?".
Ya yi murmushi ya ce'
"Kawai kace baka gan niba".
Nibras ya ce'
"In yi k'arya kenan saboda wanke ka?".
Ya ce'
"Hakan shine dai-dai akan ka furta gaskiya laifin Ummy ya bayyana".
Ya ce'
"To yanzu ka bani address d'in inda kuka koma Zan rik'a kawo maku ziyara".
Mubarak ya ce'
"Wannan kuma ka yi hak'uri Zan nemi izni daga Ammi in har ta amince Zan gayama".
Daga hakan suka rabu Mubarak ya shiga class, Nibras ya wuce.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣7⃣
Nibras na ko mawa gida ya taradda Baffa zaune falo, ga Iman zaune k'asa suna hira, ga alama shi suke jira.
Ya k'araso da sallamar shi ya gaida Baffa da gida sannan ya samu guri ya zauna.
Baffa yakai duban shi zuwa ga Nibras ya ce'
"Ya ake ciki? Ina fatar ka cika aikin da na saka ka, kuma anyi nasara?".
Nibras ya nisa ya ce'
"Baffa gaskiya babu nasara".
Kallon da Baffa ya bishi da shine na alamar ka rai na ni yasa ya yi shiru.
Ya ce'
"Bangane babu nasara ba? Kamar ya ya?".
"Yaran nan Ina jin tausayin su har cikin raina, babban abin damuwa rashin sanin takame-men abinda ya raba su da gidannan".
"Baffa ya cigaba da cewa kaga gobe ne tafiya ta Egypt, kuma abinda zai Kai ni yana da muhimmanci sosai".
"Amma gaskiya badon hakan ba gobe Zan shiga da kaina, amma dana dawo Zan shiga in yi bincike akai".
Kan 6acin rai bai ma tsaya jin abinda Nibras zai gaya Mai ba ya wuce d'akin shi.
Wucewar shi tayi dai-dai da sauke ajiyar zuciya da Nibras ya yi uhmmm!
Iman ta Kai duban ta zuwa gare shi ta ce'
"D'an Uwa meke faruwa halan?".
Ya ce'
"Kamar yadda Ummy ta gaya muna cewa ita ta Kore su to shima hakan ya gaya min".
Nan dai ya kwashe duk yada suka yi da Mubarak ya gaya Mata.
Ta ce'
"Wai ko bai yuyuwa mu gaya ma Baffa gaskiyar abinda ke faruwa?".
Ya ce'
"Yin hakan tamkar haddasa fitina ce tsakanin shi da Ummy".
"Saboda muddin ya gano gaskiya akwai matsala".
Ya cigaba da cewa "Kawai mubar maganar tsakanin mu, nasan koda zai dawo daga Egypt sun k'are exam ya bar school d'in".
"Kinga hakan in ya bincika bai ganshi ba zai hak'ura yabar maganar".
Da hakan suka rufe wannan chapter suka d'auko wata.
<<< >>> <<< >>>
Tana kitchen tana aiki ne tana y'an wak'ok'in ta, yazo ya tsaya bayan ta yafi minti uku batasan yana gurin ba.
Sai da yayi gyran murya sannan ta juyo da k'arfi, ganin mutum bayan ta yasa ta durk'usa cikin sauri ta gaida shi.
Ya amsa da murmushi a fuskar shi ya ce'
"Ki dafa min ruwan tea, ki soya min k'wai kamin in fito daga wanka".
Nan ta amsa sannan ta juya ta cigaba da aikin ta.
Har zai wuce ya tsaya ya lek'a bedroom d'in ta ya taradda ita tana ta bacci ya girgiza kan shi ya wuce bedroom d'in shi.
Nan ya had'a ruwan wanka bayan ya fito ya kimtsa, sai ya nufi dinning table ya tarar ta kammala komai nan yaci ya k'are.
Sai da ya shiga kitchen ya yi mata godiya sannan ya wuce.
Ta dad'e tsaye tana mamakin maigida da kan shi zai zo yana yi Mata godiya akan ta yimai girki.
To wai ma wannan matar wace irin Mata ce, ace kina can kina bacci har maigidan ki ya fita baki San ya fita ba".
Wata zuciya ta gargad'e ta da cewa miye naki a ciki? Ke dai kiyi aikin da ke gaban ki".
Hakan tayi duka ayukkan ta ta k'are har lokacin Rukayya na can na bacci.
