[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* 65-70
*BAYAN* *SATI* *UKU*
Yau ne dubban mutane suka shaida d'urin auren
*SHUREIM* *SULEIMAN*
*DA*
*LATEEFA* *ISMAIL*
Bayan d'aurin aure da shagul gulan biki Amarya ta tare a gidan angon ta.
Shureim yaso ya zauna part guda daga cikin gidan su, saidai Lateefa ta nuna cewa gaskiya bata iya zama gida guda da Mum, dole suka tare tasu anguwa daban.
Bayan masu kawo Amarya sun watse abokanen ango suka rako shi, bayan y'ar nasiha da tsokanar juna da suka yi nan Muftah ya rufe taro da addu'a.
Nan Shureim ya raka su suka wuce ya dawo ya rufe gidan.
Ya umurce ta data tashi ta d'auro alwala domin gabatar da nafila, bayan sun idar ya yima ta tambayoyi gwargwado ta kar6a wa'anda ta sani.
Nan ya fitar da kazar amarci suka ci saida sukayi k'attt (ina gefe ko taya ni basu yiba sai had'iyar yawu nake yi).
Da suka k'are ne suka yi wanka, su Lateefa Amarya sai tashin k'amshi ake yi, hakan suka zo suka kwanta saman gado Mai alfarma Shureim ya ja masu bargo.
(Koda na fito daga nawa wankan Shureim ya rufe k'ofa Ina waje, ```lolx```)
********************
*WAYE* *SHUREIM*?
Shureim d'a ne gun Alhj Suleiman da hajiya Safiya, Wanda shi kad'ai ne Allah ya k'addare su da haihuwa.
Ya taso cikin gata b'angaren iyayen shi duka, hakan bai hana mashi samun tarbiyya yadda ya Kama ta ba.
Yayi karatun shi na boko da Arabic duk a garin Jega, daga baya ne ya fita India ya had'a masters d'in shi b'angaren likita akan matsalolin Mata.
Yawancin abokanen shi sunfi kiran shi da S.S Kimba, wato Shureim Suleiman Kimba.
Kimba ta samo asali ne sanadiyyar k'auyen mahaifin shi, saboda Can ne tushen shi.
Alhj Suleiman da Alhj saminu sai Gwaggo Fati sune y'ay'an maigari, Wanda tun tashin Alhj Suleiman yake da sha'awar shiga jega ya siyo kaya yazo Kimba ya sayar.
Cikin hakanne Allah ya had'ashi da mahaifin Safiya wato Alhj Ilyasu, Wanda rik'on amanar shi yasa ya jashi jikin shi har ya zama tamkar d'an gida.
Daga hakan ne Allah ya had'a jinin shi da Safiya, saboda Mace ce Mai hankali da sanin ya Kama ta, kud'in Baban ta basu sa ta wulak'an ta mutum.
Hakan akayi auren su har zaman shi ya koma can Jega duka.
*****************
```Murtala``` kuma yaro ne gun Alhj saminu k'anen Alhj Suleiman, tun tashin shi yake d'an zama wurin Alhj Suleiman d'in.
Har ya fara Sana'a can sanadiyyar shagon sayar da yadukka daya bud'e Mai, sai dai yaje Kimba yayi kwana uku hud'u ya koma.
Baiyi karatun boko Mai zurfi ba, iya kacin shi primary da secondary.
*WASHE* *GARI*
Bayan tashin su daga bacci, Lateefa an yi wanka an fito tsab sabuwar Amarya. Mum ta aiko direban ta ya kawo musu breakfast.
Nan suka karya, sai bak'i ke zuwa masu ciki kuwa har da k'anwar ta Shema'u da kuma k'awar ta Shafa'atu.
Nan suka shige d'aki sai shewar su kake jiyowa.
*BAYAN* *SATI* *DAYA*
Suna zaune suna hira Shureim yace inaga yau ya kamata ki fara girki saboda Mum ta huta da kawo muna abinci hakanan, ko ya kika ce?
Tace ai inaga kabar shi kawai Mum ta rik'a aiko muna.
Nan ya bita da kallon mamaki yace ban fahimce kiba.
Tace ni gaskiya kasan ban iya shiga kicin girki saboda ban saba yi ba.
Shureim yace kenan Mum ce zata rik'a ciyar damu mu ko muna zaune gamu masu Uwa.
Da taga ya takura ta da magana, tace shikenan zata yi girki da dare d'in.
Hakan yasa yaji dad'i ya janyo ta saman jikin shi ya Kai Mata kiss.
