Thursday 6 October 2016

SANADIN KUNCI 11-15

[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣2⃣��

Nan Baffa ya bita da kallon tuhuma
Yace'
"Yaushe Mubarak ya Fara shigowa part d'in mu har ya kawo d'aki na?".

"Yaron da nasan cewa in har kin Gan shi nan to Nibras ya matsa ya jawo shi"

Nan muryar ta ta Fara rawa cikin in Ina.
Tace'
"Alh kasan lamari na shaid'an ba abinda ba ya sakawa"

"Kuma talauci na iya Kai mutum ga aika ta ko wane irin Abu"

Nan ya Kai duban shi zuwa ga Iman.
Yace'
"Garin yaya hakan ta faru, kinsan wani Abu game da barin su Mubarak gidannan?".

Girgiza Kai kawai take yi tana hawaye.

Ya koma Kai duban shi ga Nibras.
Yace'
"Kaifa baka da masaniya akan wannan maganar?".

Yace'
"Baffa Ina school lokacin"

Baffa yace'
"Kenan da rana ya shigo gidan nan amma har yakai d'aki na ba Wanda ya gan shi?".

Ummy ta yi karaf
Tace'
"Lokacin nima nayi bak'uwa na fito taka Mata ne shi kuma ya fito daga part d'in ka".

Iman da Nibras sun yi jugum suna sauraren wannan sharrin, ko a mafalki basu ta6a tsammanin cewa Ummy zata iya k'ulla wannan sharrin ba.

Baffa ya Kai duban shi ga Nibras.
Yace'
"Tun ranar da suka bar gidannan ka ta6a kiran wayar shi?".

Yace'
"Gaskiya Baffa ban ta6a tunanin hakan ba, saboda duk hankalina na ga ciwon Iman".

"Kuma sau biyu kawai muka yi lecture satin nan, makarantar ma bamu had'u ba saboda kowa da nashi course".

Baffa ya mik'o hannu tare da cewa.
"Bani wayar taka in Kira shi in ji".

Kawai jin nayi Abu na k'ulu-luluuu, tamkar injimin markad'e ya lalace koda nakai duba na naga Ummy ta rik'e ciki.

Sai zarar ido take yi tamkar 6arawo a kasuwa.

Nan Baffa ya kamo lambar Mubarak ya Kira amma ya jita kashe, sai da ya Kira sau uku computer na k'ara jadda damai sannan ya hak'ura.

Nan Ummy ta sauke wani dogon numfashi uhmmm!".

Sai ga Baffa ya bita da kallo.
Yace'
"Wannan ajiyar zuciya fa?".

Tace'
"Baffan Iman abin ne da d'aure Kai da kuma mamaki".

"Kai kan ka kasan da cewa ba yadda za'a yi yayi sata a ka mashi kuma ya tsaya inda za'a ganshi".

"Da zai so hakan ba zasu had'a kayan su subar gida ba".

Shi dai har ga Allah duk maganar da ta furta babu wadda ta kwanta mashi arai har yaji zai yadda da ita.

Saboda in har bai manta ba ta sha nuna Mai cewa ya daina wahalar da kan shi akan d'iyan y'ar aiki.

Tana nuna Mai k'yashin ganin alherin da yake masu.

Nan yakai duban shi ga Iman.
Yace'
"Kiyi hakuri Iman inshaAllah Zan sa ane mo miki Musirrah in har tana garin nan".

"In ma sun koma Jega duk Zan sa abincika, kiyi hakuri ki maida hankalin ki ga karatun ki".

Hakan ya yita rarrashin ta har ya samu ta dai na kukan.

Takai duban ta zuwa ga Baffa.
Tace'
"Yan zu ya zanyi da wayar Musirrah daka siya mana?".

Yace'
"Ki had'a duka biyun ki ajiye wurin ki, in har an gan su sai ki bata".

Ummy tayi tsagal
Tace'
"Baffan Iman ka bani ita in ba d'iyar k'awata mana".

"Tunda yanzu baka da tabbacin ranar da za'a ganta".

