Thursday 6 October 2016

SANADIN KUNCI 1-5

[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_  1⃣��


                  _SDY_ _JEGAL_


Kwance take rigingine saman katifa, kan ta na kallon ceiling sai hawaye ke zuba daga idon ta.
Wani irin k'unci ke ziyarar zuciya ta sai sak'e sak'e take yi a zuciyar ta.
Wannan rana itace rana ta k'unci da kuma farin ciki a gare ta ta wani 6angaren.
To wai ma ya akayi hakan ta faru?
Me yasa tambayar da suke yiwa Ammi a kullum amsar da take basu tasha ban-ban da abinda ya faru yau?
Tuna furucin Ammi ne yasa ta shiga wasi-wasi in har abinda Ammi ta fad'a haka ne to wannan waye shi.

Mubarak ya jima saman kan ta bata Masan cewa ya shigo ba.
Yasan tabbas yana tausayin kanshi, amma yafi jin tausayin k'anwar tashi har cikin ranshi.
Sai da ya bubbuga filon da tayi matashi dashi sannan ta zabura da k'arfi, ganin cewa Mubarak ne yasa kukan ta ya k'ara tsanan ta.
Nan ya zauna gefen katifar da take kwance yace Sister ki tashi za muyi magana.
Bayan ta tashi ne yace to ki daina kukan ya isa haka.
Tace yaya bansan Ina Zan sa kaina ba damuwa ta yimin yawa, akwai tambayoyin da bansan ina Zan samu amsar su ba.
Yace duk abinda kike so ki sani Ammi Nada amsar tambayoyin ki, sai dai itama tana cikin k'uncin da bai Kama ta mu tun kare ta da maganar ba yanzu har sai ta samu natsuwa a zuciyar ta.
Saboda haka ki yi hak'uri ki tsagaita wannan kukan da kike yi saboda bashi da amfani.


������         ������

Koma miye Kai ka janyo shi Aliyu, ba yadda banyi da Kai ba akan ka auri d'iyar d'an Uwa na kayi tsaye sai wannan shegiyar yarinya Mai Kama da aljanu, to ga abinda ka janyo nan don yau bansan wace hanya ce Zan wanke kaina ga Alh ba.
Wanda aka Kira da Aliyu ya tada kan shi yabi Haj Zainab da kallo cikin rinannun idon shi, jiyojin kanshi duk sun mik'e sai wani huci yake yi tamkar namijin zaki.
Wani irin tuk'uk'i zuciyar shi keyi yana so yayi magana amma ya kasa.
Nan abokin shi Sudais yaja hannun shi ya wuce d'akin shi dashi, suna shiga ya bud'e fridge ya d'auko gorar ruwa ya had'o da glass cup ya tsiyaya ruwan ya bashi.
Nan ya kauda kan shi sai wani huci ya ke yi.
Sudais ya sake mik'a Mai ruwan yana Mai rarrashin shi yace ka daure kasha ruwan zaka ji sanyi a zuciyar ka.
Da k'yar ya rarrashe shi ya kar6i ruwan yasha, sannan yayi wata irin ajiyar zuciya.
Yace sudais Haj ta cuce ni, ta cuci rayuwa ta duk da bansan miye silar faruwar hakan ba, amma jin kalaman Abba yasa na tabbatar da cewa Umma ce zata zama silar _sanadin_ _k'unci_ _na_.
Sudais yace kayi hak'uri idan Abba ya shigo zamu ji ya aka yi hakan ta faru.
Nan dai ya samu ya rarrashe shi har nutsuwa ta Fara sauko Mai.

***  ***  ***  ***

A can falo KuwaHaj Zainab ce sai ta Kai gwauro ta Kai Mari duk inda hankalin ta yake a tashe yake, ta rasa da wane ido zata kalli Alh in ya shigo.
Tana wannan tunanin ne taji Alh na kiran ta cikin muryar tashin hankali Zainab! Zainab!! Zainab!!! sunan da rabon da ya Kira ta dashi anfi shekara ashirin.
Nan take hanjin ta suka d'auki wata k'ara k'ululuuuuuuu!

