[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 4⃣0⃣_4⃣5⃣
Kai tsaye d'akin Musaddik ta nufa, koda tayi sallama ta shiga bai ma San cewa ta shigo ba.
Ta matsa gab dashi ta yimai tafi raf-raf cikin kunnenshi, nan take ya zabura zai Kai Mata duka ta kauce tana dariya.
Yace waike me yasa baki San lokacin wasa ba, tunda ina cousin d'inki shikenan kullum wasa.
Tayi murmushi tace yi hak'uri yaya, me ya sakaka cikin damuwa haka har na shigo d'akin nan bakasan na shigo ba? Ko murna kake yi Baba ya baka sankaceciyar budurwa?
Ya nisa yace ba kida damuwa shiyasa.
Tace yaya gayamin miye damuwarka?
Nan ya bata amsa da cewa nifa inada wadda nakeso, nayi nauyin baki ne ban samu gayama Baba maganar ba, har gashi ya riga ni furta abinda ke ranshi.
Tace tabd'ijam ni ko gashi duk duniya banda Wanda nake so sama da Kai, saboda haka k'arama ka Saki ranka muci soyayyar mu hankali kwance
Ganin da tayi ya tashi ya janyo belt zai dukanta yasa tace plxxx yaya kayi hak'uri wallahi wasa nake yi.
Yace me yasa baki San lokacin wasar ba? Kinga yadda kika Mai dani mahaukaci?
Tace to kayi hak'uri zauna muyi magana seriously.
Ya dawo ya zauna yana Mai ce Mata meke tafe da'ita?
Tace yaya ina so ka tashi muje ka gayama Baba cewa yayi hak'uri saboda baka iya aure na, kana da wadda kakeso.
Lallai yarinyannan baki da ta ido, wato nine rasa kunya Zan jema Baba da wannan maganar.
Nan ta tashi tace lallai yaya k'aryar *SO* kake yi, dama na zo ne in taimake ka saboda nasan kanada wadda kakeso.
Musaddik yace to dawo zauna muyi magana.
Bayan ta zauna, yace tabbas Ina son sweetie d'ita, but bazan iya tunkarar Baba da maganar cewa ban son kiba gaskiya, da ace ma maganar daga gare ki ta fito da abin zai d'anyi sauk'i.
Ta bud'e baki tace amma kasan cewa Baba na tausayama sama dani, yadda zai damu da damuwarka ba zai damu da tawa haka nan ba.
Ya bata amsa da nasani k'anwata amma abin da nauyi.
Ta nisa tace to kabar komai a hannu na, inshaAllah Zan kawo k'arshen abin.
Musaddik yace a'ah kin San na sanki fa ciki da bai.
Nan tayi murmushi tace amma kasan duk abinda nkeyi sai dai wasar ta tsaya tsakaninmu, ba na sako Baba ko Mama cikin wasan mu.
Yace to shikenan ba matsala zuwa yaushe Zan saurareki?
Tace Mai gobe inshaAllah.
Yace to shikenan, sai dai Ina Mai k'ara jadda da miki kada ki bari sunana ya fito cikin maganarki.
Sai da takai bakin k'ofa ta juyo tace "air ko cema Baba Zan yi kace yataima keka ya rabaka dani.
Tana ganin ya tashi ta zura da gudu sai d'akin ta.
Nan musaddik yace yarinyar nan ta raina ni dayawa, amma gaskiya ba don ina dakon soyayyar sweetie d'i naba da ba abinda zai hanani auren Munazzafa, saboda akwaita da saurin shiga rai.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn Shakur.
[6:26PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA4⃣5⃣_5⃣0⃣
Bayan dawo war k'annen mahaifin Hakeem ne daga gidan Alhj. Ibrahim suke labartama Hjy yadda sukayi dashi, kuma suna yaba hankali da nutsuwar yarinyar da suka gani, wadda Alhj ya gaya musu cewa itace surukar su.
Suna cikin maganar ne Hakeem ya shigo.
Nan suke cema Hakeem gaskiya kayi dacen Mata, kuma ga mahaifin yarinyar yana da karamci, koda kake wani cin magani zamuje gidan Ashe matar arzik'i Allah ya had'aka da ita.
Hajiya sai murna take yi tana murmushi jin samun surukar da kowa yabama halayenta yakeyi.
