[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 4⃣3⃣/4⃣4⃣
Bayan sun shigo gidan ne sun zube a falo ne aka yi gaishe-gaishe nan Baffa ya kwashe maganar ko mai ya gayawa Dad, har maganar sanya lokacin aure.
Alh Farouk ya ce'
"Ba komai Allah ya nuna mana lokacin, in har ka amince da abin ni ba abinda zance, yanzu kawai abinda ya rage shirye-shirye sauran bayani sai munji daga gare su.
Da hakan suka kai k'arshen magana suka wuce gida.
<<< >>> <<< >>>
6angaren Musirrah kuwa bayan ta dawo daga gidan su Mela Ammi ke gaya mata maganar auren ta nan da sati uku masu zuwa, cikin tashin hankali ta kai duban ta ga Ammi ta ce'
"Aure! Sati uku fa?".
"Baki san da mijin bane zaki rik'a yimin tambaya haka tamkar wadda miji yazo mata kwatsam?", kinsan dai da maganar ki ke da Haydar".
Nan dai ta kwashe komai ta gaya mata har zuwan Baffan Iman gidan su. Musirrah ta ce' "duk yadda muke gudun mutanen nan ashe dai suna mak'ale damu".
"To yanzu Ammi yaushe za ki kaimu garin mu muga dangin Baban mu koda ko shi bai raye?", za muje kafin lokacin auren amma wani hanzari ba gudu ba bazan iya tunkarar garin ni da kuba dole sai Baffan su Iman ya yi muna jagora saboda muna cikin had'ari shigar shi mu kad'ai".
"Kamar ya ya? Akan me? Muna da wani aibi ne da in muka je garin za'a koro mu?", duk Musirrah ce ke je roma Ammi wad'annan tambayoyin cikin tashin hankali da rud'u.
Yanzu dai ki bari sai munje gidan Baffan za kiji komai akai, "hala ina yaya?", cewar Musirrah.
"Tun fitar su Baffan Iman yake ta wani cika yana ba tsewa bansan me ke damun shi ba", "gaskiya Ammi sai in ke kika ta6o shi amma yaya Mubarak akwai hak'uri".
"Yanzu ko ma miye Ku ake ji ku jira lokaci yayi zaku ji duk abinda kuke son ji, ta d'ora da cewa ya kama ta in za muje gidan Baffan su Iman a kira Haj Maijidda muje ta re saboda ita ma na yi Mata alk'awarin jin tarihin rayuwa ta", haka suka k'are tattaunawar Musirrah ta tashi domin d'ora girkin dare.
<<< >>> <<< >>>
*BAYAN KWANA UKU*
Sai da ya kammala siyayyar shi duka sannan ya had'a kan yaran kaf ya ce suje su kai kayan gidan su matar Haydar.
Nan Ummy ta ce' "shin lefen matar ne aka had'a hakan?", "a'ah kayan fitar buki ne za'a kai mata".
"Miye kuma had'in ka da kayan fitar buki kai ba uban Amarya ba?", "ita ma amaryar y'a ta ce".
Nan dai aka loda kayan cikin motar Nibras akwati biyu har da kayan abinci, 6angaren spaghetti, macaroni, indomie, shinkafa da sauran su.
Duk inda mamaki yake ya cika ran Haj, miye had'in kai wa'annan kayan gidan su matar Haydar?, ita fa almubazzaran cin Alh ya fara isar ta mutum ya yita 6atar da kud'i tamkar bai san zafin suba, hakan dai ta ja bakin ta ta tsuke.
Nibras da Iman mota d'aya suka shiga sune a gaba sai kuma Babban yaya biye dasu wato Mus'ab.
Address d'in da Baffa ya basu suka bi sai ga su k'ofar gidan, razana, tashin hankali, su ne suka mamaye zuciyar Mus'ab kar dai ace Musirrah ita ce matar Haydar kuma Baffa ke jagoran tar auren?
To ko Baffa ya gano cewa Musirrah ce matar Haydar shiyasa yace wa Ummy yarinyar ma y'ar shi ce?
Tabbas Baffa ya gano hakan tunda ya ji shekaranjia yana gayawa Ummy an yi maganar aure har an biya sadaki, kuma ko da yake maganar yana cikin tsabar farin ciki.
Jin Nibras na buga glass d'in motar shi ya sa ya dawo hayyacin shi had'e da saita nutsuwar shi, nan ya bud'e ya fito. Nibras ya ce' "har mun d'ora ma yara kayan sun kai ciki kai muke jira", "ku shiga kawai zan ga wani friend d'ina wancan shagon", yana magana yana nuna wani shagon d'inki gaba kad'an.
"Amma fa yaya ka san Baffa ya ce mu shiga mu gaida mutanen gidan saboda suna da muhimmanci gare shi, ko yanzu da zamu fito sai da ya k'a ra jaddada muna hakan".