Yau yana gidan Mum sai da akayi kiran magriba ya tashi yayi salla nan masallacin gidan shida Dad da Murtala, basu shigo gidan ba sai da akayi isha'i.
Nan Mum tace ko azuba abinci yaje masu dashi?
Yace basshi Mum nasan koda Zan koma Latee ta gama girki yanzu.
Nan Murtala ya shiga tsokanar shi kan cewa za aci abincin uwargida babu ko gayyata.
Yayi murmushi yace zaku ci saidai ba yau ba kam.
Hakan ya fita gidan ya biya ya siya musu kayan buk'ata, yana shiga gidan Lateefa ta tarboshi ta kaimai kiss, tace dear kafa dad'e a waje.
Ya bata amsa da cewa wurin Mum yaje shiyasa.
Nan suka shiga d'aki ta rage Mai kayan jikin shi ta had'a Mai ruwan wanka, koda ya fito ta fitar Mai da jallabiya Fara k'al ta feshe ta da turare, nan ya shirya suka fito falo sai danning.
Suna zama ta bud'e cooler ta zuba abinci ga filet, shiko yana waya da Muftah.
Yana k'are waya ta turo Mai filet tana murmushi, yana jawowa zai Fara ci, me zai gani.
(Fan's Ku taya ni addu'ar saduwa da rahmar ubangiji zuwa ga margyayi Babba *HASSAN*)
© *SDY* *JEGAL*
[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* *70*- *75*
Rayuwar Bahijja taci gaba da kasancewa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Tayi jikin ta na alamar akwai hutu tattare da ita ga kuma wayewa.
6angaren karatun ta kuwa ansamu cigaba, saboda har ta sauke k'ur'an, shima boko tana gab zana exam ta shiga secondary school.
Rayuwar su na tafiya cikin tsabta da girmamawa ita da Murtala, akwai fahimtar juna tsakanin su.
Yau ma kamar kullum bayan sun tashi daga bacci, sun gabatar da sallah Murtala ya koma bacci ita ko ta shiga kicin, saboda yanzu ta hutadda Mum da basu girki.
Kuma yanzu ta k'ware sosai gurin girki babu irin kalar girkin da bata iya ba.
Hakan ta shiga kicin ta yi masu kunun tsamiya, sannan ta had'a da k'osai don ta nik'a waken ta a blinder.
Gefe guda kuma ta had'a ma Murtala abinci Wanda zai je dashi shago, saboda in ya fita tun goma bai dawowa gida sai biyar na marece.
Sanadiyyar hakan ta hana Mai siyan abincin kasuwa sai dai ta had'a Mai tasa a basket yaje da abin shi.
Hakan ta kammala aikin ta zuwa karfe tara, ta shiga wanka saida ta shirya tsab cikin irin course d'in kwalliyar da Lateefa ta koya Mata.
Saboda ko wurin Mum Lateefa tazo to tana part d'in Bahijja suna hira, sai an gama a d'unguma akoma part d'in Mum.
Hakan ta do shi d'akin baccin su, nan ta Fara had'a ma Murtala ruwan wanka sannan tazo ta zauna gefen gado ta rik'a hura Mai iska a kunne kad'an-kad'an.
Jin hakan yasa ya tashi yakai duban shi zuwa gare ta.
Tace ruwan wanka na jiran ka, duba lokaci kagani ta nuna Mai agogon bango da hannun ta.
Nan take ya zabura ya fad'a toilet ko da ya fito ta fitar Mai da kayan da zai saka, a gurguje ya shirya ya fito nan ya zauna suka karya.
Ta d'auko Mai basket d'in abincin shi suka fito, ya shiga ya gaida Mum sannan ta raka shi mota ta saka Mai basket d'in abincin shi.
Ya bita da kallo yana saka Mata albarka yace gaskiya Ina ga alk'awarin da na d'auka na kusa sauke shi.
Nan tayi murmushi tace kasan dai muhimmancin cika alk'awari, hakan zaka jure saura k'iris.
Dole zaki ce hakan saboda baki da damuwa.
Nan ta bishi da gwalo ta ja da baya tana yimai bye-bye.
Tuna cewa akwai Wanda suka yi alk'awarin had'uwa dashi karfe goma, kuma ya ga goma saura minti bakwai yasa ya tayar da motar yana Mai d'aga Mata hannu.
Juya war da zata yi ta koma gida sai marar ta ta k'ulle, tun jiya take jin alamar hakan ju rewa ne kawai take yi.