Nan suke gaya Mata cewa, anbiya sadaki kuma ansa rana wata biyu masu zuwa.
Ka shirya kaje ka gaidashi kuma ka k'ara yi mashi, cewar d'aya daga cikinsu.
Nan suka tashi zasu wuce, Hjy na k'ara yi masu godiya.
Nusaiba tazo ta zauna tana cewa Hjy Ashe mun kusa shagalin biki.
Hjy tace to lallai kam, amma yayan ki yak'i yasaki ranshi, bansan meke damun shi ba.
Yace Hjy inshaAllah komai ya wuce, kuma dana fita yanzu zanje wurin Alhj d'in.
Nan Nusaiba ke cewa gaskiya yaya na yima sha'awar auren k'awata Sumee, nan ya bita da harara yana Mai cewa, da auren Sumee d'in ai gara y'ar sadaka. (Novel d'in Aysha Ibrahim).
Laaah! Kai yaya y'ar sadaka fa?
Yace eh mana ko ni na ganta nace ina so? Mak'alamin ita akayi.
Hajiya tace ahir d'inka kar na k'ara jin ka Kira masu yarinya da y'ar sadaka, ko kana tunanin ba don karamci ba mahaifinta zai d'auki gudan jinin sa yabaka haka kawai.
Kaima kasan yadda mahaifinta yake da arzik'i kuma sananne cikin gari ba Dan karamcin da ka yimashi ba ko kallo baka isheshi ba.
Ganin ran Hjy ya b'aci sosai yarik'a bata hak'uri, da yimata alk'awarin bazai k'ara ba, saboda baison b'acin ranta ko kad'an.
Nan ya tashi ya fita, Nusaiba ta bishi tana Mai cewa yaya ko zaka je Dani Inga matar ka?
Nan ya bita da harara yana ce Mata hala cemaki akayi gurin ta zanje?
Nima fa ko ganin ta ban tab'a yiba.
Nan ta bishi da kallon mamaki, tana Mai tambayar kanta cewa to ko akwai wadda yake so ne, ita dai tasan Mata ma basu gaban shi.
Maganar shi ta dawo da ita daga tunanin da ta afka.
Yace Mata ta shiga ciki shi zai wuce, tace plxxx yaya in kaje kanemi ganinta ko don faran tama Hjy.
Yace to shikenan zanyi d'in, tace to yaya ka gaida ita.
Nan yayi murmushi ya girgiza kanshi ya wuce.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA5⃣0⃣_5⃣5⃣
Isowarshi kwanar gidansu, yaga ta fito daga mak'wabta ta shiga gidansu, nan ya murza idon don ya k'ara tabbatarda shin itace ya gani ko yaya? To ko dai makwabta suke da gidan?
Duk way'annan tambayoyin kanshi yake je roma su.
Wata zuciyar ta cemai itace fa, inhar zaka iya tuna sunanta shine FATEEMA MUKHTAR IBRAHIM, kuma file d'in da ka tsinta shi zai tabbatarma cewa itace.
Nan take farin cikinshi ya bayyana, yana jin wani sanyi na ratsashi ta ko ina.
Saboda tun lokacinda yasa sergeant ya yimata bulalar rashin assignment ya kamu da son ta, amma ya rasa wace hanya ce zai b'ullo har ya furta so zuwa gare ta.
Saboda ranar ya hango haushin shi kwance ga fuskatta.
Wata zuciyar ke ce mashi to Kai kanada tabbacin itace mahaifinta ya baka ko kuma yayar tace? Nan kuma sai annurin fuskasshi ya kau.
Koda ya shiga gidan suna gaisawa da Alhj, yake tambayasshi mike damun shi hala?
Ya Saki ranshi yana k'k'alo murmushin dole, ahhh! Ba komi Alhj dama na zone in k'ara yima godiya da kyautar ka zuwa gareni.
Alhj yace ba komi yaro na, Ina jinka cikin raina tamkar yaran da na Haifa.
Dama nace a turomin Kaine saboda inji ko kanada wani shiri ko tsari da kakeso kayi ga auren ku.
Hakeem ya soke Kai yana Mai cewa Alhj ba wani tsari daya wuce naku.