"Ku biyu ma kun wadatar don ba gwajin kamanni zamu je ba", har ta bud'e baki zata yi magana kallon da ya bita dashi ne yasa ta yi shiru suka wuce, shi ko ya ko ma mota ya zauna ya had'a kai da sitarin mota.
<<< >>> <<< >>>
"Ai wallahi ba zata sa6u ba wai bindiga a ruwa, shiyasa ake ta yimin 6oye-6oye akan maganar auren Haydar, ashe bayan ma yarinya y'ar gidan k'ana nan mutane ce ashe ma ba tada asali".
"To wallahi ba zai ta6a yuyuwa ba wannan auren muddin ina raye".
"Wai da kike ta yarda ji-jiyar wuya wa yagaya maki yarinya bata da asali?", cewar Dad.
"To ni dai bazan yarda ba wallahi har sai na ga uwar ta da uban ta agaba na, in ma uban ya rasu ne to inga dangin ta na kusa".
"Shi ko Haydar dashi da munafukar k'anwar zasu zo su sa me ni ne, musamman Mukarrama za musaka wandon roba mu hau risho ni da ita ne, don duk wani kinibibi ita ce silar k'ulla shi".
Hakan dai ya wuce bedroom d'inshi ya barta nan tana kumfar baki tamkar wacce ta sha guba.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 4⃣1⃣/4⃣2⃣
Jin motsin rufe k'ofa ne yasa Ammi zata shiga kewaye ta lek'o nan ta gan shi manne da k'ofa tamkar yana gudun wani ya shigo gidan, ta kai duban ta zuwa gare shi ta ce'
"Lafiyar ka kuwa, kai da wa?". "Ammi Baffa ne, wanne Baffan?", Baban su Nibras", ya bata amsa.
"Banson d'ibar albarka don ka ga Baffa ne zaka gudu, Baffan kura ne da zai cin ye ka?",
"Ammi fa da gani nan gidan yazo, don sune suka aiko yaro ne mana yanzu".
"Maza fita kaji meke tafe dashi, in ma ta kama ka shigo dashi gidan to ka shigo ka ta6a ganin inda laifin wani ya shafi wani, iya ga ta ya nuna maku ga ta wanda ko mahaifin ku sai haka".
Cikin sauri ya ta da kan shi ya ce' "dama Ammi muna da mahaifi?", "a'ah a jijji na tsinto ku".
"Don Allah Ammi ki fitar damu daga cikin wannan k'uncin haka ki gaya mana inda mahaifin mu yake wallahi zan je neman shi da kaina".
Cikin 6acin rai ta ce' "Allah in na irga uku baka fita ba sai na yi mugun sa6a ma, in ma ka fita ka shigo dashi ciki".
A can 6angaren Baffa ko mamaki, murna, farin ciki, ya rasa wanne yake cikin shi, sai dai bai yi zaton Mubarak zai gan shi ya gudu tamkar wanda ya ga wani do-do, bai san iya wahalar da ya sha gurin neman su ba.
Wata zuciya ta ce to ko yana jin nauyin had'uwa dakai ne saboda satar da Haj tace ta ka mashi ya yi ma har ya yi silar suka barma gidan ka?.
Baffa ya ce inaaa! Bazan ta6a yarda Mubarak na iya yimin sata ba, k'addarta ma hakan ta faru bazan ga laifin shi ba ai shi D'A NA KOWA NE (Dear Bebeelo) sai dai in mashi addu'a saboda ko wane bawa da k'addarar rayuwar shi.
Alh Sani ne ya da fa kafad'ar shi sannan ya dawo hayyacin shi, ya ce' "wai meke faruwa, mu da muka zo neman aure meye had'in mu da wannan yaron?".
Baffa ya ce' "ina wa'anda nake baka labari cewa sun gudu daga gida na har kai nace ka taimakamin da neman yaron makarantar su, lokacin kace min kana shirin fita London ne", "eh eh tabbas na tuna".
"To su ne, ina ma kyautata zaton k'anwar shi na zo neman auren ta".
Suna hakan ne Mubarak ya fito ya zo har inda suke ya durk'usa ya gaida su ya ce' "Ammi ta ce ku shigo daga ciki".
Je kaga murna fal a zuciyar Baffa, shi dai ya rasa dalilin da yasa yake jin yaran har cikin zuciyar shi, nan dai ya yi masu jagora har cikin gidan.
Koda suka shigo ta d'auko kujerun roba guda uku ta ajiye, nan dai suka zauna bayan an gaisa ne Ammi ta ka wo masu ruwa a jug d'in roba, ga mamakin ta kuwa sai gashi sun sha sosai.
Bud'ar bakin Baffa cewa yayi ina y'ata Musirrah?", ta bashi amsa da cewa ta yi gidan su wata k'awar ta Maryam".