Alh na shigowa ya rik'o ta yana girgiza yace me kika gayamin shekarun baya?
Dama akwai abinda kika shirya a k'asa?
Kin cuce ni kin cuci rayuwar yaron ki, miye ribar ki anan?
Cikin shesshek'ar kuka tace wallahi Alh sharrin shaid'an ne bada gayya na aika ta hakan ba.
Tsawar da ya daka Mata ni kaina sai da na razana, yace Zainab wallahi in baki gayamin ya akayi hakan ta faru ba sai nayi mugun sa6a maki.
Bud'e bakin da tayi zatayi magana, sai ga Aliyu ya shigo falon yazo gurin k'afar Abban shi ya zauna.
Cikin k'unar rai ya fara magana, yace Abba ya akayi hakan ta kasance?
Abba kar kuyi silar _sanadin_ _k'unci_ a gare ni.
Alh yace Mai Ina sudais halan?
Yace yanzu ya wuce ta k'ofar baya yabi.
Yace to sai mu saurari mahaifiyar ka domin itace ```Sanadin``` ```k'unci ```na nima.

           ```SDY``` ```JEGAL```��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_  2⃣��

*TUSHEN* *LABARI*

Suna ajiye ta cikin dajin suka gargad'e ta da cewa kar ta kuskura ta koma garin in ba hakan ba zata rasa rayuwar ta.

Hakan ta sa6o k'aramin yaron a kafad'ar ta ga ciki tsoho tana turo wa.

Sai da tayi tafiya Mai d'an nisa sannan ta Fara hango titi, ga yunwa da k'ishi na damun ta.

Tana isowa round about cikin garin Jega ta hango masu siyar da abinci ta k'ara so gurin su.

Nan tace'
"Don Allah Ku taimakamin da ruwa k'ishi nake ji.

Nan wasu matan suka bita da wani kallo tamkar mahaukaciya.

Sai da ta isa gurin wata mata nan ta tausaya Mata ta bata ruwa tasha kuma ta had'a Mata da shinkafa da wake.

Bayan ta gama cin abinci ne ita da yaron ta, takai duban ta ga matar

Tace'
"Don Allah ko Zan samu gurin da Zan d'an fake zuwa gobe?

Matar tace'
Ki jirani in zaki iya har in gama sayar da abinci na sai mu wuce gida tare.

Hakan ta koma gefe ta raku6e tana mak'ale da yaron ta har matar ta gama suka nufi gida.

Yau kwanan ta biyu gidan Baraka Mai sayar da wake da shinkafa, nan ta bata d'aki d'aya tace ta zauna har zuwa lokacin da zata k'ara gaba.

Da safe Baraka na sayar da koko da k'osai gida, sai da azzahar take fita da wake.

Hakan Hauwa'u take tashi da safe ta taya Baraka aikin koko da k'osai, cikin ma tana hana ta don ganin ta da tsohon ciki.

Yau ne ta cika sati biyu a gidan Baraka, ta fito ta saka wake a turmi zata surfe sai taji mararta ta k'ulle.

"Nan ta durk'usa gurin tare da rik'e marar ta.

Lura da hakan da Baraka ta yi yasa tazo ta rik'a ta ta mayar da ita d'aki.

Tace'
"Mike damun ki halan?

Hauwa'u tace'
Wallahi tun da asuba Mara ta ke ciwo sama-sama, amma yanzu tafi damun na.

Tace'
"Ko zamu je asibiti ne?

Ta girgiza kan ta tace ba sai mun je ba.

Baraka tace'
Bara in shiga mak'otan mu gidan Mal Issuhu in kar6o maki tofin haihuwa.

"Tana kawo tofin ta bata ta sha ba'a wuce minti goma ba da taimakon Baraka ta sunkuto y'ar ta kyakkyawa.

"Kukan jinjirar ne ya tayar da Mubarak daga barcin da yake yi.