Ya yi murmushi ya girgiza Kai
Yace'
"Ban siyo waya da sunan y'ar k'awar ki ba".

Nan ya tashi ya shige bedroom d'in shi.

<<<  >>>        <<<  >>>

Yau ma kamar kullum bayan Musirrah ta gama shirin ta na zuwa makaranta.

Ta fito ta Kai duban ta zuwa ga Ammi.
Tace'
"Ammi na fito Zan wuce school".

Tace'
"To Allah ya tsare ya bada sa'a".

"Yanzu yaushe zaku fara jarabawar?".

Tace'
"Ammi nida ko magana ba aje aka yi ba".

Tana maganar tamkar zata yi kuka.

Ammi ta Kai duban ta zuwa gare ta.

Tace'
"Kema don mahaifin ki ya rasu ne shiyasa, amma duk da hakan yayan ki zai yi maki jagora".

"Saboda kin ji ance Babban wa uba, kuma ba ke kad'ai ba har ni yanzu akace in kawo ubana ga wani lamari Zan tura Mubarak".

"Ba don komai ba sai don hankali, nutsuwa, hangen nesa, sanin ya kamata irin nashi".

Nan Musirrah tayi murmushi.
Tace'
"To wai Ammi ina dangin Baban mu da dangin ki ne da muke ta gara ranba a gari tamkar wa'anda basu da gata?".

Nan take farin ciki had'e da annurin fuskar Ammi suka 6ace.

Tace'
"Kin dai yi shirin makaranta ko, to kije kar ki makara".

Har ta bud'e baki zata yi magana sai ga wata y'ar class d'in su dake mak'ota ka dasu ta biyo Mata.

Bayan ta yi sallama ta gayar da Ammi  ne takai duban ta ga Musirrah.
Tace'
"Kiyi sauri muje mana mun fayi latti".

Tace'
"To Maryam nifa yaya nake jira batun exam d'ita".

Ammi tace'
"Kije kawai idan ya shigo Zan tura shi makarantar".

Nan suka sa Kai suka wuce, ita ko Ammi ta tsunduma baben tunani.

(Kuyi hak'uri da rashin jina jiya banjin dad'in jiki nane)

         ```SDY``` ```JEGAL```��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣1⃣��

Yau satin su Ammi d'aya da ko mawa gidan hayar da suke ciki.

Mata uku ne cikin gidan ko wacce da mijin ta.

Jummala nada yara bakwai.

Balkisu nada yara biyar.

Sai kuma ladiyo Mai yara tara.

Su dukan su masifaffi ne, Balkisu ce kawai Mai nutsuwa da hankali.

Saboda ba ruwan ta da abinda duk ake yi a gidan muddin bai shafe taba.

Acikin hakan ne Ammi ta karanci rayuwar kowa daga cikin su.

A k'a idar ta bata shiga sabgar kowa iya kacin ta da safe in sun had'u a gaisa.

Mubarak ya can jama Musirrah makaranta saboda ba suda halin da zasu bar ta taci gaba da wadda Baffa ya saka ta.

Shi kuwa Mubarak yana nan D/Fodio university yana karantar accounting, saboda Baffa ya yi masu registration na duka karatun su.

Abinda ya yi Mai saura bai wuce lalurar handout ba sai abinda ba'a rasa ba.

Yau ma kamar kullum Musirrah ta dawo daga makaran ta ta taradda Ammi d'aki zaune tana duba littafin *HISNUL* *MUSLIM*.

Tace'
"Ammi barka da gida, ya hutawa?".

Ammi takai duban ta zuwa gare ta.
Tace'
"Yauwa Musirrah, da fatar kina jin dad'in makarantar?".

Tace'
"Sosai ma Ammi, sai dai rashin sabo da d'aliban duk ba dad'i".

"Kuma wani uncle d'in mu yace ya yaba da k'ok'ari na in har Babana ya amince zai saka ni cikin masu jarabawar k'are makaran ta".

"Amma kin San me Ammi?".