"Lallai ko zan gayawa Iman ta daina wahalar da kanta ga maganar Musirrah don kuwa ta manta da ita", yana maganar ne cikin raha da sakin fuska saboda dama rayuwar Baffa kenan.
Ammi ta ce' "ita ma tana zancen ta ai", duk wannan maganar da suke yi kan Ammi na k'asa saboda tun fil azal bata saba hira da Baffa ba iya gaisuwa ce tsakanin su.
"To ga shi yanzu maganar auren ta ta zo dani ita da yaro na, sai ga shi na tarar ashe su duka yara na ne".
"Da ma Haydar yaron kane?", "a'ah yaron aboki na ne sai dai maganar na hannu na".
"Saboda haka yanzu kai Alh sani zaka zama wakilin Haydar ni ko zan zama na Musirrah, nan aka biya kud'in na gani ina so da sauran su har zuwa kan sadaki, kuma an saka ranar aure sati uku masu zuwa.
Ammi dai da Mubarak y'an kallo suka koma, amma shi Mubarak abin haushi ya bashi ya zata Baffa zai matsawa Ammi ne kan ta bada tarihin wa ye su, amma ba komai ba zai shiga maganar manya ba yanzu ace ya yi rashin kunya duk da yasan ya fi su gaskiya.
Ya san dai muddin iyayen Haydar na da hankali ba za su bari d'an su ya auri wacce ba'a san asalin ta ba ko da ko Baffa ya ce shi ne wakilin ta, sai in ko suma basu da asalin sai a had'u ayi auren marassa asali. ( *lolx Mubarak duk 6acin rai ne?, ko da fa ni ma Ammi ta fara ban haushi barranta na masu karatu, koda bara in yi shiru ance uwa uwa ce*)
Bayan sun kai k'arshen magana ya ce' "sai ga shi daga in yi tafiya in dawo kawai na tarar ba bu ku ke da yara me ke faruwa hala?".
"Eh to Baffan Iman maganar na da tsayi kuma ya kama ta a yita gaban kowa da kowa, ka baiwa Mubarak address na gidan ka zan had'o kan yara mu zo".
Saura k'iris tsakin da Mubarak ke rik'e wa ya fito, wai ga abu mai muhimman ci daya Kama ta a tattauna akai sai wani kwashe-kwashe suke yi.
To shi dai wallahi ko da hak'uri aka bada bazai ta6a ko mawa gidan Baffa da zama ba, don bazai juri wulak'anci ga kowa ba don TALAUCI BA HAUKA BANE (Namcy Garba yakasai).
Nan dai aka kai k'arshen magana Baffa ya baiwa Ammi kud'in auren, ta ce ya ajiye hannun shi, ya ce' "duk da hakan ki nemi dangin yaran ki gaya masu abinda ke faruwa".
Ta ce' "insha'Allah".
Sai lokacin Mubarak ya d'an ji sanyi a ran shi, da hakan ya ta shi ya raka su suka wuce.
Cikin mota kuwa Alh Sani ya gaza hak'uri ya ce' "wai ko a tunanin ka Alh Farouk zai bari d'an sa ya auri yarinyar da ba'a san asalin su ba?, ga shi har ka yanke sadaki da saka ranar auren".
"In har mahaifiyar su mai hankali ce to magana ta ta k'arshe zai sa ta fahimci cewa ban isa ni kad'ai in zamo gata ga yaran taba, shi ko Alh Farouk nasan ko zuwa nayi nace an d'auro aure daga can baida matsala".
"To in har ta binciko asalin su kuma babu aure saman kanta ni ko zan aure ta don na yaba da nutsuwar ta".
"Hhhh kenan kana ciki, ko ma tana da auren to shari'a ta bata za6i don ta dad'e haka", da haka suka d'auke hanya sai gidan Alh Farouk.
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_ 4⃣5⃣/4⃣6⃣
Da shigar su gidan Ammi suka fara cin karo da ita nan ta ke suka dask'are guri d'aya, nan Ammi ta k'araso ta rik'o hannun su su duka biyun da murmushi d'auke a fuskar ta.
Musirrah na d'aki tana Sana'ar ta ta watau karatun takardun kurma ta ji Ammi ta k'wala mata kira ta ce ta fito da shimfida, cikin sauri ta mayarda takardun cikin handbag ta d'auko shimfid'a ta fito.
Wa'anda ta gani ne yasa ta kasa shimfid'ar sai da Ammi ta kar6a ta shimfid'a masu, nan ta ke sai ga Musirrah da Iman manne da juna har da guntun hawayen su na farin ciki.
Nibras ya yi k'arfin hali ya ce' "Ammi da ma Musirrah ce Haydar zai aure?", "eh itace Nibras, Baffan ku ya gaya maku ko?".
"Ai mu Ammi Baffa bai ce mana komai ba, ashe don yayi surprising d'in mu ne ya ce muje mu kawo kaya", ina Mubarak hala?".