Nan Baraka ta fita dashi ta yimai wanka ta bashi koko yasha.

Da taimakon Baraka Hauwa'u tayi wankan jego ta gyra jinjirar ta.

"Bayan sati ya za gayo ne aka yankawa y'ar ta ragon suna da taimakon wani mak'ocin su Alh Bello.

Nan aka rad'awa yarinya suna Musirrah, hakan ta had'a kan y'ay'an ta tana basu kulawa dai-dai gwargwado.

"Bayan tayi arba'in ne da sati d'aya suna zaune suna hira da Baraka.

Tace'
"Na gaji da zaman nan inaso in samu abinda Zan tallafama yarona in saka shi makarantar islamiya da boko, don haka don Allah ki taimakamin ki nemo min aikatau.

Baraka tace'
"Yanzu kenan ba kida niyyar komawa gida.

Nan tayi wani murmushi Mai cin rai tace'
Baraka zamana daku ya fiyemin zama cikin garin mu, saboda kishiya ce tayi _sanadin_ _k'uncin_ da nake ciki a halin yanzu.

           _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _KUNCI_  3⃣��


"Nan ta bata labarin halin rayuwar da ta fuskan ta a baya.

"Sannan ta d'ora da cewa da wannan nake son ki taimaka min in samu wani aiki in saka Mubarak a makaranta.

Tace'
"To Zan bincika  insha Allah asa mo miki aikatau.

Nan tayi godiya sosai tana Mai gode ma Allah da ya had'ata da matar arzik'i Mai tausayin ta.

"Bayan kwana biyu ne Baraka ta samo Mata aiki gidan wani Alh Abubakar.

Baraka tace'
"Ki shirya gobe zamu je in nuna maki gidan aikin.
Amma gaskiya sai kin yi hak'uri da matar gidan saboda kwata-kwata bata shiri da talakka.

Hauwa'u tace'
"Ba komai zansha maganin zama da ita in dai har Zan yi aiki ta bani hakk'in aiki na.

"Da safe bayan ta shirya ta yiwa yaran ta wanka ta goya Musirrah taja Mubarak ga hannu, saboda Baraka ta gaya Mata gidan ba nisa.

Bayan sun isa gidan ne aka yi musu iso ga matar gidan har cikin falo.
Taci wanka ta saka wani rantsattsen less tasha a warwaro tana hakimce saman kujera three seater ga Apple a hannun ta tana gutsira.

"Nan suka durk'usa suka gaida ta cikin ya tsinar fuska ta amsa tana musu wani kallo.

Hauwa'u tace'
"Akwai aiki wannan matar, mace haka tamkar bata ta6a k'asa Allah ya bani ikon jure duk wani k'ask'anci da Zan fuskan ta daga wannan matar.

"Jin Baraka ta ta6o tane yasa ta dawo daga tunanin da ta afka.

Haj tace'
Zaki rik'a yimin wanke-wanke da shara sai kuma goge falo, sai wanke kayan baby Iman Zan rik'a baki dubu biyar a wata zaki iya?

Cikin rawar jiki tace'
Zan iya Haj na gode sosai Allah ya k'ara rufa asiri.

Haj ta bita da wani matsiya cin kallo tace'
Wa'annan yaran waye?

"Ta bata amsa da cewa yara nane.

Tace'
Gaskiya bana son aikin matar da keda yara, saboda a tsarina bana son k'azan ta.

Ba Hauwa'u ba dai-dai da Baraka sai da hankalin ta ya tashi saboda sun ga samu sun ga rashi.

"Nan Baraka ta rik'a rok'on ta kan cewa tayi hak'uri Mubarak zai rik'a zauna wa gurin ta har lokacin da mamar shi zata koma gida, tun da aikin na safe ne kawai.

Nan Haj ta bita da wani kallo Mai had'e da kin raina mutane.

Tace'
"Sau biyu zata rik'a a zuwa a rana, da safe k'arfe takwas zuwa sha biyu sai kuma laasar zuwa k'arfe shida.

