[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣0⃣0⃣_1⃣0⃣5⃣
Yau Zarah ta cika sati biyu da aure, kuma a gidan da ta rad'a ma suna cell.
Kuma har ila yau Allah bai had'a ta da angon ba, Wanda wani gefe hakan ma yafi Mata kwanciyar hankali.
Sai dai duk abinda za ayi zai yo Mata text message, itama zata bashi amsa anan.
In ya kawo cefane zai Mata text, itama inta gama girki ta jera a dinning table zata yimai text ta koma d'aki. (Ina ruwan auren text)
Yau ma bayan ta gama girkin gida sai taji tana sha'awar dafa indomie da kifin gwangwani.
Bayan ta gama ne ta zuba ga filet, juyowar da zata yi nan taga mutum tsaye bakin kicin, tsabar rud'ewa kawai jin zafi tayi saman k'afar ta, nan tayi wani ihu Mai sauti.
Bata San ya aka yiba kawai ta Gan ta rungume jikin Hakeem yasa handkerchief yana goge k'afar had'e da hura Mata iska ga k'afa.
Tuna inda take ne yasa ta zabura da k'arfi zata tashi, take Hakeem ya k'ara run gumota, ya d'auke ta tamkar y'ar tsana ya kaita d'akin ta.
Bayan ya shimfid'e ta ne yace yana zuwa, ya fita da sauri.
Yana fita ta tashi da sauri ta sama d'akin key, ta dawo ta zauna, Wanda k'afar keta yi Mata zogi sai hawaye takeyi.
Shin dama uncle Hakeem ne nake aure?
Shine ya tsinci file d'in Abba?
Ko dai k'anen shine Kama suka yi?
Kai wannan tabbas uncle Hakeem ne.
Duk ita kad'ai ke wad'annan surutun, nan take ta zabura da k'arfi jin zafin k'afar tane yasa ta tuna halin da take ciki, sauk'in ta d'aya ma bada sauke indomie d'in ta zube ta ga filet ba.
Nan naga ta nufi sef d'inta na ajiyar kaya ta rik'a tono sai can ta tsaya cak kamar wadda aka kafe.
Ashe I.V d'in auren su ce ta tono nan take tayi zaune k'asa dab'as, saboda ganin abinda ke rubuce.
FATEEMA MUKHTAR IBRAHIM
Weds
HAKEEM LATE ALHJ BAWA.
Tabbas in har ba zata manta ba da haka akayi introducing d'in shi lokacin da yazo makaran tarsu.
To me hakan ke nufi? Shi ma baisan itace matar shi ba?
Kai ba zai ma yuyu ba, yanzu haka ya gane shiyasa yake tafiyar da zaman takewar auren su ta hanyar text.
Jin an bud'e gambun ne an shigo d'akin yasa ta juya da kallon ta bakin k'ofar da idon ta taff da hawaye.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣0⃣5⃣_1⃣1⃣0⃣
*WAIWAYE* *ADON* *TAFIYA*
Tun had'uwar lirwan da Hafsat bayan ta guji Hakeem abin na su baije Ko Ina ba, saboda dama shi lirwan ba motocin shi bane yake zuwa gurin ta dasu ba.
Asalima shi wankin mota yakeyi, da an kawo and'aga zaije yawon shi wataran har ya biya da ita shaguna sayayya, sai ya dawo ne sannan ya wanke motar mutane ya ajiye.
Wanda cikin yawon sune yi Mata sayayya duk ya bita ya lagude, sauk'in abin ba atab'o headquarter ba, ko yaushe ta yimai maganar aure zai ce Mata tayi hak'uri sai Baban shi ya dawo daga Swaziland zai yimai maganar.
Itako Mamar ta Ikilima an riga an rufe bakin magana saboda anga kud'i, Wanda Baban ta bai ma San wainar da ake toyawa ba, saidai in yayi magana kan Hafsat ta fitar da miji Mamar zata ce akwai Wanda zai turo yace Baban shi bai k"asar sai ya dawo.
Yau ma yazo hira garkar su Hafsat tana cikin motar shi suna shan minti, har wata mota ta gauta su sai kuma ta dawo baya.
Daga nan mutumen ya fito ya zo wurin motar ya bud'e gambu da k'arfi sai gasu manne da juna, nan ya fizgo lirwan ya fito dashi waje ya gaura mashi Mari uku.
Ya nuna shi da yatsa yana cewa, yanzu d'anladi rashin kunyar da rashin mutuncin har ya kawo ga mota ta, tun d'azu na aika a d'aukomin mota ta akace ba aganka ba ba aga mota ba, Wanda har na gaji da jira na d'auko wannan motar na fito.