Sai wuraren 11:00 sannan ta tashi daga bacci ta duba ko Ina bata ga Musirrah ba.
Sai da ta shiga garden sannan ta gan ta ta zuba tagumi.
Nan ta umurce ta data shiga bedroom d'inta da na Baban Ilham ta gyara.
Sai da ta k'arasa aikin gyaran d'aki ne sannan ta ce ta kwashe duka abincin da ke saman dinning taje ta ci sai ta d'ora abincin rana.
Nan ta ci abincin wanda yayi saura ta samu leda ta juye ta ajiye sannan ta d'ora girkin dare.
Sai marece ta k'arasa aikin duka, bayan ta yi sallama da matar gidan ne ta kama hanya zuwa gida.
Tana fita ta had'u da maigidan ya dawo daga office.
Ya ce'
"Har kin k'are ayukkan zaki wuce kenan?".
Ta ce'
"Eh Zan wuce sai gobe".
Nan ya matsa kan cewa ta shigo ya sauke ta gida amma ta k'i shiga.
Nan tasa Kai ta wuce cike da mamakin shi a ran ta.
Shi ko ya shige gidan yana Mai tausaya ma yarinyar.
_SDY_ _JEGAL_
Blog
Sadiyajegal.mywapblog.com
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣8⃣
Tana shiga gidan ta tarar da Ammi ta zuba tagumi, da sallamar ta ta k'arasa gurin ta.
Bayan ta amsa ne Musirrah tasa hannu ta janye Mata tagumin da ta yi, sannan ta shiga kitchen ta d'auko guri ta Kai duban ta ga Ammi.
Ta ce'
"Ina Yaya Mubarak hala?".
Ta bata amsa da cewa'
"Ya fita nemo abinda zamu ci, amma nasan yanzu zaki ganshi".
Nan ta shiga d'aki ta d'auko y'ar Nokia Mai torchlight da Mubarak ya siya musu koda lalurar kiran shi ta same su.
Flash kawai ta yi Mai ta ajiye wayar gefe.
Ammi ta ce'
"Ledodin miye kika shigo dasu haka?".
Ta yi murmushi ta ce'
"Ammi sai Yaya ya shigo sannan Zaki ganin miye".
Ammi ta yi murmushi ta ce'
"Allah bada sa'a".
Rufe bakin Ammi ya yi dai-dai da sallamar Mubarak, da sauri Musirrah ta je ta tar Yoshi.
Ta ce'
"Yaya sannu da zuwa".
Ya ce'
"Yauwa k'anwata kin dawo daga aikin?".
Ta ce'
"Eh Yaya, ta d'ora da cewa ga abinci ma nazo mana dashi".
Ya ce'
"Yanzu haka koda kika Kira ni Ina waje tunani na da wane ido Zan shigo gidannan".
"Na yi yawo koda wani aiki ne in samu ban samu ba".
"Ke daga k'arshe kasuwa na shiga na yi dako aka bani d'ari biyu kin gan ta nan, ya nuna Mata".
Ya ce'
"Cikin sauri na nufo gida sai da na kawo Zan shigo nayi turus".
"Sanadiyyar tunawa da nayi cewa ba komai a gidannan na girki, to me d'ari biyu zata ce mana".
Ammi kallon shi kawai take yi tana hawaye, wannan wace irin rayuwa ce, Allah ga mu gare ka.
Jin hannu ta yi ana share Mata hawaye, Musirrah ta ce'
"Ammi kiyi hak'uri inshaAllah matsalar abinci ta k'are mana".
Nan ta fitar da ledodin da ta zo dasu, ta bud'e da d'add'aya.
Ammi ta Saki baki tana kallon ta.
Ta ce'
"Musirrah ban maki wannan horon ba, me zai Kai ki ebo abincin mutane?".
Ta ce'
"Ammi wallahi duk wannan daki ke gani ba abinda na d'auko ba'a bani ba".
"Matar ita kad'aice sai yarinyar ta d'aya ga alama iya kacin ta wata shida, sai kuma Mai renon ta".
"Amma gaskiya abincin da take bada umurnin a dafa ya fi k'arfin gidan".
"Na rana ana ci aka rage ta ce in wuce da kayan, ganin abincin nada yawa na je tambayar ta ya za'ayi dashi".
"Abin mamaki Ammi cewa tayi in inaso in d'auka in bana so in zubar in wanke Mata kwanukan ta".