Tace'
"Sai kin fad'a ina sauraren ki"

Musirrah tace'
"Wallahi Ammi na kasa cire Iman daga zuciya ta, jiya har mafarkin ta na yi wai tana kuka tana ne mana".

Ammi taja gwauron numfashi uhmmm!

Tace'
"Kiyi hak'uri ki cire ta daga rayuwar ki, saboda ba na fatar in k'ara had'uwa da mahaifiyar su".

Suna hakan ne sai ga Mubarak ya shigo, bayan ya gaida Ammi ne ya samu guri ya zauna.

Nan Musirrah ta kora mashi zancen uncle d'insu akan maganar exam.

Yace'
"Shikenan Zan samu lokaci in shiga school d'in ta Ku"

Nan ta tashi ta d'auko masu abinci suka Fara ci, saboda ga al'adar su in har yana gida tare suke cin abinci har Ammi.

<<<  >>>       <<<  >>>

Yau ne Ummy ke ta Kai kawo saboda dawowar Baffa daga England.

Duk wani shirye-shirye dangin abinci da abin sha duk an tanadar mashi.

Yanzu haka Nibras yaje d'auko shi daga airport.

Nan tazo gurin Iman tana rarrashin ta kan ta tashi ta shiga wanka.

Tana Mai k'ara jadda da mata kan cewa kar ta gaya ma Baffa cewa ita ta kori su Musirrah.

Da rarrashi ta shawo kan ta ta samu ta shiga wanka ta kimtsa.

Ana hakan ne sai ga su Baffa sun iso, bayan yaci abinci ne ya huta yakai duban shi ga Ummy.
Yace'
"Ya aka yi banga yaran ki ba, Iman da Musirrah?".

"Har Mubarak ban ji motsin shi ba shi ma".

Tace'
"Bara a Kira Iman saboda bata ji dad'i ba duk kwanan nan"

Hakan ta shiga d'akin Iman ta taso k'eyar ta gaba har part d'in Baffa.

Suna shigowa Baffa ya tashi daga kishingi d'en da yake.

Yace'
"Iman ciwo kika yi har haka? An Kira Dr Mukhtar ya duba ki? Miye matsalar ki?".

Hakan ya je ro mata wa'annan tambayoyin saboda ganin yada ta kod'e ta jeme tamkar ta yi wata a kwance.

Nan Ummy tayi karaf
Tace'
"Ai typhoid ce ta yi Mata yawa shiyasa"

Nan ya Jan yota wurin shi yana Mai k'ara ja janta yada ta koma.

Yace'
"Iman d'auko min briefcase d'ita Zan yi surprise d'in ki"

Nan tayi murmushin da bai Kai ciki ba, ta shi ga bedroom d'in shi ta d'auko ta kawo Mai"

Nan ya bud'e ya d'auko waya Apple guda biyu ta mik'a mata.

Yace'
"Ke d'aya Musirrah d'aya, ya d'ora da cewa jeki Kira k'awar ki ku zo tare".

Sai ga hawaye sharr a idon ta.

Ya Kai duban shi ga Nibras
Yace'
"Wai meke faruwa ne? Kuma naji gidan tsit ba yada na saba jin shi ba?".

Ummy tayi karaf
Tace'
"Wannan tsinannen yaro ne Mubarak ya shiga d'akin ka ya kwaso dollars d'in ka".

"Akan na kama shi ne nayi magana kuma nace Zan gayama in ka dawo shine suka bi dare suka kwashe kayan su suka gudu".

Karaf idon su suka had'e kowa da mamaki k'arara a fuskar shi, Nibras da Iman kenan.

       _SDY_ _JEGAL_��

*BLOG* *sadiyajegal.mywapblog.com*

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_1⃣3⃣��

Yau dai Musirrah an yi exam har an gama, tare da had'in Kan yayan ta Mubarak.

Shak'uwa Mai k'arfi ke tsakanin ta da k'awar ta Mela, saboda tun tana basar da alak'ar ta da Mela d'in, har yakai ta bada gari.

Saboda Mela yarinya ce Mai saurin sabo, ga iya zama da mutane saboda kowa Nata ne.