Alhj yace Zan had'aka da Shakur ranar da ka samu dama kuje ka zab'i gidan da zaku zauna a cikin gidaje na.
Nan ya k'ara soke Kai yana ta zuba godiya, Alhj yace ba komai kakka damu ai shi D'a na kowa ne (novel d'in Bebeelo).
Alhj ya tashi yace bara in shiga gida inturoma Zarah d'in.
Nan yace a'ah Alhj a k'yale ta saina sake dawowa.
Alhj yace a gaida gida, ya wuce ciki shiko ya fito.
Daka kalli fuskar shi zaka San cewa tabbas yana cikin farin ciki, saboda yanzu yana da tabbacin Zarah ce aka bashi sanadiyyar sunanta da yaji Alhj ya furta.
Kuma ya hana Alhj ya kira tane saboda baisan da idon da zai kalle taba.
Asali ma addu'ar shi Allah yasa bata san shine zai aure taba.
Yana murmushi yana k'iyasta daga yanzu zai fara wasar y'ar b'uya da ita har zuwa ranar da za ayi auren su.
Ni ko Sdy nace Anya Hakeem baka so kanka da yawa ba
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 5⃣5⃣_6⃣0⃣
Munazzafa na gama aikace-aikacen ta na gida da take taya Mama.
Ta shiga d'akin Mama ta gaida ta, sannan ta tun Kari d'akin Baban ta.
Saboda wannan al'adar tace kullum saita gaida mahaifan ta.
Tana zuwa k'ofar d'akin tayi sallama, Saida taji ya amsa tare da bata umurnin shigowa sannan ta shiga.
Ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, ya amsa tare da sa Mata albarka.
Ganin cewa ya gama magana ta kasa tashi yake tambayar ta ko akwai wani abune?
Ta Kama in-ina dam.. Uhmm maga...
Saida Babanta yace ki natsu kiyi magana mana.
Sannan ta tattara hankalin ta wuri guda.
Ta fara magana tana Mai cewa "dama Baba maganar da kayi jiya ce ta had'amu aure tsakanina da yaya Musaddik.
A hak'k'anin gaskiya yaya yana da wadda yake, kuma Ina ganin zasuyi wata uku tare.
Ka San kawaici irin na yaya, shi yasa nace bara inzo in sanar da Kai.
Saboda naga cewa yaya amana ce hannunku, ni inta nice Mai sauk'i ne Ku kuka haifeni kuma dole inyi maku biyayya.
Don Allah Baba kaduba kayi nazari akai.
Nan Baban ya nisa yace lallai Munazzafa na yaba da hankalin ki da nutsuwar ki, kuma yanzu na tabbatar cewa kuna ri'ke da zumuncin mu, Wanda ko bayan raina ke da d'an uwanki zaku had'a kan zuri'ar Ku.
Tashi kije dana fito Zan ne meku, Allah yayi maki albarka, ta amsa da Ameen tana k'ara soke Kai.
Tana shiga d'akinta ta fad'a saman gadon ta tana juyi tana k'ara jin wani nishad'i har cikin ranta.
Can na jiyo tana yima kan ta kirari "saini Munazzafa d'iyar Mama da Baba y'ar gata gurin Shakur".
Na jefi tsuntsu biyu da dutse guda.
Yaya ba Kai na taimaka ba kaina na taimaka, kasan ko yadda muke son junan mu nida *Reality*? Nasan ko Rabin *SO* baka yima taka *Sweetie* d'in.
Duk ita d'ai ke wannan maganar ta koma tamkar zararra.
Nan take ta jawo wayar ta ta danna ma *Reality* d'inta kira, inda har ta yimashi Kira uku bai d'auka ba.
Nan take farin cikin ta ya gushe.
*Reality* kakka ce fushi zakayi Dani, bamu Saba rashin jin juna ba, zakasa zuciya ta ta fashe, Zan iya d'aukar fushin kowa amma bana iya d'aukar naka.
Duk ita kad'ai ke wad'annan kalaman, Wanda ni *Sdy* har na fara tausaya Mata, lallai kin afka babban kogi.