Ganin cewa ma ya yiman yawa na d'iba na kaiwa Baba maigadi yana ta godiya".
"Na dare kuwa ita ta sakamin shi da kanta, ga alama bata da rowa, amma fa akwai hantara da izza".
Ammi ta sauke ajiyar zuciya Uhmmm!
Ta ce'
"Wannan ba rashin rowa bane almubazzaran cine, wasu na nema wasu na zubarwa".
Amma duk da hakan ki mata magana kan arage saka abincin da yawa, ko kuma ki rage gurin sakawa".
Musirrah ta gwalo ido.
Ta ce'
"Hakan ko zaisa ta kore ni aiki daga gidan".
"Yanzu haka timetable na nan na tsarin abinda za'a dafa a kullum, da kuma adadin abinda za'a saka".
Ammi ta ce'
"To Allah ya ganar da ita ta rage yiwa wannan bawan Allah 6arnar abinci".
Mubarak ya kar6a da Ameen, ya d'ora da cewa.
"Wallahi Ammi baki ganin tashin hankali sai kin shiga kasuwa, haka zaki ga magidanci da kukan shi yana yawon Neman abinda zai kaiwa iyalanshi".
Ammi ta ce'
"Mubarak Allah ya shigemuna gaba, ya kawomuna k'arshen wa'annan abubuwan".
Nan suka amsa da Ameen Ammi.
Musirrah ta bawa Ammi tuwon semo da miyar agushi, su kuma suka ci na rana d'in.
Bayan sun k'arasa sun yi hamdala Musirrah ta ce'
"Ammi ni da akwai ma Wanda zai rik'a kawo maku abincin dana rik'a aiko na ranar".
Ammi ta ce'
"Ki dai bar shi har ki tashi fitowa, yin hakan zai sa taga tamkar dama jira kike".
"Ko kuma abin ya zama laifi".
Ta ce'
"To Ammi haka zaku yita zama har sai na dawo da marece?".
Ta ce'
"Ba komai in mun samu muci, in bamu samu ba zamu jira har ki dawo".
Mubarak ya ce'
"Eh gaskiyar ki Ammi, ke Musirrah a bar shi kan hakan".
Har ga Allah ba haka taso ba, ace sai dare zasu karya akwai matsala.
Nikam gaskiya Zan duba in har akwai mafita to zanyi, saboda sai ta bani abincin ne Zan aiko gida.
Ringing d'in Nokia d'in ta ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula.
Mela ta gani rubuce a screen d'in Wayar, a fili ta furta'
"Banda mutun ci".
Jin hakan yasa Mubarak ya ce'
"Mela ko?".
Ya d'ora da cewa kan ku ake ji".
Nan ta yi murmushi ta d'aga wayar ta fad'a d'aki.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣9⃣
*BAYAN* *WATA* *UKU*
Rayuwa tana tafiya ne daki-daki kuma mataki-mataki, wani d'an Adam zaka ganshi cikin walwala da farin ciki tamkar baisan wani abu damuwa ba a cikin rayuwar shi. Sa6anin wani kullum yake ganin tamkar yafi kowa damuwa da shiga k'unci sanadiyyar wata jarabta da Allah ya d'ora mai.A cikin hakan ne ake gane mai k'arfin imani da kuma mai raunin imani, anaso kodayaushe bawa yaga jarabobi na bibiyar shi to ya k'ara k'arfafa imanin shi da cewa wani bawa bai isa ya d'ora mai lalura ba face ubangijin da ya jarabceshi. Kuma komai tsanani sauk'i zai biyo baya ko anan duniya ko a lahira.Haka rayuwa take gun Ammi ita da yaran ta abin ko yaushe sai dai hamdala. A cikin hakan ne Allah ya k'addari Mubarak da kammala karatun shi, wanda Allah bai k'addari had'uwar shi da Baffan su Nibras ba, duk da cewa ya yi iya binciken shi Allah bai kaddarto had'uwa tsakanin su ba.Yau ma kamar kullum Musirrah ta shirya domin zuwa gurin aikatau d'in ta, sai dai tun jiya suke fama da jikin Ammi wanda abin ke son gagarar su.
Bayan ta yiwa Ammi ya jiki ta samu guri ta zauna, Ammi ta ce,
"ki tashi kije gurin aikin ki saboda nasamu sauk'i sosai".