Tun da safe suke ta had'a kayan su saboda zasu bar gidan, ba akan komai ba sai don Mubarak na Lura da irin zaman takura da hakuri da Ammi ke yi gidan.

Bayan duk sun had'a kayan su ne sai ga Blkisu ta shigo d'akin ta gaida Ammi.
Tace'
"Shikenan yanzu Ammin Mubarak zaku bar gidan nan?".

Ammi tace'
"Wallahi kedai Blkisu, zama dasu ladiyo sai hak'uri masifar su ta yi yawa"

Tace'
"Gaskiya na yi maku murna Allah ya hore ma maigida muma mu bar gidan nan ko d'iyana na samun sakewa.

Suna hakan ne Mubarak ya shigo d'akin, bayan sun gaisa da Blkisu.
Yace'
"Ammi kun had'a kayan duka?".

Tace'
"Eh dama Kai kad'ai muke jira".

Hakan Blkisu tasa yaran ta suka taimaka Mai aka fita da kayan.

Sai da yaje ya Kai kayan su sannan ya dawo.

Nan suka kimtsa suka fito, Ammi ta tsaya filin gida ta yi ban kwana dasu ladiyo sai wani kallon ta suke yi shek'ek'e.

Tare da Blkisu da Maryam Mela aka je, saboda suna son ganin in da suka koma.

unguwar kasarawa opposite meenarat nan suka samu d'an matsakaicin gida.

Gida ne Mai d'aki uku kitchen had'e da toilet, sai kuma filin gida.

<<<  >>>          <<<  >>>

Yau ne Baraka ta yanke shawarar komawa garin mahaifan ta.

Saboda dama can auren Dole ne ya rabo ta da garin su.

Tana da Wanda take so tun shekarun baya da suka shak'u sosai.

Sanadiyyar mahaifinta ya bawa wani abokin shi Mai Mata uku ita yasa tabi dare ta gudu.

Bayan ta had'a duka kayan tane ta zauna tayi jugum saboda tunanin ya zata tunkarar gida? Ko a wanne hali zata taradda su?".

Nan dai taje ta samu mota d'aya ta zuba kayan ta hau hanyar kebbi fargaba cike taf a ranta.

Har k'ofar gidan su mota ta ajiye ta, gashi ba abinda ya 6ace Mata sai dai canje-canjen da aka samu a unguwar.

Bayan ya sauke ta ta sallame shine ta Kira wasu yara su shigar Mata da kayan ciki.

Tana shiga ne da sallamar ta tayi Karo da Gwaggo ta ajiye buta.

Nan takai duban ta gare ta.
Tace'
"Wa nake gani tamkar baraka dama kina duniyar nan?".

Tace'
"Gwaggo Ina nan, sai kuma ta fasa kuka ta durk'usa ta rik'e k'afar Gwaggo tana Mai Neman gafara agare ta".

Nan Gwaggo ta kamata ta mik'e.
Tace'
"Ba banza ba Baraka nasan duniya ce ta yi maki hankali".

"Tunda kika bar gida sama da shekara goma sha bakwai baki k'ara waiwayar kowa ba"

"Kin tafi kin bar Mal da ciwon zuciya saura k'iris kiyi ajalin shi".

Jin tarin shine yasa Gwaggo ta nufi d'akin shi da sauri, nan Baraka ta rufar Mata.

Suna shiga Gwaggo ta d'auko ruwa ta bashi, bayan ya sha ne yakai duban shi ga Gwaggo.

Yace'
"Wa nake gani tamkar Baraka, ko mafalki nke yi?".

Tace'
"Ita ce Mal, k'ila duniya ta gaji da ita ne shiyasa ta waiwayo mu".

Nan Baraka taci gaba da kuka tamkar ranta zai fita.

Tace'
"Don Allah Baba ka yiman aikin gafara, wallahi na tuba bazan k'ara ba".

Yace'
"Ba komai Baraka dama na jima da yafe maki, sai dai babban bak'in ciki na bansan rayuwar da kika jefa kanki ba bayan barin ki gida".

Tace'
"Wallahi Baba ba abinda na aikata na assha, asali ma tun Bari na garin nan Sana'ar sayarda abinci nakeyi".

Nan ta kwashe labarin ta tun barin ta gida ta gaya masu.

Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya uhmmm!
Tace'
"Kin yi arzik'i da baki 6ata rayuwar ki a banza ba".

"Amma duk da hakan ba kida wanda zai aure ki a hakan tsofai-tsofai dake ace wai budurwa ce ke".

Jin nauyin maganar Gwaggo yasa ta sunkuyar da kan ta k'asa.

Nan ta tashi ta bar d'akin ta Koma d'akin Gwaggo.

"Allah ina rok'on ka yada ka maida ni gaban iyaye na lafiya, ka mayar da Hauwa'u itama gaban nata iyayen lafiya".

"Ko Ina Mubarak yake yanzu? Nasan dai ya zamo saurayi yanzu".

Ita kad'ai take wannan maganar, sai gashi tana matse wasu hawaye can k'asan idon ta saboda tausayin rayuwar su.

         ```SDY``` ```JEGAL``��

Blog:
Sadiyajegal.mywapblog.com

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN__K'UNCI_ 1⃣4⃣��

Musirrah an k'are karatu yanzu sai zaman gida.

Kwana ki nata shud'ewa watanni ma hakan, Wanda a yanzu watan su takwas cikin gidan da suka dawo.

Yanzu kam rayuwa ta fara yi masu k'unci saboda duk d'an abinda suka tara sun cinye.

Dama ance yau da gobe sai Allah, duk abinda ake d'iba ba'a k'ara wani wataran za'a tarar da babu shi.

Wannan ya faru ne sanadiyyar duk cikin su ba Mai Sana'a sun dogara ne ga abubuwan da suka samu sanadiyyar zaman su gidan su Iman.

Don ma har an had'a ne da sark'ar Musirrah ta gold an sayar ne, wadda Baffan Iman ya siya musu wata tafiya da yayi Dubai.

Yanzu dai hakan abincin da zasu ci Neman gagarar su yake yi.

Musirrah ta fito daga d'aki ta samu Ammi tayi wani uban tagumi.

Takai hannun ta ta dafa kafad'ar ta.
Tace'
"Ammi meke faruwa ne? Ya kamata ki rage wannan dogon tunanin kar ya janyo maki wata illah".

Nan ta sauke wata irin ajiyar zuciya Uhmmm!
Tace'
"Musirrah wannan rayuwar da wahala take, na rasa ina Zan saka kaina".

"Gashi yau dai-dai da abinda zamu ci ba muda a gidan nan".

Musirrah takai duban ta ga Ammi.
Tace'
"Ammi ya kamata mu had'a namu da namu mu koma garin Ku".

"Ba akan komai ba sai don samun sassaucin abubuwa, na tabbatar cewa ko mahaifin mu bai raye ba za'a rasa wani taimako da dangin shi zasu yi mana ba".

"In ma baida dangi nasan ba za'a rasa naki dangin da zasu yi wani Abu akai ba".

Kallon da Ammi ta bita dashi ne yasa ta saka ma bakin ta linzami tayi shiru.

Idan da sabo har ta saba da wannan abin na Ammi, ta rasa gano me kesa da anyi maganar komawa gida sai ta had'e rai.

Ammi ta Kai duban ta gare ta.
Tace'
"Sau nawa Zan gaya maki cewa ba nason kina yi min maganar komawa gida?

"Ko kin ga d'an uwan ki na damuna ne? In kina so mu zauna lafiya to ki daina tayar min da maganar".

Tace'
"Shikenan Ammi kiyi hak'uri inshaAllah bazan k'ara ba".

"Ta d'ora da cewa Ammi inaso in je neman aikatau ko Zan samu".

Tace'
"Ki bari ni Zan nema in rik'a yi mu samu abinda zamu ci".

Musirrah tace'
"Ammi lokacinda kika yi aikatau kin yi, amma yanzu bazai yuyu Ina zaune kije yawon aikatau ba".

"Kinga yanzu na k'are school ban zuwa ko ina, ko k'awaye bana da barranta na ince Ina yawon gidajen su".

"Gidan su Mela kawai nake zuwa har in wuni, shima don hajiyar ta na tarairaya dani ne har in manta lokaci".

Ammi tayi murmushi
Tace'
"Kina dai ji da wannan Hjy taku, kullum sai kin yi maganar ta".

Tace'
"Ammi banta6a samun Mace Mai kirkin taba, ga fara'a da son mutane, Allah farko Ina ganin kirkin Mela amma dana zauna da Hajiyar ta sai naga Nata ba komai bane".

Ammi tace'
"To Allah yabar zumunci tsakanin Ku Ku d'ore har y'a y'an Ku".

Tace,
"Ameen Ammi ta, ta d'ora da cewa bara in tashi in fita cigiyar aikatau d'in ko za'a dace".

Nan ta saka hijab d'in ta ta fita Neman aikatau d'in.

Bata wuce minti biyar da fita ba sai ga Mubarak ya shigo gidan da Leda a hannun shi.

Bayan ya gaida Ammi da gida ne ya mik'a Mata ledar da ke hannun shi.

Ammi ta kar6a ta duba taga shinkafa sai Mai da yaji.

Takai duban ta zuwa gare shi.
Tace'
"Allah ya yi maka albarka ya taimaki rayuwarka".

Ya amsa da Ameen, ya tashi yace'
"Ammi bara in gyara wuta sai adafa shinkafar".

Ammi tace'
"Ka bari kawai Zan d'ora kaga k'anwar ka yau ta fita Neman aikatau".

Yace'
"Hakan nada kyau, Allah yasa adace".

Tace'
"Ameen, ya d'ora da cewa Ammi yau fa naga Baffa".

Nan ta zabura da k'arfi
Tace'
Kai! Mubarak a Ina? Ina fatar bai ganka ba?".

Ya yi murmushi
"Yace gaskiya Ammi ya ganni sai dai akwai go slow nan na 6ace Mai".

Ya d'ora da cewa' "Ammi na hango mamaki k'arara a fuskar shi lokacin da muka had'a ido dashi".

Ammi tace'
"Bawan Allah mutumen Kirki gashi da son taimako, amma Allah ya had'ashi da Mata Mai k'yashi".

"Wai har yanzu baku had'u da Nibras ko a school ba?".

Yace'
"Gaskiya Ammi sai dai muyi kuskuren had'uwa, kamar na shigo class ace yanzu ya fita".

"Kuma kinsan na canja layi yanzu ko ya Kira bai samu na, don mun ma kusa k'are school d'in".

Ammi ta kar6a da Allah ya taimaka".

Suna maganar ne tana girki, nan ta duba shinkafar ta nina ta sauke ta d'ora Mai.

Suna hakan ne saiga Musirrah ta dawo, bayan ta gaida sune takai zaune.

Ammi tace'
"Ina fatar an dace da aikatau d'in?".

Ta sauke ajiyar zuciya Uhmm!
Tace'
"Wallahi Ammi ba nasara sai dai gobe Zan k'ara fita in gani ko za'a dace".

Mubarak yace'
"To Allah ya cisuwa yasa adace".

Ammi tace'
"Ameen".

Nan ta sako masu abinci suka zauna suna ci suna tattauna lamarin duniya.

(Kuyi hak'uri dani ba kullum zaku rik'a samun posting ba kamar baya, wannan ya faru ne sanadiyyar haihuwa da aka yi mana)

      ```SDY``` ```JEGAL```��

Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: �� _SANADIN_ _K'UNCI_ 1⃣5⃣��

Cikin sauri-sauri ya shigo gidan ya rik'a k'wala ma Nibras Kira.

Sai gashi Ummy da Iman sun fito a tare.

Ummy takai duban ta zuwa gare shi.
Tace'
"Haba Baffan Iman me ke faruwa wannan Kira haka?".