Amma fa yau tafi jin abin na damun ta sosai, hakan ta daure taja jiki ta koma part d'in su da niyyar zata kimtsa wuri sai ta shiga gurin Mum.
Dak'yar ta Kai kan ta falo tana zuwa ta zube saman kujera sai juyi take yi.
Jin shiru har Murtala ya fita bata lek'o ba yasa Mum tace y'ar aikin ta taje part d'in ta ta duba Mata ko lafiya.
Koda ta shigo ta ganta k'asa sai juyi take yi, da sauri ta koma ta gaya ma Mum.
Koda Mum ta shigo ta ganta har ta Fara shiga hayyacin ta.
Nan ta tallabo ta ta rungume, tace Bahijja meke damun ki?
Ta kasa magana sai k'asan marar ta da take nuna Mata ga kuma hawaye duk sun wanke fuskar ta.
Nan Mum tace ma y'ar aikin ta Aisha Bizzy taje ta d'auko mata wayar ta.
Tana kawowa Mum ta kira Shureim tace Son plxxx kazo ka duba min Bahijja bata da lafiya.
Yace Mum gashi har na kawo asibiti Zan shiga, ko za azo da ita ne Dr Muftah ya duba ta?
Mum tace nasan da zaman Muftah na nemo ka, but in baka da time ka wuce kawai.
Jin ta kashe wayar kamar ranta a 6ace yasa ya juya akalar motar shi sai gida.
Yana shigowa ya Kira wayar Mum tana d'agawa tace kazo part d'in murtala.
Yana shigowa Mum tace Son ka duba min Bahijja Ina ga marar ta ke ciwo.
Hakan yazo ya duba ta duk ta fita hayyacin ta, nan take yaji tausayin ta ya tsirga Mai, koda yayi aune-aunen shi zai tashi kenan ya hango jini ta k'afar ta nan ya fahimci al'ada ce ta fara.
Yace Mum bara inje asbiti Zan aiko masinja na ya kawo Mata magani, kuma akwai allurar da za ayi Mata.
Mum tace to sai yaushe zaka dawo kayi Mata allurar?
Take gaban shi ya fad'i, shifa bai cika son kusanci da matar mutane ba, kuma daya gan ta gaban shi ke fad'uwa sai ya tsanan ta istigfari.
Maganar Mum ta dawo dashi hayyacin shi, yace Zan dawo in yi Mata, amma yanzu a taimaka agyra Mata jikin ta.
Yana shiga asbiti yaje pharmacy ya had'o magani da allura ya Kira wata nurse Jamila Muhammad Ali ya bata kud'i yace ta shiga napep taje gidan su zata yima k'anwar shi allura.
Su jamcy sai rawar Kai ake yi, dama ta dad'e tana shisshige ma Kimba, sai dai rashin samun fuska yasa taja baya.
Saboda Kimba akwai misk'ilan ci, ga yawan dizga mutum musamman Mata, saboda basu gaban shi.
Ga kwarji ni kullum kaga fuskar shi d'aure take.
Hakan ta fito tana taron napep sister Ummy ta ganta tace sai Ina haka?
Jamcy sai washe baki take yi, nan ta jero Mata labari.
Tana samun napep ta wuce sai gidan su Kimba, tana shiga Bizzy ta taso da nata rawar kan ta tarbo ta sai part d'in Bahijja.
Hakan ta shiga taba Mum maganukka har da pad ya had'o ita, nan ta had'a allura zata yima Bahijja, Mum ta Kai duban ta ga Bizzy tace to saiki fita kinzo kin tsare mutane.
Nan Mum ta rik'e Bahijja jamcy ta yi Mata allura ta wuce.
Mum ta yi Mata ihsani tana godiya.
© *SDY* *JEGAL*
[9:10PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* *75*- *80*
Shureim nakai duban shi zuwa ga abinci yaga indomie, nan ya maida duban shi zuwa ga Lateefa ita ko sai murmushi take yi.
Yace yanzu don Allah Lateefa indomie ce abincin dare?
Tace haba Kimba ai ko indomie ce abinci saboda ni ita nake ci da daddare in kwanta.
Yace amma ni dai kina zama gurin Mum kinsan favorite food d'ina.
Tace haba Kai ko Kimba ya Kama ta yada rayuwa ta canja abinci ma ya canja, kuma fa kasan ban girki ko a gida, yanzu ka takurani na yima duk da hakan banyi gwanin taba.