"Gaskiya Ammi bazan iya fita in bar ki hakan ba"
Dak'yar suda Mubarak suka shawo kanta ta wuce ba wai don taso hakan ba, ko shi don Mubarak ya gayamata cewa bazai fita ba har sai taje ta dawo.
Koda ta iso gidan saida ta tsaya suka gaisa da Baba maigadi sannan ta wuce cikin gidan, nan ta had'u da maigidan zaune falo yana karanta jarida saboda yau weekend ne. Har k'asa ta durk'usa ta gaida shi, bayan ya amsa direct ta wuce kitchen saboda aikace-aikacen ta.
Yau gaba d'aya jinta take yi bata da sukuni, tamkar ta cire ciwon Ammi take ji ta maidawa jikin ta.
Tana cikin tunanin ne ya shigo kitchen domin bata umurnin abinda zata dafamai. Tun shigowar ta ya lura bata cikin walwala kamar yadda yake ganin ta a kullum.
Sai da taga mutum ta gaban ta ta zabura da k'arfi ta ja baya cikin sauri.
Ya ce' "wannan dogon nazarin fa?". Tun d'azu nake magana shiru".
Hakan ta d'an Saki fuskar ta ta bashi amsa ba komai. Nan ya bata umurnin abinda zata dafamai ya fice daga cikin d'in.
Bayan ta k'are breakfast, ta d'ora abincin rana zuwa azzahar ta k'are ta jera komai a dinning table. Sai da suka k'are cin abincin ne tazo ta kwashe komai ta gyara gurin, sannan ta durk'usa har k'asa ta ce'
"Anty ina neman alfarma zanje gida in diba jikin mahaifiyata in dawo zuwa la'asar".
Mugun kallon da ta bita da shine yasa ta yi shiru.
"Sauran aikace-aikacen wa zaki barwa shi?".
"Don Allah kiyi hak'uri Anty, wallahi na baro tane bata jin dad'in jikin ta shiyasa".
"Ke tashi kije ki kula da mahaifiyar ki Allah ya bata lafiya".
Da sauri Rukayya ta Kai duban ta zuwa gare shi ta ce' "Haba Daddyn ILHAM me hakan ke nufi?, bata fa k'arasa ayukkan taba".
Kema Ina ga matar gida kike, kuma aikin ki ne, bai kamata ki tauye yarinyar mutane ba, kuma shi ciwo ya kauda komai".
Nan ya bawa Musirrah umurnin ta tashi taje sai gobe ta dawo. Har takai k'ofa zata fice ya Kira ta ya fitar da kud'i ya ce' "gashi ki kula da mahaifiyar ki".
Nan ta kar6a ta yimai godiya ta fita, saida ta zube sauran abincin ta bawa Baba maigadi ta d'auki Nata. Nan take gaya Mai zata je gida Ammin ta ba lafiya, ya ja janta mata tasa Kai ta fice.
Acan falo kuwa rigima ta kaure tsakanin maigidan da Rukayya har tana ik'irarin ya wulak'anta ta gaban y'ar aiki. Tun yana luradda ita har ya gaji ya k'yale ta, nan tayi k'wafa ta d'auki ILHAM ta wuce bedroom d'in ta.
Tana isa gida ta tarar da jikin Ammi ya motsu Mubarak ya rasa ya zai yi da ita gashi ba kud'i hannun shi. Cikin hakan ne Musirrah tayi sallama ta fad'o gidan, da saurin ta ta k'arasa inda suke taga Ammi duk ta fita hayyacin ta.
Ga Mubarak sai Kai kawo yake yi, takai duban ta zuwa gare shi ta ce' "Yaya yi sauri ka samo napep mukai Ammi asibiti".
Musirrah dame zamu Kai Ammi asibiti? Har rance na fita ban samo ba". Nan ta fitar da kud'i ta bashi, da ido ya bita da kallo Ina kika samu kud'i haka?". Saboda nasan lokacin biyan ki aikatau bai yiba".
Muyi ta lafiyar Ammi Zan yima bayani daga baya". Da saurin shi yaje ya samo napep suka kwashe ta sai specialist hospital.