Ashe da gaskiyar mutane da suke cewa in an kaima wankin mota kana fita yawo da ita, Ashe duk an saka muna najasa a mota.
Duk bambamin fad'an da Alhj keyi kan d'anladi na k'asa ko motsin Kirki bai yi.
Nan Alhj ya Kira D.p.o ya yimai kwatan cen inda yake yace yana buk'atar police uku, inda kamin su iso mutane sun cika wurin anata kallon meke faruwa.
Bayan police sun iso ne yace aje Mai dashi sai ya zo.
Bayan an wuce dashi ya buga ma Hafsat tsawa yace to a fito aban mota ta, haka ta fito sukuku yace an daiji kunya, zuwa gaba asan irin way'anda za arik'a kulawa.
Nan yara suka bita da kuwar Hafsat lashe money, nima dai nace lashe money.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn ~Shakur~.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣1⃣0⃣_1⃣1⃣5⃣
Hakeem na shigowa ta bishi da kallo da zummar yimai tsiwa, amma duk taga ya yima ta kwarjini.
Hakan ya shigo yaje wurin ta ya tada ta ya d'ora ta saman gado.
Nan ya rik'a k'afar yana Shafa Mata wani magani Wanda har cikin zuciyar ta take jin San yinshi.
Nan take duk jikin ta ya Saki saboda shak'ar numfashin juna da suke yi.
Hakeem ke tambayar ta cewa me yasa take jin tsoron shi har hakan?
Nan tayi shiru ta soke Kai.
Yasa hannu ya tallabo hab'ar ta suna fuskan tar juna, suna had'a ido tayi saurin kauda fuskar ta ta nok'e Kai.
Ta naso ta gayamai maganganu amma da sun had'a ido saita kasa, saboda tana jin nauyin gashi malamin ta, Abu na biyu kuma bata iya yima babban mutum tsiwa saboda ba tarbiyyar gidan su ceba.
Da hakan har ya samu ta d'an Saki jikin ta.
Cikin sangar tacciyar murya ta tace to ka cika ni k'afar ta daina zogi.
Nan yayi kwaikwayon maganar ta yace in ank'i fa?
Tayi murmushi ta soke Kai.
Yace Zarah na Ina Mai neman yafiya akan laifina zuwa gareki.
Bawai nak'i kula ki bane, Ina tsoron tunkarar kine saboda bansan da wane ido Zan dubeki ba.
Nan ya kwashe labarin komi ya gaya Mata, ya d'ora da cewa nima bansan kece Zan Aura ba sai gab da auren mu.
Yace tsoron in bayyana kaina gareki kice kin fasa yasa na b'oye kaina.
Gidannan kuma ina kula da takon ki, duk abinda ki keyi ina lab'e ina kallon ki, bansan da wane ido Zan kalle kiba.
Amma lokacin da kika k'one na zo ne da niyyar sa santawa tsakanin mu, saboda zuciyata ta kasa hak'ura da ganin shige da ficen ki.
Nan ta d'ago Kai suna had'a ido ya kashe Mata ido guda.
Duk ta ji kunya ta Kama ta, ta k'ara soke Kai.
Yace wannan kunyar zanyi maganin ta.
Nan yace ta tashi suje dinning table suci abinci.
Tace yaje kawai ita ta k'oshi.
Yace ai bakici indomie da kika dafa ba, tsoron uncle yasa kin zubar da ita, don haka ki tashi kawai.
Ganin yana Neman d'aukar ta yasa ta tashi da kanta ta fara jan k'afa.
Nan yaji bazai iya hak'urin ganin ta tana Jan k'afa ba yasa ya sunkuceta sai dinning.
Bayan ya zuba musu abinci ne ya tallafota ya d'ora saman cinyar shi, ya Fara bata abincin tana ci tana nok'e kai duk kun yarshi ta isheta.
Bayan sun gama ne tace uncle inaso inje inyi wanka.
Yace to muje in maki kinga baki da lafiya.
Tayi saurin kallon shi ta koma nok'e Kai.
Nan ya sunkuce ta sai toilet ya had'a mata ruwa, ganin da gaske wankan zai Mata tace ni gaskiya uncle ka fita zanyi da kaina.
Nan ya fito ya jawo Mata k'ofa.
Ita Ko mamakin abinda uncle ya yimata kawai take yi, shi bai ko jin nauyin ta matsayin ta na d'alibar shi, lallai Maza ho.
Amma duk da hakan gaskiya ya iya tarairaya da soyayya.
