Thursday 6 October 2016

FATIMA 12-16

[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 1⃣2⃣
By sdy jegal
""Fitowar Hjy kenan daga d'aki Wanda yayi daidai da shigowar Hakeem, nan yke gaida Hjy fuskasshi ba yabo ba fallasa, Hjy tace Hakeem ya kukayi da Alhjn ina fatr ka damk'amashi file d'inshi, Hakeem yace Hjy nabashi har yayimn wata kyauta Mai d'imbin nauyi, wace kyauta ce haka Hakeem cewar Hjy"""
Nan ya numfasa gami da bata labarin yadda suka kwashe da Alhj, sai Hjy tace to Hakeem Allah ytayaka rik'o kuma yabada sa'a, kuma Ina fatar xaka samu lokaci kaje kaga d'iyasshi da yace kaje kagani,,,,,,
Haba Hjy nifa gaskia kinsan maganar mace bata gabana kuma baxan koma gurinshiba, nan take Hjy ta had'e fuska tace Hakeem har yaushe nake cema ka cire abnda Hafsat tayima daga cikin ranka, wato ban isa ingyama magna kad'auka ba, nan ta mik'e tare da k'ra had'e fuska xata wuce.
""Hakeem ya durk'usa yana Mai bata hakuri yana cewa Hjy ba maganarki ce bana jiba, inada dalilin yin hakan amma kiyi hakuri innasamu lokaci xanje, to Allah ysa saboda nasanka sarai""""" nan yayi murmushi yace to Hjy kisaki ranki mana alamar kinsauko mana, sai Hjy tayi murmushi tace to na Saki, nidai fatana guda hr kullum addu'a xuwa gareku kaida k'anwarka, to mungode Hjy ni xanfita saboda inaso inje wurin Faisal ta amsa da adawo lpy.
Fitowar Hakeem daga gida bai xarce ko inaba sai wurin abokinshi Faisal, Wanda suka taso tun abotar yarinta, saboda duk Wanda ysan Hakeem ysanshi da Faisal tun primary school, yana k'arasowa gidan daidai Faisal na fitowa nan yabashi hannu suka tafa suna masu xolayar juna, nan Faisal ke tambayarshi Ina mutuniyarshi Xarah, Hakeem yace Bari kaidai ai Matsala ta gitta, Faisal yace wace matsala kuma? Hakeem ya kwashe yadda sukayi da Alhj, nan Faisal yayita dariya yana buga k'afa Hakeem ya Saki baki yana kallonshi ya k'ulu iya k'uluwa yakaimai naushi ga kafad'a yakkauce, Saida yagama yace friend aimu kakammu ta yanke sak'a.
By Sdy jegal
Dedicated to Mmn Shakur
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 1⃣3⃣
By Sdy jegal
Hajiya na dad'e Ina naxarin had'a yaranga auren xumunta, suwa kenan cewar Hajiya""", Munaxxafa da musaddiq, nima na dad'e Ina yimasu sha'awar hakan amma kuma kasan halin yaran xamani, abinda ake hangomusu daban Wanda suke hangoma Kansu daban,
Musamman shi musaddiq kaga namijine kuma gashi maraya sannan amana a hannun, bancika son atakurashiba koda baison munaxxafa nasan baxai iya furtamuna cewa bai sonta ba, hakane gaskiya Cewar Alhj""" amma kinsan yanada kunyarda nasan muddin bani na tuntub'eshi da maganar aure ba baxai tab'a yin maganar ba"""""
Hmmmm wannan kunyar tayi ywa ta musaddiq, amma kabanni dashi xantunkareshi da maganar insha Allah.
""""""Musaddiq d'ane gun Mal Musa da Inna Hindu, shiko Mal Musa K'ane ne gun Alhj Abubakar, su uku iyayensu suka Haifa, Alhj Abubakar sai Gwaggo shafa'atu sannan margyayi Mal Musa, Wanda Gwaggo shafa'atu tana Ambursa tana aure Wanda Allah bai bata haihuwa ba,,,,,,,,
Lokacinda Hindu ta haifi musaddiq anan Allah ya krb'i ranta, Wanda sanadiyyr hakan rainonshi ykoma ga Hjy saudatu saboda lokacin bata haifi munaxxafa ba, nan aka saima yaro madara tana kulawa dashi har inda yakai shekara takwas baisan cewa Hjy saudatu ba itace ta haifeshiba,,,,, sai lokacinda mahaifinshi ya gamu da ciwon ajali watau ciwon Cancer ta ciki, inda yaga cewa duk dangi da mak'wabta Ana tausayamashi har Ana furta cewa baisan mamasshi ba kuma ga babanshi ya rasu, hakan shi yayi silar tausayinshi da Hjy saudatu keyi, kuma yke hannunta tun wancan lokacin. Wannan *kenan*
Kuci gaba da kasancewa da alk'alamin y'ar mutan *JEGA*
Dedicated to Mmn Shakur.