"Nan Baraka tace koma yane Zan kula da Mubarak sai ki barta da jinjirar ta don Allah Haj.

Tace'
"Naji Zan d'auke ta amma gaskiya Inna hango wata k'azanta a tare da ita Zan sallame ta.

Nan Hauwa'u ta yi karaf tace na amince Haj.

"Da hakan suka Kai k'arshen magana suka fito a zuwan sai gobe zata fara zuwa aikin.

(Na mayar dashi *SANADIN* *K'UNCI* saboda hakan zaifi dacewa da labarin)

           _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_  4⃣��

*WASHE* *GARI*

Tun da ta tashi daga sallar subahin bata koma bacci ba.

Hakan ta fito ta hura wuta ta d'ora ma Baraka ruwan koko, sannan ta surfe wake.

Tana cikin wankin waken ne sai ga Baraka ta fito.

Tace'
"Ai kamata yayi ki Fara shirya kan ki keda zaki fita gurin aiki k'arfe takwas"

Nan ta kar6i waken ta wanke, sannan ta yiwa Mubarak da Musirrah wanka.

Zuwa takwas saura kwata ta iso k'ofar gidan.

Tana shiga bayan ta gaida matar gidan, nan tasa aka Kai ta inda suke wanke-wanke.

Hakan ta had'a kan aikin ta har ta gama Musirrah na goye tana bacci.

Saboda dama da ta yi Mata wanka da safe ta goya ta zata iya Kai sha d'aya tana bacci.

Tana goge-goge falo ne Musirrah ta rik'a mutsu-mutsu alamar zata tashi daga barci.

Ta ajiye aikin ta fito daga waje ta sauke ta ta bata mamma ta sha sannan ta goya ta ta koma daga ciki ta k'arasa aikin ta.

Tana kammalawa ne da wankin kayan Iman bayan ta shanya tazo falo ta raku6e daga gefe.

Tace'
"Haj na k'arasa Zan wuce gida sai da yamma kuma"

Haj tace'
"Shikenan sai kin dawo"

Bayan ta dawo gida ne ta taradda Baraka na shirye-shiryen fita gurin sayarda waken ta.

Nan ta hango Mubarak zaune yana cin wake, yana ganin mamar shi ta shigo ta ajiye abincin yazo da saurin shi.

Yace'
" Ammi yau Ina kika je kika barni?

Ta janyo shi ta rungume
Tace'
"Naje in nemo kud'i ne in saka ka makaranta, kana so ko?

Yace'
"Eh in rik'a zuwa makarantar su Suraj?
(Suraj d'an mak'ocin sune)

Ammi tace'
"Eh har ma da islamiya Zan saka ka"

Nan yayi murmushi, itako takai duban ta ga Baraka
Tace'
"Yanzu zaki wuce ko?

Tace'
"Eh, amma ga makullin gidan in har kin tashi fita ban dawo ba to ki rufe gidan ki kaiwa Jummai ta ajiye"

Nan ta rik'o hannun Mubarak zasu fita
Tace'
"Ki duba kicin na ajiye maki naki waken"

Nan ta yita godiya zuwa ga Baraka har ta janye hannun Mubarak suka wuce.

Tana tsaye tana hawayen k'unci da damuwa.

Haka rayuwa taci gaba da kasancewa a Gare ta.

Yau da murnar ta ta tashi gaggauce ta shirya ta wuce gidan aikin ta.

Bayan ta gama aikace-aikacen tane Haj ta Kira ta ta damk'a Mata kud'in ta na aikatau, saboda yau ta cika sati hud'u da Fara aiki a gidan.

Cikin rawar jiki ta mik'o hannu ta kar6i kud'in har ta had'a da hannun Haj.

Nan ta buga Mata wata tsawa tace'
"Kina hauka ne zaki had'a da hannuna gurin kar6ar kud'in.

Dama shi matsiya ci bai iya ganin kud'i ba, nan ta wurga Mata kud'in a fuska tace'
"Ni tashi ki 6ace min da gani tun ba kisa zuciya ta tashi ba"

Hakan ta kwashe kud'in ta tasa Kai ta fita hawaye na zuba daga idon ta.