Ganin cewa ta 6ata fuskar ta yasa ya hak'uri ya janyo filet d'in, yana Kai lomar farko take ya zabura ya Fara lezaya amai tamkar zai amayar da hanjin shi.
Ita ko ta bishi da kallon takaici, to miye illar wannan abincin, gashi nima naci tawa har na k'oshi, don ma in k'ara gyra mashi ita har da k'wai na saka aciki, zancen da take yi azuciyar ta kenan.
A fili kuma ta taso tana yi Mai sannu had'e da tambayar miye?
Nan yakai duban shi gare ta yace yanzu fisabilillah Lateefa haka ake dafa indomie, kin tashi kin zabgama Abu tarugu haka, ga k'arnin k'wai na tashi, sannan kin cika gishiri.
Tace duk Kai ka jiyo wa'annan abubuwan ni dai naci abata lafiya lau.
Hakan yaja jiki ya shiga kicin ya had'a tea yasha, sannan yayi wanka yayi kwanciyar shi.
Jin shiru yasa Lateefa ta biyo bayan shi koda tazo har ya kwanta.
Hakan tazo kusa dashi ta kwanta sai k'amshi take zabgawa, tace Kimba kayi hak'uri kar ka fara kawo muna matsala a rayuwar auren mu.
Yace Lateefa matsala ta d'aya dake rashin kulawa ta 6angaren girki, ko so kike yi afara tsegumin cewa mijin ki na yawon restaurant?
Tace to kabari muyi ma Mum magana ta samo muna y'ar aiki.
Yace au bama ki koyi aikin ba sai dai anemo Mai aiki.
Tace gaskiya sai dai kayi hak'uri ni ban iya zaman shiga kicin girki.
Hakan suka yi ta rigima tsakanin su saida Shureim yace shikenan za asamo y'ar aiki d'in, nan suka shirya sai gashi anfara shan soyayya, nan na fito na janyo k'ofa har Ina cin Karo da k'ofa ```lolx```
******************
*WACE* *CE* *BAHIJJA*?
Bahijja d'iya ce gun malam salisu da Inna uwani.
Gwaggo lami itace Mace ta farko a wurin malam salisu, auren zumunci ne akayi dashi da ita.
Sun kusa shekara takwas da aure Gwaggo lami ko 6atan wata bata ta6a yi ba.
Daga baya ne Allah ya had'a malam da uwani wurin yawon saye da sayarwar shi ya had'u da ita can k'auyen raha.
Lokacin da yazo da maganar Gwaggo lami hauka ce kawai bata yi ba, duk iya abinda zata yi tayi amma kash Allah ya k'addari sai uwani ta shigo gidan.
Bayan anyi aure ne uwani ta tare, ta Fara cin karo da uk'uba hd'e da masifa gurin Gwaggo lami.
Amma fa duk abinda take yi bata yi gaban malam akan tsananin makircin ta.
Cikin hakan Allah yaba uwani ciki Wanda Gwaggo na hango hakan ta k'ara tsanan ta k'iyayyar ta had'e da takurawa zuwa ga uwani.
Ta yita samo abubuwa masu zubar da ciki tana bata har tayi nasarar zubar da ciki uku.
Akan Bahijja ne Allah yayi ikon shi da iyawar shi har aka haife ta.
Zun azab tu kuma sunga takura a hannun Gwaggo, har uwani ta had'u da ciwon hawan jini Wanda yayi ajalin ta.
Koda ta rasu Bahijja nada shekara uku da haihuwa, y'an uwan uwani sun so su kar6e ta malam ya basu hak'uri ya rik'e abar shi.
Tun tana da shekara biyar ita ke ebo ruwa rafi ta cika duka kayan gidan.
Lokacin har islamiya malam ya saka ta cikin makircinta ta janye Bahijja daga zuwa makarantar saboda yawon talla.
Ta boko ma malam yaso ya saka ta Gwaggo tace makarantar y'an iska ce.
Hakan ya hak'ura ba don baya so ba sai don baya da yadda zai yi ne.
Akwai lokacin da yayan uwani yazo duba Bahijja ya d'an yi Mata siyayya, nan Gwaggo ta kar6e kayan ta k'ona su, kuma ya nemi alfarmar zuwa da Bahijja ta yi masu kwana biyu Gwaggo ta hana saboda lokacin malam bai gari.
Hakan Bahijja taga renon azaba hannun Gwaggo har zuwa yanzu da aka yi Mata aure tana da shekara goma sha hud'u.
© *SDY* *JEGAL*
Thursday 6 October 2016
BAHIJJA 65-70
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment