Thursday 6 October 2016

BAHIJJA 125-130

[9:11PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* *125*- *130*
Bayan sun huta ne Bahijja tace yaje kawai ita gurin Mum zata kwana saboda tayi kewar Mum.
Shi ko Shureim yace sai dai su kwana gidan gaba d'aya kuma a part d'in shi.
Jin hakan yasa Mum tace su kwashi kayan su wuce gidan su.
Bahijja na kumbure-kumbure ta shirya suka wuce, suna cikin mota sai tsokanar ta yake yi yana cewa haka kawai ki k'yale bawan Allah shi kad'ai ki je ki mak'ale gurin Mum.
Tana murmushi tana binshi da harar wasa, da hakan har suka Kai gidan.
Lokaci guda zuciyoyin su suka rik'a bugawa da k'arfi saboda abinda suka ci Karo dashi cikin falo, wato Lateefa zaune tana kallo.
Da murnar ta tazo ta rungumeshi ta Kai Mai wani irin kiss Mai nuna alamar tayi kewar shi.
Hakan ya tarye ta cikin murnar shi ta nuna shima yayi missing d'inta.
Maganar Bahijja ta dawo dasu daga duniyar da suka Lula, cewar da tayi Anty Ina wuni, da fatar mun same Ku lafiya, cikin muryar ta Mai fargabar wace irin tarba zata yi Mata matsayin ta na kishiyar ta yanzu.
Muguwar hara rar da ta bita da ita ne yasa dole ta soke kan ta.
Tace da ban wuni ba zaki ganni?
Tunda kin za6i zaman kishi dani sai kizo mu gwabza, banza kawai y'ar talakawa y'ar masu neman maula.
Nan take idon ta suka kawo ruwa cikin k'unar rai ta wuce ta nufi d'akin ta.
Shureim ya Kai duban shi ga Lateefa yace wannan kuma shine miye?
Ina hankali da nutsuwa had'e da taimakon marasa shi da kike da?
Yau har kece zaki kalli wani ki Kira shi da Kalmar matsiya ci.
Gaskiya kin ban mamaki, duk ina so kulawa had'e da tarairaya da kike nuna ma Bahijja, yau koni bazan gaya maki halayyar Bahijja ba saboda kin fini sanin waye ita.
Kin sha muna hira kina bani labarin ta da kuma yabon halayen ta na Kirki da girmamawa.
Nan ta nisa tace nidai muje kayi wanka kazo kaci abinci saika huta.
Jin wucewar su d'akin shi yasa damuwar ta ta tsananta, lallai tsakanin Mata da miji sai Allah, kuma dole ta sakama zuciyar ta hak'uri da dangana akan duk abinda yazo Mata, Wanda ya zauna da Gwaggo wace irin hantara ce bazai iya d'auka ba.
```BAYAN``` ```SATI``` ```DAYA```
Zaman su na nan ba yabo ba fallasa gwargwado Bahijja na bawa Lateefa girman ta yadda ta saba fiye da wancan lokaci.
Yau ma a daddafe ta gama abincin rana saboda tun safe take jin alamar zazza6i ga kuma tashin zuciya.
Tana kammalawa ta jera a dinning table taje tayi wanka.
Saboda duk da masifar Lateefa tare suke cin abinci har Shureim don ya tsayu da gidan sa yana d'ora doka kuma dole abita.
Hakan suka zauna cin abinci har suka k'are ba magana saboda da Shureim ya Fara hira zata ce ya karkata hankalin shi ga Bahijja.
Suna k'are cin abinci ta shiga d'akin ta ta fad'a toilet sai amai, jin k'arar aman ne yasa Shureim ya bita d'aki ya shiga toilet ya tallafota yana fad'in Heeja mike damun ki? Abincin ne ba kyaso?
Bayan ta gama ne ya d'auko ta ya dawo d'aki da ita yana rungume da ita.
Kawai jin amai yayi saman jikin shi, kuma so take ta k'wace jikin ta daga nashi.
Nan ya ajiye ta saman gado ya gyra Mata jikin ta ya cire kayan jikin shi ya saka a Wash machine.
Cikin k'ank'anin lokaci Bahijja ta fita hayyacin ta duk rashin imanin ka zaka tausaya Mata in ka ganta.
Cikin kwana biyar ta koma wata iri ba ci ba sha kullum amai ga k'arin ruwa da Shureim ke yimata kusan kullum, Mum taso ta dawo gurin ta Shureim ya hana yace zai kula da ita duk da yanayin aikin shi sai dai ya sakar ma Muftah ayukkan office.
Blkisu ma tazo ganin ta Karo biyu duk anan take wuni sai Muftah ya taso daga aiki ya biyo ya wuce da ita.
Yau ma Shema'u ta zo ma Lateefa wuni ganin shige da ficen da ake yi d'akin Bahijja yasa tace Anty hala meke faruwa?
Ta ta6e baki tace wai bata da lafiya ne, nifa rabon in saka ta a ido na tun ranar da tafara ciwon ta na k'arya.
Shema'u ta mik'e ta nufi hanyar d'akin Bahijja.
Lateefa tace Ina zaki je?
Tace Zan shiga in duba jikin ta ne, sanin cewa Shema'u akwai kafiya yasa ta k'yale ta.
Tana shiga d'akin ta Han gota kwance an sa kamata drip ga Aisha Yagani kusa gareta.
Nan ta gaishe ta da jiki abin gwanin tausayi ko magana bata yi duk ta jeme.
Tana fita ta taradda Lateefa ta koma d'aki, nan ta bita tace Anty yaushe tausayin ki da imanin ki suka ragu?
Don Allah ki taso muje kiga Bahijja wallahi abin gwanin tausayi.
Da k'yar ta shawo kanta sannan suka tashi sai d'akin Bahijja.
Tana shiga d'akin ta dask'are inda take, har ga Allah bata zaci ciwon nata yakai haka ba, kuma ta tausaya Mata over.
Da saurin ta takai gurin da take ta tallafota saboda drip d'in sun k'are an cire, tace Sister haka kika koma?
Me kike so Wanda Zan dafa maki kici ya tsaya maki?
Zaki ci d'an wake? Duk tana tambayar ne tana hawaye saboda Lateefa akwai rauni gare ta.
Ta Kai duban ta ga Shureim tace yanzu Kimba haka Sister ta koma ba a kaita asibiti ba?
Yayi murmushi yace kin manta nine asibiti gaba d'aya, dama ciki ne da ita yake wahalar da ita.
Nan ta Kai duban ta ga Bahijja da murmushi a fuskar ta, har ga Allah tana jin tausayin ta yadda ta koma, dama shaid'an ke k'ara ingiza ta abubuwan da take yi Mata.
"Da saurin ta taje kicin ta d'ora ruwa ta Kira Shema'u ta taya ta don tana da garin wake da Mmn Zahra ta bata kwanakin baya.
Cikin minti ashirin Lateefa ta had'a ta Kai mata, kuma cikin ikon Allah taci kad'an ya tsaya Mata taji dad'i har cikin ranta.
Yau Baban Bahijja ya shirya zuwa godiya ya gayyaci abokin shi malam Ado suka je tare.
Bayan sun iso ne Mum ta shirya musu abinci suna ci suna hira.
Malam salisu ya yi mashi godiya har da guntun hawayen shi.
Alhj yace haba salisu miye haka, har yaushe Zan gaya ma cewa an zama d'aya.
Ya d'ora da cewa ni garin nan ma naso in baka d'aya daga cikin gidaje na, sanin hali yasa na gyrama naka.
Nan suka yi dariya malam salisu yace lallai kam banga abinda zai rabani da k'auyen mu.
Alhj ya yi murmushi yace sai ka biya kaga d'iya ta tana jin jiki, saboda na kusa Kai ga jika.
Malam yayi murmushi yace ko dai na kusa Kai da jika ba, don 6angaren namiji sunfi k'arfi, nan suka yi dariya su duka.
Kai tsaye suka biya suka ga Bahijja, lallai tana jin jiki gaskiya, nan ya yi Mata addu'a suka wuce har k'asan zuciyar shi yake tausayin yadda laulayi ya maida ita.
Nan suka Kama hanya sai garin su Kimba.
© *SDY* *JEGAL*
[9:11PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* *130*- *135*
*BAYAN* *SHEKARA* *HUDU*
Shureim ne zaune matan shi sun saka shi a tsakiya sai hira suke yi cikin walwala da sakin fuska.
Nan yakai duban shi ga Lateefa yace ki shirya hajjin bana dake a ciki.
Tace nafa gaya ma sai dai ka biya muna muje nida sister Kai kuma kayi zaman ka.
Nan ya yi dariya sosai yace Lateefa rigima, ai kwa duk kin 6ata little Latee da irin rigimar ki.
Ya maida duban shi ga Bahijja yace to ke sai ki shirya muje tunda ita bata zuwa.
Nan tayi murmushi tace kaje Kai kad'ai in yaso daga baya mu maje.
Yace tabbb ina ga baku da rabon jifar shaid'an bai rama ba, wato Ku had'in Kai ni kun maida ni saniyar ware.
Nan suka yi murmushi Lateefa tace Kaine baka bada had'in Kai da sai mu d'an jona ka mu zama y'an uku.
Nan yayi murmushi yace to shikenan Ku shirya zamu je mu duka daga nan zamu wuce Egypt muyi sati d'aya.
Nan suka rik'a murna had'e da godiya.
Shigowar yara biyu ne da gudun su yasa suka mai da hankali garesu.
Alamein ya fad'a kan Bahijja yace Ammi kinga little zata kar6e min sweet, kuma yanzu Mum Blkisu ta bani.
Bahijja ta Kai duban ta ga little tace Ina taki sweet d'in?
Tayi narai-narai da ido tace ya shanye tashi shine ya kar6e min tawa don yaji nace sai na kaiwa Abba da Umma ta sun sha.
Nan Lateefa ta Jan yota tana rarrashi tace k'yale shi kin ji little kwad'ayi ya Mai yawa, jeka d'aki ki d'auko sweet d'in ki da Mum Shema'u ta kawo maki, kuma kakki sammai kin ji.
Nan ta yimai gwalo ta wuce shi ko ya rik'a kukan shagwa6a.
Suna hakan ne sai ga Muftah da Blkisu sun kawo masu ziyara.
Nan Bahijja ta kar6i y'rta Teema tana yi Mata wasa, nan suka zube falo su duka suna hira.
Muftah yace aboki nayi ma murna sosai da samun k'arin matsayi, yanzu yaushe zaku wuce abuja d'in?
Yace sai mun dawo daga saudiya sannan mu wuce.
Yace Allah sanya alkhairi yasamu a danshen Ku.
Nan suka kar6a da Ameen suka cigaba da hira.
Yau dai sun shirya kan zasu je suyi bankwana don saura kwana hud'u su wuce saudiya.
Gidan Mum suka Fara zuwa, daka kalli Mum zaka San cewa tana cikin farin ciki saboda ganin matan Shureim sun had'a kan su komai tare suke yi.
Tace Lateefa Ina zaku barin ya ran Ku tun da kun had'e ma son Kai dole sai yaje daku.
Nan little tayi tsagal tace ni gidan su Umma ta Zan zauna.
Shiko Alamein cikin gwaran cin maganar shi yace wurin Mum zai zauna.
Lateefa tayi murmushi tace shikenan Mum an raba.
Da azzahar suka wuce gidan su Lateefa, sai murna little ke yi an zo gidan su Hajiyar ta, nan ma sai la'asar suka fita.
Kai tsaye suka biya gidan Aisha Yagani saboda yanzu auren ta wata uku kenan.
Daga nan suka shiga mak'otan su wurin Mum Zee da Mmn Zahra.
Gab da magrib suka koma gida tare suka fad'a kicin suka yi aiki suka gama, sannan ko wanen su ya shiga wanka domin haramar sallar magrib.
*BAYAN* *KWANA* *BIYU*
Yau kam shirin tafiyar su Kimba zasu je, tun safe suke shirye-shirye zuwa goma sun gama suka hau hanya.
Ko da suka isa duk wani shirin tarbon bak'i malam yasa Inna habiba ta yi Mai matar abokin shi malam Ado kuma iyayen lantana.
Haka aka tarbe su ba laifi, su Gwaggo ana nan zaune d'aki in ba jurewa mutum yayi ba bai iya shiga d'akin da take, saboda d'akin duk wani k'azni yake yi dalilin wasu k'uraje da suka fito Mata anyi magani har an gaji sun k'i warke wa.
Nan suka gaida ta, ta amsa tana kuka tana k'ara rok'on gafarar Bahijja.
Bayan sun fito ne suka je gidan su margyayi Murtala, nan ma su little sun ga tarairaya, har gidan lantana taje kuma ta Kai Mata sutura ita da yaran ta uku ta had'a Mata da kud'i tace ta samu Sana'ar da zata Fara, har kukan murna tayi tana ta godiya.
Sai azzahar suka je raha garin innar ta, su ma ta yi masu goma ta arzik'i saboda kakar ta wadda ta haifi innar ta da sauran k'annen innar ta duk suna nan.
Nan suka kama hanya da tsara bar su ta nono da manshanu.
© *SDY* *JEGAL*
[9:11PM, 9/28/2016] *BAHIJJA* *135*- *140*
*BAYAN* *SHEKARA* *BIYU*
Abubuwa da dama sun faru a ciki kuwa har da mutuwar Gwaggo wadda taga k'ask'anci saboda ko masu yi Mata sallah dak'yar aka same su cikin garin basu wuce mutum biyar ba.
(Allah yasa muyi kyakkyawan k'arshe)
"Bahijja ta biyawa Baban ta makka cikin gadon ta na margyayi Murtala shima yaje ya sauke farali ya dawo.
Anan cikin garin su yasamu wata dattijuwa Baraka ya aure ta, gata da mutunci in ka gan ta tsakanin ta da Bahijja zaka rantse ita ta haifeta.
Yaran sune ke wasa a cikin gardener, su ko iyayen suna gefe sun yi shimfid'a suna shan kayan fruits suna hira.
Shureim yace yaushe ya kamata mu je ganin gida?
Lateefa tace mu Bari zuwa sallah babba sai muje, don gaskiya sallah babba garin nan ba dad'i.
Shureim yace shikenan mu basshi a hakan in munje sai muyi sati biyu mu dawo, yayi ko?
Bahijja tace eh ba laifi zamu yi maneji.
Suna maganar ne tari ya sark'e Shureim kowaccen su ta tashi daga ginciren da take.
Lateefa ta rik'a bubbuga bayan shi tana yi Mai sannu, ita ko Bahijja ta d'auko ruwa ta bashi sannu kawai take jero Mai.
Bayan abin ya lafa ne ya kallesu yace gaskiya kuna ji da tsohon nan naku.
Nan suka yi murmushi, Bahijja tace ai mu gurin mu yaro kake rass, baka ganka ba in kayi zanzaro zaka je office tamkar d'an 25.
Lateefa tace wama zai gan ka yace kana da yara hud'u.
Nan yayi murmushi yace tunda ban tsufa ba ya Kama ta in samu sankaceciyar budurwa cikin Abuja d'innan in auro, sai Ku samu k'anwa.
Tare suka rik'a yin dariya Lateefa tace Allah ya kawo ta lafiya, amma fa sunan ta sorry.
Shureim yace dama an ce in Mata biyu gare ka to ta uku ba zata ga nema komai ba, ni ko hakan kun isheni har agidan aljannah.
Nan suka yi murmushi suka ce Allah ya had'a mu aljanna d'in.
Yace Ameen Ameen, ya d'ora da cewa Ina ga fa gobe kayan Ku zasu iso daga Dubai.
Lateefa tace tun jiya Shema'u ta Kira ni cewa in kayan sun iso a tura Mata lace goma materials goma.
Bahijja tace saura a tura ma Anty Maijidda nasan zata saye ta bamu kud'in mu.
Lateefa tace haka ne gaskiya tun da kinga zamu wuce Jega sallah.
Shureim ya bisu da murmushi yace wai Ku y'an business, ya d'ora da cewa ya kama ta Ku fitar da kud'in mota guda cikin account d'in Ku sai in cika maku Ku siyi motoci.
Nan suka hau murna da godiya had'e da addu'ar Allah ya k'ara bud'i.
Yau kwana uku da dawowar su daga Abuja, Lateefa ta wayi gari da nak'uda saboda dama tana da tsohon ciki.
Nan gida Shureim ya kar6i haihuwar ta ta samu yaron ta namiji.
Murna gurin little tamkar ta had'iye yaron sai cewa su Alamein take yi ita ma yanzu ta samu k'ane su daina yi Mata kuri su uku suke d'akin su.