            _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 5⃣��


Ko da ta iso gida Baraka bata nan, hakan yasa ta shiga gidan Jummai ta kar6o makulli ta bud'e gida ta shiga.

Bayan ta d'auko abinci ta ci ne ta had'o kayan su har na Baraka ta wanke.

Daga nan tayi shara ta gyra gidan tsab sannan ta yi shimfid'a nan tsakar gida ta kwanta, sanadiyyar kwana kusan uku ba'a yi ruwa ba akwai zafi-zafi a garin.

Yanzu abinda kafi k'arfi ne har ake wulak'an taka akan shi.

Hassy tace'
"Don Allah Haj kitaimakamin y'ata aka kwantar asibiti kuma bani da kud'in magani"

Nan ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko dubu goma ta bata.

Tace'
"Kije kiyi lalura in ma basu isheki ba ki gayamin Zan gaya ma Alh ya baki wasu"

Nan ta durk'usa har k'asa tana hawaye tana Mai k'ara yi Mata godiya.

Tace'
"Haba tashi ba komai, kije kawai Allah ya bata lafiya"

Jin ana girgiza tane yasa tayi firgigit ta tashi zaune duk hawaye sun wanke Mata fuska.

Nan Mubarak yasa hannu yana share Mata hawaye.

Yace'
"Ammi waya dake ki in je in rama maki kinsan nayi k'arfi yanzu" ( yana maganar yana ta6a damtsen shi)

Nan tayi murmushi tace'
"Mubarak ba Wanda ya dake ni murna ce ta saka ni kuka saboda yau na samo kud'in da Zan saka ka makaranta"

Nan ya nuna murnar shi, ya Ciro biscuit d'aya cikin Wanda yake ci.

Yace'
"Ammi bud'e bakin ki in saka maki wani Abu Mai dad'i da mama Baraka ta sayamin"

Tayi murmushi ta bud'e bakin ya saka Mata biscuit.

Tace'
"Nagode Mubarak Allah ya albarkaci rayuwar ka, tana share hawayen ta"

Yace'
"Ammi ke kika ce in abin murna ya sami mutum cewa zai yi Alhamdulillah, amma ke kin samu kud'in saka ni makaran ta sai kuka kike yi"

Baraka dake zaune gefen shimfid'a tana sauraren su tana murmushi.

Tace'
"To sarkin surutu je ka ajiye takalma d'aki kazo muci abinci an jima akai ka islamiya"

Yana shiga d'akin ta juyo zuwa ga Hauwa'u.

Tace'
"Wayon Mubarak ya 6aci, yau yaje kaiwa wani mutum wake sai gashi yazo da gudun shi wai inzo Inga Baban shi"

Hauwa'u ta zabura da k'arfi tace'
"Baban shi fa, a Ina?

Baraka tace'
"Nima sai da naje muka yi magana da mutumen yace sai in kama ce shi baisan shi ba"

Sai ga wani dogon numfashi ta sauke, tana Mai godiya ga Allah da bashi bane.

Nan dai suka tattauna kan maganar karatun Mubarak.

Baraka tace'
"Ina ganin a saka shi islamiya ta Malja'u dake kusa damu, in yaso ta boko kuma asa kashi Model don bata kud'I bace"

Zuwa laasar aka shirya Mubarak Baraka ta kaishi Malja'u.

Bayan ta dawo ne Hauwa'u ta bata dubu d'aya cikin kud'in ta na aikatau.

Tace'
"Nikam bazan kar6i kud'in ki ba ki ajiye zaki yi lalurar makarantar Mubarak"

Nan dai ta yita yi Mata godiya saboda samun mutum Mai karamci tamkar Baraka sai an tona.

Da hakan kowa ya Kama gaban shi zuwa Sana'ar shi, sun ajiye kan idan Mubarak ya dawo koda basunan ya shiga gidan Jummai mak'ociyar su.


            _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu

No comments:

Post a Comment