[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 3⃣1⃣/3⃣2⃣
*BAYAN SATI BIYU*
Idan da sabo to yanzu sun yi sabo da juna ita da Musirrah har sun zamo tamkar k'awaye, saboda akwai lokacin da Musirrah ta ajiye mata waina ta d'ari hud'u akan tunanin kar tazo ta tarar ta k'are, har ta gaji da jira ganin lokacin da take zuwa ya wuce yasa ta sayar sai kuma gashi ta zo babu wainar tamkar tayi kuka. Nan Musirrah ke bata hak'uri har ta d'ora da cewa bara in baki lambata kinga ranar da duk kike so sai ki kira ni in ajiye maki da hakan suka kai k'arshen wannan matsalar wanda sanadiyyar hakan yasa ko bada siyen waina ba suna gaisawa da juna ta waya har ta ba Ammi waya su gaisa.
A gefe d'aya ko in dai har zata je siyen waina to k'afar ta k'afar Haydar, har sun d'anyi sabo da Musirrah suna gaisuwar mutunci duk da cewa ba wani surutu ne da ita ba. Tun yana 6oyewa Mukarrama yana son Musirrah har ya fito ya gaya mata gaskiyar magana wanda suke ta shawarar ta wace hanya zasu 6ullowa lamarin.
Yau haka Kawai ta saka ma ran ta ba zata je siyen waina ba har sai ta kwatanci cewa ta k'are, saboda tana so ta shiga yau har gidan su Musirrah d'in don duk abinda suke yi iya k'ofar gida ne sai kuma waya.
Da sallamar shi ya shigo falon tana zaune tana latse-latsen waya ya ce' " k'anwa yau ba zuwa siyen waina?". Abinda nake tunani kawai mu bari sai mun kwatan ci wainar ta k'are sannan muje, saboda yau ina so mu shiga har gidan su". Eh to kin kawo shawara, amma fa ki rufe d'ayan wayar taki saboda kar ta jiki shiru ta kira wayar ki", da hakan suka kai k'arshen maganar tasu.
Sai 12:00pm sannan suka shirya motar Haydar suka shiga, sai da suka biya aka yiwa Musirrah shopping sannan suka d'auke hanya sai gidan.
Bayan sun iso k'ofar gidan ne Haydar ya tsaya daga waje ita kuma ta d'auki kaya nik'i-nik'i ta shiga gidan da sallamar ta, Musirrah na shara filin gidan ta ajiye tsintsinya ta taryo ta, bayan ta yi mata shimfid'a daga waje ta shiga d'aki ta kira Ammi saboda akwai zafi kuma gashi ba nepa.
Fitowar Ammi kenan ta samu guri ta zauna suka gaisa ta ce' "ke ce sarkin cin waina ko?", nan Mukarrama ta yi murmushi ta nok'e kai.
Musirrah ta ce' "ina fatar ba ita kika zo siya ba, saboda har wayar ki na kira bata zuwa". Wallahi kedai tana gida na barta unguwa muka fita nida Bross shiyasa na ce mu biyo in baki hak'urin rashin gani na", yanzu ta re da yayan naki ki ke kika baro shi daga waje, je ki shigo dashi mana", cewar Ammi.
A can waje kuwa Mubarak ya zo shigewa ya ga mutum zaune cikin mota ya fitar da k'afarshi d'aya daga motar yana sauraren wa'azin Mal Ja'afar Mahmoud Adam kano, har ya je shigewa sai Haydar ya yi mai sallama nan ya tsaya suka yi musabaha tsakanin su had'e da gaisawa. Nan Haydar ya yi mai bayani cewa ta re da k'anwar shi yake tana daga ciki, suna hakan ne sai ga Mukarrama ta zo kiran shi nan dai suka garzaya cikin gidan gaba d'ayan su.
Bayan gaishe-gaishe tsakanin su Musirrah ta mik'e domin zuwa d'auko masu ruwa nan Haydar ya bita da kallo, sai tunani yake yi a ran shi dama haka take, ashe lokacin don tana daga zaune ne sai yanzu ya ga asalin kyawon ta, saboda zai iya cewa yadda k'irar ta take ta mafi fuskar ta d'aukar hankali, gashi tana da tsayi da jiki sai dai ba sosai ba (sauran na barwa masu karatu su k'arasa siffanta surar Musirrah, *lolx*)
Sai da Mukarrama ta zungure shi sannan ya dawo hayyacin shi, sai yaga ashe har ta kawo ruwan Mukarrama ta tsiya ya a cup tana mik'o mai shi yana can duniyar tunani.
Nan ya rik'a sosa kan shi na alamar jin kunya musamman da suka had'a ido da Mubarak, hakan ya kar6i ruwan hannun Mukarrama ya sha.
Mukarrama ta mik'e ta ajiye kayan da ta shigo dasu gurin Ammi ta ce' "to mu Ammi za mu wuce sai mun sake zagayowa", nan Ammi ta yi godiya had'e da sanya masu albarka. A ta re suka ta shi domin ta kamasu waje, bayan sun fito ne su hud'u sun zo gurin mota, nan Haydar ke ta yiwa Mukarrama alama kan cewa ta furta ma Musirrah yana son ta, ita ko sai kauda kai take yi tana dariya ciki-ciki har suka yi sallama suka juya domin shiga gida.
Nan dai yaga cewa in har ya bari wannan damar ta wuce shi ya cuci kanshi tunda yaga Mukarrama bata da niyyar fad'a, har Musirrah ta shige Mubarak ne daga baya nan ya kira sunan shi ya k'arasa k'ofar gidan hakan ya cije ya daure cikin jin nauyi ya yiwa Mubarak bayanin k'udirin shi akan k'anwar shi.
Can gefe kuwa dariya ta yiwa Mukarrama yawa nan ta fad'a mota tana jiran shi don ta san yau had'uwar ta dashi akwai rigima, hakan ta han gosu suna musayar lambobin juna.
Bayan sun k'are ne ya nufo motar ya zaga mazaunin direba ya tada mota har lokacin bai ce da ita uffan ba, nan dai ta yi k'arfin hali ta ce' "Bross ya kuka yi da yayan Musirrah?".
Mugun kallon da ya sako Mata ne yasa ta ja bakin ta ta tsuke, dama tasan a rina an saci zanen mahaukaciya.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 3⃣3⃣/3⃣4⃣
Da shigar shi gidan ko zaune bai kai ba yake gayama Ammi sak'on Haydar, abinda ya yi tunani na murna da farin ciki sai ya ga sa6anin haka saboda damuwa ce k'arara a fuskar ta.
Ya ce' "Ammi meke faruwa naga kin shiga damuwa?" Tunani na d'aya ne ta wace hanya zamu bi domin binciken waye shi", haba Ammi ba ma tunanin binciken namu asali kike yiba, sanin waye su ba zai yi wuya ba cikin sati d'aya zan yi in k'are".
Ta ce' " to yanzu kaje har ka k'are bincike akai zan yi nazarin miye mafita", Musirrah na d'aki tana sauraren su ta yi tamkar bata San maganar miye suke yiba.
Nan ya ce' "Ammi ina tunanin an kusa dacewa da aikina, saboda na had'u da wani abokina d'azu munyi magana ya ce zai yiwa Baban shi magana inshaAllah za'a samo min aiki, don har na bashi copy d'aya na takardu na". To ubangiji Allah yasa a dace" nan ya amsa da ameen".
*BAYAN KWANA UKU*
Sayar da wainar take yi amma gaba d'aya hankalin ta bai gurin ta, saboda yau kwana uku kenan bata ga mutumen da ta mak'alawa kurma ba, ko yaushe zura ido take yi taga ta ina zai 6ullo amma shiru kake ji tamkar an shuka dusa, hakan dai ta natsu ta yi Sana'ar ta wani gefe kuma tana tunanin me yasa ta damu da mutumen da bata san waye shi ba, tana hakan ne ta ji k'arar wayar ta koda ta d'auko ta ga sabuwar lamba hakan ta bita da ido har ta tsinke, sai da akayi kira uku a na hud'u ne ta d'aga da sallamar ta cikin zazzak'ar murya ta.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya uhmm! sannan ya amsa sallamar.
Sai da ya gaya mata shine Haydar sannan ta d'an saki fuskar ta suka gaisa sama-sama, har yake tambayar ta ta ji sak'on shi gurin Mubarak, nan dai ta ce yayi hak'uri in ta shiga zasu yi magana da hakan ta ajiye wayar ta koma kan sana'ar ta.
<<< >>> <<< >>>
Yau tun safe gidan nasu ake ta hada-hadar girki da kuma kayan motsa baki, sanadiyyar abokin Dad da zai zo gidan wanda rabon dasu had'u tun shekara kusan 28 da suka wuce sai ga shi Allah ya had'a su kwana uku da suka wuce wurin shirye-shiryen bud'e company na wani abokin su, inda Alh Abubukar gaba d'aya bai gane Alh Farouk ba sai dai zuwa-zuwa zai ga da ya tayar da kanshi zasu had'a ido da mutumen sai yayi sauri ya kauda kan shi har dai aka k'are taron suka fito, nan Alh Farouk ya kasa hak'uri ya je yaba Alh Abubakar hannu suka gaisa. Ya ce' "suna na Alh Farouk mai fata, kai ko Alh Abubakar ma'aji jin ya fad'i tsohon sunan da sai friends d'in shi na can baya suka sanshi dashi yasa nan ta ke ya tuno da Alh Farouk.
Nan suka k'ara gaisawa da juna had'e da murnar had'uwar su, saboda hakane suka bawa juna address har takai yau Alh Abubakar ya kira zasu kawo mai ziyara shi da iyalan shi.
Bayan an k'are shiryar da komai ne kowa yaje ya yi wanka ya kimtsa ana zaman jiran k'arasowar tsohon abokin k'urciya.
(Kuyi hak'uri da wannan wallahi hannuna ke ciwo)
_SDY_ _JEGAL_
Sadiyajegal.mywapblog.com
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 3⃣5⃣/3⃣6⃣
Suna k'arasowa gidan da murnar Haj Zainab ta fita ta taryo Haj Aisha saboda ga wancan lokacin batada k'awa sama da ita, bayan an k'are gaishe-gaishe da murnar ganin juna kuma anci an k'oshi nan aka fara hirar yaushe gamo.
Nan Alh Abubakar ke gayawa Alh Farouk cewa lokacin da yana zuwa garin kurmi Sana'a ta re da wani uban gidan sa har Allah ya d'auka kashi yana zuwa shi kad'ai ya dawo sai dai a cikin kud'in Sana'ar akwai jarin mutane da dama ga wancan lokacin da yake zuwa dasu wanda daga baya Allah ya had'ashi da y'an fashi saman hanyar shi ta zuwa kurmi d'in suka ya yemai duk dukiyar da ya je da'ita. Dak'yar ya samu kud'in dawowa nan garin su, bayan abubuwa sun yimai zafi ne mutane sun sakashi gaba kan kud'in su yasa ya gudu daga Birnin kebbi ya dawo Jega Wanda ya dad'e yana 6oye kanshi saboda gudun had'uwa da idon sani, "daga baya ne na samu wani uban gida dake zuwa sokoto ina biyar shi har Allah ya bud'a min tawa hanyar, sai bayan na samu kud'i ne na je Birnin kebbi na biya way'anda ke biya ta kud'i duk da wasu lokacin basu raye sai dai yaran su, ka ji tak'aitaccen tarihi na bayan rabuwar mu".
Nan shima ya bashi nashi tarihin a tak'aice ya d'ora da cewa nayi aure na biyu bayan tafiyar ka sai dai Allah ya yiwa matar rasuwa ita da yaron ta yanzu yara na hud'u, Jameel ne babba yana Cairo wurin masters d'in shi shida matar shi, sai Rukayya itama ta yi aure da yarinyar ta d'aya, sai Aliyu Haydar da Auta Mukarrama.
"Masha'allah Allah ya ra yamuna su akan tafarkin islama, way'anda suka riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta musu", nan Dad ya kar6a da Ameen ya d'ora da cewa yaran ka nawa halan?".
Ka gan su nan Nibras da Iman sai yayan su Mus'ab, yanzu haka daga nan za mu wuce asibiti ne gurin shi yau kwanan shi uku can saboda typhoid dake damun shi".
Haba Alh yaro baida lafiya Ku bar shi asibiti Ku fito yawo, ai da ka gaya min da sai mu muje duba jikin shi", ai jikin na shi da sauk'i saboda Nibras ke kwana gurin shi da shida wani abokin Mus'ab d'in, to shi ya dawo gida ne yayi wanka shine muka fito ta re sai mu wuce daga nan, cewar Alh Abubakar".
Ya ce'
"Mu ma bamu ga ta zama ba Ku ta shi muje gaba d'aya mu dubo jikin shi".
Haka suka d'unguma sai asibitin uduth ko da suka je jikin na shi da sauk'i sosai, nan Alh Farouk ya ce' "kenan Mus'ab shi da Haydar babu mai tunanin aure cikin su", ai ni tun ina matsawa Mus'ab maganar aure har na zuba mai ido don ma bai dad'e da dawo wa daga India ba kusan shekarar shi takwas can Saida ya had'a masters d'in shi 6angaren likita sannan ya dawo, saboda da degree da masters duk can ya yisu sai dai yad'an dawo hutu ya koma".
