Thursday, 6 October 2016

FATIMA 8-11

[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 8
By Sdy jegal
'''''Yau ne aka wayi gari gidnsu Xarah anata hada hadar dawowar Broda Shakur daga Egypt, sanadiyyr kiranda Abba yyi jiya kan cewa daga London wurin harakokinshi ya wuce Egypt xsu dawo tare da Shakur.
An shirya girki daban daban domin tarbonsu, bayan gama ayukkane da sukayi Fateema ta shiga bayi tayi wnka ta fito ta shirya cikn doguwar riga kalar black mai ratsin fari tayi roiling da dankwalin rigar, tana fitowa daga dakinta ta rega d'akin Umma domn duba ko "yan biyun Umma sun shirya,
Shigarta d'akin keda wuya ta hango Umma na saka ma khadeeja nata kayan, Mubarak na gefe ya kame cikin Qananan kaya ysha farin Glass, nan ta taya Umma shirya khadeeja ta gyramata kanta sun fito tsaf su duka tamkar larabawa,,,,,
Xarah ta rik'o hannunsu suka sauko k'asa ta kunna musu kallo sunayi suna xamn jiran isowarsu Abba don direba ya tafi d'aukosu tun d'axu.
Basu wuce minti goma da xama ba sukaji dirin mota nan take suka tashi suna rigegen fita domin tarbo Broda Shakur Wanda rabonsu dashi yanxu shekara biyar kenan saidai ta waya, su duka uku suka tunkari Shakur suna oyoyo Broad, ya duk'a yad'auki "yan biyun Umma yna juyi dasu ya ajiyesu itako Xarah yarik'ota yayi hugging d'inta yana mai cewa kinganki sister yadda kika koma, hala kai kaga kanka Broda cewar Xarah""""
Nan suka juya murnar su xuwa ga Abba, shiko yace musu yayi fushi yana mai cewa saida kuka gama murnar ganin Broda dinku sannan xa'ayimn tawa tarba,,, nan Xarah ta durk'usa gami da kama kunne tace sorry Abba"" suma "yan biyu sukayi yada tayi, nan Abba ya rik'osu yace su tashi su shiga gida, shiko broda yana kallonsu yana jin wani nishad'i cikin ranshi yana cewa lallai ba abinda yafi dad'i irin mutum na cikin yan'uwanshi.
,,,,,,,,,,,,,,Sun shiga gida aka k'ara gaisawa Shakur ya gaida Umma tana kar6awa had'e da nuna kawaici irin nasu na Fulani, nan suka hau dinning Xarah ta xubawa kowa abinci sukaci suna cikin walwala da farin ciki.........
FATEEMA 9
Waye Hakeem???
"Hakeem yarone gun margyayi Alhj. Bawa da Hjy shema'u, su biyu mahaifansu suka Haifa wato shida k'anwasshi nusayba, sun kasance yan asalin garin jega ne, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa tun shekaru hudu da suka wuce,, mahaifiyar su Hjy shema'u macece mai Neman na kanta, tun mahaifinsu Nada rai take y'an sana'o'inta da ba'a rasa ba, saboda kamin rasuwar babansu yanada halinshi gwargwado Wanda har yaje Makkah tare da mahaifiyarsu shema'u,
Daga baya kuma ya gamu da kariyar arxik'i Wanda takai Hjy shema'u ke d'auke da nauyin gidan cikin sana'adda takeyi har Allah ya karb'i ran mahaifinsu, inda yakamu da ciwon cikin rana guda Wanda yaxama ajalinshi,,
Ranar jekaga tashin hankli ga wannan family inda sukaci kukansu har suka dangana.
"Hakeem yayi makarantasshi ta primary da secondary a garin jega, inda ya xarce Aleru university wnda daga can ne aka turashi service d'inshi makarantar su Xarah,,,
Wanda itako k'anwasshi Nusayba take makarantar government day secondary school jega take gab da gamawa.
Hafsat mak'wabta ne da gidansu Hakeem Wanda shak'uwa ta shiga tsakaninsu sosai, tana shiga gidan saboda mutuncinda ke tsakanin Hjy shema'u da mamatta ikilima, Wanda sanadiyyar shiga gidan da takeyi ta lak'ema Hakeem, tun bai kulawa ta har yafara kulata soyayya ta k'ullu tsakaninsu Wanda suka shafe shekara guda da watanni suna son juna Wanda duka iyayensu sun sani kuma suna alfahari da hakan.
Kwatsam akwana atashi wani lirwanu ya bayyana yana son Hafsat sai gashi ta Fuji Hakeem sanadiyyar lirwan yafishi kuddi,,, Hakeem yashiga damuwa sosai har takai baiko son anayimai maganar macce,, saboda yaudarar da Hafsat tayi mashi.......