Ni kam nace Zarah kin yi saurin zurmawa, *lolx*.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn _Shakur_.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣1⃣5⃣_1⃣2⃣0⃣
Ta shiga gidan tana kuka tamkar ranta zai fita.
Mama Ikilima ta taso ta tar beta tana tambayar me ya faru hakan?
Nan ta kwashe komi ta gaya Mata.
Mama taja dogon salati tace amma wannan yaron anyi mugun yaro, shiyasa kullum akayi magana ya turo magaba tanshi yake cewa ajira Baban shi ya dawo daga Swaziland, Ashe k'ilama mahaifan shi na k'auye.
Oh ni Ikilima yanzu da wane ido Zan kalli mutane, haddai wannan yaron da muka cuta, gashi shi har yayi auren shi ke kuma gaki zaune.
Daka dubesu zaka ga nadama k'arara a fuskassu, ni dai nace kowa ya hau motar son rai zai sauka tashar nadama.
Hakeem na hango tsaye gaban Zarah tana taje mashi kanshi, ta gama ta d'auko babbar rigar shi ta saka Mai, daga nan ta d'auko turare ta fesa Mai.
Nan take ya fito fes ya had'e cikin farar shadda.
Ita ma ta had'e cikin less d'inta kalar purple ta fito fes da ita.
Nan ya bita da kallo yace kin fa iya tarairayar miji sai dare yayi ta shige d'aki kibar bawan Allah shi ka d'ai ba tausayawa.
Tayi murmushi ta soke Kai.
Yace yau dai ina fatar zaki shirya tar bona, ayimin sassauci hakanan na horu gaskiya.
Tace tabbb ba yanzu ba ai yau dole ka tausayamin duk kwananna bana samun zama zirga zirga ta yimin yawa, aure uku ba wasa ba.
Nan tace ya tashi suje rana tayi kuma yasan 10:00am za a d'aura auren.
Nan suka fito suka shiga mota yaja sai unguwar su Zarah ya sauke ta yace ta shiga shi zai wuce wurin d'aurin aure, sai da ya janyo ta ya tsotse lip d'in da ta Shafa ma bakin ta sannan ya sake ta ya wuce.
Ita ko duk kunya ta ishe ta, nan tayi sauri ta shige gida.
Yanzu ne aka d'aura auren
*SHAKUR* *MUKHTAR* *IBRAHIM*
Weds
*MUNAZZAFA* *ABUBAKAR*
Sai kuma na
*MUSADDIK* *MUSA*
Weds
*NUSAIBA* *BAWA*
Bayan gama d'aurin auren ne Hakeem ya dawo ya d'auki Zarah ya kaita gidan su Munazzafa.
Yace zuwa la'asar zai zo ya wuce da ita gidan su.
Nan ta shiga ta taradda gidan cike, har da k'awayen su su Asmee, nan suka shiga hira har suna zolayar Zarah ko dai ciki ne da ita?
Ta bisu da harar wasa, tace kanku akeji.
Hakeem ya Kira ta fito suje, nan suka yi Mata caaa tun yanzu.
Tace zata dawo zuwa dare don ita zata Kai Amarya d'akin ta, tace kuyi hak'uri aure uku ne gabana.
Ga na Broda Shakur, ga na Aminiya ta, sannan ga na k'anwar *Hubby* na.
Saboda kunsan itace matar yaya Musaddik.
Suna kaiwa k'ofar gidan su Hakeem zasu shiga nan suka ga Mace rakab'e bakin k'ofa, ta durk'usa tana gaida Hakeem, nan ya amsa ba tare da ya ga ne wacece ba.
Har zai wuce ta rik'o gefen rigar shi tana kuka tana rok'on shi gafarar yaudarar shi da tayi.
Sai anan ya fahimci Ashe Hafsat ce, duk ta jeme ta kod'e.
Nan Zarah taji wani kishi ya taso Mata, nan ta fizge hannun ta tayi cikin gidan.
Nan ya bita da murmushi, sannan ya kalli Hafsat yace ba komai ya yafe Mata.
Haka Zarah ta yita zirga-zirga har aka Kai amare gidajensu, Hakeem yazo ya d'auke ta, suna cikin mota sai wani shan k'amshi takeyi.
Amare Allah yabada zaman lafiya.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣2⃣0⃣_1⃣2⃣5⃣
Hakeem an zama babban mutum, saboda yanzu shine manager na company d'in Abban Zarah.
Yau lahadi yana gida yana d'an hutawa, tun jiya suna dawowa daga Kai amare ya rasa gane kan Zarah.