'Musirrah d'auko waya kira yayan ki kice yazo ina neman shi".
Bayan ta kira shi ne aka zauna hirar yaushe rabo, je kaga murna had'e da farin ciki fal a idon su Musirrah ko wacce na baiwa y'ar uwarta labarin halin da ta shiga Ammi da Nibras sai dariya suke masu.
Bayan Mubarak ya dawo suka zauna aka bud'e kayan da Baffa ya bada aka wo masu, sunyi murna sosai musamman tufafin da ya yiwa Musirrah na fitar aure.
Nan dai suka wuni gidan har Musirrah ta yi masu girki suka ci, har gurin mota suka rako su, Nibras na ta waige-waige ina zai ga babban yaya amma wayam.
Nan ya d'auko waya ya kira shi, Mus'ab ke gaya mai shi ya dawo gida saboda zazza6i dake damun shi, Nibras yake gayawa Iman ga abinda ke faruwa.
Ya ce' "Musirrah na so kiga babban yaya ku gaisa amma ke ji abinda ke faruwa dashi, ko da nasan yanzu kin manta kamannin shi".
"Ai ko in dai ba kamannin shi suka canja ba to bazan ta6a mantawa dashi ba, duk da ba wani sani nayi mai sosai ba".
Nan dai suka ajiye kan cewa sai sun zo gobe zata ga babban yaya saboda Ammi ta ce zasu zo gidan.
<<< >>> <<< >>>
*WASHE GARI*
Misalin k'arfe 11:00am Mubarak ya sa mo mai napep suka shiga sai gidan Baffan su Iman, akan zak'uwa koda suka je Iman na k'ofar gate gate tana jiran su, ita ta yi masu jagoranci har falon gidan, da yake sun tashi daga wancan gidan sun koma wani.
Ko da suka shiga falon ba kowa, nan Iman ta ce su zauna ta yi part d'in Baffan su ta gaya mai, ya ce' "ina fatar cikin ku ba wanda ya gayawa Haj bak'in da za su zo", "Baffa bamu gaya mata ba, mun dai shirya komai na tarbon su".
Nan suka fito sannan ya wuce part d'in Haj ya kira ta suka fito ta re, k'ululuuuuu k'arar cikin ta kenan sanadiyyar had'a ido da suka yi da Ammi, nan ta toge cikin falon.
Baffa ya ce' "ki k'araso mana yau Allah yasa na ka mo 6arawo na da hannu na", nan dai ta yita muzurai ta d'osana saman kujera tamkar wacce za'a cewa arrr ta zura da gudu.
Bayan sun gaisa ne ta rik'a borin kunya nan ta kwaso abinci ta jibge masu duk da sunce a k'oshe suke sai da ta matsa suka ci kad'an.
"Nan Ammi ta kai duban ta ga Baffa ta ce' "dama na had'o kan yaran ne mu zo muyi maku godiyar d'awainiya Allah ya saka da khairan yak'ara bud'i na alkhairi".
Haj nata ka me-ka me ta ce' "ai ba komai an zama d'aya ga shi za'a yi tuwo na mai na, lallai gaskiyar ka Alh an zama d'aya, Allah ya sanya alkhairi".
Baffa ya kai duban shi ga Ammi ya ce' "ina son in san miye silar ku na barin gidan nan a wancan lokaci?", ya yi wannan tambayar ne kawai don yaji me Haj zata ce duk da yasan komai saboda Iman ta gaya mai jiya amma ta nemi alfarmar kar ya gayawa Ummy.
Ammi ta ce' "ba komai kawai maganar ta wuce, muna godiya sosai".
Uhmmm! Ajiyar zuciyar da Ummy ta sauke kenan ta d'ora da cewa Baffan Iman ai ko a addini ba'a son yawan ta yarda maganar da ta wuce".
"Wacce ba ta alkhairi ko ta tayarda fitina ba akace", cewar Baffa.
Hakan dai taja bakin ta ta tsuke, amma daka ganta kasan muzance take, saboda tasan halayyar Alh muddin ya ga no wani laifi da kayi in har kai kana k'ok'arin 6oye laifin ka ne to cikin siyasa zai rik'a sakoma magana wacce kai in mai hankali kake zaka ga ne cewa ya ga no takon ka kawai ya basar ne.
Ita kam ko hakan aka tsaya ta gode Allah da ba'a tozar ta ta gaban yara ba, bata san cewa ko yaran sun san komai ba.
Baffa ko cikin ransa abu d'aya yake tunani da zai sa ya d'ebe haushin Haj kawai ya auri Ammi in har zata amince da hakan bayan auren Haydar da Musirrah, saboda dashi ta dace bada Alh Sani ba.