Ranar suna gida ya cika mak'il da jamaa 6angaren Bahijja sun zo suna ciki kuwa har da Blkisu da yaran ta biyu, Yagani da yaron ta d'aya, Shema'u da yaran ta biyu.
Su Mum zee da Mmn Zahra sune masu sallamar bak'i.
Mmn Zahra tace kinga yadda zaman su yayi dad'i ko, abin gwanin sha'awa.
Mum zee tace inda ma suka fi burge ni kamar had'in kan yaran su, ba zaka ta6a cewa Bahijja ce ta haifi little Lateefa ba, sannan ba zaka ce Lateefa ta haifi Safiya (Ilham) ba.
Nan nima mamaki yayi min yawa nidai naga yara amma ban tantance ga na wannan da wannan ba.
Little Lateefa da Alamein da sudais sune yaran Bahijja.
Ita kuma Lateefa ita keda Safiya (Ilham) da wannan jaririn da yaci sunan Shureim (Khaleefa)
Hakan taro ya watse Ana yabon wannan families.
Washe gari bayan kowa ya kimtsa ne Shureim yasa matan shi tsakiya da yaran shi suka yi selfie don tarihi.
Ni ma Jegal sun burge ni, Allah ya had'a muna kan zuri'ar mu, Ameen.
Tammat bi hamdillah, anan nakawo k'arshen wannan novel nawa Mai suna Bahijja, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min.
Matsayi na na jinjira acikin writers Ina fatar zaku yi hak'uri da yadda littafaina biyu suka zo maku wato.
Fateema & Bahijja.
Nayi wannan buk ne da sunan ki Bahijja (Bebeelo) kuma na sadaukar da shi zuwa gare ki sanadiyyar k'aunar da ke tsakanin mu.
Gaisuwa zuwa ga
Musha karatu group
Taskira group
Zarah B~B fan's
Mumbarin novels
Greatest women
Matan so group
Zumunci group
Kuna cikin raina har kullum
Mmn Shakur
Zarah B~B
Princess Meenat
Blkisu Blymnu
Aunties d'ina
Anty Innah
Anty fateema
Anty Jidda Musa
Anty Ybk
Kin fi kowa son wannan buk
Yaha Saddik (Yaha na)
Taku gaisuwar ta daban ce
Umma ta Lubiee Mai tafseer
Safiya Ummu Abdul
Hindatu shehu
Fati Salihu
Mrs Atiku
Princess Jamila
Jamila Muhd Ali
Zainab M. Bawa
Hafsat Mai sharifai
Mmn haneef
Kuna raina
Zainab Musa (Mmn miemi)
Lawiza Musa
Yara manyan gobe
Halima
Maryam
Khadeeja
Abduljalal
Allah ya rayamin Ku akan sunnah
Fata na gari zuwa ga k'anne na
Assy Jegal
Sumee Jegal
Hauwa Jegal
Allah ya Baku mazaje nagari
Two Star
Asmee Jegal Mrs Ibrahim Mai dabo (Mmn Ammar)
Blkisu Jegal Mrs Imran
Three Star
Sis Hindu
Sis Nafee
Sis Ayshat
Abokanen karatu na
Amnya Hjy shafa'atu zakariyya
Shema'u Bello Bari
Saratu Abubakar
Yazzali
Yar gidan Ango
Ban manta da kuba
Murja Madelty
Hajiya babbah
Mum Zee
Mmn Zahra
Aisha Bizzy
Aisha Yagani
Maryama (Mmn Mu'allim)
Ummu Marwah
Mmn zeenert
Shatoo
Mrs zannah
Anty Ummy
Nafi Jaudat
Masoyana
Innah Habiba
Salmatun Innah
Husnah
Hassy
Pharty JJ
Mrs Alamein
Jiddah Mx
Maryam sani
Habiba yayaji
Khadija Abdul S
Maryama
Muneeebah
Yagana Habib
Ummin Alamein
Maryam (Mmn Mamee)
Matar Mu'az
Mmn Hanan
Mmn amatullah
Fatimatuz-zahra
Zaarah gwandu
Murjanatu yar baba
Halimatussadiya
Miss softie
~@Ag
Sophy md
Faeeza
Teemseey uthman
Laurat (Mrs zubair)
Aisha misilli
Leemcy
Mmn walida
© *SDY* *JEGAL*

No comments:

Post a Comment