Yace'
"Iman shiga ciki Kira min Nibras".

Nan ta juya taje ta Kira shi sai gasu sun fito tare.

Yakai duban shi ga Nibras.
Yace'
"Da nace ka bincikamin in har Mubarak na garin nan, me yasa kake yimin k'arya cewa ka bincika baka ganshi ba?".

Yace'
"Wallahi Baffa ba kusan kullum ne bana shiga department d'in su ba".

"Sai dai mu samu akasi ace ya shigo ya fita, ko kuma ace bai zoba".

Iman tace'
"Hala Baffa me ke faruwa?".

Yace'
"Iman yau naga Mubarak da ido na, kuma sai da muka had'a ido dashi amma sanadiyyar go slow sai ya 6ace min".

"Tace'
"Baffa ka gayamin inda ka Gan su zanje in yi cigiyar Musirrah".

Tana maganar hawaye na zuba a idon ta.

Dammm! Naji gaban Ummy yace".

Nibras yace'
"Baffa kayi hak'uri na yima alk'awari zanga Mubarak kafin ya zana exam d'in shi".

Baffa yace'
"Kiyi hak'uri Iman Zan sa ak'ara tsanan ta bincike a Neman su".

Ummy tace'
"Baffan Iman ka daina wahalar da kanka ga wa'annan yaran".

"In ma banda abinka ya zaka yita bibiyar mutanen da keson ganin bayan ka?".

Yace'
"Na gaya maki in har kika ji ina magana da yarana indai akan matsalar Mubarak ce ki dai na saka min baki aciki".

"In ma banda abinki Ina ruwan k'wai da aski, wannan ni ta Shafa dani da yarana".

Nan ya k'ara jadda dama Nibras cewa yafa bincika, yasa Kai ya wuce bedroom d'in shi.

Ta kai duban ta ga Nibras.
Tace'
"Ban hana ka cika umurnin mahaifinka ba, amma nima ga nawa umurnin".

"Ina Mai gargad'in ka da cewa duk abinda kuka tattauna kazo ka gayawa Baffan Ku wallahi sai nayi mugun sa6a ma".

Nan ita ma ta wuce Nata d'akin ta bar su nan zaune kowa yayi jugum.

<<<  >>>           <<<  >>>

Yau ma kamar kullum Musirrah ta k'arasa aikace-aikacen ta na gida ta wuce Neman aikatau.

Cikin zaga yen da take yine ta dace da aiki gidan wata Rukayya.

Rukayya ta kalle ta da kyau.
Tace'
"Ke yanzu kina iya aikatau? Saboda ni girki nake so ki rik'a yimin".

Tace'
"Anty na iya girki duk Wanda kike so".

Nan suka yi magana suka Kai k'arshe tace taje gobe ta dawo.

Musirrah ta yita godiya cikin murnar ta ta nufi hanyar gida.

Tana shiga gidan da murnar ta take la bartama Ammi ta samu gidan aiki.

Nan Ammi ta taya ta murna.
Tace'
"To ki kula da aikin ki, kar ki saka kan ki abinda ba'a saka kiba".

"Ki rik'e gaskiya da amana, duk rintsi ban amince ki d'auki abincin su ba tare dasu suka baki ba, koda kuwa dafaffe ne".

Tace'
"InshaAllah Ammi zaki same ni Mai rik'e amana".

Tace'
"To hakan akeso".

(Plxxx kuyi hak'uri da wannan, masoyan SANADIN K'UNCI sun yi yawa shiyasa suka dame ni na basu wannan.
Yanzu kun yiwa Bahijja ta waye, k'yale su Bebeelo ko sun guje ki ni ina tare dake.
Ina jiran comments d'in Ku ta blog d'ina in har kuna son SANADIN K'UNCI, rashin hakan na nuna Bahijja (Bebeelo) ta tayi winning, _lolx_)

Blog.
Sadiyajegal.mywapblog.com

        _SDY_ _JEGAL_��

Dedicated to Sanah S. Matazu.

No comments:

Post a Comment