Ammi ta umurci yaran su tashi su wuce, nan Baffa ya ce yana neman alfarma kan in bai takura ta ba suje gidan su Haydar saboda kawarda zargin da Hajiyar Haydar ke yi akan Musirrah.
Ammi ta yi murmushi ta ce' "ba komai Baffan Iman ni ma na matsu in sauke wannan nauyin ko don matsowar lokacin auren".
"Amma ni ma ina neman alfarmar in har na baku tarihin rayuwa ta zaka taimaka ka raka mu garin mu saboda tunkarar garin gare ni ni kad'ai hatsari ne ga rayuwa ta".
Haj ta ce' "wannan ai har damu duka za'a je insha'Allah, ta d'ora da cewa ko yanzu zan bi ku saboda na k'a gu nima in ji tarihin ki".
Da haka suka rankaya su duka domin zuwa gidan su Haydar, sai dai ko da aka kira Mus'ab aje dashi yace shi yana gurin Dr Shureim zai yi mai allura, hakan suka rankaya sai gidan.
Bayan sun shiga gidan sun zazzauna a falo ne sai ga Alh Farouk da Haj Zainab sun fito, a k'a idar Ammi bata iya tsura wa mutum ido tayi ta kallon shi, kan ta nok'e haka ma na Musirrah da take jin tamkar k'asa ta bud'e ta shige domin kunyar ga ta gaban surukan ta.
Bayan an gaggaisa ne Baffan Iman ya ce' "ga mahaifiyar Musirrah za ta baku tarihin wa ye su, daga nan nayi alk'awari gobe zan raka ta garin su domin neman dangin ta".
D'aga kan da zata yi domin fara bada labarin karaf idon su suka sark'e da na Haj Zainab, nan ta kai duban ta ga na kusa da Haj Zainab ta ke ta zabura da k'arfi Mamar Jameel, Abban Jameel!.
Da saurin ta ta fita daga falon cikin sa'a ta samu mai napep ta shiga sai gida.
6angaren Haj Zainab kuwa tashin hankali, fargaba, rud'u had'e da dagulewar lissafi suka risk'e ta lokaci d'aya sai zarar ido take yi tamkar gunki chochi.
6angaren Alh Farouk kuwa ya koma mutum mutumi saboda ko motsi ya kasa yi sai k'ofa da yake nunawa da yatsan shi yana furta wata kalma da bata samu damar fitowa fili ba ta mak'ale saman la66an shi, sai daga baya ya iya furta Zainab kin cuce ni.
Mubarak, Haydar, Musirrah, Iman, Baffa da Haj kowa sai rabon ido yake yi da tambayoyi fal a k'wak'walwar shi.
Baffa ya yi k'arfin hali ya ce' "ku fitarda mu duhu mana mun kasa ga ne ina kuka dosa".
Mubarak ya mik'e ya rik'o hannun Musirrah suka fice daga falon, nan Baffa ya bawa su Haj umurnin su ta shi akai su Mubarak gida in yaso su dawo suji meke faruwa, haka suka d'unguma suka wuce har gate Dad ya biyo su amma fa ya kasa magana.
Baffa ya ce' "ka koma ciki zan kai yaran gida ne yanzu zamu dawo, ya yi hakan ne saboda basu guri in ma akwai wata matsala to su tattauna kafin su dawo bai dace ayi gaban yara ba, saboda yadda yaga 6acin rai k'arara a fuskar abokin nashi komai na iya faruwa.
Da hakan ya wuce yakai su Mubarak gida ya ajiye domin komawa gidan Alh Farouk.
Suna shiga gidan suka ga Ammi cikin tsananin tashin hankali, sun yi tambaya iya tambaya ta kasa magana kalma d'aya ta furta musu da ta sakasu cikin rud'u Wanda yayi silar shigewar Musirrah d'aki ta bud'e shafin kuka.
(Wayyo yatsa na, _lolx_)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ _K'UNCI_4⃣9⃣/5⃣0⃣
Ammi ta fara da ce wa nidai sunana Hauwa'u Suleiman haifaffiyar garin Birnin kebbi unguwar gwadangwaji, mahaifina ya kasance sananne kuma fitaccen malami a unguwar sanadiyyar karantarwar da yake yi a harabar gidan shi bayan magrib zuwa isha da yake karantar da matasa, sai kuma k'arfe 09:00pm zuwa 10:30pm shi kuma na magidan ta ne.
Mu biyu ne iyayen mu suka haifa wato ni Hauwa'u sai k'ane na Ibrahim, mahaifiyar mu Inna Habiba mace ce mai neman na kanta saboda tana k'ana nan sana'o'in ta cikin gida.
Mun taso cikin gata na rufin asiri da kuma tarbiyya, cikin mahaifin mu yana malami ba'a ta6a rashin girka abinci a gidan mu ba, saboda bayan karantarwa mahaifin mu na sana'ar kayan gwari.
Ina da shekara goma Ibrahim na da shekara bakwai Allah ya yi mashi cikawa sanadiyyar ciwon ciki da yake fama dashi Wanda an yita magani abin ya ci tura har aka cimma ajali.
Lokacin na yi kuka na rabuwa da d'an uwana duk da ba wani zafin mutuwa nasani sosai ba. Na ta so inada sha'awar karatun boko a rayuwa ta sai dai wannan bai cikin tsarin mahaifina, makarantar islamiyya kawai nake zuwa wanda ko da na kai shekara sha biyu na sauke Alk'uran da kuma wasu littattafai sanadiyyar da asuba Baba na gaya mana karatu ni da inna.
Ina da shekara goma sha uku Allah ya yiwa mahaifiya ta rasuwa sanadiyyar cikin da ta samu gurin haihuwa aka rasa ta ita da abinda ta haifa.
Wannan lokacin tabbas nasan na yi rashi na mahaifiya ta saboda abin haka ya so zame min tamkar mai ta6uwar hankali.
Mahaifina shi kad'ai yake ga mahaifansa wa'anda suka rasu da jimawa saboda ko ni ban san suba, sai dai sauran tsirarrin dangin shi da ba'a rasa ba.
Bayan rasuwar mahaifiya ta ne na koma hannun wadda nake tunanin mahaifiyar Inna ce, ashe kishiyar mahaifiyar ta ce, wanda sai lokacin na sani sanadiyyar azabar da take ganamin, lallai tabbas lokacin na yadda da Kalmar bahaushe da yake ce wa "ganin ido ragowar dole", ko kad'an mahaifiya ta bata d'auki Gwaggo kulu a kishiyar uwa ba sanadiyyar komai ta samu zata ce min uwa ta zo ki kaiwa Gwaggo sak'o, tana kira na da Uwar ta ne sanadiyyar sunan Gwaggo kulu da aka sakamin kuma ga ni ta farko gare ta.
<<< >>> <<< >>>
*A GURGUJE*
Ina da shekara goma sha hud'u Babana ya yi min aure da wani Alh dake zuwa karatu gurin shi, Alh shi ya ne mi aure na da Babana wanda ba'a d'auki tsawon lokaci ba aka d'aura aure na ta re a gidan shi.
"A wancan lokacin har aka yi aure ban san wa ye mijin ba saboda har magana har auren bai kai sati uku ba, Baba ya yi hakan ne ko zan samu sassauci gidan aure na saboda yana tausayamin irin izayar da Gwaggo kulu ke ga namin.
"Sai bayan na ta re ne na san waye miji na, ashe yana da mata da yara biyu wato Jameel da Rukayya. Bayan na yi sati d'aya gidan ne na fara fahimtar zaman takewa da mutanen gidan, saboda da sannu na fahimci cewa Haj Zainab kwata-kwata bata k'auna ta da Alh ya fita kasuwa zan fuskanci zagi da hantara a gare ta, wanda dai-dai da uwar ciki na dake cikin k'asa bata ragawa ba".
"In abin ya motsa ko abinci aka ci gidan akayi saura ko da kuwa ya soma lallacewa ne zata rik'a cewa a d'auka akaiwa Mal Sule mai neman maula, mai mak'alawa masu kud'i y'ar shi, hakan zata wuni ta na yimin habaici sai dai in shige d'aki in ci kuka sai na gode Allah, wanda duk wannan abin da take yi da Alh ya dawo gida zata rik'a tarairaya ta tamkar k'wai shi ko ya yita saka mata albarka".
"Lokacin da Haj ta fahimci ina da cikin Mubarak tamkar ta hura wuta ta je fani a ciki saboda uk'ubar da ta rik'a ga namin, Allah ne kawai ya yi zan haifeshi a doron k'asa".
"Bayan Mubarak ya kai shekara d'aya da wata biyar ne Alh ya biya min zuwa aikin hajji, to lokacin kam Haj ta fito ta nuna k'iyayyar ta k'arara a gare ni, don atabau ta ce bazan je ba wanda mamaki gaba d'aya ya rufe Alh sai da ya nuna mata bata isa ba har abin ya zamo fad'a tsakanin su, sai daga baya ne ta nuna mai ita dama Mubarak take tausayi ba komai ba".
"Bayan na je aikin hajji na dawo ne na tarar Mubarak duk ya je me asali ma y'ar aikin mu ke kula dashi, wanda ita ke ba ni labarin wahalhalun da aka ga na masu da ita har Mubarak d'in, ikon Allah ne kawai ya ta yarda Mubarak".
"Sanadiyyar hakan ne yasa nake kyautatawa mai aikin mu akan rik'on da ta yiwa Mubarak wanda sai da Haj ta sa aka ko reta".
"Mubarak na da shekara uku na samu cikin Musirrah, ita ko Haj lokacin ta haifi Aliyu Haydar yana da shekara biyu a duniya. Bayyanar ciki na ya saka Haj cikin tashin hankali wanda cikin hantara had'e da tsangwama ciki na ya kai wata tara gidan".
"Ana hakan ne Alh ya shirya tafiya sokoto da ma wancan lokacin yana zuwa jefi-jefi".
"Bazan ta6a mantawa ba wani dare ina kwance misalin k'arfe d'aya na dare sai ga wasu k'atti sun fad'o gidan mu, ji nayi kawai an bud'e k'ofar d'aki na sai ga su sun shigo su hud'u duk fuskokin su a rufe, nan suka ba ni umurnin in ta shi in d'auki ya ro na muje".
"Nan na tsaya ba su hak'uri na had'o kan y'an kud'a d'e na na ba su suka ce ba sune gaban su ba, haka suka tasa k'eya ta muka shiga wata mota suna ta yankan da ji, nan aka kira wayar mai tuk'a motar muryar Haj naji na ce mai ka tabbatar kun kawar da ita daga doron k'asa kar ku bari asa mu matsala.
Sai da muka ka wo dajin Jega bayan asibitin Aisha Buhari sannan muka tsaya, nan suka fito dani d'ayan ya d'auko adda zai sa ramin, sauran suka ce kakka manta oga ya ce duk rintsi kar muyi kisa saboda haka mu k'yale ta.
Nan suka gargad'e ni da babbar murya kan cewa muddin na koma garin aka samu matsala wallahi sai sun kashe ni, saboda ina ji da kunne na ce wa aka yi su kashe ni, to wannan bai cikin tsarin ogan su shiyasa suka k'yale ni.
Daga nan ne na sa6a Mubarak a kafad'a ta har na shigo garin Jega na had'u da Baraka, nan dai ta d'ora masu da sauran labarin ta ka wowa yanzu.
Ta ce' "abinda ya tsora ta ni na ka sa waiwayar garin mu, banda kowa sai mahaifina sai Allah, nasan ko na ko ma garin Baba zai tilasta ni ko mawa gidan Alh, yin hakan kuwa tamkar na d'auki wuk'a ne na baiwa Haj na ce ta kasheni da hannun na ne".
Tana kai k'arshen labarin ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, wanda ya yi silar kacamewar falon da kukan d'aukacin mutane.
(Ni kam bara in yi sallar magrib ka fin su k'arasa kukan)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
[8:38AM, 9/27/2016] Jidda Musa: _SANADIN_ K'UNCI_ 4⃣7⃣/ 4⃣8⃣
*KOMAWA ASALIN LABARIN*
Ganin wucewar su Baffa ne yasa Alh Farouk ya dawo gidan har yana kiran Haj cikin tashin hankali, kafin ya shigo Sudais abokin Haydar ya zo saboda kiran da ya yi mashi kan cewa yazo yaga matar shi tun kafin su Ammi su iso, shi ne bai samu zuwa ba sai yanzu.
Ko da ya iso ya tarar da Haydar d'in cikin tashin hankali kuma Haj na yi mai fad'an cewa wurin jaye-jayen shi ya janyo mata masifa, nan ne ya jashi d'aki yana rarrashin shi sannan ya fita ta k'ofar baya.
Duk wannan abin da ake yi Mukarrama na falon zaune ta ka sa wani dogon motsi har wani zazza6i take ji, sai bin su take yi da ido.
Bayan Alh Farouk ya tasa Haj Zainab a gaba ne yana tambayar ta abinda ke faruwa, nan ne Aliyu Haydar ya fito har Alh ya ce su saurari bayani daga bakin Haj.
Su na haka ne sai ga Baffa ya shigo shi da Ummy don ya bar su Iman daga waje cikin mota, bayan sun ne mi guri sun zauna ne Baffa ya kai duban shi ga Alh Farouk ya ce'
"Mu fa duk kun saka mu cikin rud'anin meke faruwa, don Allah ku yi muna bayani".
Alh Farouk ya ce' "ni ma kaina ita nake jira tayimin bayanin abinda ke faruwa, saboda ita ce silar shiga *SANADIN K'UNCIN* Kowa anan.
Nan ta ke kowa ya bi Haj Zainab da kallo wacce fuskar ta ta cika taff da hawaye idon ta har sun kumbura.
Cikin shesshek'ar kuka ta ce' "Abban Haydar kayi hak'uri ko da zuwa gobe ne in na sa mu nutsuwa kowa ya had'u in gaya maku abinda ke faruwa, amma wallahi sharrin shaid'an ne".
Alh Farouk ya ce bazai yarda ba saboda yana ganin tamkar in maganar ta kai gobe akwai wani abu da zata ko ma iya yi akai.
Sai da Baffa ya saka baki saboda cewar da Haj Zainab tayi ta fi son ayi maganar gaban kowa har Ammi d'in, da kuma yara gaba d'aya don ta san za su d'auki darussa da dama a cikin labarin da za ta basuwa.
Da hakan Baffa ya kira wayar Mubarak yake gaya mai kan cewa gobe k'arfe goma zai turo direba a d'auke su su da Ammi saboda za'a tattauna a gidan shi.
Nan Mubarak ya amsa mai da ba damuwa, sai gobe d'in. Da hakan aka ajiye magana kan cewa gobe k'arfe goma na safe duk za'a kammalu gidan Baffa domin war ware tarihin wad'annan mutane.
Ba don komai Baffa ya sa ya ce aje gidan shi ba sai don tunanin da wuya ne Ammi ta yadda a dawo gidan Alh Farouk irin yadda ta fita daga gidan, kuma gidan ta bazai wada ce su zama ba.
Da haka kowannen su ya kama gaban shi tattare da tunane-tunane a zuciyar shi.
<<< >>> <<< >>>
6angaren su Musirrah ko bayan Mubarak ya k'a re rarrashin ta da ba ta magana kan ta cire damuwa a ranta, sai ga shi Baffa ya kira wayar shi, nan ne yake gaya mai za'a had'u gidan shi gobe kan wannan matsalar.
Bayan sun k'are waya ne yake cewa Musirrah ki kwantar da hankalin ki inshaAllah gobe za muji tarihin su wa ye mu, don haka ta shi muje mu rarrashi Ammi daga nan mu gaya mata sak'on Baffa.
Mubarak ya ce' "ai ma abin zai zo da sauk'i tun da Ammi na jin nauyin Baffa, tunda ya saka lokaci ba za ta k'e tare maganar shi ba".
Da hakan suka je gurin Ammi suka tarar sai ajiyar zuciya take saukewa, nan dai suka rarrashe ta kuma suka gaya mata sak'on Baffa cewa ya ce a had'u gobe k'arfe goma na safe.
Ta ce' "wannan gidan ne dai bazan ta6a ko mawa ba", "ba can yace za'a yi taron ba gidan shi za'a je", cewar Mubarak.
Ta ce' "Allah ya kai muna rai, ke kuma Musirrah ki kira Haj Maijidda ki gaya mata in har tana da lokaci mu had'u can gobe d'in, in ya so har da address d'in gidan ki had'a mata".
Musirrah na sha re hawayen da suka ka sa d'aukewa a idon ta ta ce' "yaya ka kira Hajiyar", hakan dai ya fitar da wayar ya Kira ta ya gaya mata ta ce to ba matsala da hakan suka kai k'arshe ya kashe wayar shi.
Wannan daren ba kowa ne ya samu runtsa shi da kyau ba musamman Ammi, Umma, Alh Farouk kowa da abinda yake sa k'awa a cikin zuciyar shi.
<<< >>> <<< >>>
~WASHE GARI~
Falon cike yake taff da mutane, lallai tabbas da gaskiyar Baffa da yace gidan Ammi bai d'aukar su, ko wa ya kammalu Haj Maijidda kawai ake jira. Da mamaki ta shigo falon saboda tana ta tunanin mi ye had'in Ammi da gidan Alh Abubakar.
Bayan ta shigo ne an gaisa take tambayar Ammi da ma tasan gidan ne ko da suka had'u asibiti?, ita ko Ammi mamakin gaisuwar sanayyar da suka yi da Baffa da Haj kawai ta ke yi.
Ammi ta ce' "nemi guri ki zauna za kiji komai yanzu".
Baffa, Haj, Iman, Nibras, sai kuma Abba, Haj Zainab, Jameel da yake ya dawo daga masters d'in shi shekaranjia, sai kuma Haydar, Mukarrama, da Rukayya da ta bi Musirrah da kallon mamaki saboda jiya Haj wato Umma ta kira ta take sanar da ita akwai meeting na gaugawa shine ta zo gida suka zo ta re.
Sai kuma gefe d'aya Ammi ce da Mubarak sai Musirrah, babban yaya ne kawai babu sai dai yana mab'oya tai yana sauraren su.
Nan Baffa ya fara bud'e ta ro da addu'a sannan aka ace Ammi ta fara bada tarihin ta sai Umma wato Haj Zainab ta d'ora.
Nan Ammi ta ce' "da farko dai zan fara da cewa babu aure tsakanin Musirrah da Haydar domin dai uban su guda".
Kawai ido na hango suna ta had'ewa guri d'aya, in wannan ya kalli wannan cikin tashin hankali sai kaga wannan ya kalli wancan cikin rud'u.
(Nima dai haka ta kasance gare ni sanadiyyar rud'un da Ammi ta saka ni sai da keyboards d'in waya ta suka cije, *lolx*)
_SDY_ _JEGAL_
Dedicated to Sanah S. Matazu.
No comments:
Post a Comment