(Ammi Allah ya tada kafad'a ki rayu da y'ay'an ki, _lolx_)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN K'UNCI 2⃣0⃣
Direct suna shiga asibitin aka kar6i Ammi, bayan gwaje-gwaje sakamako ya fito cewa tana fama da hawan jini ne sanadiyyar yawan tunani da take yi, hakan yasa aka bata gado ana kulawa da ita. Bayan ta d'an samu bacci ne Mubarak ya kai duban shi ga Musirrah ya ce' "na tambaye ki tun gida ina kika samu kud'i har dubu goma kin ce in bari afara ta lafiyar Ammi, gashi yanzu ta samu bacci ina sauraren ki".
Nan ta sauke wata ajiyar zuciya uhmmm!, "yaya kasan dai ba inda zan je in samo kud'i da ya wuce gidan aikina". Nan dai ta zayyane mai komai har zuwa dawowar ta gida.
Amma gaskiya wannan mutumen ya taimake mu, ba don hakan ba bansan ina zamu samu kud'in kawo Ammi asibiti ba, Allah yasaka mai da mafificin alkhairi".
Bayan ta amsa ne ta d'ora da ce wa' "wallahi yaya matsalar rashin sanin ina takamemen dangin mu suke na damuna, nasan ko Ammi ita ce babbar matsalar ta, gashi har ciwo ya kwantar da ita".
"Wannan matsalar ni kai na tana damu na sosai wallahi sai dai na rasa ya zan shawo kan Ammi da maganar, kwata-kwata bata ma son ayi mata maganar". Akwai rai akwai mutuwa kuma ga yanayin aure, yanzu ko aure zaki yi wa zai zamo wakili agare ki, abin nima na damuna sosai gaskiya".
"Yaya mu bari in har ta samu sauk'i mu tun kareta da maganar ko zamu dace ta saurare mu". Da hakan suka kai k'arshen maganar tasu.
<<< >>> <<< >>>
Sallamar da taji ana rafkawa ne yasa ta fito da masifa taff a idon ta. Had'a idon su yasa ta shek'o da sauri ta rungume ta, nan k'anwar ta Mukarrama ta gaida ta.
Bayan sun gaisa da juna ne ta ce' "kwana dayawa Khairat kin 6uya".
Wallahi abubuwa ne suka yi yawa kwanan nan muka dawo daga Egypt nida Mum". Ke gashi kin yi aure har da rabon ILHAM".
To ba ke kin tsaya ruwan ido ba kin k'i tsayar da gwani musha shagali". Suna cikin hirar ne take tambayar ta ina Sultan bata ganshi ba". Nan ta bata amsa yana office sai marece.
Takai duban ta ga Mukarrama ta ce' "ki shiga kitchen ki dafa mana abinci mai sauk'i". Ita ko a gurguje ta fad'a wanka koda ta fito Mukarrama ta had'a masu indomie da kifin gwangwani. Hakan suka zauna suka ci.
Khairat ta kai duban ta zuwa gare ta ta ce'
"Hala ina y'ar aikin ki?". Hmmm! Kedai bari ai nagamu da jaraba". Nan ta kwashe maganar Musirrah ta gaya mata.
"To ke wane mataki kika d'auka akan hakan? Ni wallahi ko aure nayi y'ar aiki bata isa ko hanyar da miji na ke bi tabi nan ba, kina zaune kina kallo za'a yi maki sakiya. Tunda aka fara da hakan wataran zaki ji an Shafa fatiha wallahi sai dai ki ganta gidan ki".
Nan ta sauke ajiyar zuciya Uhmm! Na rasa wane mataki zan d'auka wallahi. To ki tsaya kallon ruwa kwad'o yai maki k'afa, kawai ki sallame ta ki samo wata".
Yauwa yar'uwa hakan za'ayi yau ma kwanan ta biyu bata zo ba". Sai a lokacin Mukarrama ta saka bakin ta ta ce'
"Gaskiya in kuka yi hakan babu adalci a lamarin Ku".
"Bai dace ku tsinke mata gurin cin abinci ba, kuma shi ciwo ya kauda komai, mahaifiyar ta ce fa ba lafiya ke ya kamata ace kin tallafa mata tun da kina da sararin hakan".
Fad'an da suka rik'a yi mata ne yasa taja bakin ta ta tsuke domin su dukan su basu son gaskiya. Amma ta k'udurta ma rayuwar ta koda ta Kore ta in ta gano in da suke zata tallafa mata.
( *BARKA* *DA* *JUMA'A* *MY* *FAN'S*)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
No comments:
Post a Comment