Nan Mukarrama ta yi karaf ta ce' "Baffa shi kam Bross ya samu mata", nan Alh Abubakar ya ce' "da gaske ne yaro na?", yana maganar da murmushi a fuskar shi.
Ya ce'
"Baffa zan zo in sa meka har gida gobe", nan kowa ya yi dariya, hakan suka kasance cikin walwala da farin ciki har azahar sannan su Alh farouk suka wuce gida.
<<<< >>> <<< >>>
Wuraren k'arfe biyar Mela ta iso gidan su Musirrah da murnar su suka taryi juna, bayan ta raka ta ta gaida Ammi ne suka koma d'akin yaya Mubarak nan suka fara hira.
Mela ta ce'
"Baki ajiye min waina ba ko?", wainar da ke k'a rewa tun 11:00 tsanani ta kai 11:30, ai ke k'awas ni wannan wainar ta zamo min jaraba, nan ta kwashe maganar Haydar ta gaya mata da kuma mai zuwa siyen waina fuska rufe , ta d'ora da cewa yau kwana hud'u ban saka shi a ido ba na rasa me yasa na damu Inga fuskar shi, kuma nafi kyautata zaton mutumen kurma ne saboda bai ta6a magana ba".
Mela ta ce'
"Kawai kice kin fad'a tarkon son wani na daban, har Haydar ya bani tausayi".
Ni fa ban ce maki ba na son Haydar ba, saboda mun shak'u cikin k'an-k'anin lokaci har ina ji babu wanda ya isa ya raba ni da shi, ya zama jinin jiki na".
Mela ta yi dariya sosai ta ce' "su soyayya manya, Allah yabar laila da majnun", suna cikin hakan ne sai ga kiran Haydar ya shigo bayan sun gaisa ne ta bawa Mela waya, hakan ta yita tsokanar shi tamkar dama can sun yi sabo da juna.
_SDY_ _JEGAL_
Sadiyajegal.mywapblog.com
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 3⃣9⃣/4⃣0⃣
Duk inda ake tunanin shak'uwa tsakanin Haydar da Musirrah to abin ya wuce nan Wanda ta kai yanzu har ciyar war su tamkar ya dawo saman kan shi, saboda lokacin da yasa aka kawo kayan abinci gidan way'anda zasu fi wata d'aya basu ne mi koda gishirin miya ba sai da Ammi ta saka shi gaba tana ta yi mai fad'a kan cewa bata son hakan da yake yi ga shi har yanzu magabata basu shiga maganar shi da Musirrah ba, saboda haka komai kar ya k'ara ka wowa gidan kar ya janyo mata zagi ga mak'wabta amma duk da hakan tamkar Ammi ta k'ara zuga shi ne kan wasu abubuwa.
Don yanzu haka sai da ya yi bincike ya san waye maigidan da suke haya a ciki har sun yi cinikin gidan ta re da shaidu, yanzu haka takar dun gidan na hannun shi yana tsoron kawo masu ne Ammi tayi fad'a shiyasa ya ajiye hannun shi har sai an kai k'arshe kan maganar auren su.
Yanzu ma halin da ake ciki ya yi tsaye kan cewa gaskiya bai yarda da Sana'ar waina ba kowa na gane mai mata a cewar shi, nan dai Mubarak ya bada shawara kan cewa a mayar da Sana'ar cikin gida ko ma a canja Sana'a saboda zama gurin wuta ko yaushe nada matsaloli da dama. Nan dai suka yanke shawarar ajuya kud'in 6angaren siyar da kayan miya irin citta, daddawa, magi, gishiri da sauran su da hakan Mubarak ya kar6i kud'in ya siyo aka fara.
6angaren Musirrah kuwa har ga Allah bata ji dad'in sana'ar ta ta waina da aka hana ta ba, babban tunanin ta ina zata k'ara ganin kurma saboda taso ko ya ya ne taga ya fuskar shi ta ke, kuma bata ta6a ganin shi a tsaye ba sai dai saman mashin amma duk da hakan ba zata gaza siffan tashi kad'an ba, domin daka gan shi kaga mutum mai k'arfaffen jiki kuma bazai rasa tsayi ba, duk yada ta so ta siffan ta fuskar shi sai abin ya gagara.