Yanzu ma hakan ta k'are girki ta ajiye ta koma d'aki, nan ya tashi ya bita d'aki.
Yana shiga ya ganta saman mirror ta fito daga wanka zata shirya.
Nan ya k'araso ya zo ya lak'aci Mai yana Shafa Mata a bayan ta, nan taji salon ya canja yana yi yana Shafa jikin ta har ya zura hannunshi wurin na fulanin ta.
Nan ta zabura tana kumbure-kumbure, ta kwashi kayan ta dake saman gado data fitar domin sakawa ta fad'a toilet.
Saida tasa kayan ta sannan ta fito, shi ko yana saman gado.
Nan ta zarce saman mirror ta d'anyi make up.
Ya taso yazo gurin ta, yace My Zarah har yanzu fushi akeyi Dani?
Ta k'yale kawai taci gaba da nad'a d'aurin ta.
Nan ya kwashe komi tsakanin shi da Hafsat ya gaya Mata, ya d'ora da cewa kin San dai ba abinda zanyi da Hafsat yanzu sai dai in d'auko maki ita za ayi matsayin y'ar aiki.
Nan ya samu ta Saki fuskar ta sannan ya rik'o hannun ta suka dawo falo suka karya.
Bayan sallar isha'i ya shigo suka ci abinci, yana manne da Zarah bai ko Bari ta d'aga nan da can.
Nan dai Zarah ta gane take-taken shi, har ta fara tsora ta dashi.
Nan yace ta shiga ta d'auko Mai key d'in mota zai fita ya dawo.
Bayan ta d'auko ta marairaice Mai kan ya fita da ita, nan dai ya lallab'ata yace minti goma ya isa yanzu zai dawo.
Bayan ya dawo ne tazo ta tarbeshi suka shiga daga ciki.
Ya bud'e kayan da yazo dasu, yace zoki zauna kici kazar ki ta amarci da baki ci ba, yana maganar yana murmushi.
Nan taji duk kunya ta rufe ta, ta ajiye ledar zata gudu ya ka mota.
Nan ya tashi ya d'auko filet kicin ya juye kazar.
Ya janyo ta saman jikin shi, da hakan har ya ciyar da ita suka Kora da fresh milk.
Nan ya umurce ta da ta shiga ciki suyi alwala su gabatar da nafila.
Bayan sun gama ne ta d'auki towel ta fad'a toilet don tayi wanka, saboda wannan al'adar Zarah ce tun gida bata iya kwanciya batayi wanka ba.
Bayan shima Hakeem ya kimtsa ne ya dawo d'akin ta suka kwanta.
Nan yake jero Mata tambayoyi akan abinda ya shafi addini, gwargwado Zarah tana da sani b'angaren addini saboda ta sauke k'ur'an makarantar tahfiz kuma tana karantar littafai da dama.
Nan yaja bargo ya lullub'e su Wanda gaban Zarah ya tsanan ta fad'uwa.
Niko Jegal na ja masu k'ofa nace asuba ta gari, su o'eeee har an baza kunne, lolx.
Baban Hafsat ya samu labarin yaron da ke zuwa wurin ta ya gudu, saboda haka ya d'auke ta ya had'a da wani abokin shi aure.
Mutumen ma zai girmi Baban ta, harakar cinikayya ce ke had'asu, yana da matan shi uku da yara ashirin da shidda.
Mamar ta tayi ta fad'a har taso Hafsat ta kauce ma maganar mahaifin ta.
Nan tace gaskiya Mama ni Zan hak'ura in zauna dashi hakan nagaji da zaman gida, ko wancan lokacin ke kika k'ara zugani kika sa na guji Hakeem, gashi Ina ganin jarabobi iri-iri.
Mama tace ni dama ke nake ji saboda zama cikin Mata uku sai an daure.
Tace ba komai Mama, fatana guda kiyimin addu'ar zaman lafiya.
Nan aka tarkata Hafsat sai gidan mijin ta Alh muttak'a.
*washe* *gari*
Alhj Muttaka sai tarairaya yake yi da Hafsat sanadiyyar samun ta da yayi cikakkar budurwa, wannan shi ya jan yo Mata martaba agare shi.
Nan ya taran matan had'e da yaran su ya jama yaran kunne kan su ba Hafsat girman ta, itama yace ta girmama matan shi, kowa ya tsaya matsayin shi.
To da yake Alh muttaka tsayeyyen namiji ne Mai fad'a aji gidan sa, wannan shi ya wanzar da zaman lafiya da girmama juna a gidan Alhj Muttaka.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn ~Shakur~.