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 1⃣4⃣
By Sdy jegal
"""Yau ta Kama Monday duk d'alibai Nata hada hadar shirin makaranta, Wanda haka take ga Xarah itama, xuwanta makaranta suka had'e da munaxxafa da Asmee sunata tad'i, sanadiyyr yau sunxo makarnta cikin lkc, nan munaxxafa ke cema Xarah yau kam xakiyi xaman nutsuwa cikin class saboda bamuda dodonki yau wato uncle Hakeem, nan Xarah ta k'ara had'a rai tana Mai cema munaxxafa ta daina yimata maganar wannan axullumn mutum da bashi da tausayi, Asmee ta karb'e da cewa Kai Xarah saboda kina tsoronshi ne har kike ganinshi da mugunta, malaminda ko bulala baya rik'ewa a Ina yagamu da mugunta,,,, nan Xarah kecewa ke kike ganin hakan, nida shekaranjia yasa sergeant yayimin bulala goma akan rashin assignment,,,, Allah tun ranar na k'ara tsanarshi kuma naji tsoronshi ya fita a kaina, Kai Xarah kar fa ynxu kiganshi jiki ya kwashi rawa Cewar munaxxafa""""" suna cikin hirar ne aka shiga class nan malamai suka shiga kowane da period d'inshi har aka tashi Xarah bata saka uncle Hakeem a idontaba"""""
Sun fito ne suna xaune xaman jiran direban su Xarah yaxo saiga wata d'aliba taxo tace Xarah uncle Hakeem na nemnki, nan take ta had'e rai tace ita ba inda xataje, su munaxxafa sukayi rarrashin duniya tace fa ba inda xataje,, suna hakn saiga uncle Hakeem ya gitta ta gabnsu shida uncle Emanuel,,,,, nan take Xarah ta kauda knta tamkar bata gansuba,
Saiyace Xarah ba'a gayamaki ina nemankiba, nan ta juyo ta k'ara had'e fuska tace uncle ni ba Wanda ya gayamn, sai yace OK dama buk d'inki na English xki bani akwai abubuwnda xnduba, nan ta d'auko ta bashi tana Mai tunanin Mai xaiyi da buk d'in English shida ke yimasu chemistry, can na hango munaxxafa Nata k'ok'arin k'unshe dariyrta amma wucewar uncle Hakeem tasaki abitta son ranta, tana Mai tambayr Meye gaminshi da English nan Xarah tace fad'i kedai wai kicihi shege da Gwaggo .
Daga alk'alamin Sdy jegal
Dedicated to Mmn Shakur.
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 1⃣5⃣
By Sdy jegal
Shigowar Xarah kenan ta hango Broda Shakur xaune falo yana kallon wrestling, nan tayi sallama ta xauna kusa dashi tana Mai cewa washhh""" Shakur yabita da Harar wasa yana Mai cewa wannan anyi sangartacciya, xuwa makarantar ne abin Kirama washh kije ckn mota kidawo ciknta amma da kindawo sai xubewa kina kingaji, nan tayi murmushi tana Mai cewa Allah Broda karatu akwai wuya kuma kasan munkusa xana exam dinmu ta k'are makarnta, nan yace to Allah yataimaka ta amsa da Ameen Broda,,,,
Rufewar bakin Xarah kenan taji y'an biyun Mummy aknta wato khadeeja da Mubarak suna rigima akan sweet, Nan Xarah ta shiga tsakaninsu tana Mai cewa sweet d'in waye daga cikinku,,,, nan suka had'a baki kowa na cewa tashi ce,, nan khadeeja ke cewa Anty tayi tambaya ckn class nabada Amsa shine tabani, Mubarak ya karb'e da cewa wlh ni aka bama ta d'auke,, Shakur yace to naji duk kuxo nan, take sukayi wurin Broda saiya karb'e sweet d'in yace suje d'akinshi xsuga sweet su d'auko su kawomar,
Xarah tace xaka had'a wani fad'an kenan, ke khadeeja xo nan Kai kuma Mubarak jeka ka d'auko sweet d'in, tafiyasshi kenan khadeeja ta had'e fuska xatayi kuka sai Xarah tayimata rad'a a kunne take saita washe baki.
'''''Bayan Shakur ya sallamesu sai suka haura sama gurin Mummy, Kai way'annan yaran ai xsusa mutum ciwon Kai, haka kike fama dasu,,, cewar Shakur, Xarah tace don dai bakason hayaniya ne shiyasa, amma y'an biyun Mummy akwai dad'in xama, don ni inbasu gidannan hka nakeji tamkar gidan makokin mutuwa.
Xarah ta mik'e xata haura sama tace Broda anjima xaka fita damu musha ice cream,, Shakur yce kinemi direba don ni ba direbanki bane, anan ta marairaice fuska tace haba Broda kasan fa nayi missing d'inka ka daure muje plxxx, nan yace to naji sai xuwa 5'o'clock sai muje.
Daga alk'alamin *Sdy* *jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 1⃣6⃣
By *Sdy* *Jegal*
*5*' *O'clock*
Kinga fa abinda ke had'ani dake, zaki matsa mutum yafita dake amma ki shige d'aki fiye da minti 30 wai kwalliya kikeyi.
Zarah ta fito cikin sauri tana yafa k'aton gyalenda ta rik'o a hannunta, tana cewa Broda kayi hak'uri har xan fito k'awata munaxxafa ta Kira wayata.
Nan Shakur ya bita da kallo yana cewa Ku kenan kullum Baku gajiya da juna, ko weekend kuna manne da juna.
Zarah tace aini Abu d'aya nake tunawa in muka gama skul xamu rage ganin, ai kamata yayi ku auri miji guda sannan xansan cewa kun shak'u da juna " cewar Shakur.
Zarah ta murmusa tace aikwa Broda kamr kasan abnda xamuyi kenan, nan yayi murmushi yace ba dai Mata da kishi ba.
****
"Umma na ganin sun fito tace lallai Zarah kin nuna yayanku ya dawo har kin Fara waremin y'an biyu na.
Zarah tace laaah Umma ba haka bane, kinsan Broda baya son hayaniya sosai, kuma kinsan yaranki da rigima, tana maganar had'i da dariya, nan ta shige Mota Shakur yaja suka wuce sai B.L.B plaza, inda suka sayi abinda suke so aka yoma y'an biyun Umma tsarabar ice cream.
Zarah ta kalli Shakur tace "Broda ko xaka biya Dani gidansu munaxxafa indibo Mama?
Shakur yace bamuyi hakan dake ba daga gida, saboda haka ko ina baxan jeba.
Nan Zarah ta d'an marairaice tace plx Broda ka taimaka Mama kawai xan dubo, munaxxafa tace batajin dad'in jikinta.
Nan ya juya akalar motarrshi sai unguwar su munaxxafa, suna isa yace tayi sauri ta shiga ta fito akwai inda xaije inya ajiyeta, shigatta gidan kenan ta hango munaxxafa na shara, sallamatta daidai take da shek'owr munaxxafa suka rungume juna tamkar sun jima basu had'u ba.
Nan suka Saki juna tana tambayar jikin Mama, munaxxafa tace da sauk'i nan taja hannunta suka shiga wurin Mama, Zarah ta durk'usa ta gaida Mama gami da yimata ya jiki?
Mama ta amsa tana tambayr ya Umma da y'an biyu, Zarah tace kowa k'alau, xamu wuce Mama tare da Broda muke, nan ta yimata godiya gami da cewa ta gaida gida.
Suna fitowa munaxxafa tace ba dai har zaki wuce ba, Zarah tace wlh sauri nakeyi kinsan halin Broda, nan munaxafa ta yomata rakiya har wurin motar Shakur.
"Saida yaji tafi daidai kunnenshi sannan ya dawo daga duniyar kallon da yabi munaxxafa dashi, Zarah tace Broda anata gaidaka baka jiba, nan ya waske gami da cewa hankalina na wurin Wanda ke jirana, sungaisa da munaxxafa har yana xolayar ta cewa ta girma sosai itako tana Mai soke Kai gami da jin kunya, sukayi sallama da munaxxafa suka Kama hanyar gida.
"Nan nace Kai Shakur kodai ankamu ne. _lolx_
Taku ce *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.

No comments:

Post a Comment