Da haka ta zabura ta d'auko wata hand bag d'in ta ta d'auko short note d'in da yake rubutawa ta tsura masu ido, duk da ba wani dogon rubutu ne a ciki ba amma bata gajiya da kallon hand writing d'in sa tamkar mai karanta wata doguwar wasik'a mai tattare da kalaman soyayya masu sanya ya zuciya.
Jin motsin cewa Ammi zata shigo ya sa da saurin ta ta had'a takardun ta mayar dasu. (Ni dai Jegal na tausayawa Haydar, Allah yasa ba irin na gangar jikin sa na aura za'a yi ba, na JUT. _lolx_)
Yau kwanan shi biyu kenan ko ya zo k'ofar gidan wayam yake gani Wanda ke nuna alamar an daina wata Sana'a gurin, yana wannan tunanin ne wani yaro ya zo gilmawa nan ya kira shi yake tambayar shi ina mai siyar da waina nan gurin?", da bud'ar bakin yaro ya ce' "ai mijin ta ya hana mata Sana'ar waina", what!" Ba yaron ba ko ni kaina sai da na tsora ta, baya-baya yaron ya rik'a yi sannan ya tattara rigar shi ya zura da gudu saboda ya zata dukan shi zai yi.
Ya fi k'arfin minti goma gurin yana tunani a ran shi da ma yarinyar tana da miji ne? Ko kuwa sati d'ayan da ya yi bai zo bane ta samu miji har aka yi mata aure? To ko dai mijin da ke neman tane ya hana mata sana'ar? Duk wa'annan tambayoyin ya kasa sanin waye zai bashi amsar su, ga shi ya tsora ta yaron ya gudu barrantana ya samu k'arin haske daga gare shi, gashi unguwar yanzu tamkar anyi ruwa an d'auke har wani zazza6i yake jin na shigar shi kad'an kad'an, hakan ya daure ya ja mashin d'in shi ya wuce cikin rud'a ni da tashin hankali.
<<< >>> <<< >>>
K'arfe biyar na yamma. ya shirya shi da wani abokin shi Alh Sani suka do shi unguwar su Musirrah, basu tsaya ko ina ba sai k'ofar gidan saboda address d'in da Haydar ya bashi kenan. Nan suka samu yaro suka ce ya yi masu sallama da mutumen gidan, yaro ya shiga ya fito ya ce' "wai ga shinan zuwa", nan Alh ya ciro naira d'ari ya baiwa yaron ya wuce yana ta murna. Ko da ya fito sun juya baya Alh Sani na nu nawa Baffa wani fili yana yi mai bayani kan cewa shi ne yake ciniki yana son sayen shi in har sun dai-dai ta da mai filin.
Sallamar da suka ji bayan su ne yasa Baffa ya juyo da k'arfi saboda ba zai ta6a man tawa da muryar ba, karaf idon su suka had'e guri d'aya kowannen su ya ka sa magana illa Baffa dake nuna Mubarak da d'an yatsan shi, kad'an -kad'an Mubarak ya rik'a ja baya shi ko Baffa yana girgiza mai kai had'e da nuna shi da yatsa amma ya ka sa furta uffan. Nan ta ke wulak'an ci had'e da korar Karen da Ummy ta yi masu ya dawo mai sa bo k'al a cikin k'wak'wal war shi, ya ga cewa har ga Allah ba zai iya zama da mutum mai halin k'yashi irin ta ba, da saurin shi ya fad'a gidan ya turo k'ofa.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 3⃣7⃣/3⃣8⃣
Kamar yadda Haydar ya yi alk'awari cewa zai je ya gaya wa Baffa yarinyar da yake so to haka ya kasance saboda tun safe yake ta shirye-shirye tamkar wanda zaije gurin wani ga garumin aure, haka ma Mukarrama ta shirya ta fito ya kai duban shi zuwa gare ta ya ce' "ke ina zaki je?", zan raka kane in yiwa Baffa bayanin yarinyar da kake so".
"OK ai ban San kin iya bayani ba sai yau, da yake ranar kinso muguntar ki ina ta yi maki alama ki isar da sak'o na gurin Musirrah kika mayar dani wani sha ka wuce, sai yau don yana gulma zaki ce wai zaki rakani ki yiwa Baffa bayani, to don Allah in kika rakani kar ki yiwa Baffa bayani ki dak'ushe maganar in kinsan yadda zaki yi, algunguma kawai".
Duk yada ta so rik'e dariyar ta sai da ta ku6uce mata nan abin ya k'ara k'ular dashi ya biyo ta zuwa duka sai ga Haj ta kawo nan ta 6uya bayan ta.