Jin k'arar wayar ta ya dawo da ita daga k'aramar haukar da ta shiga, tana ganin *Reality* d'in tane saita basar kamar bata d'akin, sai da yayi kira biyu ana uku ta d'aga kiran, nan ta sassauta murya Wanda iya k'ok'ari na naso inkwaso maku hirar masoyan amma banji mi suke fad'a ba, saidai in hango hak'oran ta tana washe su tamkar Mai tallar makilin, _lolx_.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 6⃣5⃣_7⃣0⃣
Bayan Baban su Munazzafa ya ta rasu, yace Ashe musaddik akwai abinda zaka b'oyemin?
Tunanin cewa nasan bazaka iya tunkara ta da maganar ba yasa na yanke hukuncin had'a ka da y'ar uwar ka.
Sai gashi jiya k'anwakka ta iskeni da wata magana cewa kana da wadda kake so, har ta gayamin maganar da tasa jiki na sanyi.
Saboda haka na janye maganar da na furta, zan nemi Aboki na Alhj. Imrana muje gidan su yarinyar ayi magana da magaba tanta.
Ke kuma Munazzafa kiyi hak'uri Allah ya baki miji nagari.
Ta amsa da Ameen Baba, tana murmushi had'e da soke Kai.
Baba na sallamar su ta biyo Musaddik tana cewa, to abani tukwici saboda yau na taimake ka.
Yace gaskiya kinyi jahadi kuma kinyi k'ok'ari, fad'i duk abinda kike so.
Tace sai na tashi aure Zan gayama abinda nakeso.
Nan take ya Kama dariya yana cewa yarinya kinyi kwantai, ba mashin shini.
Nan ta yita dariya tamkar zararra saida tayi Mai Isar ta.
Tace wai Kai yaya kana tunanin Kai na taimaka ma ko kaina?
Yace banfa gane inda kika nufa ba.
Nan ta kwashe soyayyar ta da Shakur ta gayamai, tace to wannan abin Kai na taimaka ko kaina?
Nan ya bita da kallon mamaki yama kasa magana, Saida ta yimai tafi wurin kunne sannan ya dawo daga tunanin da ya afka.
Lallai na yadda Mace shu'uma ce, kuma da kissar ta ake haihuwar ta.
Nan tayi murmushi tace yaya ba haka bane, Ina son Shakur ne fiye da tunanin ka.
Kuma kaga Baba bazai yi maganar had'amu aure ba in fito in nuna Mai ba Zan amince ba.
Amma kaga yanzu na warware matsala ta cikin sauk'i.
Ka samu wadda kake so nima na samu muradin raina
Musaddik yace ai ko yanzu zanje incema Baba k'arya kike yi banda wadda nakeso.
Tayi dariya tace kaje ai ba matsala tare zamuyi jinyar zuciyoyinmu.
Yace yarinya kin kuru, tace mun dai kuru ta bishi da, ta shek'a d'aki.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 6⃣0⃣_6⃣5⃣
Fitar Hakeem daga gidan su Zarah bai zarce ko Ina ba sai wurin frnd d'inshi Faisal.
Yana ganin shi yace waya yima wahayi da aljanna wannan murmushin da kake? Da an ganka ansan yau kana cikin farin ciki.
Hakeem yace kaidai bari friend, al'amari na Allah yana Shir yadda shi yada yaso, kuma a lokacinda yaso.
Faisal yace haka ne friend.
Yace yau Allah ya wankemin bak'in ciki da damuwa dana shiga sanadiyyar Mace.
Nan ya kwashe labarin komi ya gaya Mai, ya d'ora da cewa kasan na cema duk yada naso in kauda son Zarah ga raina na kasa.
Ina cikin shawarar yada Zan tun kareta da maganar sai gashi anbani kyautar Mata.
A lokacin na shiga tashin hankali da rud'ani fiye da lokacin da Hafsat ta gujeni.
Kullum tunani na miye mafita gareni ta yadda Zan kaucema wannan kyautar don in samu tunkarar FATEEMA.
Sai gashi Allah ya warwaremin komi cikin sauk'i, Ashe dama itace na tsinci file d'in Baban ta sanadiyyar hakan har yabani ita kyauta.
Faisal yace gaskiya friend ba k'aramar sa'a ka taka ba, kuma kaji ance matar mutum k'abarin sa.
Ya amsa da hakane wallahi, yau jin nake kamar ace an maida auren sati biyu ba wata biyu ba.
Faisal ya kaimai duka yace wallahi friend baka da dama, ai zaka ce hakan tunda ka gano cewa wadda kake so ce.