[6:27PM, 9/29/2016] Sis Hauwa: FATEEMA 1⃣2⃣5⃣_1⃣3⃣0⃣
*BAYAN* *SHEKARA* *BIYAR*
Yara biyu na hango suna guje-guje cikin lambu.
Islaha tace yaya kabani sweet d'ita ko inje In gayama Mum.
Suna hakan sai ga iyayen su sun fito.
Ganin hakan yasa Mukhtashim yayi sauri ya bata alawar ta, nan suka shek'a sai gurin mahaifan su.
Nan suka d'unguma cikin mota suka fita.
Koda suka zo wuri ya cika mak'il da mutane.
Nan ta taradda Munazzafa har sun hallara ita da Broda Shakur.
Ashe yau ne ake graduation d'in su Zarah na k'are makarantar school of health technology dake garin jega.
Bayan dogon baya nai daga manyan malamai, nan aka bada kyautukka ga way'anda suka dace.
Nan taro ya tashi suka fito, Munazzafa na hango da tutse tsen cikin ta, ga wata d'iya rik'e hannun Shakur.
Nan Jazla yarinyar su Shakur ta lak'e cewa sai ta bi su islaha gidan su.
Nan su Shakur suka wuce, su kuma su Zarah suka wuce gidan Nusaiba.
Nan suka taradda ita da yaran ta uku, Maryam, Zainab sai k'aramin su Ahmad.
Bayan sun fito ne suka biya gidan Faisal abokin Hakeem wanda shiko Allah bai basu haihuwa ba har yanzu, Sai dai matar shi Hauwa da keda tsohon ciki.
Daga nan suka wuce gidan su Zarah, nan zarah ke cewa har yanzu su khadeeja basu samu hutu ba?
Nan Umma ke bata amsa da eh, saboda tana makarantar kwana secondary saboda itace zab'in ta, Mubarak kuma yana India.
sai marece suka Kama hanyar gida suka biya gidan su Hakeem dake mak'wabta ka dasu, saboda ya dad'e da gina masu gida kusa dasu.
Nan su islaha suka lak'e zasu zauna wurin granny.
Nan suka wuce gida suka bar yaran duka gidan su Hakeem.
Shigar su gidan keda wuya ya rik'o hannun ta sai d'aki, yace yau sai an sama ma islaha twins.
Bayan sun shiga wanka sun fito ne, ya d'auko fresh milk ya bata bayan tasha itama ta bashi yasha, bayan sun gama ne suka ja bargo suka rufa.
Asuba ta gari.
Tammat bi hamdillah
Anan na kawo k'arshen wannan buk nawa, kuskuren da ke ciki Allah ya yafemin, da fatar zaku amfana da wani b'angare daga ciki.
Gaisuwa zuwa ga Anties d'ina
Anty Innah
Anty fateema
Anty Ybk
Anty Jidda Musa
Anty Habby.
Ban manta daku ba
Safiya Ummu Abdul
Bahijja (Bebeelo)
Tsakanina daku sirri ne.
Wannan littafi kyau tace zuwa gareki Mmn shakur, Allah yabar k'auna
Nayi wannan buk ne Da sunan ki Zarah B~B, na gode da kulawa.
Fata nagari zuwa gare Ku k'anne na
Sumee Jegal
Assy Jegal
Hauwa Jegal, Allah yabaku mazaje nagari.
Kuna raina
Sis Mrym
Sis Atiks
Manyan yara na
Zainab Musa (Mmn mimie)
Lawiza Musa
Yara manyan gobe
Halima
Maryam
Khadeeja
Abduljalal, Allah yaraya min Ku akan sunna.
Abokanen karatu na
Aminiya Hjy Shafa
Shema Bello Bari
Saratu Abubakar
Yazzali
Yar gidan Ango
Gaisuwa ta musamman zuwa gareku.
Hindatu shehu (K'awar amana)
Fati Salihu
Mmn Zahra
My Bizzy
Ummu Marwah
Mmn Xeenert
Sophy MD
Nana khadija
Anty Ummy
Yaha saddik
Jamcy
Meenat
Khadeeja Abdul s
Maryama
Douter Halima Bungudu
Sumee Firchn
Mrs Atiku
Princess Jamila
Hauwa Muhammad
Maryam (Mmn Mamee)
Mmn Amatullah
Mrs zannah
Bilkisu Bilyaminu
Taku gaisuwa ta daban ce princess Meenat & Umma ta Lubiee Mai tafseer.
By *Sdy* *Jegal*
Dedicated to Mmn *Shakur*.
No comments:
Post a Comment