Ni fa masifar ku ta fara damuwa ta ku ba k'ana nan yara ba amma kullum cikin hayaniya, me ya had'a ku kuma yanzu?".
"Wai fa Haj daga na ce zan raka shi ya gaya wa Baffa wacce yake so shine kawai zai dakeni".
Haj ta ce' "ni kin ma tuna min, ku zo mu zauna a gaya min y'ar gidan wa ye za'a kawo min suruka, saboda yadda kuke da halin k'aranta komai naku tamkar ba d'iyan kowa ba to ban son kuje Ku kwaso min d'iyan k'ana nan mutane".
Tunawa da yadda Dad ya so Jameel ya auri y'ar k'anen shi wato Yasmeen abin ya gagara shi ya kayar mai da gaba yanzu, saboda daga Birnin kebbi in Yasmeen ta samu hutu takan zo sokoto hutu gidan su, ta so Jameel tamkar ranta amma Haj da Jameel suka k'ek'ashe k'asa ba zai yi auren k'aranta ba, inda har takai rigima ta shiga tsakanin Haj da Dad sai da Baban Yasmeen ya kashe magana inda ya yita luradda Dad kan cewa ba'a yiwa namiji auren dole, hakan ya janye maganar har aka yiwa Yasmeen aure da wani Kabeer dake mutuwar son ta acan B.k, shi ko Jameel ya auri wata Badi'at da suka yi karatu ta re. Wannan tashin hankali da ya tuna yasa ya kasa magana sai dai kallon-kallo tsakanin shi da Mukarrama.
Nan ta mik'e ta ce' "Haj bara mu dawo zan gaya maki ko ita wacece, ta kai duban ta ga Haydar muje ko Bross", da saurin shi ya mik'e suka wuce. Har ya manta da fad'an da suke yi don shi har zufa ta fara karyo mai.
<<< >>> <<< >>>
A can cikin mota ko Mukarrama ta kai duban ta zuwa ga Haydar ta ce' "ni dai tsoro na d'aya Allah yasa wannan Musirrah na da asali", mugun kallon da ya mata ne yasa ta yi shiru ta soke kai, ban ga ne me kike nufi da tana da asali ba, kenan kina nufin kice min shegiya ce". Cikin 6acin rai yake sako mata maganar, "wallahi ba hakan nake nufi ba, ina ganin na ma fika jin wannan yarinyar a raina, abinda nake nufi ina fargaba ne kan ina dangin su, saboda in har zaka lura tun ranar da muka fara ganin su bamu ta6a ganin wani makusan cin suba, daga su sai mahaifiyar su suke rayuwa".
Jin maganar da ta yine ya sa duk jikin shi ya yi sanyi, saboda har ga Allah bai ta6a lura da wannan abin ba sai yanzu da ta yi maganar. Nan dai ya sauke wata irin ajiyar zuciya uhmmm!, ya kai duban shi zuwa ga Mukarrama ya ce'
"Wallahi wannan yarinya ko da ace shegiya ce Allah kawai zai hana min auren ta, saboda bazan iya furta maki yadda nake jin ta a raina ba", "kabi abin a hankali saboda ka san ko Haj rigimar ta ba k'arama bace wadda ta guji talaka ina ce ga wanda ba'a san wa ye shi ba, kawai dai mu yita addu'a da fatar abinda muke tunani ba haka bane".
Nan dai suka ka wo gidan jikin kowa a mace, bayan sun shiga ne anyi gaisuwa da kuma d'an ta6a hira duk da ba wani sabone tsakanin su ba, sai dai iyayen surutu ne suka k'arfafa hirar wato Iman da Mukarrama saboda kowanen su ba baya ba gurin surutu barranta na Iman dake ganin Mukarrama tamkar Musirrah d'in tace ta dawo.
Nan dai Baffa ya kalli Haydar ya ce' "ina jinka yaro na gaya min inda ka samo muna suruka", Haydar sai murmushi yake yi yana nok'e kai, "to ta shi muje falo na kagaya min don naga k'annen ka da Haj sun saka muna ido dayawa", Baffa yana maganar d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar shi.
Bayan sun koma falon Baffa ne ya zayyane mashi komai da kuma address d'in gidan su, Baffa ya ce' "zan je in bincika inshaAllah".
Da hakan suka kai k'arshen magana inda suka fito shi da Baffa suka zube falo ana ta hira.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
No comments:
Post a Comment