Faisal yace yaushe zamu shirya muje gidan su?
Ya bashi amsa da cewa sai randa zaka rakani sayen baki, yana maganar yana dariya.
Nan Faisal ya bishi da kallo Mai cike da alamar tambaya, yace ban fahimci maganar ka.
Nan yayi murmushi ya bashi amsa da cewa ba naso ma taganni sai an kaita gidana.
Saboda me? cewar Faisal.
Ya bashi amsa da cewa Ina gudun ta ganni ta birkicema Abban ta cewa bata so na, bansani ba ko tana k'anwa ko yaya a musan yamin da ita, saboda nasan ni Mai laifi ne gare ta.
Eh to maganar ka gaskiya ce, amma wani hanzari ba gudu ba, kana ganin mahaifin ta bai tunanin ko kyautar da ya yima ce baka yaba da ita ba shiyasa kak'i zuwa kaga y'ar tashi?
Eh to hakane kuma, amma inshaAllah zanyi abinda bazai zarge niba.
Faisal yace to Allah yasa.
Ya amsa da Ameen.
Nan suka rabu Hakeem ya Kama hanyar gida, bakin shi yak'i rufuwa kamar gonar auduga. _lolx_.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 7⃣0⃣_7⃣5⃣
Bayan sun gama breakfast Abba ke cema Shakur ya kamata kazo kanemi Mata kaima, kaga auren k'anwarka saura sati biyu yanzu.
Shakur ya Kama soshe_soshe yana cema Abba ai shima ya samu Mata.
Nan Abba ke tambayar shi y'ar wane gida ce?
Yace Abba ai ta gida ce, wannan k'awar Zarah dake zuwa gidannan.
Nan Zarah ta bishi da kallon mamaki, saboda bata San cewa har sun shirya maganar aure tsakanin suba, ta daisan cewa taga alamar Broda nason Munazzafa d'in.
Abban su yace to ba matsala zamuje muyi magana gidan su yarinyar, in har sun shirya sai a had'a auren ka dana k'anwar ka.
Koya kake gani?
Yace hakane Abba.
Bayan sun gama Zarah ta shiga d'aki, ta d'auki waya ta Kira Munazzafa ta fara zazzaga Mata masifa.
Ta yi shiru tana jinta, saida ta gama sannan tace kiyi hak'uri.
Dama inada niyyar kiran ki yau inshaida maki maganar sai gashi kin kira.
Ai zaki ce hakan tun da kinga naji maganar har na tunka reki da ita.
Munazzafa tace kaina bisa wuya, ayi hak'uri k'anwa, tana maganar tana dariya.
Zarah tace jeki nemi k'anwar ki, wato tun yanzu za afara nuna min son girman.
Tayi dariya tace sosai ko.
Munazzafa tace ya kamata mu fara shirye_shiryen aure, kinga yanzu saura sati biyu fa.
Zarah tace in kin tashi saiki had'a da naki saboda Abba yace had'ewa za ayi.
Tace gaskiya ni ban shirya ba ad'an d'agamin k'afa saina ci bukin k'awata, inba hakan ba ai Zan takura.
Zarah tace sai ki gayama Abba don ba ni nace hakan ba.
Munazzafa tace Zan dai rok'i alfarmar *Reality* kuma zaisa Abba ya d'agamuna k'afa.
Tace a'ah *Royal* ba *Reality* ba, ai naga laila da majnun banji tsoro ba.
Munazzafa tayi dariya sosai, tace yarinya na tausaya miki da baki d'and'ani zumar *SO* ba.
Ke da kika d'and'ana kinji dad'i.
Munazzafa tace wai yaushe Angon namu zai zo ne inzo mugaisa?
Tace babu rana babu lokaci, aini wallahi ba a kyauta min ba, nasan sai naga wulak'anci ga wannan mijin.
Abba ya bada ni sadaka ai dole yaga cewa tamkar kwantai nayi, baida lokaci na, baida lokacin Kira na kota waya ne, nan ta fashe da kuka maicin rai.
Nan Munazzafa ta dawo rarrashi itama tamkar tayi kuka, saboda tana tausaya ma k'awar tata, har tana tunanin da akwai mafita data taimaka Mata.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
No comments:
Post a Comment