Gaisuwar kice Anty na Ybk
Kina raina Jabo
Dedicated to Mmn Shakur
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 10
By sdy jegal
Yau ne lahadi aka wayi gari da lumshi sanadiyyar hadarin da akayi adaren jiya" uncle Hakeem yau yana gida saboda weekend ba school yau, fitowasshi kenan daga toilet yayo wanka ya kimtsa saiya d'auko wayarshi yana mai addu'ar Allah yasa yadace yasamu number d'inda ba kusan kullum ne bai kiranta ba, saidai kash kullum ya kira computer bata gajiya da gayamai cewa wayar is switch up"
"Saidai yau yana kira yaji wayar ta shiga amma har tayi ringing ta tsinke ba'a d'agaba, a karo na biyu ne naji yayi sallama gami da gaida Wanda yake wayar dashi, saidai banajin mai d'ayan b'angaren ake cewa, "Alhj xuwa 10am xansameka gida kuwa? Saboda ina tafe ne da abubuwa masu muhimmanci, "cewar Hakeem sai naji yana cewa to shikenan sai naxo gami da kashe wayarshi''''
'Hajia ''Hajia ""Hajia Ana ukkun ne ta fito tana mai cewa haba Hakeem wannan kiran fa, ko k'anwrka nusayba baxata yimin kira haka ba cewar Hjy, Hakeem yace kiyi hakuri Hajia ina cikin farin cikine yau nasamu lambadda nace maki kullum ina kiranta amma kashe take, ana nan naga Hajia itama tana mai washe, nan nkoma gefe inata tunanin meyasa suketa murna haka daga ankira lamba ta shiga.
Shin lambar waye?
Kuma waye Hakeem ya kira?
Kubiyo y'ar mutan jegal domin samun amsa.
Gaisuwar taki ce Anty na Ybk
kina raina Jabo
dedicated to Qawata Mmn Shakur
[6:26PM, 9/29/2016] FATEEMA 11
By sdy jegal
K'ARFE GOMA NA SAFE!!!!
"Hakeem na k'arasowa k'ofar gidan ya d'auko wayar shi ya kira, ringing biyu ana ukku aka d'aga wayar nan yake cewa Alhj gani k'ofar gidan.
Nan akayimai iso tare da turo wani yayi mashi jagora har xuwa falon Alhj na karb'ar bak'i,,,, nan ya durk'usa har k'asa ya gaida Alhj,,, haba tashi xauna saman kujera mana cewar Alhj, take aka kawoma Hakeem ruwa da d'an abin motsa baki, bayan yasha sai Alhj ykai dubanshi xuwa ga Hakeem yna mai cewa yaro ka kirani kace kanada magana mai muhimmanci har gashi kaxo gidan bnga alamar cewa nasanka ba, """"nan Hakeem ya amsa da cewa eh gaskia Alhj baka sanniba.
''''''''''''''''Amma sati biyu da suka wuce ka fito daga BLB plaza kana sauri kana waya sai wani file ya fad'o daga cikin takaddunda kake rik'e dasu, Niko ina wurin xaune naga ka shiga mota ka wuce, koda na d'auki file d'in na hau mashin d'ina domn inkaima shi sai motakka ta b'acemn saboda go slow,
A lokacin na ajiye file d'in cikin mashin d'ina koda naje aiken Hajia na dawo nashiga d'akina, sai na bud'e file d'in naduba naga cewa na company d'inka ne had'e da takaddunka masu muhimmanci.
'Anan naga lambar wayrka na d'auka nayita try bansamu ba, kuma naje har company d'inka nake tambaya aka cemin baka 9ja,,,,,,,,,,,,, shiyasa nakaisu na ajiye gami da try lambakka sai jia na dace.
Nan Alhj yayi murna da farin ciki yana mai godema Hakeem yna cewa Ashe yadda duniyar nan takoma hr ynxu akwai masu Amana,,,,,, yarona na gode sosai banma San dame xansaka maka ba, nan Alhj ke tambayrshi sunanshi da aikinshi, nan take ya gayamai yana mai cewa service ykeyi yanxu.
Sanadiyyar amanata daka rik'e yarona inason inbaka wata amana, nan Hakeem ke cewa Alhj wace Amana kuma,
''''Alhj yace nabaka amanar d'iyata randa duk ka shirya katuro magabatanka ayi maganar aure, kuma banason komai daga gareka bayan sadaki.
Ba Hakeem ba koni kaina jegal saida gabana ya tsananta fad'uwa, saboda tuna cewa yafara dakon soyayyar Xarah.
Muje xuwa
Takuce jegal
Gaisuwarki ce Anty na Ybk
kina raina Jabo
jinjinar ki Anty Habby
dedicated to Qawas Mmn Shakur
Daga taskar jegal

No comments:

Post a Comment